← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 78

Sashe 5

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To yi sallar. Nima sai na yi muje mu É—uro gas, ko rabi ne sai kuma na sayo gawayi, Ummi ta bani kurfoti, na din ga haÉ—awa da shi" Ya jinjina mata kai ya tayar da salla.
Yana kallon ta ta idar, ta buÉ—e jakarta ta É—ebo sauran kuÉ—in da suka dawo da su, ta nufi wardrobe ta haÉ—a su da waÉ—ancan kuÉ—in. Kawai ta ga kayan wardrobe É—in a hargitse.
Mamaki ya kama ta, ta san Sayyid ba ya taɓa mata wardrobe, kuma ita ba a haka ta bar wardrobe ɗin ba.

Ta janyo jakar gidan Sarkin baka, ta duba ta ga kuɗin nijar a ciki. Ta laluba ta ɗauki ledar, da kuɗin Nigeria ke ciki ta rasa. Ta watso kayan wardrobe ɗin gaba ɗaya, tana ƙara haskawa da fitilar wayarta.
Yana tsaye yana kallon ta. Muryarta na rawa ta ce "Sayyid"

Ya kalle ta. "KuÉ—inmu, kuÉ—in da ka bani na saka a cikin wardrobe na...naa..ajiye a nan ban gani ba, ko ka É—auka?"

Ya yi shiru yana kallon ta, a zuciye ta nufi hanyar fita daga ɗakin, ya riƙe ta. Jikinta yana tsuma take ƙoƙarin fizgewa amma ya riƙe ta yana girgiza kai ya ce "Kar ki yi magana, ki yi shiru ko waye mu bar wa Allah. Tun da na shigo, na ga alamar an buɗe ɗakin. Kuma laifinmu ne, da ba mu saka mukulli ba, muka rufe ɗakin kawai."

"Sayyid ba a yi mana adalci ba. Kuɗin Abincinmu da maganinka, sun kwashe gaba ɗaya wace irin masifa ce wannan? Daga wannan sai wannan ya ake so na yi ne?" Ya riƙe ta gam yana shafa bayan ta, a hankali ya ce "Ki yi haƙuri, ki daina ɗaga murya, akwai Allah"

Kuka take yi iya ƙarfinta, tana sheshsheƙa, ya rungume ta gam a jikinsa, shi kansa ya ji zafi da raɗaɗin satar da aka yi musu. Ba iya kuɗi ba, har da wasu daga kayan amfaninsu na ɗakin an ɗauka, ya san kuma hakan sabon ƙalubale ne, saboda ba su da wata hanyar samun kuɗi a yanzu.
Ji ya yi jikin Nana ya saki, kuma jikin yana É—aukar sanyi. Karkarwa ta fara yi, tamkar ana jona mata shocking.
Cikin matsananciyar damuwa, ya zauna da ita a jikinsa, ya ɗauki wayarta da ta saki a gurin, yana haska fuskarta. Ya ga hawaye na fita ta gefen idonta. Hannayenta da ƙafafuwanta su na lanƙwashewa, goshinta kuma yana tsatstsafo da gumi.
Jin ta ta yi, jingine da wani abu da ba ta san ko mene ne ba. Ta shafa abin ta ji ƙurzunu-ƙuruzunu, tamkar dutse. Gurin baƙi ƙirin duhu ya gauraye gurin, ko tafin hannunta ba ta iya gani. A hankali haske ya fara shigowa gurin, har gurin ya yi haske ba ki ɗaya. Ta ɗaga kanta ta ga ba ta iya gano ƙarshen ɗakin.
Jin tari ta yi a bayan ta, ta waiwaya da sauri, ta ga Ƙaisar a zaune lulluɓe da wani abu mai haske sosai.

"Ƙaisar. Ba ka da lafiya?" Ta yi maganar tana nufar inda yake.

Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta sake cewa "Dama kuma ku na rashin lafiya, kamar ka canza gaba É—aya" ya yi murmushi ya ce "Mu na rashin lafiya mana, guba na ci" Ta waro ido ta ce "Guba kuma? Me yasa?"

"Tsohon nan na jikin mijinki, ya bani."

"Kuma ka sha? Wai meye alaƙar ka da shi? Kuma dan Allah me yasa yake bibiyar mijina?"

"Ba wannan ba, me yasa ki ka kira ni?" Cikin mamaki ta kalle shi ta ce "Kamar yaya? Ni ban kira ka ba ai"

"Fushi da ɓacin rai, duk wanda ki ka yi tamkar kin kira ni ne. Kuma ni yanzu ba ni da wani tasiri sosai, saboda jinya nake yi. Babu wanda ya san ina nan. Giyaz ya saka ni a gaba, ya mamaye Library ɗi na, yanzu rashin ganina zai sanya ya ci gaba da cutar da ku. Ba zan iya wani abu ba sosai yanzu, sai dai zan iya tasiri a kan bil'adama.
Duk ba wannan ba, duba can."
Ta ɗaga kai ta kalli inda ya nuna mata, Library ɗin Ƙaisar ta gani. Ta ga gangar jikin Sayyid a kwance. Tsohon nan ya ɗaɗɗaure shi da wata irin igiyar ƙarfe. Ƙasan gadon da yake kai kuma, wata irin wuta ce take ci a ƙasa. Nana ta zabura a rikice, ta ce "Wannan ai Sayyid ne"
"Ƙwarai shi ne, ba wani ba. Kuma Giyaz shi ya sanya masa matsalar da ku ke ciki na auratayya. Sai dai abu ɗaya zan iya gaya miki. Matsalar zuciya da hawan jini da yake fama, wannan ciwo ne yake damun sa. Amma Giyaz na assasa wani abin. Kuma... Amma dai shikenan"

Nana ta buÉ—e baki za ta yi magana, ya ce "Kar ki tambaye ni komai, kin san sharaÉ—in. Kalli" ya yi maganar yana sake nuna mata gurin.

