Sashe 60
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammy buÉ—an idon da zata yi ta tarar da su Abbah,
Razhdeen ne ya fara miƙe wa yayo kan Abbah ya tallafa masa ya tashi tare da zaunar da shi akan kujera, shima Roshan tashi yayi ya ɗago da Baiwar ALLAH da Ƴar Amana sai kuma sojojin da suka miƙe suma,
Ammy cike da mamaki take bin su da kallo É—aya bayan É—aya tana zazzaro ido waje....
Typing âœï¸ Asmeetah writer
*MY ENEMY*
*TAKUN ƘARSHE*
*BOOK 3*
91 to 95
A falo suka cigaba da zama kowa jiki a ma ce babu ƙwari domin ba ƙaramin gajiya sukayi ba,
à yau Abbah ya ƙira Malaminsa yazo yayi Addu'o'i, ya yi magani sosai wa Reemah sannan ya ba da magani akan kowa ya shafa akan goshi,
Baiwar Allah itama karɓa tayi ta shashshafa sannan ta shafawa Ƴarta Biju Mama ta ko ina, Ummy uwar masu gida itama shafawa tayi akan goshi sannan ta buɗe ƙaton cikinta ta shafa,
Ammy ta ce "ha'a Ummy har da tumbin ma?..."
Ummy ta ce "Ammy bar ni kawai ai dole na shafa wa Babyn cikina shima ya samu kariya..."
duk sukayi dariya.
Itama Minal shafawa tayi ita da yaranta biyu duk maza, babban É—anta da wanda take goyo yanzu...
Pinky itama shafawa tayi akan goshi da tumbin cikin ta wanda ya girma sosai, tana nemawa É—an cikinta kariya...
Sai Rukky itama ta shafa sannan ta buÉ—e shafaffen cikinta tana shafawa,
Pinky ta ce "ke kuma me zaki shafawa cikin nakin da babu komai a ciki..."
Rukky ta ce "wa ya gaya miki to naje an gwada ni nima inada cikin wata biyu, kinga dole na shafa kar amun gadara..."
Minal ta ce "to ikon ALLAH meye abun gadara wanda in kinje labour sai kin mance kan ki..."
Duk dariya suka yi cikin raha.
Hajiya Kilishi ma ta Shafa sannan ta shafa wa Autar ta Ƴar tinny, sai Ammy itama ta shafawa Ra'ees yaron Roshan...
Abbah ma ya shafa sannan yasa Roshan shima ya shafa,
Razhdeen ne ya nuna gardama akan shi bazai shafa wannan abun ba, daƙer daƙer Abbah ya tilasta masa ya shafa ba'a son ransa ba,
Malamin ya sanar musu cewa "wannan maganin yanada matuƙar tasiri a jikin ɗan Adam, ƙamshin maganin Aljanu basa son sa balle su raɓi jikin mutum, sannan maganin ratsa jiki yake wanda zai zauna ne har ƙarshen rayuwa, ya tabbatar musu cewa da yardar Allah wani Aljan bazai ƙara raɓen jikin wani daga cikin yaron gidan nan ba...
Anan Abbah ya masa godiya sannan aka sanar cewa gobe za'ayi sauƙar Alkur'ani mai girma a gidan gaba ɗaya na tsawon kwana uku...
Ɗaya bayan ɗaya haka kowa ya watse zuwa ɗakinsu domin suna buƙatar hutawa...
Bayan kwana biyu duk Abbah ya hallara su a falo, sai da yayi musu nasiha mai ratsa jiki sannan ya ƙarfafa musu gwiwa akan rayuwar Auren da zasu yi, a wannan ranar ne aka yanke bikin Razhdeen da Baiwar ALLAH, Roshan da Reemah zuwa nan da sati biyu,
Soyayyar Roshan da Reemah sai dai su bawa maƙiya mamaki domin in ka gansu sai kayi Alfahari da su, domin soyayya suke zubawa na bugawa a jarida, kullum suna manne basa rabuwa, sometimes Reemah takan bi Roshan zuwa hospital saboda ta taya shi aiki, yanzu soyayyar Roshan ya maye mata gurbin komai a cikin zuciyar ta, domin sai ta wuni bata ga Biju Mama ba tana can tare da mijinta Roshan...
