Sashe 9
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta daɗe idonta biyu, kafin bacci ɓarawo ya sace ta. Sai dai kamar a zahiri, kuma kamar a mafarki ta fara jin hayaniya a kanta. Ba ta gama tantance hayaniyar mece ce ba, ta ji wani abu na wucewa ta saman roofin ɗakin. Idan abin ya daki kwanon ɗakin da abin da yake takawa, tamkar kwanon zai buɗe ya faɗo musu a ka.
Ayshercool
08081012143
55
Wata irin yinƙurawa Nana ta yi, cikin azama da tashin hankali ta kifa a kan Sayyid, saboda kar abin da yake takun koma mene ne, ya faɗo masa a ka.
"Ma vie" ya furta da ƙyar can ƙasan maƙoshinsa. Ta ɗago ta fara laluben fuskarsa a cikin duhu.
"Sayyid, ba ka ji wani abu zai faÉ—o mana ba?"
"A'a"
Ta sake cewa maganar ta dawo "Maganar ta dawo?"
"Eh"
"To sannu" ta furta a hankali cikin tsoro, ta mayar da kanta kan ƙirjinsa a tsorace. Sai dai kamar dole, ta ƙarfin tsiya, wani baccin ya sake awon gaba da ita, tana cijewa da ƙoƙarin hana idonta sake yin bacci, amma abu ya ci tura, baccin ya kuma awon gaba da ita.
Ganinta ta yi a tsaye a tsakiyar ɗakin, itakaɗai babu Sayyid. Ana ta cigaba da hayaniyar da ba ta gane me ake faɗa. Ta din ga waige-waige tana tunanin ina ya shiga haka? Sai dai ba ta gama tunanin ba ta ji muryoyi daban-daban suna faɗin "Lale da manyan baƙin garin Buda. Barka da zuwa." Sai kuma ta ji ana dariya tare da ci gaba da hayaniya.
Idonsa biyu, yana jin yadda ta yi wa hannayensa wata irin muguwar damƙa, ta nutsa faratanta a jikin fatarsa, dan tuni ya karaya jini ne yake fita daga fatar tasa. Ta din ga juya kanta a kan ƙirjinsa tana kuka tana faɗin "A'a, mu ba baƙin ku ba ne ba, ba gurinku muka zo ba, mu ba baƙinku ba ne" jin ta fara ɗaga murya, ya sanya ya murginata gefensa, ya zame hular kanta yana shafa gashinta a hankali, tare da hura mata iskar bakinsa a kunnenta. Daga haka sai ta yi shiru, ta ci gaba da bacci.
****
Barira sai da ta sha jini leda biyu a Asibiti da allurai da magunguna, amma tana komawa gida, abu ya ƙara rikicewa. Domin kuwa babu damar ta sanya haƙarƙarinta a ƙasa ta fara bacci, wannan jibgegiyar magen za ta bayyana, su hau kokowa da ita. Duk sai magen ta yayyage mata fuska da jikinta. Idan ta tashi sai ta ji jikinta na yi mata wani irin zugi da raɗaɗi.
Ta cewa mijinta ita fa ba za ta koma wannan gidan ba. Ya sanar mata an tashi su Nana, daga su sai su Sajida a gidan kamar da, amma ta hau kujerar naƙi ta ce gidan ne ba za ta koma ba. Shi kuma ya ce sai dai ta yi ta zama a gidansu, dan ba shi da kuɗin kama wani gurin.
Shukura ce tare da Hajiya Amina, suke hira. Ta je yi mata sannu da zuwa dawowar da ta yi daga umara. Alhaji Zailani ya yi sallama ya shigo falon.
"Daddy sannu da zuwa"
Ya ƙare mata kallo ya ce "Yauwwa, mara tawakalli da ba ta san ƙaddara ba" Ta yi shiru tare da sunkuyar da kai. Duk irin kashedin da nake yi miki, da rarrashin da na yi miki, ba ki ji ba abin har ya kai ki dizga bawan Allah nan, a gaban mutane kina cewa yana kashe mutane, idan ya yi ƙarar ki kina da shaida a kan haka?"
Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. "Tambayarki nake yi" Ta girgiza kai alamar a'a.
"Amma ki ke wannan iƙirarin, maimakon ki mayar da hankali a kan fatan Allah ya raya na gabanki, ya ba ki wani. Ba ki kyauta ba" Hajjya Amina ta yi ta kallon Shukura ko za ta ba shi haƙuri, amma ta yi mursisi.
Ko da ya shiga É—akinsa, babbar rigarsa ya cire saboda azabar gumin da yake yi. Dan tun da Doctor Sharif ya gaya masa ga yadda suka yi da Shukura hankalinsa ya yi mummunan tashi. Ya kuma sake jaddada wa Sharif, muddin wani abu ya fita to babu hannunsa a ciki. Kuma likitan ya yi masa bayanin process É—in da ya bi, abu ne mai wahala a gano. Ya yakice gumi ya nemi guri ya zauna.
Hajiya Amina ta ce "Me yasa ba ki ba shi haƙuri ba, kina kallon yadda ya yi fushi?"
"Mummy, duk wannan abubuwan kamata ya yi a tsaya a saurare ni, a kuma fahimce ni. Da hankalina fa ta yaya zan din ga iƙirarin an kashe mini ɗa haka kurum. Mummy ranar da za a yi mini aiki, kina bacci cikin dare, na kasa bacci saboda damuwar da nake ciki, aka buɗe ƙofar ɗakin, aka zo aka kama hannuna aka laluba cannula, aka yi mini wata allura a cikin duhun nan. Tun da aka yi mini allurar nan. Na ji kaina ya fara juyawa, ina neman na fita hayyacina, duk iya ƙoƙarina na kasa, na ji jikina na ƙamewa kamar zan yi jijjiga. Saɓanin da da idan za a yi mini allura cikin dare, za a ƙwanƙwasa ɗakin, sai kin tashi kin ce a shigo tukuna, a kunna ftila a yi mini"
Mummy ta ɗan yi shiru, cike da mamakin me yasa tuntuni ba ta faɗa ba, amma domin kawo ƙarshen maganar, sai kawai ta kawo gigin ciwo ne ya sanya ta ga haka a lokacin. Dan haka ta ce "Duk da haka wannan ma ba hujja ba ce, ke da ki ke fama da ciwo ina za ki tantance wani abu ma. Dan Allah ki bar zancen nan"
Shukura ta yi murmushi ta ce "Shikenan, na bar shi"
Sai kuma ta sake cewa "Mummy, Nana shiru, ni yakamata ki kwatanta mini gidan da suke na kai mata Haidar"
"Gidan Alhaji Garba giwa ne fa, kuma fafur babanku ya hana ni zuwa ban san dalili ba" Dummm! Ƙirjin Shukura ya buga, ta ce "Saboda ne ya hana ki zuwan?"
"Ban san dalili ba, za ki je ne? Sabon gidansa nan Kano"
Shukura ta ce "Wace matar ce a gidan?"
"Halima ce, uwar gidan sa"
Shukura ta girgiza kai ta ce "Ba zani ba, gidansu tsohuwar matar Sagir ce"
Mummy ta waro ido ta ce "Ke haba? Dama 'yar Halima ce matar Sagir É—in?"
"Eh mana"
"Ikon Allah, da na ce wa Daddy, ya taimaka musu, a samo wa mijin Nana, gurin da zai yi gadi, su samu su zauna, shi ne aka samo gidan"
Shukura ta ce "wai canza masu gadi ku ka yi ne?"
"Ina fa, ina nan cikin gida, daga baya ma Yusuf yake gaya mini. Wai zuwa aka yi da motoci da alama daga ƙasar su ne ma, motocin duk rubutun fransanci aka kwashe su kaf, kuma babu wanda aka yi wa bayanin me yasa"
"Ikon Allah, kuma ba laifi suka yi ba?"
