← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 68

Sashe 22

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammy ta ce "a'a wannan azabar ai tayi musu tsauri su na Æ´aÆ´a mata..."

Abbah ya katse ta da cewa "babu ruwan kowa, sai yanda naso ayi da su..."

Hajiya Kilishi tana hawaye haka take kallon Abbah domin hukuncin yayi tsauri duk da sun cancanci hakan,
Pinky da Rukky haka suke ƙanƙame jikin Hajiya Kilishi suna faɗin "wayyo Allah Mommy kar ki bari a tafi da mu, ki taimaka mana Mommy, wallahi kashe mu zasu yi wayyo Allah...."

Daƙer Sojan ya fincike su daga riƙon da sukayi wa Hajiya Kilishi, ita kuwa kanta na kallon gefe tana jin yanda suke ta faman rirriƙe ta amma bata kula su ba sai zubda hawayen da take, da haka aka fita da su suna ihu,
Maamie kuwa itama an daÉ—e da ficewa da ita, ita wannan direct zaman prison zata yi....

Bayan awa guda kowa ya gama jimamin abinda ya faru, suna cikin jajanta wa juna suka fara jin kuka ana faÉ—in "Mama! Mama!! Mamana!!! Mamana!!!!...."

Duk juyowa sukayi suna kallon yanda Ƴar Amana take a kwance kan cinyar Mahaifiyar ta akan kujerar falon,

Baiwar ALLAH zaro ido waje tayi baki a buɗe tana kallon Ƴar Amana ganin bakinta ya buɗe,
babu abinda take furtawa illa Mamana..

Kowa na falon farin ciki ya shiga yi, Mai martaba kamar bazai bar duniya ba tsabar farin cikin bayyanar É—iyarsa sannan bayan ita akwai namiji wato Yarima amma sai dai zasu binciko a yanda yake...

Aunty A'isha shafa fuskar Ƴar Amana take da murmushi akan fuskar ta,
Itama Maimuna murmushi take tana sharar hawayen farin ciki, yau ga Reemah da iyayenta...

A hankali Ƴar Amana take ƙoƙarin buɗe idanuwan ta, har sai da ta gama buɗe su gaba ɗaya, babu fuskar da ta fara gani illa na mahaifiyar ta wato Aunty A'isha dake ɗauke da ita akan cinya...

Daƙer take shirin tashi zaune har sai da Aunty A'isha ta tallafa mata tukun ta iya tashi, tana kallon kowa na falon ɗaya bayan ɗaya...

maida kallon ta tayi kan Baiwar ALLAH taga yanda take ta mata murmushi itama mayar mata da martani tayi lokaci guda kuma ta tuno da video da ta gani a plasman ita da Razhdeen, da sauri ta kawar da kanta gefe,
Aunty A'isha ce ta riƙo fuskar ta da hannu biyu suna fuskantar juna ta ce "Yarinya ta Reemah yau ga ki a gaban iyayen ki da kika rasa tin haihuwa, ni ce mahaifiyar ki na halal, ni ce wacce na haife ki a cikina Reemah..."

Ƴar Amana kallon Aunty A'isha take itama idonta ya cicciko da ƙwallah, sai ga Mai martaba shima yazo ya zauna a gefen ta tare da riƙo hannunta yana faɗin "Shalele..."
da murmushi akan fuskar sa...

Jan hannun rigar sa yayi sama sai ga zanen tambarin masarauta akan dantsensa, Ƴar Amana idonta akan zanen ganin irin na kan cinyar ta sak yasa ta washe baki tana dariya bata san lokacin da ta furta "Babaaa...". ta rungume shi sosai tana kuka...

Aunty A'isha itama rungumar ta tayi ta haÉ—e Mai martaba da Reemah duk ta rungume su tana kukan farin ciki...

Kowa na falon bai san lokacin da ya tsinci kansa cikin farin ciki ba, itama yanzu Ƴar Amana tasan su waye iyayenta...

Maimuna itama tsabar farin ciki haka ta tashi ta nufi wurin su ta durƙusa tare da sa hannu ta rungume su gaba ɗaya, daga Mai martaba har Aunty A'isha sai Reemah da suka sakata a tsakiya, shima Mai martaba hannu yasa ya ɗora akan gadon bayan Maimuna ya rungume ta haka itama Aunty A'isha tasa hannu itama ta rungumi Maimuna duk suka haɗe kayuwan su guri guda su huɗu...

