Sashe 39
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Reemah ƙoƙarin tunowa take tana faɗin "ni gaskiya ban san su ɗin meya same su ba amma dai nasan cewa Aunty Baiwar Allah da Aunty Ramlat suna kan faɗa ne sai Aunty Ramlat ta mari Aunty Baiwar ALLAH, ni kuma bazan iya barin a mareta a gabana ba hakan yasa nima na rama mata marin har sau biyu, shine Aunty Ramlat ta ɗauki ƙwalba ta ƙwaɗa mun akai na...."
daga nan Reemah ta fashe da kuka...
Roshan zuciyarsa ba ƙaramin sosuwa tayi ba idonsa akan Reemah ya ce "Ramlat ce tayi miki wannan aikin? okay shikenam...."
Rai a ɓace ya tashi zai fita Abbah ya dakatar da shi da cewa "ina zaka je?..."
Roshan ya ce "zanje na same ta ne, na gaji da ita, ta fara takura mun..."
Abbah ya ce "bakada hankali ne, ka je ka ce mata mai? baka ga halin da take ciki bane? da wanne zata ji ga abinda yake cikin ta ta rasa shi kuma du kaje ka sake hawa kanta meyasa haka?...."
Roshan ya ce "Abbah baka ga halin da ta jefa su bane? kuma nasan duk laifin ta ne me zai kaita room É—insu alhalin ba shiri suke ba..."
Abbah ya ce "ita bata shiga halin bane? to ban yadda kaje ka sameta da wannan batun ba..."
Roshan ya ce "shikenam..." yana kai wa nan yayi ficewar sa...
A wannan Daren akayi wa Baiwar ALLAH Operation an ciro mata zureriyar yarinyar ta kyakkyawar balarabiya cikin ƙoshin lafiya, jaririyar sai kuka take ta sha ga sumar gashi ya rufe mata fuska tsabar yawansa...
Ita kuwa Baiwar ALLAH tana kwance bata san a yanda take ba, shin a duniya take ko a lahira duk bata sani ba domin ko alamar farfaÉ—owa babu....
Washe gari da safe an fitar da Baiwar Allah daga operation room an maida ta wani room ita da jaririyar ta amma sai dai har wannan lokacin bata farfaÉ—o ba,
Hajiya Kilishi ce take tare da ita, ga jaririya a kwance a cikin gadon jarirai an gyara ta an sanya mata kayan sanyi farare na jarirai masu kyau da tsada an rufa mata mayafin kayan, Roshan ne ya shugo da sallama a bakinsa, Hajiya Kilishi É—agowa tayi ta amsa, samun wuri yayi a bakin gadon da Baiwar ALLAH take ya zauna idonsa akan ta yana faÉ—in "har yanzu bata farfaÉ—o ba?..."
Hajiya Kilishi ta ce "wallahi ni ko motsi ban ga tayi ba..."
Jan dogon numfashi yayi tare da faÉ—in "Insha Allahu zata tashi bada jumawa ba saboda akwai alluran da aka mata..."
Hajiya Kilishi ta ce "Allah ya tashi kafaÉ—unta..."
taje ta ɗauko jaririya tana ƙudundune a cikin mayafi ta kawo wa Roshan tana faɗin "to ga ƴarku nan cikin ƙashin lafiya..."
Roshan hannu yasa ya karɓe ta da murmushi akan fuskar sa, ya ɗan buɗe mata fuska sai yamutsa ɗan ƙaramin bakin ta take kamar wacce take shan nono, fatar bakin jajawur, haka Roshan yake bin fuskar yarinyar da kallo, ganin sumar gashin dake kan yarinyar har zuwa kan goshin ta yasa ya kalli Baiwar ALLAH yaga itama irin sumar gareta ga gashin gira itama yarinyar hakane da zararan gashin ido, amma kamannin sak irin na Razhdeen ta ɗauko da hancin kamar an tsaga kara, ga yarinyar fara sol har ta fi uwarta da ubanta fari..
