Sashe 45
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta gyara zamanta sosai ta ce "A duk Duniya waye ya koyar da mu azkar É—in? Na san za ka ce manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, amma an yi wa fiyayyen halitta sihiri, kuma ya kama shi.
Daddy ka yi haƙuri da abin da zan faɗa maka. Kana ibadarka ta farilla daidai gwargwado, amma ba ka damu da nafilfili ba, da tsananta addu'a. Kana ganin Allah ya baka duk abin da ka ke buƙata, ba ka fiye tsananta addu'a da neman kariyar Allah ba.
Sannan azkar da ka ke yi, kuma a yi shiri ya kama ka, ba ya nufin Allah baya kare ka, amma wataƙila jarrabawa ce daga gare shi, kamar yadda ya ce zai jarrabe mu, ba a fasa jarraba mai imani, kuma jarrabawa alama ce ta soyayyar Ubangiji. Allah ya jarrabe ka da cuta, ka nemi magani shi ma a cikin jarrabawa ne, amma Daddy ka naɗe ka dage, kai sai na Asibiti kawai, bayan akwai magungunan musulunci da suke na halal babu kauce hanya, idan an jarraba ba a san inda za a dace ba, amma ka ƙi ka ce kai sai na bature, na baturen kuma ba a gano komai ba, kame-kame kawai ake yi."
Ya yi shiru yana nazarin kalaman Fadila, ya numfasa ya ce "To yanzu mene ne abin yi? Kin ga yanzu bani da kuÉ—i, kuma irin wannan abubuwan sai da kuÉ—i".
"Kar ka damu, zan yi wa Kawu magana, shi ma ranar da ya zo duba ka, ai ya ce a yi na islamic, Alhaji Zailani ya ce ba za a yi ba. Da haka za tuntuɓe shi, in sha Allah ba zai gagara ba"
Alhaji Fatuhu ya ce "Allah ya sa, dama duk ina tsoron, kar a aikata abin da zai kauce wa hanya ne, amma na amince yanzu a yi É—in"
Ta yi murmushi ta ce "To shikenan, yaya ita yarinyar an gano ta É—in?"
Ya girgiza kai ya ce "Ina fa, an ce wai ba ma ta ƙasar nan, amma ina ta mamakin dalilin da ya sanya nake mafarinta, kuma idan na farka sai na ji kamar a zahiri, shi ya sanya ma na fara yarda"
Fadila ta ce "To Allah ya sanya a dace" ya amsa da "Amin"
*****
Æangaren Nana kuwa, gaba É—aya kanta ya kulle a kan lamarin nan, kawai sai ta dasa addu'a, a kan idan da alkhairi a tafiyarta, Ubangiji Allah ya sanya mata son tafiyar, ya tsare mata Muhsin, idan kuma babu, Allah ya cire mata abin daga zuciyarta.
Kamar yadda ta saba ji haka ma wannan karon, ta ji muryarsa, da gudu ta ajiye abin da take yi, ta nufi taga ta leƙa sai ta hango giftwarsa da doguwar riga baƙa a jikinsa.
Da gudu ta fita daga gurin, ta nufe shi tana ƙwala masa kira, amma ya ɓace mata.
Cike da takaici ta yi juyi, tare da jan guntun tsaki, kawai ta ji hancinta ya fara shinshino mata, ƙamshin wannan ɗakin na cikin dutse, da take ganinsi tare da Sayyid.
Ta buÉ—e idonta a hankali, ta ji ana shafar cikinta a hankali, tare da yi mata numfashi a wuyanta.
"Sayyid" ta furta a É—an tsorace.
"Asmyna, ina kewarki da yawa, gangar jikina na ta kewarki. Idan ina jin zafi babu mai bani sanyin da ki ke bani, babu wanda yake iya fahimtar kurman baƙin rayuwata, ki ƙaraso gare ni Please" ya yi maganar yana shafa wuyanta, tare da yin maganar ƙasa-ƙasa.
Ta saka hannu ta shafa gashinsa ta ce "Ina ta gaya wa Allah Sayyid, ya san lokacin da ya dace ya haÉ—a mu, amma jikina yana ba ni, ina daf da kai in sha Allah"
"Ki ƙaraso da wuri Asmyna, ina cikin matsananciyar buƙatarki"
"Ina ta ƙoƙari Sayyid, kuma ina gaya wa Allah, na san zai haɗa mu a nan kusa, kuma ina roƙonsa ya kare mini kai a duk inda ka ke, na san kuma yana ji ya kuma amsa in sha Allah"
"Nana, wai ba kya salla ne, gari ya fara haske fa" ta ji muryar Nene. Ta tashi tana mustustuke idonta, hancinta na ci gaba da jiyo mata sauran ƙamshin turaren nan.
Da ta yi salla ta idar, ta je ta samu Nene a É—akinta, suka gaisa.
Ta ce "Nene na amince"
"Da me?"
"Zan tafi gurin yin girkin nan"
Nene ta ce "Ina fatan ba wani ne ya matsa miki ba? Ko kuma kunyata ki ka ji ba ki ka ce za ki je?"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a, wa ma na sani na saba da shi, da zai ziga ni na É—auka? Babu wanda ya ziga ni"
Nene ta ce "To shikenan, zan kira ta a waya na ji, idan ba a samu wata ba, sai ki je. Sai mu je gurin jami'an tsaro mu yi yarjejeniya mu yi rubutu, mu je a yi a gaban su Auwwalu ma da Hajara"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a Nene, na yarda da ke, abin duk bai kai haka ba ai"
Nene ta ce "A'a, haka kurum wani irin ki ka yarda da ni, ɗan mutum fa zan riƙe miki, a'a, mu je mu yi a rubuce, yadda jami'an tsaro ma za su din ga sanya ido, kar wani abu ya faru ma. Sai dai abin da Allah ya aiko na ƙaddara wannan ba yadda muka iya, kuma na san za ki yi mini uzuri a wannan. Amma idan aka yi haka kema sai kin fi sakewa, hankalinki ya kwanta.
