Sashe 19
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana dariya ta ce "Wai Sayyid ni fa ban gane maka ba kwana biyun nan, rigima ka ke ji, amma Alhamdillah alamun sauƙi ne da nasara.
Aka shiga kwana na huɗu, tana shafa masa tofi tana kunna masa hayaƙi ta gudu ta bar shi a ɗaki. Yau sai dai ta gama shafa masa, za ta gudu ya riƙe ta gam. Duk yadda ta so guduwa ta kasa. Ya kalle ta yana murmushin mugunta. Aikuwa jikinta ya fara tsuma ta saka masa kuka, jin yadda gaba ɗaya duniyar take juya mata, tana shirin fita hayyacinta.
Har dare ya yi suka kwanta, ba ta kula shi ba, dan gaba É—aya jikinta ya mutu murus, babu abin da yake yi mata daÉ—i.
Can cikin bacci ta ji ya yi magana"Ma viee"
"Sayyid"
"Na'am"
"Magana ka yi?"
"Eh, yanzu na ji ta zo"
Ta tashi zaune cikin murna tana taɓa shi ta ce "Alhamdillah Sayyid, Allah ya ƙara lafiya"
"Taɓa ni na ji, ko zan ji wani abu"
Ta ce "Ga shi ina taɓa ka"
Ya ce "Ba wannan ba" ya yi maganar yana rungumota da duk hannayen sa biyu.
"Sayyid hannunka ya warke?" Ta tambaye shi a kiÉ—ime cikin farin ciki.
"Eh" ya amsa a taƙaice yana ƙoƙarin yin wani abin daban.
"Bari na lalubo waya na haska ka na gani"
"Kar ki haska ni"
"Me yasa ganinka fa zan yi, hannun zan gani"
"Kar ki haska ni" ya sake maimaitawa.
A ɗan tsorace ta ce "Anya kai ne?" Ya yi dariya ya ce "A'a Ƙaisar ne. Idan ma ba ni ba ne, ai kina ganewa"
Ta yi dariya ta ce "Wai Sayyid ya haka ne? Ka tsaya mu yi murnar ka samu sauƙi"
Ruf ya rufe bakin Nana, bayan ya tabattar da lafiyarsa ta dawo. Duk da ya yi farin ciki da miƙewar da hannunsa ya yi, wanda farkawa ya yi daga bacci kawai ya ji hannun ya saki, duk da ya yi masa wani iri babu daɗi.
Bayan wani lokaci, ya saka hannunsa ya É—aukko fitila a gefen Nana, ya kunna ya haske ta. Rufe fuskar ta ta yi, ta juya bayan ta da sauri.
Ya kwanta a jikinta yana yi mata raɗa a kunnenta. "To tashi ki haska ni ki ganni, kin ga hannun" Nana ta ƙare rufe fuskarta a fulo, ta ƙi ɗagowa.
"Kin ga" ya yi maganar yana taɓa ta da hannun. Shi wannan abubuwan da take yi ma, ba ƙaramar dariya take ba shi ba.
Da ƙyar ta tashi, tana kallon hannun nasa da take ganin, tamkar almara ya miƙe.
Ta ja hannun ta ga ya miƙe, ta ce "Kuma ba ya ciwo?"
Ya girgiza kai yana taɓa hannun ya ce "Ba ya yi"
"Allah ya ƙara maka lafiya mai ɗorewa"
"Amin. Na gode. Na gode" ta rufe bakinsa ta ce "Ya isa haka. Allah za mu godewa"
"Alhamdillah. Amma ya zama dole na yi godiya, kuma na jinjina miki, saboda" bai ƙarasa maganar ba ta cije shi a kafaɗarsa, kamar yadda ya kan yi mata, idan yana jin raha.
Kamar ba su ne cikin zullumi da damuwa ba, suka koma shagalinsu. Dare ya tsala amma tamkar rana a gare su, ƙarshe ma zaman hira suka zauna. Da anjima sai ta tattaɓa hannun nasa, dan ta tabattar lafiya kalau yake bai kuma maƙalewa ba.
