← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 78

Sashe 50

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda yake ɗabi'ar ƙungiyar, suna sanye da jajayen kaya. Sai dai a wannan karon Jamila ta gusa daga matakin farko na shiga ƙungiyar.
Babban abin da ya bawa Jamila mamaki, bai wuce yadda aka fesa wani abu a gurin, sai ganinsu ta yi a dokar daji ba.
Wani irin daji mai ban tsoro, mai ɗauke da manyan dogwayen bishiyu, ga shi baƙiƙirin ɗauke da duhu.
A wani fili suke a gaban wani dutse, babu tsammanni ta ga wuta takama a tsakiya tana ci bal-bal.
Daga bisani dajin ya din ga amsa kuwwa da wata irin ƙara mara daɗin ji.
Aka din ga karanto abubuwan da Jamila ba ta iya fahimta.
Aka jefowa kowa ƙyalle da abin da zai sadaukar na shekara, kafin zagayowar wani taron.
Jamila ta kalli ƙyallen da yake gabanta, jawur da shi.
Hannunta na rawa ta ɗauka ta fara ƙoƙarin warwarewa. Da hasken da wutar ta bayar Jamila ta karanta abin da yake rubuce a jiki, da aka rubuta da jini.
Ta din ga kallon ƙyallen tare da rubutun. Ta duƙunƙune ƙyallen ta jefa a wuta, kamar yadda kowa ya yi.
Sai dai jikinta a sanyaye, gabanta kuma ya tsananta faɗuwa. A wannan karon har da wasu irin dogayen mutane, da ta kasa gane mutanen ne ko kuwa wani jinsin ne, saboda yadda suka shallake kowa tsawo a gurin kuma suna sanye da baƙaƙen kaya har kansu a rufe yake.
A wannan karon abubuwan da Jamila ta gani sai da ta tsorata, ashe wancan karon babu abin da ta gani. Ƙungiyar mataki-mataki ce.
Su matakin su Alhaji Zailani ma, kowannensu yana da aljanin da kusan bauta masa yake yi. Sun ba wa aljanun jini babu adadi, na makusantansu, da wanda ma ba makusnatansu ba. Aljanun na iya shiga kowane irin hatsari, dan ganin buƙatar irin su ta biya komai wahalarta.
Haka suma su Alhaji Zailani, duk abin da Aljanun suka buƙata suna yi musu, domin ɗorewar biyan buƙatunsu. Alhaji Zailani ya kan karɓi saƙonnin nasa Aljanin ta hannun Malam Gambo, wanda su ne manyan malaman da suke gudanar da sihiri a cikin ƙungiyar bayan ɓangaren neman Duniya da samun kuɗi da suke yi.
Su kan kira aljanu daban-daban da sanya su aikace-aikace na sihiri.
Aljanin Alhaji Zailani ya buƙaci aiki da jinin Nana, da kuma mu'amala da mai irin tauraronta dan biyan buƙatun Alhaji Zailani, sai dai abu ya gagara kamar yadda dariya ta gagari kare. Hakan ya sanya a wannan karon ma ya sake buƙatar jinin Alhaji Zailani, wanda idan ba Shukura ko Yusuf ba, sai dai abin da Shukura za ta haifa.
Ɓangaren Hajiya Sa'a ma hakan ne, bayan sanin fa'idar jinin irin na masu tauraron Nana, da yadda bayan haɗuwarta da Nana karon farko, Aljanin ya yi mata bayanin irin tagomashin da za ta samu, idan ya sha jinin Nana, da kuma bautar da zai yi mata idan ya sha jinin ko kuma ta kawo Nana ƙungiya, ta hanyar na ta bokan na cikin ƙungiyar, kuma bokan ya kwaɗai mata damarmakin da za ta iya samu idan ta mallaki Aljanin kan Nana kamar yadda aka gaya wa Alhaji Zailani ma.
Ita ma a wannan karon, an sake buƙatar jinin makusancinta, wanda ko dai Abba, ko Alhaji Fatuhu ko kuma dai ɗansa Muhsin, su ne shaƙiƙanta.

