Sashe 69
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sultan ya sake numfasawa ya ce "Hammad, haryanzu babu wani abu da ka iya tunawa bayan fara rashin lafiyarka?"
"Ban tuna komai ba"
Ya É—ago hannun Hammad ya ce "Bamu san fa inda zobenka yake ba haryanzu, abin ya dame ni, ina tsoron a farga da babu zoben nan, ina tsoron abin da ka iya biyo baya, idan aka gano babu zoben nan"
Ya kalli yatsun nasa ya ce "Abiena, duk abin da Allah ya ƙaddara zai faru dole zai faru ka daina damuwa. Ni yanzu ina mamakin Mamudu bai san ina Agadez ba ne?"
Sultan ya É—an ji dumm, sai kuma ya ce "Ni na hana a sanar da dawowarka, sonake ka samu lafiya sosai, amma dole za a sanar masa da dawowarka"
Imam ya ce "Ni zan je na same shi, ya ganni a bazata"
Sultan ya ce "A'a zan saka a sanar masa, zai zo har gida ya same ka"
Ya ji daÉ—in kasancewa da mahaifinsa, sai dare sannan suka tafi gida tare da Asal. Duk wunin da suka yi bai ci komai ba, har suka koma gida.
Nana ta kammala aikinta na yau, ta yi wanka tana zaune a É—akinta, tana karatun Alkur'ani. Kawai ta din ga jin kamar akwai wani abu da ba daidai ba.
Ta ajiye Alqur'anin ta tashi ta tafi É—akin girkin Abincin Imam.
Wata mata ta gani ta kawo kai za ta fita daga kitchen É—in, alahalin babu wanda yake shiga sai ita sai Balaraba ko Asal.
Nana ta ce "Baiwar Allah lafiya kuwa?"
"Saƙo ne aka bayar, ke ce mai girkin Imam, dan haka ke za ki kai masa"
Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wace ce ke? Kuma waye waye ya bayar da saƙon, kuma saƙon mene ne?"
"Ba ni da lokacin amsa tambayoyinki, babu ruwanki da kuma saƙon na mene ne, ga shi can na ajiye miki a cikin kitchen ɗin, kaiwa ne kawai naki"
Nana da mamaki ta bi matar ta kallo dan ba ta taɓa ganinta a gidan ba.
Ta shiga kitchen É—in da sauri, ta fara kalle-kalle tana tsoron kar ta je wani abin cutarwa ne.
Wani ɗan kwando ta gani ƙarami, an nannaɗe shi ba za ta iya ganin mene ne a ciki ba.
Wata zuciyar ta raya mata, ta kwance ta ga mene ne a ciki, wata kuma ta hana ta,sai dai har ta gama grkin dare tana kallon kwandon tana tunanin mene ne a ciki? Waye zai bayar da saƙo babu suna, kuma me yasa sai ita za ta kai? yanayin saƙon dai kamar babu gaskiya a lamarin.
Da fargaba ta haÉ—a da É—an kwandon ta nufi sashinsa gabanta yana faÉ—uwa.
Yau shikaÉ—ai ne a zaune, babu Asal. Duk da ruÉ—ewar da yake yi idan ya ganta, amma ya ji daÉ—in ganin ta kawo masa Abinci, dan tun safe bai sake cin komai ba.
Sai dai yau ba iya faɗuwar gaban yake ji ba, har da wata ƙara, mara daɗin ji makamanciyar wadda ya din ga ji daren da zai fara ciwo.
Ta ajiye kwanukan ta ce "Barka da yammaci Sayyid, fatan ka na lafiya."
"Alhamdillah" ya furta ba tare da ya shirya hakan ba, yana mamakin daga ina wannan sautin yake. Ita kanta Nana ba ta zata zai amsa mata gaisuwar da ta yi masa ba.
Ganin babu Asal a gurin, ya sanya Nana zuba masa Abinci da shayi. Ta kalle shi duk da yadda yake yi mata wani irin kwarjini da a baya bata taɓa zaton yana da shi ba ta ce "Ko yanzu ma sai na ɗanɗana?"
