Sashe 24
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Madam Parveen ta ce "idan kuwa yana da laifi to kema kinada laifi tinda ke kika ƙira shi gidan ki, meyasa zaki ƙira shi? Kuma kina ga ƴan uwansa ne suka jefa ku cikin matsala, kinsan ƙarfin turaren nan kuwa? ki daina ganin laifin kanki da kuma Razhdeen ki ɗauka cewa ƙaddarar ki ce tazo da haka..."
Baiwar ALLAH ta ce "Mommy na fuskanci duk bakwa son ganin laifin Razhdeen, duk kunfi son Razhdeen..."
Madam Parveen dafa kafaÉ—arta tayi tare da faÉ—in "duk muna sonku hakan yasa za'a haÉ—a ku Aure..."
Baiwar Allah a zabure ta doke hannun Mommynta daga kan kafaɗarta tana girgiza kai tare da faɗin "har abada bazan taɓa auransa ba, sai dai idan mutuwa nayi aka ɗaura masa aure da gawata, wallahi tallahi idan har ku ka dage akan haɗani da Razhdeen saina kashe kaina, gwara kawai na mutu nabar muku duniya, domin yanda na tsani Razhdeen ko mutuwa ta ban tsane ta ba, kuma wallahi cikin nan zubar shi zanyi bazan haife shi ba...."
Madam Parveen rarrashinta take tana bata haƙuri akan ta dakata da wannan shirmen nata amma Baiwar Allah sam taƙi fahimta sai surutan ta take tayi marasa kan gado, ganin ta kasa dawo hayyacinta ne yasa Madam Parveen zabga mata mari tare da faɗin "wani irin hauka ne wannan, shin kin manta a inda kike ne? bafa a gidan ubanki kike ba, a gidan ubansa kike amma kike faɗin cewa kin tsane shi bakya sonsa har kina iƙirarin zaki zubar da cikin anya kinada hankali kuwa? yanzu idan iyayensa suka ji wannan furucin nakin zasu ji daɗi ne? shikenam kije ki zubar tinda ke mahaukaciya ce...."
Madam Parveen tana kaiwa nan ta fice a É—akin,
Baiwar ALLAH fashewa tayi da kuka tare da kifar da kanta a kan gado....
Abbah yana zaune idonsa akan Ashmar ya ce "taso kazo yanda nake magajin gobe...." da murmushi akan fuskar Abbah..
Ashmar kallon Mamansa yayi tayi masa alamar yaje da idonta, tashi yayi ya nufi yanda Abbah yake zaune yaje ya zauna kusa da shi,
dafa kafaÉ—arsa Abbah ya yi yana tsokanan sa, daga baya yake cewa "meyasa ka tafi ka bar Mamanka?...."
Ashmar É—ago wa yayi yana kallon Abbah kamar zai yi kuka domin abubuwan da suka faru da shi bazai misaltu ba..
Abbah ya sake tambayar sa cewa "shin zaka iya tuno duk abinda ya faru dakai bayan tafiyar ka?
Mahaifiyar ka ta sanar mana cewa ka nufi ƙasar Jidder zaka je ka bayyar da kanka cewa kai ɗan sarki ne, shin meya faru baka je ba sannan kai baka koma gurin mahaifiyar ka ba...."
Hawaye ne suka gangaro masa daga cikin ƙwayar idanuwansa yana girgiza kai tare da faɗin "bazan iya tunawa ba ...."
Abbah ya ce "meyasa? zaka iya mana please nan duk Æ´an uwanka ne family mahaifinka da shi kansa mahaifin nakan ne..."
Ashmar ya ce "a shekara takwas da suka wuce akwai jirgin da aka rasa daga Iran zuwa ƙasar Jidder wanda aka ɗau tsawo kwanaki ana nema amma ba'a gani ba, nasan kun san da wannan labarin, to a cikin mutanen jirgin har da ni a ciki, jirgin ba ɓata tayi ba sace wa akayi, duk mutanen jirgin an yi kidnaping ɗin su, wasu manya-manyan ƴan fashi ne waɗanda suka amsa sunan su, a cikin mu an kashe wasu, wasu kuma sun maida su yaran su, aciki har da ni suka mayar mu yaran su, mata kuma sun kashe tsofi, ƴan mata kuma sun mayar su karuwen su, akwai alluran da suke mana wanda zai sa mu manta gida, mu daina tunanin gida sannan ya dasa mana rashin imani acikin zuciyoyin mu, waɗannan ƴan fashi akwai baƙaƙen fata sannan akwai turawa, sun bamu horo na musamman, duk wanda ya kasa jure horon nan sai dai asa bindiga a harbe masa kai domin a tunanin su babu abinda zai iya, an fita da mu ƙasashen waje mabanbanta domin aiwatar da fashi, duk wani fashin da za'ayi mu ake turawa, a cikin bama so har muka saba,
a cikin mu akwai waɗanda suka zamo manya-manyan ƴan fashi wanda babu imani a tattare da su, wanda idan basu yi kisa ba basa jin daɗi daman ƴan fashin ƙasar waje ne ,
Amma ni yanda na gode wa Allah har yau Allah bai bani iko da damar aiwatar da kisan kai ba, da hannaye na ban taɓa yin harbi da hannuna ba, sannan ban taɓa kashe wani bawa ba, kuma ban taɓa buɗe baki nayi magana ba hakan yasa suka bani wani matsayi da ban suke ƙirana da Guess bana magana, na mayar da kaina kurma sannan bana haɗa ido da mutum,
hakan yasa suka bani umarnin rufe fuskata saboda zan zamo musu mai leƙen asiri,
A cikin mu an zaɓi babba sannan an bashi yara waɗanda zasu yi aiki a ƙarƙashinsa duk ƙasar da aka tura ka nan zaka je ka zauna a cikin daji,
A ciki har da ni, Ni kuma sai aka turo ni nan Nigeria da yarana waɗanda zasuna mun aiki, aka ƙera mun gida a cikin daji anan ake aiwatar da aikin ta'addanci, har Allah yasa wani mutumi da ya ji labarin mu sai yazo yanda muke ya haɗa hannu da mu, ya zuba maƙudan kuɗaɗe sosai hakan yasa daga ƙungiyar mu aka bashi matsayi domin yana bada gudumowa sosai waran tura wa shuwagabannin mu ƴan mata, yakanyi safaran ƴan mata ya tura su sannan a bashi kuɗi ganin aikin da yake musu ni banayi yasa suka karɓi matsayin da suka bani suka bashi, sai ya zamana sai abinda ya cemun ni kuma saina saka na ƙasa dani suyi, haka rayuwar mu ta cigaba a cikin daji, har Allah yasa aka kawo mana wannan yarinyar ....".
