Sashe 68
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sauƙe numfashi Reemah tayi sannan ta ce "Yaya Roshan na gaya muku cewa tin kafin a Aurar da ni da matsalar aljanu suka shigo mun su suka cire mun, daman sun sanar mun cewa idan nayi Aure ba batun haihuwa, sun cire mun mahaifa yanda bazan haihu ba amma tinda suka bar ni a matsayin mutum ɗina sai mu gode wa Allah kuma yanzu sun cire hannunsa akaina nan ma abun godewa Ubangiji ne, ni bana damun kaina da rashin haihuwar nan saboda Ra'ees ɗina kaɗai ya isheni, kuma ina mai farin ciki da ya tashi yake gani na a matsayin mahaifiyar sa har yake ƙirana da Mommy,
Yaya Roshan sai dai kai idan kana buƙatar samun ƴaƴa ban toshe maka hanya ba kuma bazan dakatar da kai ba kaje kayi Aure dan Allah, na baka goyon baya kaje kayi, idan na hanaka ma na cutar da kai ne...."
Roshan a tsawace ya ce "ya isa haka dallah..." cikin ɓacin rai ya tashi ya nufi part ɗinsa domin ba ƙaramin ɓata masa rai tayi ba da ta masa maganar Aure...
Reemah ganin yanda ya tashi rai a ɓace yasa ta ce wa Ra'ees "jira ni ina zuwa ..."
itama ta bi bayansa, a cikin room ɗinsa ta iske shi yana zaune a bakin gado, itama zama tayi tare da ɗora hannunta akan cinyarsa tana faɗin "Yaya Roshan kullum burina shine na faranta maka, bana son ganin ɓacin ranka ko da wasa, Yaya Roshan a cikin maganganu na meya ɓata maka rai? ka sanar mun ni kuma sai na kiyaye faɗin haka..."
Juyowa ya yi yana kallon ta ya ce "Shalele banaso idan muna maganar da ya shafi haihuwa kina kawo mun zancen Aure, kina nufin ki ce dan bakya haihuwa ne zai sa na ƙara Aure? a misali ace bani da Ra'ees wallahi bazan ƙara yin wani Aure don na haihu saboda bakya haihuwa ba, zan cigaba da zama da ke a haka har ƙarshen rayuwar mu, bana ƙaunar wata ta shigo mana cikin rayuwa Shalele, don haka ki sa wa bakinki linzami...."
Reemah gaba É—aya ta rasa abun cewa a wannan al'amarin rungumar Roshan kawai tayi tana kuka,
shima ƙara mannata yayi a jikinsa yana rarrashin ta....
Bayan wasu Æ´an kwanaki ana washe garin suna kowa ya hallaru a gidan General dake Nigeria Abuja City,
Baiwar Allah da ƴan ukun ta tare da Afaf duk sun dawo Nigeria har da su Minal da Rukky wacce itama bata samu haihuwa ba har yanzu, idan ta samu ciki sai ya zube ko tayi ɓari, wasu likitoci sun sanar cewa mahaifar ta ne yayi ƙarami bazai iya ɗaukan jariri ba, yanzun ma ciki gare ta taƙi haƙura duk da ta dage da neman magani haka mahaifiyar ta Hajiya Kilishi tana nema mata magani sosai...
Pinky itama tazo da ƴan uwan mijinta dake tsatso ɗaya ne, ƙasar Jiddah su ma kowa yazo, su Ummy uwar masu gida da ƴaƴanta biyu itama,
Roshan da matar sa Reemah da ɗansu suma sun zo, kowa yaga Reemah sai ya yi maganar ƙibar ta, ta zama ƙatuwa babbar mace duk wani farin ciki da jin daɗi da hutu tana samu sosai, matsalar ta ɗaya shine rashin haihuwa...
Ranar suna kowa ya cika a gidan, triplets sunyi mutane sosai Alhamdulillah,
ÆŠaya ta ci sunan Aunty Yolash wato Khadijah (NIHLA)
É—ayar kuma sunan mahaifiyar Baiwar ALLAH wato Zainab (NIHAL)
Namiji kuma ya ci sunan Roshan, junior Roshan (NU'AYN)
Roshan ba ƙaramin farin ciki ya yi ba, ya haɗa kayan mai suna na hauka, domin duk wanda yaga kayan sai ya yi magana, har da gadon jariri...
Abbah kuma ya haɗa wa mai sunan Aunty Yolash kayan mai suna, tin daga ƙasar Ethiopia aka haɗa kayan, shima har da gadon jaririya..
Madam Parveen itama ta haÉ—a kayan mai sunan ta, itama har da gado..