Alhaji Fatuhu ta gani, ta yi ƙuri da ido ta ce "Kamar na san wannan"

"Ba kama ba ce ba kin san shi, ciwo ne da zafin sihirin da aka yi masa ya mayar da shi haka. Sai kuma albishir da nake yi miki, da ƙanwar ki ta zama cikakkiyar 'yar ƙungiyar asiri. Ɗayar kuma wannan bararojin da ta taɓa baki magani, ta aura mata ɗanta, wanda yake baƙin aljani ne. Kuma ta tarkato kan iyalanta duk su na jikinta. Kuma kowanne akwai abin da yake mora a jikinta. Ke in taƙaice miki ma, a kowane lokaci za ta iya rasa hankalinta ko ma rayuwarta gaba ɗaya. Shikenan bissalam"

"Ƙaisar" sai kuma ta yi ido huɗu da Sayyid.

"Kin tashi?" Ta yinƙura ta tashi zaune, tana kallon ɗakin.

Sayyid ya ce "Ƙaisar ɗin ba shi da lafiya ne?" Ya yi maganar yana tsare ta ido.

"Wane Ƙaisar ɗin?"

"Tambayata ki ke yi?" Shiru ta yi, ita ba ta iya tuna koma ma a cikin abin da ya faru ba. Idonta ne ya sauka a kan kayan da suke gaban wardrobe a ƙasa, sai kuma abin da ya faru ya faɗo mata. Afujajan ta tashi ta sake nufar wardrobe ɗin, tana zazzage kayan tana kuka.

"KuÉ—in nan fa babu su, an kwashe ki daina wannan dube-duben" ya zauna ta yi shiru ta sanya kayan a gaba tana kallo.

Ya yi mata shiru ya ƙi kula ta, ya kwanta a kan katifa, yadda take a hasalen nan, idan ya matsa faɗa za su yi. Cikin ƙanƙanin lokaci nannauyan bacci ya yi awon gaba da shi.

Barira na kwance a ɗakinta, ta yi ɗaiɗai tana bacci, ta ji kamar ana karta mata farce a ƙafafuwanta. Har ta maze ta ci gaba da bacci, amma ta ji an cigaba. A fusace ta ce "Gali meye haka, za ka din ga karta mini faratanka, ina cikin bacci ne?" Shiru bai amsa ba. Ta laluba ta ji yo ƙeyarsa a can ƙarshen gado, yana bacci. Ta koma ta kwanta, amma ta ji an cigaba, ta tashi zaune tana zabga ashariya.
Ta kunna fitila, ta ga babu kowa. Ta yi tsaki ta sauka daga kan gadon, ta fito tsakar gida domin ta yi fitsari. Bayan ta fito daga banÉ—akin, kanta ko É—an kwali babu, kawai ta yi karo da Nana a tsakiyar tsakar gidan tana yi mata wani irin mugun kallo.

Ta haska Nana ta ce "Nana lafiya kuwa?"

Sai dai Nana ba ta yi magana ba, ta sake haska ta, za ta yi magana. Ta ga ta rikiɗe ta zama wata irin ƙatuwar mage, baƙa ƙirin, girman ta ya yi na tunkiya ƙosashiya da ita, ta yo kanta tana buɗe haƙora.
Da gudu Barira ta shiga É—akinta, tana ihu tana kiran sunan Gali.

"Ke mahaukaciya, mene ne haka za ki din ga ihu kina kiran sunana a tsohon daren nan?"

Ba ta ce masa uffan ba, ta duƙunƙune, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da ƙyar ta samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta.

Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haÉ—a kai da gwiwa.
Ya yinƙura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya ɗauke ta.
Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan.

Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu.

Kwanki biyu da sace kuÉ—in nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daÉ—i. Dubu talatin ce ta ragu a hannunta, shi ma cikin irin kuÉ—in da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. KuÉ—in Nijar É—in kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin É—in nan, ba tare da ta rushe gaba É—aya ba. Ga shi magungunan da yake sha kawai, na wata É—aya dubu goma sha biyu take sayen su.
Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi haƙuri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin.

Kwana biyar da kwashe kuÉ—in nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci, saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haÉ—o mata da su, take ta cancana musu.
Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daÉ—i, yana ta numfarfashi.

Abin Duniya ya ƙara damunta, ya kuma ƙi cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana maganganu tana ba wa su Sajida labari.
Chapter 5 · 0% Book details