Ya girgiza kai alamar a'a. Ya sauka daga kan kujerar, yana jin ƙarar nan na ci gaba da addabar kunnuwansa.
Cike da son basar da abin da yake ji, dan gujewaa sake faruwar abin da ya faru a wancan karon, ya yi Bismillah ya fara cin abincin.
Duk da a takure yake da yadda take kallonsa, kuma ba zai taɓa iya cin abinci a gaban wanda bai kamata ya ci ba, amma ya kasa yi mata magana, kuma bai ji hakan da ya yi a matsayin wani laifi ba a matsayin sa na ɗan gidan mulki ba, wanda hakan yana cikin kamewa da suke da ita, musamman ma shi da hakan ya haɗu da ɗabi'unsa.
"Sayyid, ina jin yadda mutanen gidan nan suke yabon ka, sosai da sosai da yabon karamcinka. Duk da a baya ban so zuwa gidan nan aiki ba, amma sai dai na ji babu daɗi da yadda ni ban samu wannan karamcin daga gare ka ba, sai ma ƙyama da ka ke nuna mini, da ƙabilanci ban sani ba ko dan ni ba ƙabilarku ba ce, kuma ba 'yar ƙasarku ba ce ba, shi ya sanya ka ke yi mini haka. Amma ina neman afuwa idan na faɗi wani abu ba daidai ba ko ya ɓata maka rai, bana nufin hakan shugabana"
Gaba ɗaya babu tsoro ko fargabar Asal ta fito ta tarar da ita a ranta, daɗi ma ta ji na ko ba komai yau ta keɓe tare da shi.
A wannan karon ma, jin maganganun nata ya din ga yi da matuƙar muhimmanci. Yaya zai yi mata bayanin ba tsanarta ya yi ba, baya iya tantance abin da ruhinsa da gangar jikinsa ke nufi a kanta ne. Shirun da ta ga ya yi, da yadda yake jujjuya cokalin ya sanya ta yin ajiyar zuciya, ganin alamun saƙonninta na isa kai tsaye inda take so.
Ta nuna masa kwandon da aka bayar aka ce a ba shi, ta tashi ta fita.
Kitchen ta koma tana ƙarasa goge-goge, kawai. Sai dai ta ji alamun mutum a bayanta. Ta waiwaya ta gan shi a tsaye a ƙofar kitchen ɗin, idanunsa jawur, ga Giyaz a gefensa, cikin suffarsa ta tsohon nan mara kyan gani.
Ya fara takowa cikin kitchen É—in, yana kusanto ta, gabanta yana faÉ—uwa ta zuba masa ido.
Ya ɗago mata wata takarda ɗauke da hoton ƙwarangwal yana ci da wuta, an rubuta Imam Hammad Jalaludeen a jiki.
"Waye ya bayar da wannan saƙon?"
Kan Nana ya sara mafarkin da ta taɓa yi, ya fara ƙoƙarin zuwar mata kanta.
"Waye na ce waye ya bayar da wannan saƙon?" Ya yi maganar cikin wata irin murya da ba ta taɓa jin sa da ita ba a rayuwar da suka yi!!!
Cikin rawar murya ta ce "Nima ban sani ba, saƙo ne kawai aka ba ni aka ce na baka"
"Waye? Waye ya bayar da saƙon? Ki gaya mini?"
Ta kame jikinta cikin tsoro ta ce "Ban santa ba wata ce?"
Launin idonsa ne ya fara canzawa, baƙar ƙwayar idon ta ɗauke, sai farin kawai.
"Giyaz" Nana ta furta a hankali.
AREWABOOKS.
Jikinsa ne ya fara ƙamewa, fitilun kitchen ɗin suka ɗauke gaba ɗaya, ta ce "A wannan karon me ka ke buƙata kuma?"
Muryar Giyaz ta din ga ji, yana wata irin dariya. "Ai dama na gaya miki, ki jira dawowata".
