Sashe 35
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abduou ya É—an yi shiru sannan ya ce "Zoben Azurfarsa fa guda É—aya da baya hannunsa, ina fatan ka san inda wannan yake?"
A zabure Mahmudu ya kalli Abdou matawalle, jin abin da ya faÉ—a.
"Ka daina zaro mini ido, kwanaki biyu kawai ka ke da su, ka faɗi inda zoben yake, ko kuma ka rasa rayuwar ka baki ɗaya, zaɓi ya rage naka"
Abdou ya miƙe, ya ja rawaninsa ya rufe fuskarsa ya fice daga ɗakin.
Cikin matsanancin tashin hankali, ya bi bayan matawalle da kallo. A Nigeria babu wanda ya san ma'anar zobunan da suke hannun Imam. Kuma ya yi iya ƙoƙarinsa gurin ba shi dukkanin kariya, balle ya ce wani ya san muhimmancin su ne ya karɓa.
Matuƙa ya ji yana son ya ga Imam, ya gana da shi, sai dai ya san ko mai zai yi babu mai ba shi wannan damar. Ga shi ya ji Abdou ya ce tun da aka dawo da shi, bai farfaɗo ba balle ya yi magana. Gefe guda kuma yana jin tsoron kar a koma a Nigeria a bibiyi Nana, saboda za ta shiga matsala ba kaɗan ba.
Koma a wani hali take ciki yanzu? Ya tambayi kansa yana jin wata irin damuwa ta mamaye zuciyarsa, tare da ɗora wa kansa laifi amincewa da auren Imam da Nana, ya kuma ɓoye mata komai a kan Imam ɗin. Ya dafe kansa da yake jin tamkar zai tarwatse dan damuwa.
****
Nana ta nutsu da zaman gidan Nene, duk Nenen akwai faÉ—a kamar yadda Hajara da mijinta suka din ga faÉ—a, amma sam hakan bai damu Nana ba, dan ba ta yi mata abin da za ta yi faÉ—an.
Nana ta fuskanci Nene sana'ar Abinci take yi, wasu lokutan tun safe idan ta fita sai daf da magariba take dawowa. Ta kan dawo tar e da yaran da suke yi mata aiki, su fara rage aikin Abincin sayarwar da za a yi washegari.
Nana tana jin yadda Nene take yi musu bala'i bisa kuskure kaɗan. Nene ta din ga gwada Nana, da ajiye kuɗi ko ina ta ga dama, ko ma ta fita ta bar ɗakunanta a buɗe, amma ko allura ba ta taɓa rasawa ba.
Kullum sai ta ba wa Nana Abinci, na safe kan su fita na sayarwa ta ba ta na rana, idan sun dawo ta ba ta na dare, har da ma tsaraba ta masu ciki.
Ma'aikatan Nene sun É—auka ma, Nana 'yar uwatta ce.
Idan sun dawo Nana kan fito ta ce za ta taya su aiki, Nene ta yi ta faÉ—a ta ce ba za ta yi ba. Sai dai hakan ba ya hana Nana kama musu wasu ayyukan.
Nana ta shafe kusan wata guda a gidan Nene, ta ga kullum sai Nene ta ba ta Abincin nan sau uku, ba ta taɓa nuna mata ta gaji da ciyar da ita da take yi ba, wasu lokutan har tambayarta take yi, ko tana son cin wani abin ne daban.
Da daddare ta kira Nana, Nana ta fito ta zauna a kusa da ita. Ta buɗe takarda fal kifi ta ce "Nana ga kifi ko za ki iya ci, idan ƙarnin ba zai dame ki ba".
Nana ta dube ta ta ce "Nene, dama ina son mu yi magana ne"
Nene ta ce "To ina jin ki"
"Na ga kullum sai kin bani Abinci sau uku a rana, na ce ko za ki ba ni wani aikin na din ga yi miki, a maimakon Abincin da ki ke ba ni, ko gurin sayar da Abincin sai na din ga bin ki, ko wanke-wanke na din ga yi miki"
Ta dubi Nana, sannan ta numfasa ta ce "Ni kuwa duk rashin imanina, da wannan tsohon cikin sai na saka ki aiki, dan dai abin da za ki ci sau uku ba zai gagara ba. Ban san takamaiman abin da ya kawo ki ƙasar nan ba, ban san kuma lokacin komawar ki ba, amma ba na tunanin abin da za mu ci ni da ke zai gagare ni. Ba zan ɓoye miki da fari ban so zamana da ke a gidan nan ba, saboda ba na son matsi da takura ko kaɗan, da su Auwwalu sun matsa ne, dan kora da hali na so yi miki. Amma yanayin ki ya nuna mini ki na ɗauke da damuwa mai nauyi a zuciyarki. Ba ƙaramin dalili ne zai sanya yarinyar mace, mai ƙanan shekaru kamar ki, ta baro gida ta taho uwa Duniya ba ga juna biyu. Kuma ki na yawan zama ki yi shiru, fuskar ki ɗauke da damuwa. Na kuma jarraba ki ta ɓangarori da dama, ban ga alamar rashin nutsuwa a tare da ke ba, shi yasa na ji zan iya zama da ke. Amma Nana tsakaninki da Allah wannan juna biyun na ki, na halal ne? Kuma da sanin iyayenki ki ka taho nan?"
