Sashe 48
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amreesh ta ce "ko ban tambaye ta ba ai tana cikin raina..."
Roshan ya ce "let us go idan kun gama shan love..."
dariya suka yi duk suka bar wurin,
Kowa shiryawa yayi tsab za'a tafi Nigeria, Minal da Rukky murna suke zasu je su ga iyayen su...
Roshan gaba É—aya zumuÉ—in sa shine yaje ya ga handsome boy É—insa duk da an turo masa photon yaron a waya,
har da Madam Parveen itama ta shirya zasu tafi....
°°°°°°°°°°°°°°°
Nigeria
Kowa ya taru a babban falon gidan General, Mai martaba shima ya samu zuwa shi da iyalansa Aunty A'isha da Aunty Maimuna da kuma Ummy uwar masu gida da mijinta Yarima,
Ga kuma Abbah da iyalansa shima Hajiya Kilishi da Ammy da kuma Aunty Yolash wacce take riƙe da jariri a hannunta, ga Pinky itama tazo da mijinta Arash,
Reemah da Afaf kuma suna cikin ɗaki dake Reemah ba mai son zama a cikin mutane bane shiyasa take fakewa a wuri guda ita da abar ƙaunar ta Afaf,
Sai yanzu isowar su Roshan suma samun wuri sukayi shi da Razhdeen suna zauna,
Madam Parveen itama zama tayi kamar yanda taga kowa a zaune falon yayi tsit ko motsi bakwa ji,
Minal da Rukky suma a kujera É—aya suka zauna, ita kuma Amreesh kujerar da Ummy take nan taje ta zauna,
Aunty Yolash ce ta miƙe tsaye taje gaban Roshan wanda yake zaune yana bin kowa da kallo fuskar kowa ba annuri, haka yasa hannu ya karɓi yaron dai-dai lokacin da hawaye ya ɗigo a hannun Roshan, da sauri ya ɗaga kansa yana kallon Aunty Yolash wacce hawaye ya gama wanke mata fuska,
Wani irin bugu zuciyarsa tayi wanda bai san lokacin da jikinsa ya É—au kakkarwa ba,
Ummy itama hawaye take wanda Amreesh gaba É—aya ta kasa gane wa,
Sai a lokacin Abbah ya ce "Yolash zo ki zauna..."
haka taje ta zauna jiki ba ƙwari,
Razhdeen cikin rashin fahimta ya ce "wai me yake faruwa ne?...."
Roshan yana riƙe da jariri idonsa akan fuskar sa yana sakin murmushi ga hawaye shima yanda yake zubo mishi ya ce "Boy kaga suna ɓoye mun cewa Mamanka ta rasu ko, kaima kan ka kasan Mamanka ta rasu bazaka kasa ɓoye mun ba tinda ga nan bakinka yana motsi, Mamanka ta tafi ta bar mun kai why?...."
Razhdeen a ruÉ—e ya daga kafaÉ—arsa yana faÉ—in "twins wai me kake faÉ—i haka ne?..."
Cikin ɗaga murya Roshan ya ce "My Man ka dubi duk fuskokin su hakan yana nuna alamar isar da wani mummunan saƙo ne, shin idan ba saƙon mutuwa suke son isarwa ba to saƙon meye? shin ina Ramlat? ban ganta a cikin ku ba hakan na nufin tabar duniyan nan, Ramlat ta tafi tabar jaririn yaro, nasan in ba mutuwa ba babu yanda za'ayi Ramlat tabar mun jaririn yaro dole sai aikin mai yankan ƙauna wato mutuwa...."
Duk matan falon fashewa suka yi da kuka, Minal da Rukky ne suke tambayan Abbah cewa "Abbah da gaske ne wai Aunty Ramlat ta rasu?..."
Amreesh ƙafewa tayi gaba ɗaya ta kasa yin kukan ma jin yanda zuciyar ta yake bugawa jin mummunan labari,
Razhdeen shima idonsa ya kai kan Abbah yana son jin ƙarin bayani,
Abbah jinjina kai yayi tare da faÉ—in "tabbas wanda ya fi mu sonta ya É—auke kayan sa..."
