Sashe 65
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To ai ba ka karya ba, kuma mu É—auki tsawon wannan lokacin ba ma tare baka nan, kuma yanzu ka ce fita za ka yi?"
Ya ci gaba da ƙoƙarin fita, amma ta tare shi.
"Haba Imam, ko kewata ba ka yi ba? Ba ka yi farin ciki da ganina ba ne? ka ke shirin ficewa ka bar ni?"
Ya tsaya yana ƙarewa fuskarta kallo ya yi murmushin gefen baki ya ce "Abincin ne ban ji daɗin sa kamar na jiya ba. Sannan Gimbiya Bilkisu zan je na gaisar".
Noƙe masa kafa ta yi tana riƙe rigarsa.
Ya ajiye agogonsa ya nemi guri ya zauna, hakan ya sanya ita ma ta zauna tana murmushi.
Nana kuwa tana tsaka da kuka ta ji an dafa ta, ta ɗaga kanta a hankali ta ganta a ɗakin karatun Ƙaisar.
Sai dai wannan karon tsawonsa daidai da ita, ya zauna sosai ya fuskance ta.
Ta sunkuyar da kanta hawaye na ci gaba da kwararowa daga cikin idanunta.
"Uwar gijiyata" Nana ta É—aga idanunta a hankali ta dube shi, ta mayar da kanta ta sunkuyar.
"Bai kamata ki nuna karaya a wannan gaɓar ba, duk da ina jin zafin yadda ki ka yi burus da ni, da buƙatata da gargaɗin da na din ga yi miki a baya, amma wannan kamar ita ce gaɓa ta ƙarshe mai kuma matuƙar wahala, idan ki ka sare a yanzu wahalar da ki ka yi tuƙuru a baya za ta tashi a banza kenan.
Ba ki da tabbacin ya gane ki? Ko kuma bai gane ki ba, sai dai komai ya zo da sauƙi. Ita wannan matar sauƙaƙa miki aiki ta yi, tun da ta kawo ki kusa da shi, ta kawo ki har inda yake, godiya ma yakamata ki yi mata.
Ki kawar da kai daga kan duk wani abu na wulaƙanci da za ta yi miki a yanzu, a ƙarshe ke ce da riba, ki fara tantance halin da yake ciki, kafin ki ɗauki mataki na ƙarshe"
Cikin kuka Nana ta ce "Ƙaisar na karaya, na sare ba zan iya ba, wa zai yarda da ni matarsa ce, banbancim da ke tsakanina da shi tazara ce mai nisan gaske.
Ba na buƙatar ya gane ni, gida zan koma na nemi gafarar iyayena na kula da yarona"
"Ba za ki koma gida yanzu ba, yaronki yana hannu na gari a yanzu duk ban san gaba ba. Na daɗe ban ga bil'adama mai juriya sadaukarwa da tsantsar juriya kamar ki ba. Imaninki da Allah ina da tabbacin ba zaki wulaƙanta ba kamar yadda ki ke yawan faɗa mini. Kar ki karaya ki tsaya ki karɓi abin da yake naki ne, idan ki ka karaya ki ka tafi kin yi biyu babu, wahalarki kuma ta tashi a banza"
Da wannan maganganun ta buÉ—e idonta, tana sauke numfashi a hankali.
Daki-daki ta din ga jin maganganun Ƙaisar na dawo mata. Ta yi shiru tana nazari, ta tashi zaune a hankali.
"Abin da yake nawa? Eh Ƙaisar, Sayyid nawa ne, bai kamata na karaya a wannan gaɓar ba" ta furta idanunta na sake cika da hawaye bayan tuna Asal matarsa ce.
Ta din ga tunanin suwaye suka tafi da shi lokacin suna Buda? Ko dai da kansa ya gudu ya bar ta? Ina su Habu, ta gan shi shikaɗai? Da gaske taɓin hankali ya yi a baya ya manta wace ce ita, ko kuwa dai raina mata hankali ya yi, ko kuwa dai duk wannan abin ba Sayyid ɗin ta ba ne?"
Wata zuciyar ta ce "Haba dai, ko na makance na shafa na san Sayyid, ko za a ajiye irin sa dubu zan fitar da Sayyid a cikin su. Ina zan samu amsoshin tambayoyina ne?" Ta yi maganar tana dafe kanta da yake yi mata wani irin ciwo.
Ƙaisar kuwa yana sakin Nana, ɗakin karatunsa ya gauraye da sautin dariyar Giyaz, dariya ta rashin imani mara daɗin ji.
Ƙaisar ya waiwaya, yana kallon inda Giyaz yake shawagi a sama yana ƙyaƙyata dariyar, hakan ya tabattar masa da Giyaz ya gama jinyar abin da Nana ta yi masa.
Ya yi wata irin girgiza ya bayyana a gaban Ƙaisar, ya din ga zagaye Ƙaisar yana ci gaba da dariyar cike da mugunta, daga bisani ya tsahirta da dariyar ya ce "'yan samari, yaushe imaninka ya ƙaru haka, har ka ke yi wa uwar gijiyar da ba ta ɗauke a bakin komai ba, nasiha da ba ta shawara?"
Ƙaisar ya tsuke fuska ya ce "Ban yi maka iyaka da zuwa inda nake ba?"
Giyaz ya ce "Daɗin abin har gori ta yi maka a kan butulcin ka yi mini, amma da yake ba zuciya ce da kai ba, ka na liƙe da ita. To bari na gaya maka abin da ba ka sani ba, ni ne na sake juye tunaninsa na shafe masa wancan tunanin, yadda abin zai yi mata ciwo, dama na gaya mata dawowata ba za ta yi mata daɗi ba, tun da na tashi daga jinya nake tunanin yadda zan ƙuntata mata na ƙuntata maka.
