← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 78

Sashe 3

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana ta karɓa tana murmushi ganin sa fal a roba, ta ce "Allah ya yi miki abin da ki ke yi mini na alkhairi na gode sosai" suka yi sallama Nana ta fita.

Tana cikin bin wani lungu, ta ji Muryar Saleh na kiran ta. Ta ƙara saurin da take yi, amma ya cimma ta. "Nana dan Allah ki saurare ni".

Rikicewa ta yi, gani take a kowane lokaci za ta iya ganin Sayyid, ba ta san da wani yaren za ta yi masa bayani ba ya fahimta.

"Nana ki tsaya ki ji mana"

"Wallahi zan yi maka ihun kwarto, wace irin jaraba ce wannan ina ruwan ka da ni ne?" Ganin tana É—aga murya, kuma Akuyarsa ta yi kuka a unguwar, ya sanya sum-sum ya koma da baya.

Tana zumbuɗa sauri, ta je gida, ta san yana can yana jiran ta. Kawai ta ci karo da shi a wani lungu, yana zaune a kan wata sokawe, ya jingina da jikin bango, shikaɗai ƙwal a layin. Sai da ta razana, ta waiwaya bayan ta, cike da tsoron ko Saleh ya biyo ta.

"Sayyid me ka ke yi a nan kuma, ba ka shiga shiga gida ba?"

"Ba zan iya shiga nikaɗai ba" Ta miƙa masa hannu ta ce "Taso mu tafi" ya miƙa mata hannunsa. Sai dai tun da ya saka hannunsa a nata, sai da ya kalli fuskar ta.

Da suka je gidan, danƙam da mata, ana ta hayaniya. Ya rufe fuskarsa Nana ta yi sallama. Gaba ɗaya suka yi tsit, suka zubo wa su Nana ido, musamman ganin hannunta riƙe da na Sayyid.

Kawai ta ja hannunsa, suka nufi É—akin su.

"Nana kun dawo" Sajida ta yi maganar, tana kokowa da zaninta tana fitowa daga É—akinta, saboda kar su wuce ba ta gan su ba.

"Eh sannun ku" daga haka ya tura ƙofar ya fara shigewa. Suna shiga ɗakin matan suka saka shewa, ɗaya ta ce "In dai Namiji ne, yarinya za ta gama wannan iyayin ne"

Nana su na shiga É—aki Sayyid ya tsare ta da ido ya ce "Nana ba ki da gaskiya"

Gabanta ya faÉ—i cikin tsoro ta ce "Me na yi?"

"Gumi ki ke yi a iya goshin ki, da karan hancin ki. Kuma tafin hannunki ya ya sanyi, zuciyar ki na bugawa da ƙarfi kuma da sauri. Kin yi wani abu da ki ke ɓoye mini ko?" Haɗe rai ta yi ta fara ƙoƙarin ƙwace hannunta daga nasa.

Sai kuma ya sassauta muryarsa ya ce "Ki daina fushi, ba zan iya barin, duk wani abu na ƙi ya tunkaro rayuwata da ke ba, ki daina fushi"

"To sai ka din ga zargina da rashin gaskiya" ta faÉ—a a hasale.

Ya girgiza kai ya ce "Ba zargin ki nake yi ba. Na tabattar da wani abu ya faru ne, da ba za ki so na sani ba, idan na sani zamu samu saɓani. Kin manta mu ba kamar sauran mutane ba ne. Kuma ina iya jin abin da yake ranki, kin manta ne?" Ya yi maganar yana murmushi da shafo fuskarta. Dole ta saki murmushi.

Nana dai ta din ga yi wa Allah godiya, da ba ganta da Saleh ba.

Nana tana yi wa Allah godiya, ganin yadda jikinsa ya yi kyau. Duk da yana haki bai daina ba, amma yanzu yana cin abinci. Sayyid na matuƙar son zuwa masallaci salla, amma dole yake haƙura. Saboda da gayya matan gidan suke wata shigar, duk da ba tsayawa kallon su yake yi ba. Ga shi ba ya son kallo, amma yana fitowa sai su yi shiru su zura masa ido.
Ita kanta Nana lamarin gidan ya ishe ta, ba ta ƙaunar zaman gidan nan ko kaɗan.
Maman Nana ta aiko mata da barkonon nan, har da awon kayan Abinci, tamkar ta san a halin da take ciki.
Ummi da kanta, ta je ta É—auki barkonon, domin kuwa Nana daina zuwa gidan Ummi ta gaba É—aya saboda Saleh.

Abu kamar wasa har zuwa wannan lokacin, Sayyid ya kasa gane kansa, abin ya fara damunsa sosai da sosai. Ga shi ya kasa cewa Nana komai a kan hakan. Ita ma kuma ba ta ce masa ba, sabgoginta kawai take yi.

Tun Yamma Nana, ke ƙoƙarin shirya duk abin da za su buƙata, saboda washegari za su tafi Asibiti, kuma sammako take so su yi, saboda su ga likita da wuri.
Sai dai duk dauriya kawai take yi, wani irin zazzafan zazzaɓi ne a jikinta, ta kasa cin abinci. Babu abin da take son ci, sama ds kazar da Habu ya kawo farkon auren su. Ga shi ba ta son yin duk wani abu da zai ɗaga wa Sayyid Hankali. Ta fuskanci ko saɓani suka samu, ƙaramar magana sai ta sanya ya fara haki, ya fara nema ya faɗi.
Tana ƙofar ɗakinta, tana soya miya, su Barira su na hira, tana yi wa wata maƙwabciyar su kitso. Suke zancen wata mata a bayan layin, wai sai mijinta ya neme ta ya rasa, sai a yi kwanaki ba a ganta ba, sai bayan wani lokaci a tsinto ta a wani gurin, ko a ganta a ɗaki.
Barira ta kada baki ta ce "Amma ta mayar da mijin nan tasono, ƙarya take yi gantalinta kawai take tafiya. Meye matan auren ba sa yi yanzu?"