Haka suka kwana cikin nishaÉ—i, da kewar juna.
Da safe ta gama abin da take yi, ta shigo da maganin da take shafa masa, ya kalle ta ya ce "Wallahi ki ka zo kaina da wannan abun, sai na yi miki wanka da shi, ke ma na kulle ki a É—akin, ki ji abin da nake ji" Ganin yadda ya haÉ—e rai ya sanya ta rabu da shi.
Wunin yau ma lafiya suka yi shi, babu damuwa, duk da jikinsa babu ƙarfi sosai.
Ya ci Abincinsa ya yi sallolinsa babu wata matsala. Sai dai yau ma Nana ba ta samu rintsawa yadda yakamata ba, sai da ta san ya warke. Wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.
Wani mutum ta gani a tsaye a jikin bishiya, ya lulluɓe jikinsa da mayafi. Ta yi tsuru tana son ta ga waye haka.
Yana ɗaga mayafin ta ga fuskarsa, ta ja da baya, ta tsorata. Tsohon nan ta gani, jikinsa yana ta fitar da wani irin baƙin abu, fuskarsa ta yi baƙi ƙirin, ga hayaƙi na fitowa daga cikin bakinsa da hancinsa gaba ɗaya siffarsa ta yi muni babu kyawun gani.
Sai da Nana ta ja da baya, cikin tsoro da razani.
"Kin tafka kuskure yarinya, kuma za ki san kin taɓa Giyaz bin Jaddul Jinn. Babu wanda ya taɓa karya alkadarina, abu ya yi tasiri sosai haka a jikina. Dan a duk lokacin da aka yi yinƙurin illata ni, barin guri nake yi. Sai dai kash kina ɗauke da abin da aka yi mini tarko da shi a wancan karon." Ya jefo mata wani littafi jikinta ya ce "Ga shi nan, littafin da ki ke ta bibiya sai kin ji ƙwaƙwaf, ki ƙarasa karantawa kafin na je na yi jinya na dawo. Amma ki sani dawowata ba za ta haifar miki da ɗa mai ido ba. Domin illar da ki ka yi mini sai na ninka wa mijinki, wahalar da ki ka sha ba ki ga komai ba." Kawai ya ɓacewa ganin Nana.
Nana ta kalli littafin hannunta, na gurin Ƙaisar ne, da take ta bibiyar sai ta karanta hanata.
Da kansa littafin ya buÉ—e, a daidai shafin da tsaya da karantawa wancan karon.
Jiki na tsuma ta ci gaba da karantawa.
Jama'ar da suke gurin girkar, wasu suka watse a dalilin gakin sarkin Aska ya bayyana a gurin, kar ya gansu ya hukunta su. Bayan musayar yawu a tsakanin Duna da uban duƙusa, Sarkin Baka ya yi girgiza ya ɓace.
Uban duƙusa ya saka aka ɗauki kakan Lanti, a ka kai shi gida. Ita ma Lantin tana zuwa gida ta faɗi ƙasa.
Ba ta sake farfaɗowa ba sai washegari. Sai dai bayan farfaɗowarta, ta tarar da kakanta cikin mawuyacin hali, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba.
Cikin damuwa mijinta ya ce "Lanti sai da na gaya miki ina jin tsoron wannan abun, ki ka ce babu komai, ina tsoron kar rikici ya ɓarke a garin nan"
"Babu rikicin da zai ɓarke, ka kwantar da hankalinka, ni dai kawai fatana na kawo ƙarshen Sarkin Aska."