Su ma ta ɓangaren su Razhdeen sai abinda ya ƙaru a soyayyar su, rayuwa suke kamar ma'aurata ga ƴarsu a tare da su, dake yanzu Biju Mama ta dawo hannun uwarta ganin Reemah yanzu ta makance akan soyayya,
Baby Ra'ees kuma yana hannun Ammy ita take rainonsa...
★★★★★
Bayan sati Ummy ce ta tashi da naƙuda, cikin ikon Allah ta haifi ɗiya mace bayan kwana biyu itama Pinky ta haifo ɗiya mace, a cikin kwanakin nan gidan Abbah cike suke da farin cikin samun ƙaruwa har mutum biyu ga shirye-shiryen biki yana ta matsowa, sauran Rukky ce kawai ta saura wacce ƙaramin ciki gare ta bai wuce 3months ba...
A yau ranar Wednesday Aunty Yolash tana zaune a falo ita kaiɗai tana bawa Ra'ees madara, jin sallama yasa ta ɗago tare da amsawa, Abbah ta fara gani ya shigo sai Mai martaba, bayan su kuma sai wani babban mutumi dake biye da su kana ganin sa kasan hutu ya zauna masa, asalin mai kuɗi ne domin baya zaman Nigeria, yana gudanar da kasuwancin a can ƙasar London...
Aunty Yolash ganin mutumin yasa ta miƙe tsaye tana zaro ido cikin tsoro da fargaba, a ruɗe murya na rawa ta furta "Mansur...."
Shima tsayawa yayi yana kallon ta ya ce "Khadijah..."
Abbah ne yayi masa iso da cewa "ka shigo ka zauna mana..."
Haka ya shigo cikin tausayawa kansa da kuma Aunty Yolash, duk zama suka yi su huɗu a falon, Abbah da Mai martaba da kuma mutumin da ake ƙira da Mansur sai Aunty Yolash,
Abbah ya ce "to Alhamdulillah yau dai zan kawo ƙarshen wannan al'amarin da ya kasa wuce wa..."
ya kalli Aunty Yolash sannan ya ce "Saboda shi kika ƙi yin Aure yanzu kinada shekara kusan arba'in a duniya, kuma shima Mansur saboda ke yaƙi yin Aure tsawon shekaru yana gudanar da kasuwancin sa a ƙasar waje, to yanzu lokaci yayi da za'a kawo karshen wannan al'amarin..."
Aunty Yolash tana hawaye ta ce "aka ce Mansur ya yi hatsarin a jirgi ya mutu ashe duk ƙarya ne kawai so ake a rabani da shi..."
Mansur ya ce "Khadijah wannan shine solution da nake da shi, iyayena basa son Aure na da ke, hakan yasa suka nema mun wata a cikin dangi, a lokacin na ƙi karɓar yarinyar a matsayin matata na dage akan sai ke, iyayena suka ce idan har ke zan Aura sai dai na mutu banyi Aure ba, duk wata hanyar da zan bi akan na mallake ki babu mafita, na yanke shawara akan nazo na same ki mu gudu muje muyi Aure kika ƙi amincewa, sannan suma iyayenki suka ce bazasu bani Auren ki ba tunda iyayena basa so, daga lokacin na shiryawa kaina mutuwa a idon kowa yanda zan yi nisa da kowa, akwai wani jirgi da yayi hatsari nasa aka sa sunana a cikin waɗanda suke cikin jirgin, ni kuma na wuce ƙasar wajen da babu wanda ya sanni, anan nake gudanar da kasuwanci na, sannan nayi alƙawari a kaina cewa bazan taɓa yin Aure ba indai ba ke ba, tsawon shekaru babu wanda yasan a yanda nake kowa ya ɗauka cewa na mutu amma duk da hakan ban daina bibiyan yanda kike ba, duk wani motsin ki akan idona yake, ganin kema har yanzu kina nan kin ƙi yin Aure saboda ni yasa na bayyana kaina a yanzu domin bazan so ki ƙare rayuwarki a haka ba, zan so kema Allah ya ɗauki rayuwarki a gidan mijinki, inasonki Khadijah har zuwa yanzu har kuma ƙarshen rayuwata...."