Roshan shi kaÉ—ai sai sakin murmushi yake,
A hankali ya furta "so beautiful..."
Hajiya Kilishi ta ce "ai kwana tayi tana kuka sai da aka kawo madara tasha kafin tayi bacci..."
Jinjina kai yayi sannan ya ɗago ta tare da kai bakinsa saitin kunnen ta yayi mata ƙiran sallah tare da jero mata Addu'o'i a kunnen duk biyun..
Hajiya Kilishi ta ce "amma har yanzu ba'a sanar wa Razhdeen yanada jini a ajiye ba ko?..."
Girgiza kai Roshan yayi sannan ya ce "bai san ta É—auki cikinsa ba, har sai ya dawo tukun ya gani da idonsa..."
Suna cikin hirar su sai ga Abbah da Reemah sun shigo, da sauri Reemah ta nufi kan Baiwar ALLAH ta zauna a kusa da ita dab da Roshan tana shafa fuskar ta tare da faÉ—in "Allah sarki Aunty nah ashe haka kika shiga wannan halin ban sani ba, Allah ya baki lafiya..."
ta É—ago tana faÉ—in "ina jaririyar tamun?..."
hannu tasa ta karɓe ta a hannun Roshan tana dariya, ganin yarinyar yasa ta calla ƙara tana dariya ta ce "wayyo kyakkyawar halitta, anya wannan mutum ce? kyan ta yayi yawa wallahi tafi mamanta da babanta kyau wallahi, ga fara ce sosai har ta fi ƴan india kyau, kamar balarabiya amma kuma kamar tafi su kyau su ma, ni na rasa gane kyan su wa ta ɗauko yarinyar nan, ga gashi tin yanzu ya rufa mata kafaɗu, amma sumar gashin Maman ta da babanta duk sunada sumar gashi don haka su ta ɗauko, amma kuma ina ganin kamannin Yaya Razhdeen a fuskar ta fa...."
Haka Reemah take ta maganganu marasa kan gado, su kuwa su Abbah sai dariya suke ta mata,
Hajiya Kilishi ta ce "ke wai ni zaucewa kika yi ne?.."
Reemah ta ce "ai dole na zauce Mommy Babba Yarinyar ta shiga mun rai sosai..."
A wannan ranar duk a asibiti suka sake wuni, Abbah ne kawai ya tafi, dake an sallami Reemah yanzu su biyu suke zaune da Baiwar Allah da ita da Hajiya Kilishi,
Ammy kuma tana É—akin da Ramlat take itama babu halin tashi sai an zauna da ita,
A haka har suka yi kwana uku a hospital a wannan ranar ne mutanen ƙasar Jidder suka zo, Aunty A'isha da Aunty Maimuna da kuma Ummu uwar masu gida yau anzo Nigeria sai murna take, duk sun zo asibiti duk wanda ya ɗauki jaririya sai ya yi hamdala, itama Ummy ba ƙaramin zaucewa tayi akan yarinyar ba, duk ta tafi da imanin duk wanda yazo ganin ta,
Baiwar ALLAH tana zaune jikinta ya fara warwarewa, tin da ta tashi bata ɗauki jaririyar nan ba idan aka bata kawar da kanta take gefe taƙi karɓa, sai dai taga yarinyar a hannun mutane amma bazata ɗauke ta ba, especially idan ta tuno ta hanyar da aka sameta sai taji ta tsani kanta da jaririyar gaba ɗaya, Nono kuwa ko sau ɗaya bata ba ta ba sai madara mai kyau da tsada ake bata..
Washe gari da safe Reemah da Ummy sune suke tare da Baiwar ALLAH yau sun ci alwashin dole sai Baiwar Allah ta É—auki jaririyar nan sannan ta bata Nono,
Babu yanda basu yi ba amma Baiwar Allah fur ta ƙi, daƙer da dabara da lallami suka sa Baiwar Allah ta karɓi yarinyar sannan Reemah ita da kanta ta buɗe rigar Baiwar Allah takai bakin yarinyar sai tin ƙirjinta, da haka har yarinyar ta kama, babu yanda Baiwar ALLAH ta iya haka ta bar yarinyar ta sha nono har sai da ta ƙoshi tukun...
