← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 78

Sashe 33

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To a haka dai ta yi zubin nutsuwa, dan dai ka matsa ne, amma ni ba na son yayime-yayime na je na É—aukko wadda za ta hana ni sukuni, shi yasa duk girman gidan nake zamana nikaÉ—ai abina.
Sannan zan fara zama da ita na wata É—aya, idan ba ta da matsala mu ci gaba da zama, idan akwai matsala na mayar mata da kuÉ—inta ta tashi ta bani guri. Kuma wallahi dan ma dai kai ne, da ba zan yadda ba".

Nana cikin girmamawa ta ce "In sha Allah ba za ki same ni da matsala ba, in Allah ya yarda".

Nene ta ce "To Allah ya sa, bari na buɗe ɗaya daga cikin ɗakunan ta zaɓa"

Mijin Hajara ya ce "Ɗakunan a rufe, ai na san sun sha ƙura yanzu, ki yi haƙuri tun da akwai gyararru ki kwashe kayanki daga ɗaya ki ba ta. Kin ga ɗakin da ba komai, sai an nemi labule, da sauran abubuwa". Haka ya takure Nene, ta bawa ɗaki ɗaya, mai ɗauke da labulaye da carfet.
Nana ta din ga godiya, ta ce  "Saura kuɗin hayar, nawa ne zan biya?"

"Ai na biya ta, ba wani abu in sha Allah, ki zauna kawai"

Nana ta ce "Ai da kuÉ—i a gurina"

Hajara ta ce "Kar ki damu, ba wani abu ya biya, idan akwai wata matsala ko ba za ki iya zama ba, ki ce Nene ta kira mu a waya, in sha Allah babu wani abu"

Nana sai da ta yi hawayen murna, ta raka su har waje sannan ta dawo.
Ta tarar da Nene ta fito da wake fal za ta tsince. Nana ta lallaɓa ta zauna a kan tabarmar ta ce "Kawo na tsince miki"

Nene ta ce "A'a ke da ki ke baƙuwa, yi zaman ki ki huta, kan Auwwalu ya dawo ya ce ina azabtar da ke, tun da ya ce ni masifaffiya ce". Ita Nana har ta gama zaman gidan ma, ba ta san sunansa ba.
Ta yi murmushi ta ce "A'a ba komai, dan Allah ki bani na taya ki, ai na ga waken da yawa, kuma daga zaune zan taya ki"
Ta dawo da robar waken tsakiyar su, ta kalli Nana ta ce "Nana ko?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Eh"

"Ciki ne da ke haka ne?" Nana ta sunkuyar da kai tana tsince wake.

"Ke kuwa me ya yi miki zafi, ki ka baro ƙasar ku da wannan tsohon ciki ki ka taho inda ba ki da kowa? Amma fa ki yi haƙuri da tambayoyina, kin san yanzu duniya babu gaskiya sosai"

Nana ta ce "Haka ne. Mijina ɗan ƙasar nan ne, nice 'yar Nigeria. Na zo neman danginsa ne a nan"

"Allah sarki, to a ina dangin nasa suke? Kuma shi yana ina" Nana ba ta son yayata halin da take ciki, ta fi son sai ta nutsu, ta ga kamun ludayin mutanen ƙasar tukuna, kafin ta saki jiki, amma ga Nene ta saka ta a gaba da tambayoyi. Kafin ta ba ta amsa, Allah ya taimake ta, aka kira Nene a waya, hakan ya sanya ba su ci gaba da zancen ba.

****
Cikin tsananin tausayawa, yake bin matashin da kallo, saboda yadda duk ya fita daga hayyacinsa.
Cikin damuwa ya kira sunansa a hankali ya ce "Mahmudu" ya É—ago idanunsa a galabaice, ya kalli wanda ya kira sunan nasa.
"Ka yi musu bayanin duk abin da ya faru, ka faÉ—a musu iya gaskiyarka, ko Allah ya sanya su rabu da kai, wannan wahalar da ka ke yi ta isa haka?"
Murya a cunkushe ya ce "Me zan gaya musu? Me zan ce da ka ke tunanin idan na faÉ—a za su yarda da ni?"

"Iya abin da ka sani É—in zaka faÉ—a"

"A tunaninka tsawon wannan lokacin, ba iya abin da na sani É—in ba nake gaya musu? Sai dai akwai abin da ko za a kashe ni, ba zan furta ba"

"A'a Mahmudu, idan har za ka ci gaba da shiru da ɓoye wasu abubuwan, ba fa za a ƙyale ka ba, za su ci gaba da azabtar da kai ne kawai a banza. Ni dai zan faɗi abin da na sani"