Ya ɗagowa Ƙaisar wata kwalba, da wani farin haske yana yawo a cikin ruwan da ke cikin kwalbar.
"Ka ga wannan, tunaninsa ne a ciki na duk wani abu da ya shafe ta na rufe shi ba zai taɓa tuna ta ba har abada. Sai dai ta dauwwama gararamba babu makoma. Na ga ka yi wa ɗanta riga-kafi, dan ka hana ni cutar da shi, sai dai ka riga ka makar...
Ƙaisar ya ce "Kai ne ka makara, dan cutarwar da ka yi masa a ciki ma bai yi tasiri ba. Kar ka manta Bil'adama ce. Kar ka manta aiki aka baka ka shafe wancan tunanin nasa, ba ka taɓa tunanin zai tuna waye shi ba, sai ga shi yanzu ya tuna waye shi, dan haka wannan ma baka da tabbacin zai manta rayuwarsu har abada"
Giyaz ya ce "Za ka gani, ka zuba ido zaka ce na gaya maka, duk wata hanya da zan bi na tsohe farincikin yarinyar nan na ƙuntata mata sai na yi"
"Kana tunanin akwai sauran wahalar da ta rage wadda ba ta sha ba a baya? Haryanzu ba ka san suwaye biladama ba, waɗanda ka ke ta'amalli da su miyagun cikinsu ne, hatsabibancinsu kawai ka ke gani. Amma wannan karon ne za mu yi fito na fito na gasken gaske tsakanin ni da kai a kan yarinyar nan. Kar ka manta ka fi ni shekaru da daɗewa a duniya, hasali ma kai ka haife ni, amma ni marubuci ne, kuma manazarci sannan masanin magunguna kar ka ƙetare iyaka, zan iya baka mamaki."
Giyaz ya sake kecewa da dariya ya ce "Gaskiya ne marubuci, kuma masanin magani, ka buÉ—e wannan kwalbar idan ka isa ya tuna waye shi saboda ka taimaki uwar gijiyar ka, ka faranta mata.
Ƙaisar ya ce "Kai ka yi imani da cewa ka rufe tunaninsa a kwalba, amma kai zan cewa ka zuba ido ka ga ikon Allah"
Giyaz ya ce "Shikenan ina zuba ido" daga haka ya ɓace ɓat daga libraryn.
Har bayan azahar Imam yana tare da Asal, sai dai da aka kawo abincin rana, ba Nana ce ta kawo ba, Asal ta yi ta bala'i a kan kar wanda ta sake gani a sashen, idan ba a nemi izini ba ko kuma idan Nana ce ta kawo ba.
Ta kira Imam da nufin ya ci abincin rana, sai dai ya yi loma biyu ya kalli Asal ya yi shiru, ya tsiyayo shayi daga cikin haɗaɗiyar butar shayin, ya kai bakinsa, ya ɗan sha kaɗan ya ajiye, ya ɗauki robar madara ya buɗe yana sha.
"Amour" ta furta a shagwaɓe ya ɗaga idanunsa ya kalle ta.
"Ba ka ci abincin ba fa"
Ya girgiza kai ya ce "Ba irin na jiya ba ne"
"To wai meye a cikin na jiyan ne da ya sanya shi daban?"
Ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba, kawai dai wannan É—in ban ji É—anÉ—anonsa ba, kin san haryanzu jikin nawa sai a hankali, ba na cin abinci sai da na dawo É—in nan"
"Kuku fa na samo maka mussaman daga Nigeria, ta iya girki ita ta yi maka na jiyan ma, sai dai muguwar kidahuma ce, kuma ba ta da kirki amma ina da tabbacin ba za ta cutar da mu ba, a can gidan cin abinci na MaraÉ—i na É—aukko ta mussaman saboda kai" Ya jinjina mata kai tare da yi mata alamar jinjina.
Sai dai a baɗini cikin ƙwaƙwalwarsa, Nigeria da ta ambata sai da tsigar jikinsa ta tashi, gabansa kuma ya faɗi. Duk dabarun da Asal yakamata ta yi ta saka ya ci abincin nan ya ƙo ci, ya sha madarar raƙumi ya ce ta ishe shi ba sai ya ci abincin ba.
Asal ta É—anÉ—ana Abincin, sai dai ba ta ji wani rashin É—anÉ—ano ba, abincin ya yi daÉ—i amma shi ya ce babu É—anÉ—ano.
Da daddare Asal ta tafi ta yi wanka, ta je ta samu Nana, idan ba ta yi girkin daren ba, za ta gwada mata mene ne matsayinta a gidan.
Sai dai ɓangaren Nana, tun da ta ji su Ramata duk sun ruɗe, wai an yi girki Imam ya ƙi ci, Asal sai bala'i take yi, kuma ta ce kar su sake dafa wani abu a kai masa muddin ba Nana ba ce ba.
Yana zaune yana kallon labarai, shikaÉ—ai a falon ya ji yanayinsa ya fara canzawa. Ya yi shiru yana tunanin me yake shirin faruwa da shi ne haka.
Ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da sallama, tana shigowa idanunsa suka haɗe lokaci guda. A zahiri ya ga shocking ɗin da jikin Nana ya yi, dan sai da farantin hannunta ya yi rawa. Sai dai shi ma na sa jikin ya yi, amma da sauri ta sunkuyar da kanta. Gabanta ya yi mummunan faɗuwa bayan ganin Giyaz da ta yi a tsaye a gefen Sayyid yana kallon ta yana dariya.