← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 68

Sashe 27

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce "which something?..."
ta ƙarasa maganar tana kallon Baiwar Allah.

Baiwar Allah riƙo hannunta tayi tare da ɗagota suka fita waje,
Falon nan a cike da mutane maƙir anata kai kawo, haka Baiwar ALLAH tana jan mahaifiyar ta suka fice daga falon gaba ɗaya, kai tsaye falon Meeting ɗin Abbah suka nufa wanda ba kowa ne yake zuwa nan ba sai baƙin Abbah, baƙin ma manya-manya,
Madam Parveen ta kalle ta sannan ta ce "ke ina zaki kaini ne?..."

Baiwar ALLAH tana murmushi ta ce "You should see...."

Shiga cikin falon suka yi da sallama a bakin su, Madam Parveen ganin Mijinta Chief yasa ta washe baki cike da farin cikin ganinsa,
Baiwar ALLAH ta ce "daman cewa akayi na ƙira ki, ganan Daddy yazo..."

Madam Parveen jinjina kai tayi tsabar farin ciki ta ma rasa mai zata ce,
Sai Abbah dake wurin ne ya ma ta iso da cewa "ki zo ki zauna mana, kema Daughter zauna..."

duk zama sukayi, ga Mohandas da Rakesh su ma suna wurin, sai Chief da Abbah da kuma Madam Parveen da Baiwar Allah iya su kaÉ—ai ne...

Abbah ya ce "Alhamdulillah duk abinda yayi farko zai yi ƙarshe, idan akayi haƙuri da juna wata rana sai labari, yanzu dai Allah ya bada iko Chief Suraj shima ya musulunta ya dawo kan ƴaƴansa..."

Madam Parveen hannu tasa ta toshe bakin ta duk biyu tana zaro ido cike da farin ciki da kuma mamakin yanda ya amince ya musulunta,
Baiwar ALLAH itama murmushi take ta yi tsabar yanayin farin ciki da ta tsinci kanta.....

Mohandas da Rakesh su ma ba ƙaramin farin ciki suka tsinci kan su ba,
Chief yana zaune shima sai zuba murmushi yake domin yanda yaga iyalansa a cikin farin ciki sai abun ya bashi sha'awa...

Chief ya ce "Insha Allahu idan aka ɗaura Auren yau gobe zamu koma ƙasar U.S, zan bar Daughter ana hannun General har Allah yasa ta haihu....".

Baiwar ALLAH sai da taji wani irin bugun zuciya jin anyi maganar cikin ta, ita kwata-kwata bata so ayi maganar cikin domin ba ƙaramin takaici take ji ba, gaba ɗaya ta tsani cikin jikinta don babu yanda ta iya ne amma ta so ta raba cikin da jikinta, idan tana cikin farin ciki har mantawa take da Razhdeen amma idan akayi maganar cikinta sai ya faɗo mata a rai daga nan ne zata nemi farin ciki ta rasa,
yanzun ma shuru tayi ranta a matuƙar ɓace, kamar zata yi kuka ta ce "ni dai zan bi su mu tafi..."

Abbah ya ce "kiyi haƙuri Daughter zaki zauna da mu har sai kin haihu, bazaki koma ƙasar can da ciki a jikin ki ba, shin yanzu cikin ya shiga wata nawa?..."

Shuru Baiwar ALLAH bata bada amsa ba, sai Madam Parveen da ta furta cewa "yanzu five months..."

Abbah ya ce "to kinga idan kika kwantar da hankalin ki ma sauran wata nawa, Insha Allahu zan yi ƙoƙarin ganin na faranta miki sannan duk abinda kike so za'ayi miki, kinji ko?..."

Baiwar ALLAH kanta na kallon ƙasi sai ji tayi Madam Parveen ta dafa kafaɗarta, ɗagowa tayi tana kallon ta, Madam Parveen ɗaga mata kai tayi alamar tayi haƙuri ta zauna...

Sai da suka gama tattaunawar su tukun Abbah ya ce "toh masha Allah yanzu lokacin É—aurin Aure ya yi ku tashi muje..."