A firgice Madam Parveen wacce itama take son ji daga bakin su ta dafe ƙirji tare da faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un...."
A ruɗe Baiwar ALLAH ta ƙanƙame hannun Ummy wacce take kusa da ita tana jinjina labari, haka kanta yake juyawa domin labarin mutuwar Ramlat ba ƙaramin girgiza kowa yayi ba....
Roshan jaririn hannunsa ya manna a ƙirjinsa tare da fashewa da kuka, haka Razhdeen yake bubbugan bayansa yana rarrashinsa...
Mai martaba ya ce "kuyi haƙuri haka rayuwar take wata rana kayi farin ciki wata ran kuma kayi kuka, hakan ma mun godewa Ubangiji da Allah yasa muka sake samun ƙaruwar ahali, kuka ba maganin mutuwa bane hakanan zamu cigaba da yi mata addu'a domin tafi buƙatar sa a halin yanzu...."
Madam Parveen ce taje ta karɓi jaririn hannun Roshan domin yanzu ba'a cikin hayyacinsa yake ba, ba abinda yake sai kuka...
Suna cikin wannan halin sai ga wasu mutane sun shigo da sallama a bakinsu, ƴan uwan Ramlat ne suka zo ta ɓangaren mahaifinta da kuma mahaifiyar ta domin daman su ake jira, an gama gyarata tana can cikin ɗaki a kwance cikin makara...
Roshan a zabure ya miƙe tsaye yana faɗin "ina take?...."
Mai martaba ne ya nuna masa É—akin da take kafin a fita da ita gurin jana'iza domin an sanar wa mutane har an taru,
Roshan da gudu ya wuce É—akin a yayin da Razhdeen ya bi bayansa, itama Baiwar ALLAH bin bayan su tayi, a É—aki suka tarar da gawar Ramlat a cikin makara an gama rufa mata likkafani,
Roshan durƙusawa yayi a gabanta yana kuka tare da faɗin "Ramlat ashe daman yafiyar da kike cewa nayi miki tafiya daman xakiyi ki barni? hawayen da kike zubar wa a gabana ashe daman kukan ƙarshe kike mun? Ramlat inasonki, na yafe miki duniya da lahira, Allah Ubangiji ya haskaka miki kabarin ki yasa kina ɗaya daga cikin salihan bayi ƴan aljanna....."
Daga nan ya fashe da kuka, Razhdeen ne shima ya durƙusa a gabansa tare da dafa shi ya rungume shi a jikinsa yana rarrashin sa,
Itama Baiwar ALLAH durƙusawa tayi tana kuka ta ce "Ramlat yau Amreesh ce a gabanki wacce muke yawan faɗa tsawon shekara guda bamu ga juna ba, nasan na ɓata miki rai dan ALLAH ki yafe mun, kin tafi kin bar mu amma nasan kina ji na, ki yafe mun ɓata miki rai da naita yi ashe ma haka duniyar take ba waran matabbata bane, ni na yafe miki kema nasan kin yafe mun ko? yawwa Ramlat ɗina nagode sosai..."
Itama fashe wa tayi da kuka ji take kamar ba da gaske bane mutuwar Ramlat....
Suna cikin wannan halin har aka shigo É—aukar gawa....
Duk mazan fita sukayi zasu yi sallar jana'iza daƙer Razhdeen yaja Roshan suka fita,
Matan kuwa duk a falo suka taru ana jimamin mutuwar Ramlat,
Amreesh tana zaune a ƙasin carpet ta kifar da kanta akan gwiwowinta sai sharar kuka take, tana cikin wannan halin taji ana bubbuga mata kai, a hankali ta ɗago da rinannun idanuwanta tana kallon yarinyar da take tsaye a gabanta tana faɗin "Mamma! Mamma!!...."
Amreesh cikin kuka ta rarumo ta tare da rungumar ta a jikin ta sosai tana kuka domin tasan É—iyar ta ce...