Mahmudu ya ce "Ka kwana da sanin, ka na furta wani abu, to tabbas kai ma za ka tsinci kanka, a halin da nake ciki yanzu. Ka yi shiru mu bar komai a yadda yake. Rufe sirrin Imam wajibi ne, akwai abin da idan na furta, zai iya janyo asarar rayuka ba É—aya ba ba biyu ba, in dai wahala ce na san É—ayan biyu ne, ko na mutu ko ta wuce. Abu É—aya nake so da kai, shi ne; dan Allah Ashiru, ka binciko a wani hali yake ciki? Tun da muka baro Nigeria, ba a haÉ—a mu a mota É—aya ba ma, ban san ina aka yi da shi ba"
Ashiru ya ce "Kai wannan fa babban aiki ne, tun ɓatansa fa, ba a bari labarin ma ya fita ba, balle a sanya ran jin halin da ake ciki yanzu, amma dai zai ɗan ƙyanƙyasa a ɓoye, na ga ko za a samu wani bayani. Sannan ina ƙara neman afuwarka a kan abin da ya faru"

"Babu komai kar ka damu, an saki sauran ko? Su Sulei"

"Eh an sake su, ai tun da suka fuskanci, ba su ma san a kan me ake binciken ba, an sake su amma fa an killace su"

"Shikenan tashi ka je, kar a fahimci wani abu" Haka Ashiru ya tashi ya tafi yana waiwayen sa.

*****

Sannu a hankali take tafiya, yana zaune a cikin mota yana hangen ta, ta tsallako titi, ta nufo motarsa tana murmushi.
Ta buÉ—e motar ta shiga ta ce "Yaya Abba me ka ke jira a titin ne haka?"

Ya lumshe idanunsa, jin yadda ƙamshin turaren jikinta, ya gauraye motar baki ɗaya. Ya ce "Wa zan jira ban da ƙanwata, kwana biyu ban gan ki ba, da gida zan bi ki ma, to sai na ji tsoron kar na je ko ki na da baƙo, ban sanar da ke zan zo ba. Kawai na tsaya a nan na ce bari na jira fitowar ki"

Ta yi murmushi ta ce "Ko akwai baƙo, ba dolena na sallame shi na saurari yayana ba, kuma wani baƙi zan yi da safe haka?. To me ma zan samu ne?" Ta yi maganar tana laluba motar.

Ya yi dariya ya ce "Laluba ki É—auki duk abin da ki ke so" ta yi dariya ta ce "Dan ka san ba ka ajiye komai ba ko? Mu je kar Mummy ta yi ta jira na"

Ya ce "Ok" ya fara tuƙa motar a hankali. Yana tuƙi yana satar kallon Jamila, wani irin kyau take ƙarawa a idanunsa kullum. Kullum ƙara shiga ransa take yi, ga shi ya kasa fitowa ya sanar mata da ainihin abin da yake cikin zuciyarsa. Duk wasu alamu da zai nuna mata sonta yake yi, ya yi amma ya kasa gaya mata baki da baki. Su na daf da shiga layin gidan ya tsaya ya ce "Ƙanwata"

"Na'am Yaya Abba"

"Ina son za mu yi wata magana da ke, amma maybe sai na dawo tukuna"

Ta yi murmushi tare da gyara zaman mayafinta, ta ce "To shikenan babu laifi, a dawo lafiya"

"Allah ya sa, ki kula mini da kan ki Please, zan kira ki idan na je kasuwa"

Ta ce "To, ka sayo mini aya mai sukari a kasuwa"

Yayi dariya ya ce "Aya kawai?"

"Eh ita kawai"

"To an gama ranki ya daÉ—e" ta fita daga motar tana É—aga masa hannu"

Da ta shiga cikin gida,ba ta tarar da Hajiya Sa'a a falo na, dan haka ta bi ta bedroom.
Ta tarar tana wanka, ta nemi guri ta zauna tana danna wayarta. Can Hajiya Sa'a ta fito daga ita sai towel. Jamila ta kalle ta ta kawar da kai.

"Jamila har na fitar da ran za ki zo ai"

"Ba na jin daÉ—i ne, shi yasa da kamar ma ba zan zo ba fa"

"Eyya sannu, bari na shirya ki raka ni mu je na duba Fatuhu"

Jamila ta ce "Tom"
Hajiya Sa'a ta zauna a kusa da Jamila, ta ɗan riƙo hannunta ta ce "Daughter wai ke haryanzu ba za ki waye ki faso gari ba? Ina ta saita ki a hanya kin ƙi yarda ki shiga layi"

Jamila ta ɗan ɓata fuska tana zame hannunta ta ce "Gaskiya ni Mummy ba na so, ni me zan tsinta a jikin mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi"

Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda É—aukar ciki. Kuma...

"Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni me zan tsinta a jikin mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi"

Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda É—aukar ciki. Kuma...

"Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni ban ga abin da mace za ta tsinana mini ba, ni bai ma yi mini tsari ba gaba É—aya gaskiya. Ba gara na bi maza ba"

Hajiya Sa'a ta kwashe da dariya, ta ce "Yaro man kaza, ai shikenan Daughter, bari na shirya mu fita". A gaban Jamila ta gama shirinta, ba tare da jin nauyin abin da ta tunkari Jamilan da shi ba, ta gama suka fita.

Umman Fadila ce take kallonta a tsanake, bayan ta gama yi mata komai za ta tafi. "Fadila"

"Na'am Umma"
Chapter 33 · 0% Book details