Sashe 66
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ƙura mata ido yana son gane wani abu da shi kansa bai san mene ne ba.
"Ita ce 'yar Nigeria da Asal ta samo?" Ya tambayi kansa a zuciyarsa.
Zaucewa ya kusa yi, bayan da Nana ta ƙaraso daf da shi ta ajiye farantin, ya ji ƙamshin turaren sa na tashi a jikinta.
Ko da Nana ta ɗago ta saci kallonsa, ta gan shi a nutse yana kallon talabijin ɗin sa yana kaɗa ƙafafuwansa, kamar ma bai san ɗan Adam ya wanzu a gurin ba.
Tuni hawaye ya cika mata ido, ganin mutumin da ta yi rayuwa mai cike da so da ƙauna tare da shi, abokin wasanta abokin hirarta, ya zame mata wani na daban a yanzu. Ba ta kai ƙofa ba Asal ta ƙwala mata kira.
Ta yi maza ta goge hawayenta ta juyo.
Wani abu ya caki zuciyar Nana, ganin Asal da wata 'yar riga a da guntun wando, babu kunya ko makamancin ganin idon Nana ta ce "Zo zan gabatar wa da amour ke"
Ta zauna a kusa da shi tamkar za ta shige cikinsa, ta ce "Imam, ga wadda nake gaya maka, kukun da na samo maka 'yar Nigeria"
Sayyid ya yi wa Asal wani kallo yana ɗan lumshe ido, Nana tamkar ta zunduma ihu, sassaucin da ta samu ɗaya shi ne ganin ƙirjin Asal babu wani abin kirki na jan hankali, duk da yadda ta taƙarƙare tana banƙarewa. Guntun tsaki ya kusa ƙwacewa Nana.
A hankali cikin magana daki-daki ya ce "Babu masu girki a Niger, har sai an tsallaka Nigeria?"
"Eh mana, duk dan saboda na burgeka ne" ta yi maganar cikin shagwaɓa tana shafa sajensa.
"Idan ba ki burgenin ba fa?"
"Haba Imam, me yasa haka dan Allah?"
"Na ji, amma idan ta girka a samu mai kawowa ba na son ta din ga shigo mini nan"
Nana ta kalle shi, zuciyarta ta tsananta bugawa.
"Gaskiya Imam ba na son barorin nan su din ga shigowa sashenka, mugwayen munafukai ne duk nan yadda da su ba, ba kuma zai yiwu maza su din ga shigo mini"
Ya buÉ—e baki zai yi magana, Nana ta tsare shi da ido.
Asal ta kalle ta ta ce "Je ki kawai sai da safe, rigima yake ji" Nana gani take kamar da gayya Asal take wannan abubuwan.
Ba ta san lokacin da ta furta "Shegiya" ba a hankali.
Bayan fitar ta, Asal ta ce "Imam me yasa baka son ta din ga shigowa ne?"
Ya lumshe idanunsa ya buÉ—e ya ce "Tsoro take bani, idan na ganta gabana faÉ—uwa yake yi."
A zaton Asal, Nanan muni ta yi masa, shi yasa baya ƙaunar ganinta, dan haka wani irin farinciki ya kama ta, ta ci gaba da lallaɓa shi a kan ya yi haƙuri Nana ta din ga shigowa sashen tana kawo masa abincin.
Shiru ya yi mata ganin ba ta fahimci mai yake nufi ba, dan da suka yi ido huɗu da Nanan gani ya yi tamkar ta na yi masa kallon tuhuma, shi da bai taɓa ganinta ba, da zai iya zai so ya samu dama ya tambaye ta, ya ji ko laifi ya yi mata. Ko kuma ma ba mutum ba ce ba, da yake jin jikinsa ya canza a duk lokacin da ya ganta.
Sai dai ya ci Abincin da ta kawo, da daddaren.
Nana kuwa rabi da kwata kwanan tsaye ta yi, tayi kukan har ta gaji. Ita yanzu kawai ta zuba wa sarautar Allah ido.
Furucin Sayyid ya rusa duk wani ƙwarin gwiwa da take da shi.
Da safe kuwa da ta yi girkin, da wuri ta kai cikin ikon Allah, ba kowa a falon.
Kusan awa É—aya da rabi da kai Abincin aka aiko kiran Nana, ta san za a rina, saboda abin da ta aikata, ta san dole a neme ta.
Kanta tsaye ta shiga falon Imam, ta tarar da fuskarsa jawur hatta idonsa ma ya yi ja.
Asal cikin bala'i ta hau Nana da faÉ—a.
"Kashe mini miji za ki yi? Na ɗaukko ki ina tunanin za ki yi abin arziki, amma ki yi yinƙurin kashe shi, ban gaya miki sharaɗin wani abu ya samu mijina a dalilin abincinki ba?"
AREWABOOKS
Nana ta zuba wa Asal ido, sannan ta kalle shi ta mayar da idonta ga Asal ta ce "To ai ni ba ki gaya mini me na yi ba"
"A kan me za ki cika yaji a cikin abinci ki cika tafarnuwa? Bayan ba ya son abinci mai yaji da yawa"
"Ki daina yi mini faÉ—a, tun da ba ki gaya mini baya cin abinci mai yaji ba, kuskure ne bai kamata ki yi mini faÉ—a ba dan yau É—aya na yi kuskure ba, amma bari na É—anÉ—ana Abincin na ji, sai na ga me zan gyara a gaba"
Ta nufe shi gadan-gadan ta kalli fuskarsa, yadda ta koma sak lokacin suna tare, tana ba shi abinci mai yaji, ba zai yi magana ba sai dai ta gani a fuskarsa.