Nana ta jinjina kai ta ce "Ni dai, bakin da zan yi miki godiya ba ni da shi, amma ina fatan Allah ya yi miki tukuici da abu mafi dacewa da abin da ki ka yi mini na alkhairi, a duniya da kuma Lahira"
"Amin Nana, ai É—a na kowa ne, Allah ya tabattar mana da alkhairinsa, ya kuma bayyana miki mijinki da ahalinsa cikin aminci".
"Amin uwata ta kaina" ta yi maganar tana murmushi.
Sai dai tun da Nana ta amince za ta bar wa Nene Muhsin, ta fara jin kewar ɗan nata, ta din ga jin kamar ta ce ta fasa. Saboda kallonsa kawai na sanya mata matsanancin farinciki da nishaɗi, idan ta tuna mallakinta ne shi ɗin. Tana jin ko ba ta ga Sayyid ba tana da ƙaramin Sayyid, duk da tana fatan ta gan shi ɗin, ko ba komai al'umma sa kalli ɗan nata da kima da daraja.
Ko da Nene ta kira matar, Matar ta tabbatar wa Nene, akwai sauran space É—in da Nana, za ta yi musu aiki, sai dai a saka ranar da za su tafi ta kai ta.
Haka nan fargabar Nana ta ƙaru, ta rasa murna take ko tsoro, duk da abu mafi rinjaye kewar ɗan jaririn ɗanta ne, da yanzu take ƙara shaƙuwa da shi,ƙaunarsa take ƙara shiga ranta. Tana jin tamkar ta fasa tafiyar nan, amma ƙasan zuciyarta tana jin tafiyar ta ta alkhairi ne.
*****
Æangaren Abba kuwa, sai da aka yi wa Jamila Æ™arin ruwa, typhoid ne ya yi mata mummunan kamu.
Sai kuma damuwa da take ciki, jininta ya É—an hau. Abba ya biya duk bills É—in, ya janyo kujerar É—akin, ya zauna a gaban gadonta, ruwan da aka saka yana shiga jikinta.
"Ko a kira Mama a waya a sanar mata ne?" Ya yi maganar cikin kulawa.
Ta ce "A'a, na gaya mata Asibiti zan je, ana gamawa sai ka mayar da ni gida"
Ya ce "To shikenan, mai zan sayo miki ki samu ki ci?"
"Ba na son cin komai, kawai kar ka matsa daga kusa da ni, ka zauna a nan" ta yi maganar tana riƙe hannunsa a cikin nata.
Ji ya yi zuciyarsa ta narke, da matsanancin tausayin kan su, ya ce "Ina tare da ke matata, har abada in sha Allah" ta yi murmushi tana ƙara riƙe hannunsa. A hankali kuma ta saki hannun nasa, da tuna rashin dacewar hakan, sai dai wani irin abu mai wuyar fassara take ji, game da Abban.
Yana kallon kiran Hajiya Sa'a, amma ya ƙi ɗagawa, kawai ya din ga jin zafinta.
Har azahar sannan ruwan da ake saka mata ya ƙare, ya ɗauke ta a motarsa, ya yi mata sayayya sannan ya mayar da ita gida.
Sai da ya tabattar ta shiga gida, sannan ya kira Mummy.
"Sai yanzu ka ga damar É—aga wayar tawa?"
"A'a caji take yi ne, ki yi haƙuri?"
"Kana ina ne?"
Ya ce "Na É—an je wani uzuri ne, na zo ne?"
"A'a shikenan" ta ƙyale shi, bayan tuna shawarar da Safiyya ta bata, wato maman Khairat.
*****
Kamar yadda Nene ta buƙata, sai da suka je gurin jami'an tsaro, suka yi yarjejeniya, aka rubuta da yaren hausa, French da kuma turanci, duk suka sanya hannu, a gaban su Auwwalu da jami'an tsaro.
Daga nan suka dawo gida Nene ta ba wa Nana wata 'yar madaidaiciyar Jaka, da za ta haɗa kayanta da za ta buƙata a ciki.
Ta kalli Nana ta ce "Nana dan Allah ki kula da kan ki, duk da na san ke kamammiyar yarinya ce, ba mutuniyar banza ba, amma tunatar da mumini abu ne mai kyau, ki riƙe mutuncinki, ki kiyaye hakkin aurenki. Idan ki ka ga wani abu na ba dai-dai ba, ko wanda ya saɓawa addininki, a haƙura da sabgar nan. Kuma cikin hikima za ki din ga bincikawar,ba sai kowa ya fuskanci ainihin abin da ya nai ki gurin bax
Nana ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Nene zan kula da kaina, ba zan ba ki kunya ba, ki taya ni da addu'a, Ubangiji Allah ya sanya zuwana ya zame mana alkhairi baki É—aya"
"In sha Allah, addu'a ina nan zan ci gaba da yi miki ita da yardar Allah."
Nana ta haɗa kayanta, amma ji take kamar ta fasa tafiyar, amma ta ƙarfafi zuciyarta, ta hana hakan yin tasiri a ranta.
Ranar Asabar, da safe matar ta zo domin tafiya tare da Nana.
Nene ta ce mata "Dan Allah gata nan amana, Hansatu, kar ki kai ta idan za a cutar da ita, kin ga yaro ne da ita ƙarami, dan Allah idan akwai matsala a gurin nan, gara ki saka a sallamo ta ta dawo gida."