Tambayar Nene ta yi wa Nana mugun zafi a ƙirjinta, amma sam ba ta ji haushinta ba, dan kowaye dole ya yi irin wannan tambayar. Sai da ta ji hawaye ya cika mata ido, da tuna ire-iren waɗannan tambayoyin dole ta ci gaba da amsa su, a cikinta da abin da za ta haifa, muddin ba gano inda Sayyid yake ta yi ba.
Ta haÉ—iye wani irin yawu mai zafi ta ce "Nene cikina na halal ne, ni matar aure ce, ban kuma gaya wa iyayena zan taho nan ba, sai da na riga na yo nisa da gida"
"To saboda me, kuma ina mijinki?"
Kawai Nana ta fashe da kuka, ta ce "Shi na fito nema, mijina da danginsa"
Nene ta ce "Shikenan, ya isa haka ki kwantar da hankalinki, mu bar maganar ma yi wani lokacin. Amma sai dai ki yi haƙuri, dan dole sai mun ƙarasa wannan maganar Nana, saboda ni uwa ce, dole na mu'amalance ki na yi miki nuni da abin dai-dai da akasin haka. Ban ga alamar ki na magana da wani a can gida ba, ko ta tarhon hannunki ce ba. Mahaifiyarki tana raye?" Nana ta jinjina kai tana share hawayenta.
Nene ta ce "Shikenan, share hawayenki mu ci kifin"
Ta girgiza kai ta ce "Ƙarnin hawa kaina yake yi na ƙoshi" daga haka Nana ta tashi, ta koma ɗakinta. Sai dai ta din ga kuka, saboda ita kanta ba ta san ta ina al'amuran za su warware ta cimma abin da ta fito nema ba.
Shukura ta rasa gane kanta da kanta, saboda rashin lafiya da take ta fama, ga Sagir ya rage ba ta kulawa, duk da yana ta ɓoye-ɓoye amma tuni ta daɗe da gano shi, sai dai ta maze ita ma ba ta nuna masa ba.
Hajiya Amina ce ta je gidan, Shukura ta ji daÉ—in zuwanta sosai da sosai, a nan Hajiyar take gaya mata batun Nana.
Cikin damuwa Shukura ta ce "Wallahi Mami, tun da aka yi auren nan, nake jin tausayinta, gaba É—aya ban ga riba a abin da babanta ya yi mata ba. Babu bincike babu komai a ce an aura mata mutum, wasu lokutan na kan rasa ina tunanin mutanenmu yake tafiya"
"Ke dai a yi sha'ani kawai, amma na jinjina batun ni kaina"
"Shikenan an saka rayuwarta a gagari, ga ƙarancin shekaru" suka ci gaba da jajanta lamarin. Hajiya ta fuskanci yanayin Shukura kamar ba ta da cikakkiyar lafiya, ta kira Doctor Sharif ya zo ya duba ta.
Shukura ba ta so ba sam, dan ko ƙaunar ganin Sharif ɗin ba ta yi, amma tuna ta yi wa Hajiya Alƙawarin komai ya wuce, ta yi tawakalli ta dangana ya sanya ta haƙura.
Ya zo har gida ya yi mata gwaje-gwaje, ya kuma tabattar mata da tana da juna biyu.
Hajiya Amina ta din ga murna, a duk lokacin da aka ce ga wata mace da ciki, sai ta yi ta murna, ta ji dama ita ce.
Shukura ba ta wani yi murna ba, saboda ita gaba É—aya haihuwar ma ta fita daga kanta.
Da yamma Hajiya Amina ta koma gida, saboda tsabar zumuÉ—i, tana zuwa ta tarar da Alhaji Zailani a gida, ta hau ba shi labarin Shukura wani cikin ne da ita. Wata irin mummunar faÉ—uwar gaba ce ta ziyarce shi, yana tsoron a wannan karon ma, kar a nemi ya bayar da wani abu da ya danganci iyalinsa.
Hajiya Amina ta din ga jin wani irin bacci, tana idar da sallar isha'i, ta ɓungire a gurin ta hau bacci.
Ita da Nana ta gani a falo, a zaune suna hira, kamar yadda suka taɓa yi kwanaki lokacin Nanan, na zuwa gidan rainon Haidar.
Ta ce "Hajiya, kin kuwa ci gaba da bibiyar Likitoci a kan matsalar rashin haihuwar ki?"
Hajiya Amina ta ce "Nana ai ni na haƙura ma na bar wa Allah, yanzu shekaruna sun wuce na haihuwa"
Nana ta ce "A gurinki ba, a gurin Allah yana bayar da falalarsa a inda ya so, da kuma lokacin da ya so ne. Ki daina biye wa wannan mijin naki, ya din ga sarrafa rayuwar ki yadda yake so. Ki nemi mafita a kan matsalolinki.
Kuma Shukura ta dage da Addu'a, kar wannan É—an ma ya sake raba ta da shi"
Maganar Alhaji Zailani ce ta tashi Hajiya Amina daga mafarkin da take yi, tana kallonsa kawai ta ji gabanta ya faÉ—i"
"Lafiya ki ke kwance a ƙasa haka ki ke bacci?"
Ta ce "Bacci ne ya É—an É—auke ni ban sani ba"
Ya ce "To ki tashi ki koma gado mana, kar wuyanki ya yi ciwo" Ta yinƙura ta tashi ta canza kaya ta hau gado ta kwanta, sai dai ta din ga jin mafarkin da ta yi da Nana a jikinta, tamkar a zahiri ya faru.