"To ina zan sani, ina nan cikin gida?" Suka ci gaba da tattaunawa da jajanta lamarin. Har wayar Nana suka jarraba kira, su ji ko ita nata mijin yana nan, ba a kama shi ba amma wayarta ba ta shiga sam.
****
Da safe Nana ta tashi, ta fara alwala sannan ta zuba wa Sayyid ruwan da yara suka ɗebo musu jiya, dan gidan babu ruwa. Ya yi alwala a ƙofar ɗakin, sannan suka koma ciki ya yi salla. Sai dai bai ga alamun ta san abin da ta yi cikin daren jiya ba.
Ƙarfe tara da rabi, Uwani ta aiko yara da kunu da 'yar tsala aka kawo wa su Nana.
'yar aiken ta ce "Uwani ta ce idan kin gama karayawa, wai ki je"
Nana ta ce "To, zan zo a ce mata mun gode sosai da sosai, Allah ya biya ta"
Ta koma ta zauna a gaban Sayyid ta ce "Sayyid, ka ga kunu ne da 'yar tsala za ka iya ci, ko na nemo maka wani abin?" Ya girgiza kai.
"To za ka iya cin wannan É—in?" Ya gyaÉ—a mata kai.
Kunun tsamiya ne, na daka ba niƙa ba, ya sha kayan ƙamshi, sai dai babu suga ko kaɗan a ciki, ga tsamiyar nan cau har ka.
Ƙuli-ƙulin 'yar tsalan, ya sha barkono, ta zuba masa a kofi ta ba shi. Ya saka hannu ya karɓa.
Tun da ya yi kurɓa ɗaya, ya yi shiru. Nana ta ce "Za ka iya sha kuwa?" Ya jinjina kai ya ci gaba da sha, saboda Nana.
Ya haÉ—a da 'yar tsalan nan, duk da ba son Abincin yake yi ba.
"Sayyid, idan ba zaka iya cin Abincin nan ba, ka bari na nemo maka wani"
Ya É—aga kai ya kalle ta, sai dai ba baki, dan haka ya harare ta, ya ci gaba da cin abincin.
Ta yi murmushi ta ce "Ni ka ke harara ko, aishikenan"
Ya gama karyawa, ta saka É—ankwalinta, ta goge masa bakinsa da hannunsa. Ta ce "Bari na je kiran da Uwani take yi mini, daga nan na saka a raka ni, na É—an yi mana sayayya, dan na san dole za ta daina bamu Abinci yau da gobe sai Allah"
Bai ba ta amsa ba, ya jingina da bango, saboda yadda yake jin daÉ—in hakan, yana lumshe ido.
"In je?" Ya yi mata shiru, kuma yaƙi yi mata wata alamar, da za ta gane ya amince ko a'a.
Cikin shagwaɓa ta ce "Sayyid" ya kawar da kansa gefe, ya ƙi buɗe ido.
"Duk da maganar nan ɗaukewa take yi, amma dai tun asalinka miskili ne, ina ta magana ka ƙi kula ni, ni ce fa rayuwartaka guda ka ke wa haka?"
Murmushi ya yi, tare da saka hannunsa a cikinta, yana shafawa a hankali.
"Wai ba za ka kalle ni ba?" Ta yi maganar tana juyo da fuskarsa. Ya ƙara rintse idanunsa, wai ba zai kalle ta ba. Nana ta din ga dariya.
Ya ja jikinsa a hankali, ya kwanta a kan cinyarta, ya zuba wa cikinta ido, tamkar zai gano abin da yake cikin.
"Idan na haihu na ga yadda za a yi, da kai da jaririn wa zai bar wa wani cinyar nan" Ta yi maganar tana shafa gashin sa.
*****
Hajiya Sa'a ce take cin abinci, tana kallon Jamila, da take ta cakala kaÉ—an-kaÉ—an.