← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 68

Sashe 53

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummy uwar masu gida ce ta buÉ—i baki zata yi magana yayi saurin katse ta da cewa "bana son abinda zaki ce duk ba ke kika fara mun kallon mahaukaci ba, meye zaki ce mun?..."

Pinky ƙare shi da kallo tayi taga yana masifar ma abun dariya bata san lokacin da ta ƙara tintsire wa da dariya,
cikin zafin rai Roshan ya É—auki pillow ya wurga mata,
Baiwar Allah girgiza kai tayi cike da mamakin taya kwalliya ta bayyana a fuskar Roshan alhalin bai san da kwalliyar ba, tunani tayi gwara ta sanar masa gaskiyar lamarin tinda ta fahimci bai san da shi ba,
buÉ—e baki tayi ta ce "Yaya R...."
É—aga mata hannu yayi ya ce "ke ma ki dakata mun haka? meyasa tinda na fito baki yi magana ba sai da kika gama mun kallon mahaukaci kafin zaki samu bakin yin magana..."

MINAL ta ce "kaga Yaya Roshan dan Allah kayi haƙuri....." tana kaiwa nan itama ta ƙara tintsire wa da dariya...

Roshan har ya buÉ—e baki zai yi magana suka yi motsin Abbah wanda ya shigo falo yanzu, yana faÉ—in "lafiya kuwa nake jin hayaniya?..."

Kowa ya yi tsumu da bakinsa sai Roshan wanda ya fuskanci Abbah tare da faɗin "Abbah yaran gidan nan sun haukace, suna buƙatar zuwa sakatiri..."

Abbah dai ya kasa sauƙar da idonsa akan Roshan sai baki da ya sake yana jinjina kai ya ce "Ahhh gaskiya a cikin kai da su za'a tantance mahaukacin da za'a kai shi sakatiri..."

Roshan ya ce "Abbah saboda iskanci sun gama rainani ni suke É—auka mahaukaci tunda na fito suke mun dariya, meye a jikina?..."

Abbah ya ce "ai dole suyi maka dariya irin wannan shirmen da ka aikata, kai É—an daudu ne?..."

Roshan cike da mamaki yake bin Abbah da kallo a ƙasin harshen sa ya furta "bayan an ƙira ni da mahaukaci sannan kuma du ɗan daudu?
daudu kuma?..."

Ammy ce ta riƙo hannun Roshan tana faɗin "kazo kuyi breakfast Roshan..."

Zame hannunsa yayi yana girgiza tare da faÉ—in "sai an sanar mun meye abun daudancin da nayi, shin an ganni ina É—aure da zani ne ko É—an kwali ko kuma kwalliya ku ka gani a fuskata..."

Abbah ya ce "au baka ma san da abun a fuskar ta ba?..."

Roshan fara shafa fuskar sa ya yi, sai ga Baiwar ALLAH wacce ta koma É—aki ta É—auko madubi tana zuwa ta saita masa, Roshan kallon cikin madubin yayi a ruÉ—e ya zaro ido waje yana furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allahumma ajurni fi musibati wa akhlifli khairan minha, taya hakan zata faru kuma?..."

Ummy ce ta ƙara kwashe wa da dariya har da tafa hannu,
cikin nuna fushi Roshan ya juya yana kallon ta tare da faÉ—in "nasan ba mai mun wannan aiki sai ke, meyasa kika mun haka?..."

Ummy ta ce "ni kuma? taya zan maka haka Yaya Roshan..."

Tsawa ya darara mata wanda tin da yake bai taɓa ɗaga murya wa Ummy ba sai yau,
"Ƙarya kike kin shiga kin same ni ina bacci shine zaki mun wannan shirmen, shugowar ki na biyu kika fara mun dariya bayan na farka, kin kyau kin ɓata mun fuska hankalin ki ya kwanta, bazan ƙara shiga shirgin ki ba balle ki sake mun wannan haukar..."