Duk tashi suka yi dake duk mazan a shirye suke waÉ—anda zasu fita É—aurin Aure,
Mohandas yana sanye da wata danƙararriyar shaddar sa yasha gariya ba ƙaramin kyau yayi ba, yana ɗauke da yaron sa shima yasha shadda irin na Babansa ga wata hula kalar shadda mai tsada suka fita domin a ƙofar gidan General za'a ɗaura Auren ga manya-manyan baƙi duk sun hallaru.

Rakesh ba ƙaramin kyau yayi ba dake tinda yake bai taɓa sanya manyan kaya ba, shadda ne mai bala'in tsada wanda suka sha anko duk Angwayen, duk fararen shaddodi ne a jikinsu da hular sa ko wanne yasha kyau,
Commender Rakesh da Yarima Ashmar da kuma Barrister Arash duk sun jeru suna takawa kamar masu tambayar ƙasa ana yayyafa musu ruwan kuɗaɗe...

Bayan la'asar da yamma kowa yana shirin tafiya wurin dinner...

Ɓangaren Amare masha Allah tufarkallah duk sun sha swezlace iri ɗaya masu bala'in tsada, da gyalellukan irin na kayan ba ƙaramin kyau suka sha ba, dake yaran duk babu laifi duk kalolin Camera ne da hasken su, musamman aka ƙira wacce ta ƙware wurin makeup ta zo ta tsara musu,
Pinky da Rukky da Ummy tare da Babbar yayar su Minal duk ba ƙaramin kyau suka yi ba na bugawa a jarida....

Wacce ta ɗara kowa a ɗaukan wanka ta ci gasar kwalliya hatta Amaren ma sai da ta ɗara su kyau wato Ƴar Amana, daman ita can ƴar wash ce kuma tayi kalar wash, wani irin dogon riga na net ta sanya har jan ƙasi yake, fari tass mai duwatsu a jere ta ko ina, rigar daga sama ta matse zuwa kunkumin ta kuma ya baje sosai, hannun rigar dogo ne mai net tana sanye da takalmi jinin sarauta mai tsini fari mai duwatsu ta sama, takalmin tana yin ƙwaƙƙwaran tafiya da shi zata faɗi tsabar tudun sa, ga anyi mata wani irin gyaran gashi na musamman, ga yanda yake sheƙi tsabar mayukan da yake, ta gaban gashi zuwa baya an ɗame yayi tsantsi sai aka ɗaure da revon mai duwatsu, zirin gashin kuma sai aka bar shi a murɗi-murɗin sa har gadon bayan ta, sai aka ɗora mata kambun sarauta akan ta na zinare, ga sarƙoƙin da aka jera mata wurin kala uku hawa-hawa da ɗan kunne su ma a jere hudi huɗu duk da ɗan kunne ga warwaraye da zobina da sarƙar ƙafa yanda kasan itace Amaryar kuma ta fito asalin ƴar sarki, tana fitowa falo idon mutane duk suka sauƙa akan ta wasu har suna tambaya cewa shin ita ce amaryar?...

Aunty Yolash mutanen fashion itama tana sanye da danƙareren shadda lace na bugawa a jarida, ba ƙaramin kyau tayi ba,
Duk matan gidan su ma sun sha wankan gezner matan Abbah da Matan Mai martaba...

Ga itama Madam Parveen ta sha wanka ta zura itama shaddar ta mai bala'in tsada da ɗaurin goggoro ga ta sha sarƙoƙi kalar shaddar akan wuyan ta daman ga wuya ba ƙashi ko ɗaya, bayan ta kammala shirin ta tsab zata fita ta kalli Baiwar ALLAH dake zaune a bakin gado sai kallon Mommynta take domin ba ƙaramin kyau tasha ba,
Madam Parveen cike da mamaki take bin Baiwar ALLAH da kallo ta ce "ke bazaki shirya bane kina ganin kowa yana ƙoƙarin fita zuwa wurin dinner party..."
Murmushi Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "Mom kawai ku je, ni bazan je ba domin idan naje ma zaman takura zanyi sannan ga cikina ya fito sosai ba yanda zan yi nayi gadara da shi...."