Jamila a firgice ta farka, a tunaninta ko duk mafarki ne, ta farka da wani irin matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ƙoƙon kanta tamkar zai tarwatse saboda azabar ciwo.
Maman Khairat ta taso tana yi mata sannu. Ta ce "Wai ke Jamila wace irin raguwa ce ne haka? Ai yakamata a ce zuwa yanzu kin riga kin saba fa"

Hajiya Sa'a ta ce "Dole za ta razana dama, yanzu ta shiga mataki na biyu sai a hankali"

Jamila ta ɗan yi shiru tana so ta fuskanci ko a wannan karon ma an yi lalata da ita, amma ba ta ji hakan ba. Sai kanta da yake ta wata irin azaba, ga jikinta tamkar ana ƙona ta saboda zafin zazzaɓi.

*****

Shukura ta je awo, likitan da yake duba ta doctor Sabo, ya na ta ƙara kwantar mata da hankali, saboda a wannan karon ma akwai hawan jini a tattare da ita. Har za ta tashi ta tafi ta ce "Doctor dan Allah wata tambaya ce da ni"

Ya ce "To Allah ya sanya na sani"

"Wai dan Allah ana iya samun mace wadda ba ta da mahaifa?"

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Eh ana samu, amma a mafi ƙanƙantar lokuta sosai, saboda a cikin mata dubu biyar da ƙyar ake samun mace guda ɗaya da irin wannan case ɗin"

Ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce "To Doctor kai ka taɓa haɗuwa da irin waɗanda ba su da mahaifar?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a. Amma me yasa ki ke tambaya?"

"Mamana ce ba ta taɓa haihuwa ba, da tana zuwa ganin Likita amma ta daina, sai last week ta je Egypt, aka duba ta ska ce ba ta da mahaifa"
Ya waro ido ya ce "Ba ta da mahaifa, kuma ta taɓa haihuwa?"

"A'a ba ta taɓa haihuwa ba, step mum ɗina ce"

Ya ce "Ikon Allah, kuma ba a taɓa yi mata aiki ba ko makamancin haka?"

Ta yi shiru ta girgiza kai ta ce "Bana tunanin haka, amma bari na kira maka ita"

Shukura ta kira lambar Hajiya Amina ta É—aga.

Suka gaisa ta ce "Mami, ina Asibiti ne na yi wa likitan da nake awo a hannunsa magana, ya ce na haÉ—a ku"

"Shukura, ba na ce a bar maganar nan ba kawai?"

"A'a ki yi haƙuri, na riga na yi magana da shi ai" ta ba wa Doctor Sabo waya. Suka gaisa ya ce "Hajiya garin yaya aka ce ba ki da mahaifa ne?"

"Wallahi nima ban sani ba, abin da dai suka ce mini kenan"

"A Nigeria an taɓa duba ki a baya an gaya miki hakan?"

Ta ce "A'a"

"An taɓa yi miki tiyata?"

"A'a Likita ba a taɓa yi mini ba"

Doctor Sabo ya ce "Ikon Allah, kuma yaushe rabon ki da Al'ada?"

Ta ce "Ai dama ba regular nake yi ba, wasu lokutan sai na yi wata shida ma ban yi ba, idan ya zo kuma ba ya fin kwana biyu wataran ma wuni É—aya ne shikenan"

"To dama tun kina budurwa haka ki ke yi?"

"A'a gaskiya, da lafiya ƙalau nake al'ada daga baya ne ya koma haka".

"Bayan ya koma hakan kin taɓa zuwa an ƙara bincikawa, kuma a baya ba a taɓa gaya miki mene ne ya hana ki haihuwa ba?"

