← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 78

Sashe 13

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uwani ta din ga yawo da Nana a cikin ƙauyen nan, tana nuna ta a dangi, tana gaya musu 'yar gurin Isa ce. Dan galibi ba su santa ba.
Nana gaba ɗaya hankalinta yana kan Sayyid da ta baro a gida, shikaɗai tana gudun kar ta je yana buƙatar wani abin. Ganin gantalin ya yi yawa, ga duk inda suka je sai Uwani ta tsuguna ta surutu kamar babu gobe.
Tun Nana tana jurewa, har ta gaji ta ce "Uwani, na bar mara lafiya a gida, ko za mu je inda zan yi sayayyar, na koma kar na je yana buƙatar wani abin.

Uwani ta ce "Kuma fa haka ne, to mu je na raka ki. Na so ma sai ranar kasuwa za ki je sayayyar, an fi samun rahusa. Ai tun da Allah ya sa ki ka zo garin nan, za ki yi ta ganin 'yan uwa da dangi, za a yi ta zuwa duba mijin naki ma"

Ita dai Nana ta yi shiru, dan duk surutunta, Uwani sai da ta saka ta gaji, ga azabar tafiyar ƙafa da suka sha.

Ta rakata inda ta yo musu 'yan sayayyar kayan abinci, gaba ɗaya tsoron taɓa kuɗin take yi. Gani take yi kamar ƙarewa za su yi.

Uwani ta raka ta har gida, sannan ita ma ta zagaya, ta koma nata gidan.

Nana ta shiga ɗakin da Sallama, tana faɗin "Sayyid, ka ganni sai yanzu ko, ka yi haƙuri Uwani ce ta din ga ja na, ƙafafuwana kamar su karye" Sak dai ta yi shiru ganin wata irin kwanciya da ya yi a kife a kan cikinsa, hannunsa a lanƙwashe, kuma ba kamar mai ruf da ciki ba.
Ga shi a tsakiyar É—akin, ba inda ta tafi ta bar shi ba.

Ta zube kayan ta nufe shi jikint a sanyaye, gabanta na bugawa saboda fargaba da tsoron ko mutuwa ya yi.
Aikuwa tana juya shi ta É—an ja da baya a tsorace tana sauke numfashi.

Wayarta ta gani a ƙarƙashin inda ya kifa, idanunsa a kakkafe, babu baƙar ƙwayar idon, sai farar. Ga jikin zafi rauuu tamkar wuta.
Ajiyar zuciya ta yi cike da damuwa, ta matsa kusa da shi ta yi Bismillah ta fara rage masa kayan jikinsa. Ta É—ebo ruwa ta din ga shashshafa masa tana sake nanata Bismillah.
Ta je ta rufe ƙofar gidan, ta dawo ta cire rigar jikinta, ta kwanta a jikinsa, tana rintse idanunta saboda raɗaɗin da take ji a fatarta.
Wani irin nishi yake, tamkar zai yi gurnani, yana miƙa jikinsa yana ƙara sandarewa.
A hankali ta ji tamkar hankalinta yana gushewa, ita ba a farke be, kuma ita ba mai bacci ba. Ta ɗan ɗaga idonta, ta ga Ƙaisar tsaye a jikin ƙofar ɗakin yana kallon su. Ta yi shiru ba ta yi motsi ba, kuma ba ta yi magana ba, fatanta Sayyid ya samu sassauci daga azabar raɗaɗin da yake ji.
"Ko dai ki bi a hankali, ko wannan ɗan tayin na cikinki ya yo waje saboda zafin jikinsa. Ko kuma Giyaz ya yi masa mummunar illa." Nana ta ɗaga kai ta kalli inda Ƙaisar yake, jikinta ya yi mata wani irin nauyi, ba ta ko iya motsa ɗan yatsanta.