Yana kaiwa nan ya haura upstairs saman É—akin sa,
Ummy lokaci guda idanuwanta suka kaÉ—a sukayi ja, hawaye ne suka fara gangaro mata.
Baiwar Allah ta dafa kafaɗar ta ta ce "dilla kar kiyi kuka, kin san Yaya Roshan bashida hayaniya yau ne ransa yayi matuƙar ɓaci shiyasa amma zaki ga zuwa anjuma zai kula ki..."

Ummy tana kuka ta ce "saboda ni ya raina shine zai je nina masa kwalliya har yana mun tsawa? babu abinda na tsana illa mutum ya mun tsawa amma ba komai ..."

Hajiya Kilishi ta ce "to ke meyasa zaki masa kwalliyar?..."

Ummy cikin ɓacin rai ta ce "wai wa ya ce muku nina masa? tinda nake a cikin gidan nan na taɓa masa makamancin irin haka? shima hasashe kawai yayi ya ce ni ce, Amma sai Allah ya saka mun?..."

Abbah ya ce "ya isa haka kuje ku zauna akan dinning kowa ya yi breakfast..."

Ummy a zuciye ta nufi upstairs yanda zai kaita room É—insu tana faÉ—in "Ni dai bazan ci ba..."

Abbah ya ce "Uwar masu gida ki zo ku zauna ku ci abinci...."

Ta juyo tana faÉ—in "Abbah bazan iya cin komai a halin yanzu ba, zuciya ta tafasa take..."

tana kaiwa nan ta haura upstairs,

Su kuwa duk hallaruwa sukayi akan dinning sai da Abbah yayi musu faÉ—a akan dariyar da suka yi wa Roshan...

Roshan yana zuwa room É—insa kai tsaye bathroom ya shige, ya tsaya a wurin sink yana kallon kansa a cikin madubi ga yanda yake ta huci, ruwa ya kunna ya haÉ—a da sabulu ya fara wanke fuskar sa,
Ƴar Amana ce itama ta tsaya a gefensa tana murmushi ta ce "Allah sarki masoyi maimakon kayi farin ciki sai kuma ka shigo a cikin ƙunci? kar ka damu da abinda akayi maka ni ina tare da kai, kuma zan cigaba da sanya ka cikin Dawwamammiyar farin ciki mai ɗorewa har abada...."

Zuwa tayi ta tsaya ta bayansa sannan ya zura hannayenta ta gaba ta rungume shi sosai a jikin ta tare da kwantar da kanta akan bayansa..

Roshan wani irin yarrr yaji a jikinsa, tsinkar jikinsa ne yake tashi lokaci guda ya tsinci kansa a cikin wani hali ga yanda sanyi yake ratsa shi,
Lumshe idonsa yayi a hankali yake furta "me yake faruwa da ni ne?..."

Ita kuwa hannunta ta sa a cikin rigar sa tana shafa jikinsa a hankali lips ɗinta na motsi haka take furta "Yaya Roshan ina matuƙar ƙaunar ka, inasonka sosai da sosai har cikin zuciyata nake jin ka, bazan iya misalta yanda nake tsananin ƙaunar ka ba...."

Gaba É—aya jikinsa mutuwa yayi babu wani sukuni, haka yake É—ebo ruwa yana watsawa akan fuskar sa har sai da ta koma normal,
Lumshe ido yayi yana sauƙe numfashi daga bisani ya buɗe su a hankali idonsa ne ya sauƙa akan mirror wanda ya hango mace a tsaye ta bayansa kuma kamar fuskar Reemah ya gani, tana tsaye sai zuba masa murmushi take ta goga hannayenta akan ƙirji, bayan ta gama rungumar sa shine ta bayyana masa kanta a cikin madubi,
Zaro ido waje Roshan yayi a ruɗe ya waiga baya da sauri ya ga wurin wayam ba kowa, maida idonsa yayi cikin madubin nan ma ta ɓace wa ganinsa,
haka yake sakin numfashi ya É—ora hannunsa akan goshi yana faÉ—in "Oh my God! Reemah where are you, ki daina fito mun a mafarki ko gizo i just want to see you actual not your spirit please I beg you....."