Baiwar ALLAH ganin yanzu burikansu ya cika yanzu bata san lokacin da ta fashe da kuka ba ta rungumi Mamanta itama, Madam Parveen wacce akafi sani da Zainab itama rungumar ta tayi sosai a jikin ta...

Bayan wasu Æ´an mintuna kowa ya dawo cikin nutsuwar sa,
Abbah ne ya kalli Maimuna sannan ya ce "yanzu haka zamu iya samun photon Yarima a wurin ki?..."

Maimuna da sauri take É—aga kai sama tana faÉ—in "eh! eh akwai suna cikin wayata bari na duba..."
haka ta fara daddanna wayar ta, cikin lokaci ƙanƙani ta taso tare da bawa Abbah wayar ta ce "gashi nan shine..."

Abbah ƙarewa photon kallo yayi sannan ya ce "Insha Allahu zamu nemo shi..."

Roshan ne ya taso ya karɓi wayar yana dubawa, yana ganin photon ya zaro ido waje tare da faɗin "wannan ai GUESS ne, yana daga cikin mutanen da Razhdeen ya kamo acan daji suna safaran Ƴar mata, yanzu haka suna can gadurum na sojoji, yaron kullum da baƙar hula akan fuskar sa, sanadin kamashi ne yasa muka ga fuskar sa shine daman Yarima?...."

Maimuna haka zuciyar ta yake bugu da ƙarfin gaske jin suna safaran Ƴan mata, haka shima Mai martaba da sauri ya karɓi wayar yana dubawa gaba ɗaya ya zamo kalar tausayi.....

Abbah ya ce "ina buƙatar ganin sa a yau ɗin nan..."

Nan ya ɗauki wayar sa yayi dialing call bugu ɗaya aka ɗauka ya kara a kunne yana faɗin "hello akwai yaron da ake ƙiransa da Guess ina son ganinsa yanzu, a kawo mun shi..."
daga nan Abbah ya katse ƙiran...

Chief Suraj ne yayi gyaran murya tare da faɗin "Halaluyya! a yau na shiga wani tashin hankali dana ji labarin wasu daga cikin mu abun tausayi amma yanzu Masha Allah tinda an kawo ƙarshen komai, sannan nayi matuƙar farin ciki sosai ganin yanda iyaye suka haɗu da ƴar su na taya ku farin ciki sosai...."

Mai martaba shima cewa yayi "Alhamdulillah kuma muna taya ku cikar family, mun gode wa Allah...".

Gaba É—aya kowa ya taya Æ´an uwansa murna...

Daga baya ne Chief ya sanar cewa zasu koma ƙasar U.S...

Abbah ya ce "kar dai da Daughter nah zaku tafi?..."

Chief ya ce "duk tare zamu tafi, babu abinda zamu ce sai dai Allah ya saka da alkhairi, kun riƙe mun yarinya tamkar ku kuka haife ta, thank you very much...."

Abbah ya ce "ba komai ai duk ƴaƴa ne, kuma Insha Allahu zamu rinƙa zuwa muna duba ku kafin Razhdeen ya samu lafiya sosai...."

Baiwar ALLAH cikin rashin fahimta take binsu da kallo a cikin ranta tana faÉ—in "meyasa za'a sako Razhdeen a cikin lamarina, shin idan ya samu lafiya me zai faru?..."

Chief ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Daughter zamu iya tafiya ko?..."

Baiwar ALLAH girgiza kai tayi tare da faÉ—in "ni da Mommy bazamu tafi ba..."

Chief cike da mamaki yake kallon ta ya ce "why?..."

Ta ce "saboda mu É—in musulmai ne, idan kuna son zama da mu to kuma ku musulunta, Daddy Kai da Yaya Rakesh kune ku ka saura baku musulunta ba...."

Chief sai da yaji bugun zuciya da sauri ya kalli Madam Parveen cike da mamaki ya ce "wai ke É—in kin musulunta ne?..."

Madam Parveen tana hawaye ta ce "ey na musulunta na koma suna Zainab..."