Ta durƙusa ta ɗauki cokalin da ya ci abinci da shi, ta ɗiba ta kai bakinta, ta ɗago suka yi ido huɗu da shi, ya sunkuyar da kansa da sauri.
Ta risunar da kai ta ce "Tuba nake Shugaba, na yi kuskure in sha Allah zan kiyaye hakan ba zan sake ba. Ba a gaya mini ba ka cin yaji da yawa ba ne, amma zan kiyaye"
Ya sake É—aga ido suka yi ido huÉ—u. Ya rintse idanunsa yana tunanin wace ce wannan? Meye haÉ—insa da ita jikinsa yake rikicewa a duk lokacin da ya ganta? Sai dai duk da wannan tambayoyin da yake da su, kalmar shugaba da ta kira shi da ita, ta din ga yawo a cikin kansa.
Nana ta miƙe tsaye ta kalli Asal da tsaya tamkar ta fashe, ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri zan sake kiyayewa, ba zan sake maimaita kuskuren da na yi ba".
Kawai Asal ta janyo Nana, cikin mamaki take kallon Asal. "Nana ina ki ka samu wannan turaren?"
Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wane turaren?"
"Wanda yake tashi a jikinki, Imam ba ka ji ba?"
Shi dai ya yi shiru bai ce komai ba.
Nana ta ɗage hijjabin jikinta, doguwar rigar da aka ba ta ta bayyana a jikinta da tamkar sai da aka aunata aka ba ta ta ce "Rigar da aka ba ni ce take ƙamshin, nima a haka aka bani ita"
Ta tsaya tana yi wa Nana kallon tuhuma da rashin gamsuwa da abin da ta faɗa, sannan babban abin da ya ƙara ɗaure mata kai, yadda Nanan yau take ɗauke da ƙwarin gwiwa yau.
"Cherie, ki sallame ta kawai ya wuce"
Asal ta saki Nana tana bin ta da kallo.
Ta ce "Na tafi da Abincin na dafo wani ne?"
Asal za ta yi magana ya ce "A'a"
Nana ta É—auki farantin Abincin nata ta yi waje tana murmushin nasara, dan ta fuskanci ta fara dagula wa Asal lissafi.
*****
"Ba wai-wai nake ki ji ba, gaskiya ne Hammad ya dawo Agadez kuma cikin hayyacinsa ba hauka ba, ya aka yi haka ta faru, kuma har Sultan yana iƙirarin ya yi jinya ne a faransa, yanzu ya warke zai ci gaba da gudanar da ayyukan sa, yaya aka yi aka haihu a ragaya?"
"Waye ya ce ya warke É—in ne? Babu waraka a tattare da Imam Hammad"
"Amma kai ka ce zai haukace ya bar ƙasar nan baki ɗaya, amma ya dawo cikin ƙoshin lafiya, an ce ma wai jinya ya yi a faransa"
"Imam Hammad bai warke ba, kuma ba jinya ya yi a faransa ba, ya bar ƙasar nan ya yi nisa ya je ya yi rayuwar ƙasƙanci ba tare da tuna waye shi ba ma. Sai dai an samu mushkila inda ya tafi ɗin, wanda a can nake tunanin an ɓata mana fiye da rabin aikin ma, akwai dai yadda aka yi aka gano inda yake, amma tabbas ya yi nisa da gida ba tare da sanin waye shi ba. Amma warkewa kam bai warke ba, an samu matsala ne wani ya shiga cikin aikin ya ɓata wani abu , amma wannan ce gaɓar da ta fi cancanta mu sake hargitsa shi, za a ƙara ƙaimi a kan aikin, komai zai tafi yadda yakamata, a ƙaryata Sultan ya kunyata a idon duniya, a lokacin da ɗan nasa abin ƙaunarsa zai yi hauka tuburan duniya ta sani"
"To shikenan, ina nan ina zuba ido, ina kuma jiran ji daga gare ka, da kuma abin da zai faru."
*****
Nana ta girka Abincin rana, ta shirya shi a kan tray, ta je ta ajiye a falon Imam.
Ta ja ta tsaya ta ƙi tafiya.
Ta daɗe a tsaye, kafin su fito tare da Asal. Ganinsu taren ba ƙaramin dukan Nana ya yi ba, amma ta danne ta koma gefe ta sunkuyar da kai.
Ja ya yi ya tsaya, saboda yana kusanto Nana, yana jin tamkar zuciyarsa za ta tsaga ƙirjinsa ta fito, ya din ga jin tamkar zai fita hayyacinsa.
Asal ta kalle shi ta ce "Yaya dai?" Ya É—aga kai ya kalli inda Nana take, kawai ya juya ya koma É—aki.
Ta ƙaraso gaban Nana ta ce "Ke ya aka yi ne? Ba cewa na yi miki, ki din ga ajiye abincin ki tafi ba?"
Nana ta haɗiye wani abu mai ɗaci ta ce "Ki yi haƙuri, dama wata alfarma zan nema na a gurinki"
"Ta me?"
"Kin ce dole na kula da abin da mijinki zai din ga ci na yi taka tsantsan, to kuma gurin girkin yana can waje, duk da idan ina girki tsayawa nake yi a gurin girkin, amma ina jin tsoron kar wani ya shiga ya yi wani abu na ba dai-dai ba a yi zaton ko nice, shi ne na ce ko za a yi wa É—akin girki mukulli a bani?"
Asal ta É—an yi shiru, sannan ta ce "Kuma kin yi magana mai kyau, zan san abin yi in sha Allah, za ki iya tafiya" Bayan Nana ta fita, ta koma da bayata shiga É—akin, ta tarar da shi a kan gado ya takure jikinsa ya yi shiru, jin motsinta ya sanya ya waiwayo.
"Imam, meyafaru ne wai?"