Gaba ɗaya ya fita hayyacinsa lokaci guda, haka ya fara jan ƙafa a hankali ya fice daga toilet, yana fita ɗagowar da zai yi yayi ido huɗu da Ƴar Amana zaune akan kujerar mirror tana facing ɗinsa, haka take ta sakin murmushi idonta akan sa, shima sake baki yayi yana kallon ta, a hankali ya sau murmushi tare da faɗin "kin dawo gare ni Shalele? nagode! nagode!! nagode!!!..."
ya nufi wurin ta da gudu yana faÉ—in "Nagode..."
yana zuwa yasa hannu zai rungume ta sai yaji ya rungumi iska, tinin ta ɓace masa,
ganin ta ɓace yasa shi lumshe idonsa da ƙarfi cikin takaici, bai san lokacin da ya fara cakurkuɗa sumar kansa ya fara ihu, duk abubuwan da suke kan mirror haka yasa hannu ya faɗo da su, shima kansa mirror haka yasa hannu ya doko shi madubin ya dagargaje ihu yake bana wasa ba,
Ammy wacce lokacin ta iso bakin ƙofar sa da trey ɗin kayan abinci a hannun ta cike da tsoro ta tsaya tana jin yanda Roshan yake ta ihu, tana cikin wannan hali na tsoro sai ga su Abbah da Razhdeen da sauran ƴan gidan jin ihun Roshan ya karaɗe gidan,
Abbah yana zuwa ya tura ƙofar ta buɗe a hanzarce suka shiga ciki, suka tarar da shi a durƙushe ya kifar da kansa ƙasin carpet, hannayensa a cikin sumar kansa, Abbah yana zuwa shima ya durƙusa tare da sa hannu ya jawo shi jikinsa yana faɗin "Look Roshan me yake faruwa da kai ne haka? ka sanar mun idan abun na magani ne sai mu nema maka..."

Ɗagowa yayi da jajayen idanuwan sa yana kuka ya ce "Abbah! Abbah magani na ɗaya ne shine Reemah ta dawo gare ni, ina buƙatar ta a kusa da ni, meyasa zata rinƙa fito mun a spirit, ina son ganinta a zahiri, tana cikin ɗakin nan ku gaya mata ta fito, Abbah ka gaya mata mana..."

Abbah rungumar sa yayi sosai yana rarrashin sa,
Roshan sake ganin Ƴar Amana yayi a zaune a bakin gado itama sai kukan take tana son dawowa yanda take a zahiri amma sai dai ba halin yin haka domin akwai lokacin da aka yanka mata..

Roshan a ruɗe ya fara nuna Ƴar Amana da yatsa yana faɗin "Abbah gata can ku ce mata da dawo, bana son ta ƙara tafiya ta barni, kuka take Abbah ku ce ta daina tana taɓa mun zuciya ta, dan Allah Abbah...."

Abbah kuwa girgiza kai yake yana faɗin "Roshan ya haukace da gaske, Roshan ɗina ya haukace, ƙwaƙwalwarsa ta taɓu ya zan yi..."

Razhdeen shima durƙusawa yayi a gabansa yana ambaton sunan sa "twins kayi haƙuri zata dawo, kana ta cewa gana nan kuma mu bama ganin komai, gizo kawai take maka..."

Roshan ne yayi saurin katse shi da cewa "Ya zaka ce gizo take mun alhalin gana nan ina ganinta ido da ido, itama kukan take..."

Ammy durƙusawa tayi tana tofa masa Addu'o'i...

Hajiya Kilishi itama tana nan har da hawayenta tsabar tausayinsa da ya kamata tana riƙe da yaron Roshan wanda yayi wayo yanzu mai sunan Mai martaba wato Abubakar Sadeeq inkiya kuwa (Ra'ees)....
Chapter 53 · 0% Book details