Ta girgiza kai kamar yana ganinta ta ce "Ko a baya komai lafiya ƙalau ake ce mini, daga baya kuma da ya koma haka, mijina ya ce na haƙura da yawon Asibitin nan, dan haka ban sake zuwa a kan issue ɗin haihuwa ba. Amma ina fuskantar matsalolin gynea sai dai akwai likita da nake gaya wa ya rubuta mini magani kawai".

Doctor Sabo ya ce "Idan babu damuwa, akwai buƙatar ki zo Asibiti mu ƙara bincikawa sosai da sosai, wannan serious issue ne"

"Doctor na gode sosai da sosai, amma ba na tunanin zan iya zuwa, na haƙura dama buri ne irin na ɗan Adam amma shekaruna sun ja, na bar wa Allah ikonsa."

"A'a kar ki ce haka baiwar Allah, akwai Abubuwan da farwuarsu daga Allah ne mun sani, wasu kuma akwai sababi. Wataƙila akwai wani abu na musamman a tattare da ke da ya dace a bankaɗo. Ina doubting a ce Egypt su bayar da result ɗin da ba shi ba ne ba. Amma dai za mu ƙara bincikawa." Hajiya Amina ta amsa masa da to, ta yi masa godiya amma sam ba ta ji za ta iya zuwa a wani bibiya ba, kamar tana tsoron wani abu.

Doctor Sabo ya ce lallai Shukura ta lallaɓo ta, su zo Asibiti yakamata a yi ƙwƙƙwaran bincike a kan lamarin.

Alhaji Zailani yana kashingiÉ—e ya kira Doctor Sharif.
Bayan sun gaisa ya ce "Ina cikin uzuri ne kwana biyun nan, shi yasa ban É—aga wayarka ba, ya ake ciki?"

"Dama zan gaya maka ne, Hajiya ce ta kira ni tana tambayata wai ko ana iya samun mace wadda ba ta da mahaifa, to ban san dai mene ne ba, amma na ce maya eh."
Wata irin zabura Alhaji Zailani ya yi ya ce "Daga nan me ta ce maka?"

"Ba ta ce mini komai ba ta kashe wayar"

"Shikenan na gode" ya kashe wayar ya dafe goshinsa, "Amina kin fiye taurin kai, dama kaza garin tone-tonenta take tono wuƙar yanka kanta!"

Sannu a hankali Nana take bin doguwar barandar, tana hangen masu shigowa da masu fita daga cikin gurin cin abincin. Tun safe motoci suke shiga su na fita.
Sai dai ta jima a tsaye a gurin, ba ta ga wani abu da za ta iya riƙa, ko wani wanda za ta tunkara ta yi wa magana ba. Duk manyan mutane ne na alfarma ba ta tunanin akwai wanda ma zai tsaya saurarta, su kuma ma'aikatan gurin da take sanya ran za ta iya tambaya wani abu, ba zaman lafiya suke yi ba.

Jiki a sanyaye ta juya, ta kama hanyar komawa gurin girke-girken, Al Hassan yana hango ta, ta ofishin sa.
A kan hanyarta ta komawa, suka yi kiciɓis da Hasna. Nana ta ɗan raɓe gefe ta ce mata "Ina kwana"

"Lafiya" ta amsa har za ta wuce Nana, sai ta dawo da baya ta ƙara kallon ta ta ce "Au ashe ke ce fitsararriyar nan ko?"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a rashin fahimta ne, yanzu da na san wacece ce ke ai ga shi na gaishe ki" Ta so ta yi wani abu da za ta yarfa Nana da za ta saka ta ji zafi a ranta, amma sai ta kasa. Gaba É—aya ma sai ta ga Nanan kalar abin tausayi a yau, kamar ba ta da kuzari ko kaÉ—an fuskarta É—auke da damuwa.
"Amm ki kawo mini shayi ofishina, shayin girfa, kar kuma a cika sugar ba na son sugar da yawa"

"To ina ne ofishin"

"Ki tambaya" ta amsawa Nana tana yin gaba abin ta.
Chapter 50 · 0% Book details