A ruɗe Chief ya miƙe tsaye tare da faɗin "whattttt?...."

Abbah shima miƙe wa yayi tsaye ya nufo wurin da yake tare da dafa kafaɗarsa yana faɗin "relax Chief, inaso kabi komai a hankali...."

Chief cikin ɓacin rai ya ce "wani irin robish ne wannan, kin musulunta ba tare da kin sanar mun ba? ita Amreesh daman nasan dole ta zauna cikin musulunci saboda wanda zata aura musulmi ne, tin tana ƙarama nayi alƙawarin ta a musulmi, Razhdeen zata Aura....."

A ruɗe Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye itama tana zazzaro ido waje tare da faɗin "meeeeeeeee?...."

Itama Ƴar Amana bata san lokacin da ta zabura ta miƙe tsaye ba, zuciyar ta na bugun uku-uku....

Lokaci guda kan Baiwar ALLAH ya sara ga wani irin tashin zuciya da yake shirin hargutsa mata tunani, yunƙirin amai ta soma yi, da sauri tasa hannu tana toshe bakin ta ganin bazata iya riƙe aman ba yasa ta ru ga da gudu ta shige room ɗinta, kai tsaye toilet ta shige...

Madam Parveen ganin haka yasa ta bi bayanta da sauri itama ta shige cikin room É—in, a toilet ta tarar da Baiwar ALLAH sai kwarara amai take tayi a cikin sink...

sai da ta gama mai isar ta tukun ta wanke bakinta ta juya tana kallon Mommyn ta, jikinta har wani ɓari yake yana kakkarwa alamar zazzaɓi ne ya rufe ta,
Madam Parveen hannu tasa tana taɓa jikinta ganin jikin ya ɗau zafi sosai yasa ta faɗin "Ya Allah! zazzaɓi ne a jikin ki fa, meyasa baki ce baki da lafiya ba?...."

Riƙo hannun Baiwar ALLAH tayi suka yi waje, kai tsaye falo suka koma,
Madam Parveen ce ta sanar cewa Daughter bata da lafiya...

Abbah a ruÉ—e ya ce "ba lafiya kuma?..." ya kalli Roshan sannan ya ce "kaga kaje ka duba ta shin me yake damun ta..."

Baiwar ALLAH kifar da kanta tayi akan cinyar ta tana tariyo maganar Daddyn ta na cewa Razhdeen zata Aura, É—agowa tayi a gigice tana faÉ—in "ni wallahi bana son Razhdeen, bazan Aure shi ba...."

Roshan ne yazo gaban ta tare da riƙo hannunta ya ɗagota suka nufi medicine room acan kayan gwaje-gwaje yake,
Baiwar ALLAH tana kuka idonta akan Roshan da haka suka tafi...

Chief cike da mamaki ya kalli Abbah sannan ya ce "shin Auren Roshan da Amreesh akwai ne ko babu?..."

Abbah girgiza kai yayi tare da faÉ—in "a gaskiya babu, saki ne anyi shi yanzu tsawon wata huÉ—u kenam, ta gama iddar ta...."

Acan kuma Roshan ne ya duba ta, gaba ɗaya jikinsa ba warki domin ya tabbatar da wani abu, nan da nan idonsa ne suka cicciko da ƙwallah ga yanda suka kaɗa suka yi jawur,
Baiwar Allah ganin yanda ya chanza lokaci ƙanƙani yasa zuciyar ta bugawa ...

Murya ciki-ciki ya ce "kwanta akan gado...."

Kamar yanda yace haka tayi, ta hau ta mimmiƙe idonta akan sa, hannu yasa ya buɗe mata riga idonsa akan cikinta,
anan yayi mata scanning ya gama tabbatar da komai,
jinjina kai yayi sannan yasa hannu ya ɗago ta yaja ta suka fice, suna isa falo ya miƙa wa Abbah wata takarda...

Abbah karɓa yayi tare da dubawa a ruɗe ya ce "whattt? pregnant? har na tsawon wata huɗu?..."

Baiwar ALLAH a ruÉ—e ta É—ago tana kallon Abbah tare da zazzaro manya-manyan idanuwanta,
Chapter 22 · 0% Book details