Anyi bikin suna cikin ƙoshin lafiya, anan ne Baiwar ALLAH tasa aka tara mata mutane a babban falo tana son isar da saƙo akan wani lamari, bayan kowa ya hallaru har da su Abbah da mai martaba da Razhdeen da Roshan da kowa da kowa, Baiwar ALLAH cikin nuna farin ciki tayi wa kowa godiya akan hidimar da suka mata sannan ta sanar wa kowa cewa "a cikin ɗaya daga cikin jariran mata biyunta zata bayar wa Reemah ɗaya duniya da lahira sannan ta sanar cewa tana neman alfarma a wurin kowa na cewa koda yarinyar ta girma kada a sanar mata cewa ba Reemah ce mahaifiyar ta ba, domin ta mallaka mata ita har abada...
Kowa ba ƙaramin farin ciki ya shiga ba, sai fatan alkhairi ake musu da sanya albarka,
Reemah kamar ta haukace tsabar farin ciki ga tana masifar son yara, bakinta ya ƙi rufuwa ta kasa furta komai,
Shima Roshan ya yi matuƙa farin ciki da jin wannan sanarwa kamar wanda aka masa bushara da gidan Aljanna, ga yaran sun shiga ran kowa,
Baiwar Allah ganin yanda Reemah take ta dariya tsabar farin ciki ta kasa furta komai, ta tashi tana riƙe da yara mata biyu daƙer take tafiya dake operation aka mata ta nufi yanda Reemah take a zaune, ta zauna a kusa da ita fuska ɗauke da murmushi ta ce "Ƴar Amana ta tinda Afaf ta miki butulci ga wata zan baki ita, kiyi nesa da ita kar ma ta rinƙa ganin fuskata, ki nuna mata cewa kece mahaifiyar ta, don haka a cikin su biyun nan ki zaɓi ɗaya,
Aunty Yolash ko kuma Mommy na wato NIHAL ko NIHLA ki zaɓi ɗaya,
Reemah har da hawayen farin cikinta ta ce "haba Aunty Baiwar Allah nah, ki mun babban kyauta hakan ma sai na zaɓa?..."
Baiwar Allah ta ce "eh mana wacce hankalin ki yafi kwanciya da ita zaki É—auka..."
Reemah ta ce "a'ah duk sun shiga raina sosai, hankalina a kwance yake da su amma tinda kin bani zaɓi, na zaɓi Aunty Yolash wato NIHLA...."
Tasa hannu ta karɓe ta tana sakin murmushi tare da faɗin "ban san da wani baki zan fara miki godiya ba Aunty Baiwar ALLAH, babu abinda zan biya ki da shi sai dai nace Allah ya saka da alkhairi..."
Baiwar Allah ta dafa kafaɗar ta tare da faɗin "kar ki damu Shalele daman nayi niyyar yin haka, na ɗau alƙawari a kaina cewa idan Allah ya ƙara azurtani da ƴa ko ɗa zan mallaka miki shi ko ita..."
Kowa hamdala ya yi tare da nuna farin ciki,
Abbah idonsa akan Baiwar ALLAH ya ce "amma sai kin shayar da ita ko kuma tin yanzu kin bayar da ita?..."
Baiwar Allah ta ce "shayar da ita ya ƙare daga yau Abbah, zasu cigaba da shayar da ita..."
Jinjina kai Abbah yayi tare da taya su murna...
Bayan wasu watanni Baiwar ALLAH ta gama hutun ta a Nigeria, tana riƙe da Nu'ayn da Nihal sun shirya zasu koma U.S.
Reemah kuwa sun juma da komawa ƙasar da suke da jaririya Nihla da kuma Ra'ees...
Itama Rukky Allah ya sauƙe ta lafiya ta hanyar yi mata operation bayan aikin da akayi akan ta na gaske kafin cikin ya zauna, an cire mata ɗiya mace tayi wa mahaifiyar ta mai suna wato Hajiya Kilishi....
🕊ï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸
*ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALI*
*ALLAH NA GODE MAKA DAKA BANI IKON KAWO ƘARSHEN LITTAFINA MAI SUNA MY ENEMY WATO MAƘIYI NAH*
*NAGODE SOSAI MASOYANA DA BANI HAƊIN KAI DA ƘWARIN GWIWA KAMMALA LITTAFIN, DOMIN DA TAIMAKON KU NA KAMMALA BOOK ƊIN MY ENEMY TA HANYAR DAMU NA DA CEWA UPDATE! UPDATE!! UPDATE!!!*
*NAGODE MUKU SOSAI, YAU DAI ALLAH YA KAWO ƘARSHEN LITTAFIN....*
*SHARHI, COMMENTS, SHARHI, COMMENTS, DUK DA KUNA MUN SOSAI AMMA INA SO NA YAU YAFI NA KULLUM👌👌👌*