Ummy ce ta kalli Reemah sannan ta ce "ni bakije kin duba jikin Aunty Ramlat ba koh?..."
Reemah ta ce "ina ruwana da ita bazan je ba, naji wai har yau kuka take saboda cikin ta ya zube ko...."
Ummy ta ce "ai dole tayi kuka ɗora rai akan cikin, kuma ya wuce zube wa sai dai ɓari domin cikin ya fara zama mutum fa kuma naji tana cewa ke kika yi silar ɓarar mata da cikin..."
Reemah ta ce "ai dole nasan sai ta ɗora mun sharrin nan, kinga fa ciwon goshi na ita ta kwaɗa mun ƙwalba fa har sai da bottle ɗin ya fashe da yanzu ƙwaƙwalwata ta juye...."
Ummy ta ce "ai kuwa ran Mamanki ba ƙaramin ɓaci yayi ba har sai da tayi kuka, wai ma duk mai ya jawo hakane ?..."
Reemah ta ce "au ita bata sanar akan meye akayi faÉ—an ba?..."
Ummy ta ce "wallahi kuwa ita matsalar ta ta faÉ—a..."
Reemah ta kalli Baiwar ALLAH wacce take zaune tana jinsu ga yanda ta kwantar da Æ´arta a gefen ta, Reemah ta ce "ki ji Aunty Baiwar Allah..."
Baiwar ALLAH jinjina kai tayi ba tare da ta furta komai ba..
Ummy ta ce "akan Yaya Roshan ko?..."
Reemah ta ce "zancen maganar kenam, ita ta jawo ruwa sama, ruwa kuwa ya mata shegen duka, ba gashi ta jawo abinda zai dame ta yanzu ba tinda ta sanadin haka ta rasa cikin da take burin haifan sa..."
Suna cikin hirar su sai ga Roshan ya shigo tare da faÉ—in "shikenam in an haÉ—u an ringa tsegumi kenam ko?..."
Murmushi Ummy tayi ta ce "Yaya Roshan kenam ka ji abinda muke cewa?.."
Roshan ya ce "ina zan tsaya sauraron shirmen ku nan da baya ƙare wa..."
Reemah kawar da kanta tayi tana kallon gefe fuska a haÉ—e,
Roshan ya ce "ƙanwata ya dai kwana biyun nan nake ganin ki a haka?..."
Juyowa tayi ta harare shi sannan ta ce "Ni ba ƙanwar ka ba ce, ban san ka ba baka sanni ba.."
Roshan ya ce "Ni ban isa nace ban sanki ba Ƙanwata, amma me yayi zafi haka, idan nayi laifi a gafarce ni..."
Reemah ta ce "Yaya Roshan ba ka ce baka sona ba, to tinda baka sona sai ka daina kulani, duk wanda baya sonka ai maƙiyin ka kenam..."
Roshan ya ce "subhanallahi maƙiyi kuma? ni na isa nace bana sonki Shalele?..."
Reemah ta ce "a gaban kowa ka sanar wa Abbah cewa baka Sona, kai da iya matarka zaka zauna har ta samu bakin yi mana rashin kunya ...."
Murmushi Roshan yayi sannan ya ce "wannan ai akan Aure yake tambayata, kinga kuwa ba soyayyar Aure muke ba..."
A zabure Reemah ta miƙe tsaye cikin kuka take faɗin "to ni Soyayyar Aure nake maka Yaya Roshan, ina sonka ina son Auren ka..."
Daga bakin ƙofa suka ji ance "to kuwa bazaki taɓa Auren sa ba dan ubanki wawuyar yarinya marar sanin kara..."