Haka take sumbatar da akan goshi tana shashshafa sumar kanta ji take kamar ta mayar da Afaf cikin cikinta domin ba ƙaramin ƙaunar ta take ba, da kuma kewar ta haka take kuka tana faɗin "Yarinya ta ki gafarce ni dan ALLAH, nasan nayi miki kuskure Please ki yafe wa Mamanki, na tafi na bar ki cikin jin haushi na, ban barki kin sha nono ba, ina ji kina kuka amma haka na tsallake ki yanzu kuma maimakon ki guje ni sai kuma kika yo kaina Allah sarki abar ƙaunataa, ga shi wasu suna haifan ɗansu suka rasu ko tsaya shayar da su basu yi ba, ni kuma da Allah ya bani dama da áron rai sai na tsallake nabar Jaririya ta wayyo Allah....."
Baiwar Allah ƙara rungumar Afaf tayi tana kuka...
Duk mutanen wurin babu wanda bai tausaya mata ba....
Itama Reemah (Ƴar Amana) tana zaune fuska da idanu duk sunyi jawur tsabar kukan da ta sha...
A wannan ranar Ramlat ta riga mu gidan gaskiya anje a bisine ta a cikin É—akin ta mafi daraja...
Ana zaman makoki har akayi kwana uku yau, daga can prison sun yo waya akan ko za'a kawo Maamie amma Mai martaba ya dakatar saboda a halin yanzu hauka take tuƙuru bata hayyacinta kowa ya ji abinda ta aikata sai yayi Allah wadar da ita, hatta ƴan uwanta sun ƙi karɓan ta suka ce ta cigaba da zama a gidan prison har ƙarshen rayuwar ta...
Kowa ya watse yanzu iya family ne suka rage, Roshan kuwa kullum Razhdeen ne a wurinsa domin har yau bai dawo taitayinsa ba, sai lissafe-lissafe yake yana faɗin "wani irin ƙaddara ce take bibiya ta? farkon masoyiya ta wacce na bata zuciyata gaba ɗaya hatsari tayi ta mutu ta barni har an tsayar da maganar Auren mu, masoyiyata ta biyu Allah yasa ba rabona bace itama bata mutu ba amma tsautsayi ya gibta a tsakanin mu sannan na samo wata itama Allah bai bar mun ita ba ta tafi ta barni, ta bi bayan wancan, wannan al'amarin daga jini nane babu wacce zan ƙara zaman Aure da ita gwara kawai nayi zaman kaɗaici ni kaɗai ....."
Haka yake ta wannan surutan har Allah yasa masa sukuni da tawakkali a cikin ransa, yau kwana bakwai da rasuwar Ramlat, akan kai wa Roshan jaririnsa sa'in-sa'in,
Amreesh kuwa kullum Afaf tana jikinta bata bari tayi nisa da ita domin yanzu wani irin ƙaunar ta ne ya shiga cikin zuciyar ta fiye da yanda take ƙaunar Razhdeen, itama Afaf har ta saba da Amreesh duk da wani sa'in ana shan gwagwarmaya da Reemah akan Afaf,
Ita Reemah bata so Afaf tayi nisa da ita itama Amreesh kullum tana riƙe da ita, haka Reemah zata shiga ɗaki taita kuka duk da ita Amreesh bata san meye a tsakanin Reemah da Afaf ba,
Itama Afaf idan ta kasance a wurin Amreesh bata son barin jikinta....
Da haka ake kan ɓoye wa Amreesh cewa Afaf yarinyar Reemah ce yanzu, ba'a son barin Amreesh ta san halin da Reemah take shiga akan Afaf idan bata jikinta.....
Typing âœï¸ Asmeetah writer
*MY ENEMY*
*TAKUN ƘARSHE*
*BOOK 3*
76 to 80
Baiwar Allah tana tsakiyar gado ita da ƴarta Afaf suna wasa tare sai ga Madam Parveen ta shigo, itama zama tayi a bakin gado tana sakin murmushi ganin yanda suke ta ƙyalƙyala dariya suna wasa,
Baiwar Allah juyowa tayi tana kallon Madam Parveen da murmushi akan fuskar ta ta ce "Mommy kin shigo ne?..."
Madam Parveen ta ce "eh daman akwai maganar da nake so nayi dake..."
Baiwar Allah ta ce "to ina jinki Mommy..."