Aunty Yolash tana kuka ta ce "kana nufin ka dawo gareni?..."
Mansur ya ce "na dawo gareki Khadijah..."
Aunty Yolash ta ce "naga ƙiyayya ta a idon iyayenka shin taya yanzun ma zasu amince maka?..."
Mansur ya ce "na dawo na samu iyayena cikin ƙoshin lafiya na kuma nemi gafarar su akan ƙaurace musu da nayi sannan sun goya mun baya akan nazo na nemeki bayan sun ji labarin har yanzu bakiyi Aure ba..."
Aunty Yolash ba ƙaramin farin ciki ta shiga jin wannan kyakkyawan labari, hawayen farin ciki kawai take zubdawa...
Anan Abbah ya yanke cewa a rana É—aya za'a haÉ—a bikin su Razhdeen da na Aunty Yolash....
Bayan kowa yaji labarin Auren Aunty Yolash ba ƙaramin mamaki kowa ya sha ba domin har an fidda zaton zata yi Aure, ba ƙaramin farin ciki kowa ya tsinci kansa ba,
Auran mutane uku duk a lokaci É—aya sannan ga hidimar suna na haihuwan mutum biyu...
Ana washe garin ranar ɗaurin Aure gida ya cika fam da al'umma dake Abbah mai jama'a ne da zuriya har da ƴan ƙasar waje, duk wanda yaji har da Auren Aunty Yolash ko mutum bashi da niyyar zuwa sai yaje domin tayi farin jinin mutane, ƙawaye da mutanen ta na bauchi, kowa yana ta shabta, Amare duk suna killace Amreesh da Reemah ita kuma Aunty Yolash tana wani ɓangare daban ita da ƙawayenta domin ita ɗin babba ce bata son shiga hidimar yara...
A washe garin ranar juma'a a masallaci aka É—aura Auren su gaba É—aya,
Roshan and Reemah
Razhdeen and Amreesh
Mansur and Khadijah (Aunty Yolash)....
A cikin wannan al'umma Reemah ta fito tana zazzagaya ko ina cikin mutane kowa ta gani sai ta tambaye shi Roshan, domin rabon da ta gà nshi tin jiya, abokane sun riƙe su shi da Razhdeen especially Razhdeen wanda yanzu ne bikinsa na farko, abokansa sai tsiya suke masa na cewa yana saurayi ya Auri bazawara suna tsokanansa da mijin bazawara...
Minal ce ta riƙo hannun Reemah a wajen cikin mutane tana faɗin "ke ina zaki je kuma? wa ya gaya miki Amarya tana yawo ne?..."
Reemah ta zamar da hannunta tana faɗin "ni neman Yaya Roshan nake ban gà nshi ba..."
Minal ta ce "ina zaki gan shi ana tsaka da hidima, me zaki masa ai gwara ki ƙira shi a waya ko ki jira idan aka kai ki ɗakin ki sai ku haɗu..."
Reemah kamar zata yi kuka ta ce "Ni gaskiya bazan iya jira ba, kuma na ƙira wayansa bata tafiya nayi kewar ganinsa sosai, so nake na gà nshi Ni kam..."
Minal ta ce "ikon Allah, to ai baza ki ga Yaya Roshan a halin yanzu ba..."
Ƴar tinny ce tazo wuce wa da ƙawayenta ƴan uwanta waɗanda suka zo daga ƙasar waje,
Reemah tayi saurin tsayar da ita tana faɗin "yawwa Ƴar tinny baki ga Yaya Roshan ba?..."
Ƴar tinny ta ce "yana can waje shi da Abokansa har da Uncle Deen..."
Reemah ta ce "Æ´ar albarka Nagode..."
Da gudu ta nufi hanyar waje tana jan dogon rigar ta wanda ya sha aikin wuta dake gizner ne, kuma sai ta saje da ƴan matan baƙin da suka zo biki babu wanda ya lura da ita,
Minal girgiza kai tayi tare da faÉ—in "Allah ya shirye ki Reemah..."