Ashmar ya ƙarasa maganar tare da nuna yanda Ƴar Amana take a kwance, ganin ya nuna ta ne yasa tayi saurin tashi tana tuno da abinda ya faru da ita a baya, a cikin ranta ta ce "kenam wannan shine mai rufe fuskar sa da baƙar hula?..."
Duk mutanen falon kallon yanda Ƴar Amana take suka yi suna jinjina lamarin...
Ashmar sai da ya gama basu labarin abinda ya faru da shi kab sannan ya ce "a rana ta ƙarshe da ake son kashe ta ni na tura wa Major Razhdeen saƙon yanda take saboda na bincika sunada kyakkyawar alaƙa a tsakanin su, daga lokacin da aka kamani Razhdeen bai bari an azabtar dani ba saboda ni na bayyanar masa a yanda yarinyar take, su kuma sauran mutanen mu ban san a ina suke ba, shin an kashe su ko suna raye sai Allah, a lokacin da Razhdeen ya sanar cewa a barni nayi tafiyata na roƙe shi akan ya ƙyale ni a wurin sojojin sa domin zan fi samun nutsuwa, nasan ina fita daga waransu za'a nemi rayuwata ce domin mutanen mu kashe ni zasu yi....."
Maimuna ba abinda take sai kuka jin ƙibtili'in da yaron ta ya shiga,
Kowa ba ƙaramin tausaya masa ya yi ba..
Mai martaba yana sharar hawaye ya ce "ni kuma tawa ƙaddarar kenam, duk a cikin ƴaƴana babu wanda yayi rayuwar jin daɗi, duk su biyun sun shiga bala'i da masifar rayuwa, Allah sarki...."
Abbah ya ce "kar ka damu duk jarabawar rayuwa ne, Allah yasa mu ci jarabawar...."
Duk suka amsa da Amiin....
Ramlat ce ta tashi jiki ba ƙwari zata wuce Abbah ya tsayar da ita tare da faɗin. "zo ki zauna mana..."
Zama Ramlat tayi kai a sunkuye sai zubda hawaye take,
Abbah ya ce "kar ki sa damuwa a ranki saboda a halin da kika ga Ƴar uwarki da kuma hukuncin da za'a yanke mata, duk ita ta ja wa kanta...."
Ramlat tana kuka ta ce "Abbah banji takaicin hukuncin da aka yanke mata ba, babban takaicina shine da na haÉ—a jini da ita, ban so hakan ba, amma dan ALLAH kada laifin da ta aikata ya shafe ni, wallahi ban san duk ta aikata wannan ta'addanci ba..."
Abbah ya ce "ai daman ko a wurin Ubangiji laifin wani baya shafan wani, mu dai abinda zamu gaya miki shine ki kwantar da hankalinki ki zauna a ɗakin mijinki, kada kiyi abinda zai sa kema a tsane ki, kinga dai halin da ƴar uwarki ta tsinci kanta abun babu daɗi, kada ki ɗauko halin ta ko kaɗan, domin a zamanin yanzu ka zama mutumin kirki ya ka ƙare da duniya balle ka zaɓi abun tsiya, ita duniya budurwar wawa ne, wanda bai zo cikinta bama ya yaƙare balle wanda yake cikinta, don haka kiyi ƙoƙarin aikata abin alkhairi dan ALLAH....."
Ramlat tana kuka ta ce "Insha Allahu Abbah ba zaku samu matsala daga gareni ba, zan zamo mai muku biyayya da kuma mijina, Allah ya huci zuciyar ku...."
Abbah ya ce "ba komai Allah ya miki albarka...."
ta amsa da Amiin...
Sannan ta miƙe taje ta zauna a gefen Ƴar Amana tare da kamo hannunta tana murmushi ta ce "Ƴar uwata ina taya ki murnar dawowa gida..."
Ƴar Amana jinjina mata kai tayi ba tare da ta ce komai ba,
Domin Ƴar Amana har yanzu akwai wannan miskilancin nan....
Anan Abbah ya sanar cewa za'a fita da Razhdeen ƙasar Ethiopia domin zai fi samun sauƙi anan sosai....
Daga nan bayan an wuni guda Minal da mijinta Mohandas da yaronsu Afif tafiya suka yi gidan da suke kafin lokacin komawar su ƙasar U.S saboda aikin da Mohandas yake acan...
★★★★
Bayan Sati biyu