Sajida ta ce "A'a Barira, ki daina cewa ƙarya ne"

"Ke wallahi, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, a gidan uban wa Aljani zai ɗauke mutum ya kai shi wani gurin? Ke ni fa da ake cewa ana ganin aljanu, ko su tsorata mutum ban taɓa yadda ba, iskanci ne kawai da ƙaryar banza ce, ba wani aljan duk 'yan iska ne kawai.

Nana ta ji wani abu mai zafi ya soki zuciyarta, duk da ba da ita suke ba, kawai ta ƙura wa Barira ido, ko ƙiftawa ba ta yi.
Tun Barira ba ta ankara ba, har ta lura, take ta ji tamkar an kwarara mata ruwan sanyi a jikinta, sai kuma ta É—an tsorata ta ce "Nana lafiya kuwa?"

Ayshercool
08081012143

53

"Barira, kin taɓa haihuwa?"

Nana ta tambaye ta. "A'a me ki ka gani?"

"Amma dai ki na ganin mata su na ɗaukar ciki su haihu. Kuma kin yarda da abin da suke faɗa cewar haihuwa akwai wahala, duk da ba a bakin mutum ɗaya ko biyu ki ka ji ba. Kin yarda wannan ciwon na haihuwa akwai shi, duk da ba ki taɓa yi ba?"

Barira ta ce "Eh mana, ai wannan kowa ya san haihuwa akwai wahala"

"Kin yadda akwai ciwon haihuwa, amma ba ki yadda akwai na aljanu ba, saboda Allah bai jarabce ki ba, har ki ke ƙarar da cewa matar mutane yawon iskanci take tafiya? Duk wanda zai shaide ta, barin mijinta ne, tun da yake zaune da matarsa a haka, ke mene ne naki da za ki ce mutuniyar banza ce? Idan aka rutsa ki shaidar ina take tafiya iskancin za ki faɗa? Idan aka faɗi abu, ko baki yarda ba gara ki yi shiru ki ce Allah ya kyauta, musamman larura. Idan ba haka ba maganganu irin naki za su iya zama cutarwa a gare su". Jin Nana yau ta saka musu baki a magana ya sanya suka din ga goyon bayan abin da Nana ta faɗa gaskiya ne.
Da fari jikin Barira ya yi sanyi, daga baya ganin kowa ya hayayyaƙo mata, ya sanya ta hau bala'i, har abin ya koma faɗa.

Ita kuwa Nana tun da ta gama zazzagar abin da yake ranta, ta kammala girkinta, ta kwashe kayanta, ta koma ɗaki ta bar su da mayar da zance. Dama ga zafin laulayi, ga takaicin mutanen da ake tarawa a gidan babu dalili, ga kuma zafin ƙazafin da Barira ta yi wa matar, da ita kanta Nana ba ta sani ba, amma maganar da ta yi ta ji sanyi a ranta.

Yana daga kwance a kan katifa ya ce "Rayuwata" Ta É—aga kai ta kalle shi ya ce "viens(zo) yana yi mata alama da hannunsa.

Ta ƙarasa gabansa ta zauna. "Dan Allah ki daina shiga maganar mutanen nan, ki daina kula su. Ni na daɗe ban ji mutanen da ba na ƙauna kamar su ba. Ba na son su zo su yi miki abin da ba zamu ji daɗi ba"
Ta jinjina kai ta ce "Haka ne, ka yi haƙuri nima ban so na shiga ba, haka kurum na ji maganar ta su kamar da ni suke yi. Sayyid ni da kai mun san azaba da raɗaɗin larurar nan. Ire-iren waɗannan maganannun da yadda wasu suke ganin kamar ciwon nan ƙarya ne, ya sanya da yawa masu larurar da dama a cikin wata damuwar ciwon ya yi musu illa, tun da ba a yarda da ciwon ba balle a ɗaukar musu mataki."

"To ai ba su ce da ke suke ba"

Murya a sanyaye ta ce "Sayyid, duk lokacin da aka yi maganar irin wannan larurar, ina jin tamkar da ni ake. Nima wasu lokutan na kan shiga ɗimuwa, na bar gida a gano ni a wani gurin, duk da ni ban taɓa kwanaki ba a ganni ba. Ta kai ta kawo har a zahiri ina ganin abubuwan nan. Sayyid kai ma fa wasu lokutan ina yi a gabanka ka na gani, to yaya za a ce mutum yana sane ya din ga mayar da kansa mahaukaci? Wanda kuwa duk aka samu da yin ƙaryar irin wannan ciwon, yana buƙatar kai shi gurin likitocin ƙwaƙwalwa, Sayyid ciwon nan babu daɗi, akwai wahala" ta yi maganar hawaye na zirarowa daga cikin idanunta.

Ya tashi zaune ya kai hannunsa jikinta zai rungumota, zafin zazzaɓin jikinta ya ziyarce shi. Ya kalle ta a tsorace ya ce "Ba ki da lafiya?" Ya furta maganar haɗe da haki, saboda yadda ya ji zafin a bazata.
Chapter 3 · 0% Book details