Madam Parveen kamar zatayi kuka tsabar tausayin É—iyarta,
Ta ce "shikenam amma bana so kina zaman kaÉ—aici, gashi duk gidan za'a tafi babu wanda za'a bari..."

Baiwar ALLAH ta ce "ni daman nafi son haka saboda bacci nake son yi sakamakon ciwon da kaina ke yi..."

Madam Parveen matsowa kusa da ita tayi tasa hannu tana shafar gefen fuskar ta tare da faÉ—in "shikenam Daughter ki kula mun da kan ki..."

Baiwar Allah murmushi tayi tare da jinjina kai, amma har cikin zuciyar ta taso itama taje, amma bazata iya shiga cikin jama'a a wannan yanayin ba saboda tana matuƙar jin kunyar haka, ga ciki ya fito sosai...

Madam Parveen fita tayi itama.

tana fita Baiwar ALLAH ta fara zubar da hawaye, ta juma tana zaune bata motsa ba tana tunanin yanda zaman ta zai cigaba da gudana a haka,
Iya sleeping dressing ne a jikinta sai dogon hijab da ta zura har ƙasi mai hannu...

Jin tashin motoci yasa ta miƙe a zabure taje jikin window ta tsaya tana kallon kowa da kowa, haka tana ganin yanda mutane suke ta shiga mota ana tafiya da su, motar Amare kam an daɗe da tafiya da su,
Wata mata ce tayi magana tana ɗaga murya tare da faɗin "iyyeeee masoyan juna kyau haka, ahh lallai Roshan dole ku ƙi fito wa da wuri..."

Baiwar ALLAH ce ta ɗan juyar da kai abinda ta gani ne ya tayar mata da hankali, ganin Roshan yasha farar gezner da gariya har ɗaukar ido yake, ba ƙaramin kyau yayi ba, most especially hular da ya sanya yanda kasan Balarabe ga takalmi sahun ciki fari da ɗan kwalliya ata sama...

Gefensa kuma Ramlat ce itama ta ɗau fashion ba ƙaramin kyau tayi ba, tasha lace mai tsadar gaske sannan ta ɗora alkyabba a kai har ƙasi yanda kasan sarauniya, ta ɗaura siririn sarƙa akan goshinta da wuyanta da ƙafarta duk da warwaraye da zobina, Ramlat asalin kyakkyawar mata ce Black beauty amma yanzu ta ɗan yi haske alamun ciki gare ta,
Haka suka jeru su biyu suna takawa a hankali cikin izzah,
wasu har photo ake ɗaukar su da video tsabar ba ƙaramin burge kowa suka yi ba,

Baiwar ALLAH idonta akan su ta window ga yanda hawaye yake zuba mata kamar da bakin ƙwarya,

Ramlat ce ta ɗan ɗago tana kallace-kallace idonta ya sauƙa akan Baiwar ALLAH ta window dake window a buɗe take ga kuma yanda ta ɗage labule,
ganin haka yasa Ramlat yin murmushi takai hannunta cikin na Roshan ta riƙe hannunsa duk akan idon Baiwar ALLAH,
Shi kuma gaba É—aya bai lura da hakan ba,
Ramlat ce ta ƙara matsawa jikin Roshan suna riƙe da hannun juna idonta akan Baiwar ALLAH,
cikin takaici Baiwar ALLAH ta juya zata koma ciki kenam taji an soma hura algaita tare da buga ganga maroƙa ne suka fara ƙirari da cewa
"to jama'a gimbiya sarautar mata ta fito, ya ke ƴar sarki, jikar sarki, tattaɓa kunnin sarki, gabanki sarauta bayan ki sarauta Ƴar sarki, Allah ya rabaki da sharrin mahassada masu son ganin bayan ki...."

Ramlat murmushi take tana wani ɗagun kai hannunta riƙe da na Roshan ganin ana mata ƙirari...
Chapter 27 · 0% Book details