Kakan Lanti da ya yi tari, sai aman jini, dama ga jikin tsufa, ya zamana ko tashi baya iya yi saboda buguwar da ya yi. Kwanaki huɗu da faruwar lamarin, Lanti tana yi masa hayaƙi da ganyen ɓaure. Ya riƙo hannunta ya ce "Ya ke jikata, ki sani na yi miki Girka da babban Aminina, kuma ya ɗaukar mini alƙawarin ba ki duk wata kariya, da zama mai hidima a gare ki, kuma ya yi alƙawarin bawa zuriyarmu kariya daga cutarwar miyagun Aljanun cikin su. Dan haka a duk lokacin da ki ke buƙatar ganawa da shi, ki sanya kayan saƙin ki, ki ɗaura gurunki. Sai dai kar ki kira shi a guri mai ƙazanta, ba ya son zama a guri mai ƙazanta, kuma ba ya zama a guri mai najasa. Sannan 'yar ki Duna ne ya shafe ta, kuma ga wannan abu da ya faru, abu ne mawuyaci ta warke, sai dai idan uban duƙusa ne ya samo mata magani. Ni na san ba zan rayu ba, Duna ya riga ya yi mini illa, dan haka ki kula da mutanen Buda. Yana gama faɗin haka wuyansa ya karye. Lanti ta fashe da kuka, ya buɗe baki yana son ya yi mata magana amma ya kasa, har ya daina motsi ya mutu.
Nana ta yi kuka ba kaÉ—an ba, da mutuwar Kakanta.
Ƙaisar ne a tsaye a kan wani dogon tsauni, gabansa kuma Giyaz ne, da yake kamannin da shi sak, tamkar ya yi kaki ya ajiye.
"A kan me za ka je ka aikata wannan shirmen da ka yi? Ko har ka manta da cewar fansarmu za mu É—auka a kan abin da mutanen nan suka yi mana?"
"A'a Giyaz, mutanen nan ba su ne ainihin waɗanda suka fara rigimar nan ba, kuma ɓarnar da aka yi musu ta yi yawa. Babu amfani rashin zaman lafiya da tashin hankali. Kuma ka duba irin cutarwar da abokinka Duna ya haɗa kai da sarkin Aska yake yi wa mutanen garin nan. Yakamata a zauna lafiya, haɗa kai da bil'adama ana cutar da jinsinsu ba zai haifar da ɗa mai ido ba."
"Rufe mini baki Ƙaisar" Ƙaisar ya kalli mahaifinsa jin ya kira shi da sunansa na yanka, saɓanin sunan da yake masa kara da shi, na uban duƙusa wanda da shi ake kiransa saboda kara ga mahaifinsa. Dan duk cikin bataliyar 'ya'yan da ya haifa, ya fi ƙaunar sa. Ya ɗora da cewa "Kar ka manta abin da suka yi wa Mahaifina Jaddul Jinn wanda yake kaka ga duk wani Aljani da yake nahiyar nan, da yadda ake girmama shi, sai mene ne dan a azabtar da su. Dan mene zaka hau kan bil'adama a matsayin bawa, duk da kasancewar ka ƙasaitaccen matashin aljani da ake ji da shi a jinsinmu" ya yi maganar cikin ɗaga murya, muryarsa na amsa kuwwa a ilahirin dajin.
"Zaman lafiya da kwanciyar hankali, mu rayu mu da su babu cuta babu cutarwa. Lalata musu amfanin gona, sanya musu rashin lafiya da makamantansu duk ba zai sanya ku huce ba, tun da waÉ—anda suka yi laifin na sun mutu basa nan"
"Uban duƙusa yanzu ka fifita bil'adama a kan ni mahaifinka?"
"Ko É—aya, sai dai ka san muna mutunta yarjejeniya. Mun yi yarjejeniya da abokina, zan ci gaba da bawa zuriyarsa kariya, zan kula 'yar sa zan din ga kawo mata magunguna tana bayarwa. Kuma ya yarje mini ci gaba da yi wa zuriyarsa hidima, da bayar da magani ta hanyar waÉ—anda aka haifa da tauraron 'yar sa Lanti"