"Na fi ƙarfinka, a waccan rayuwar da ya yi, da wannan ɗin ma, na fi ƙarfinka har abada".
"Kar 'yar ƙaramar ƙwarin gwiwar da wancan yaron ya baki, ya sanya ki yi tunanin za ki iya yi mini wani abu, mu zuba mu gani".
Nana ji ta yi abu ya faɗo jikinta mai nauyi, suka faɗi ƙasa tare. Wal hasken fitilar kitchen ɗin ya dawo. Imam ta gani a kwance a gefenta.
Da sauri Nana ta nufe shi, jikinta na rawa za ta taɓa shi.
Amma ta ganta itakaɗai a ɗakin karatun Ƙaisar, cikin azama ta tashi tana waige-waige, ta ga Ƙaisar a tsaya a bayanta.
"Yana ina?" Ta faÉ—a a sanyaye.
"Na san abin da ki ke ji, amma ya yi wuri, kuskure kaɗan za ki aikata ki lalata komai. Kar ki yi mamakin a din ga bibiyarki, saboda zaɓar ki da matar nan ta yi a matsayin mai dafa abincinsa, kuskure kaɗan ki na iya kwana a ciki ki shiga matsala. Kuma Giyaz zai yi ta tunzura ki, har ki yi wani abin da za ki saka kan ki a zargi. Ki din ga bin komai a hankali"
Nana ta yi ajiyar zuciya, itakaɗai ta san abin da take ji, a kan Sayyid. Dan a gare ta gara lokacin da ya ɓata ba ganinsa take yi ba, amma yanzu ga ta ga shi, amma ya yi mata nisa.
*****
Sagir kuwa ya zama tamkar zararre, aka kwana uku babu Shukura babu labarinta, sai a kwana na uku ya sanar da gidansu Shukura halin da ake ciki.
Hajiya Amina ta gigice ta rasa inda za ta tsoma ranta. Hankalinta ya yi mummunan tashi.
Alhaji Zailani ya din ga yi wa Sagir bala'i, a kan me tun ɓatan Shukura bai gaya musu ba sai yanzu.
Aka ƙara sanar da jami'an tsaro, aka kuma baza komar neman Shukura.
****
Ummi ce ta kawowa Baba ziyara, sai dai yanzu Baba duk ya zama abin tausayi, duk inda ya zauna sai da ya ja uban tagumi ya yi shiru, da ya samu dama kuma sai ya hau zancen Nana. Yanzun ma hirar da yake ta yi wa Ummi kenan.
"Ummi kin ga Nana haryanzu shiru ko? Babu ita babu ɗan uwanta, shi ma tun wannan zuwan da ya yi bai sake zuwa gidan nan ba. Gara shi namiji ne ita kuwa ban san halin da take ciki ba. Nan gida kuma ita Suwaiba yanzu ba ta da maraba da mahaukaciya, na ce a kaita Asibiti babarta ta ƙi yarda.
Ita ma Jamila 'yan kwanakin nan, gaba É—aya ba na gane kanta, dama kuma babarta ta nuna mini in daina shiga sabgarsu 'yarta ce, saboda abin Duniya"
Ummi ta ce "Gaskiya ne Baba, abin duk babu daɗi kam, amma Baba wani abun an bar gini tun ran zane ne, wannan abubuwan tun daga tushe yakamata a ce an yi wani abu na kaucewa farwuarsu, yanzu sai dai a yi ta haƙuri ana gaya wa Allah. Ta dai ɗan ba shi baki sannan ta tashi ta shiga cikin gidan.
Suka gaisa da Mama a tsakar gida, suka hau hira.
"Wai ina Jamila ne?"
Mama ta ce "Tana É—aki"
"Amma tana ji na zo, ta yi burus?" Ta yi maganar tana leƙa ɗakin.
Ta tarar da Jamila a kwance ta yi rigingine.
"Jamila yau 'yar shariya ce babu magana ma?"