"Babu irin kashedin da ban yi miki ba tun da fari, ki ka yi burus da ni, gani ki ke kawai cutar da ke ne kaÉ—ai abin da nake yi.
Amma tun da jimirnki taurin kai, wahala sai ranar da Allah ya yanke miki, tukuna ma." A hankali ta lumshe idanunta har ta daina jin muryar Ƙaisar.

****

Cikin damuwa Maijidda take kallon Saude ta ce "Yaya Saude haryanzu lambar Nanan ba ta shiga ko? Gaba É—aya na kasa nutsuwa duk ji nake hankalina a tashe".

Saude ta ce "Dan Allah ki daina damun kan ki, in sha Allah tana cikin ƙoshin lafiya, kin san sharrin wayoyin nan, da rashin network, amma zan ci gaba da kiran ta, da na same ta zan sanar miki, kuma zan sake zuwa har gida na haɗa ki da ita."

"To Allah ya sa dai lafiya, kin ga na yi, na yi, na kaɗa na raya, Baban su Walida ya ƙi ba ni wayata, tsawon wannan lokaci haka nake zaune babu waya. Kuma duk wasu dabaru da zan yi na samu dama na je Kano na samu na ga yaran nan, abu ya ci tura sai ka ce ba Muslimi ba, ba ya jin magiya ba ya jin rarrashi".

"A'a kul Maijidda, uban 'ya'yan naki ki ke cewa kamar ba musulmi ba, kar ki sake. Ki rabu da shi da halinsa. Duk da Nana tana cewa za ta zo ita da mijinta, idan ma ba su zo ba, ni zan sake komawa na gano miki ita in Allah ya yarda. Iliyasu kuma ki rabu da shi ku lallaɓa kar ki fusata shi ya yi wani abin da ba a fata"

Maijidda ta yi ajiyar zuciya, ta jinjina kai kawai, amma gaba É—aya ba ta cikin nutsuwarta.

****

Abu kamar wasa, aka shafe kwanaki biyar, Sayyid yana cikin wannan yanayin, sai dai Nana ta juya shi, ta goge masa jikinsa, ta yi masa ƙanin wanka a ɗaki, ta shafa masa turare ta saka masa kaya.
Ga shi juya shi kawai aiki ne, saboda yadda ya yi mata nauyi, ga jikinta babu ƙwari saboda azabar laulayi. Juriyarta ce kawai ta sanya ba a gane mawuyacin halin da take ciki, dan ba ta taɓa yarda ta kwanta.
Ga shi jikinsa duk ya kumbura, mussaman ƙafafuwansa.
Tana zaune ta yi shiru tana kallonsa, kawai tamkar an yaye mata wani abu daga kanta, sarkin baka ya faÉ—o mata. Sai da ta É—an zabura ta tafi tunanin ko yana wani hali yanzu?.
"Ko dai can zan kai ka Sayyid?" Ta yi maganar tana kallonsa.

"To ni da ban ma san a ina yake ba, ta yaya zan kai ka?"

"Kul mene ne sahihancin magungunan da yake bayarwa? Mene ne halacci ko haramcin abin da yake yi, da za ki je neman magani gurinsa?" Wata zuciyar ta gargaÉ—e ta.
Sai kuma ta yi shiru, tana tuna irin wahalhalun da ta sha, da faɗi tashin gurin masu magani, ita dai tana da yaƙinin har gurin bokaye da 'yan tsubbu an kai ta, domin a nema mata magani. Domin wasu ƙarara ayyukansu da abubuwan da suke faɗa, ne nuni da kaucewa hanyar gaskiya.

"Allah na tuba, Allah ya sanya ba wannan ne dalilan da ya sanya nake ta shan wannan wahalar ba. Allah ka yafe mini, ba da son raina aka din ga kai ni wasu guraren ba.
Allah ka bamu lafiya da ni da mijina, Ubangiji Allah ka yaye masa wannan larurar, ka dawo masa da tunaninsa. Allah ban yanke tsammanni da daga falalarka da ni'imamominka ba"

Ta juyo a hankali ta dubi gurin da yake, ta ga idanunsa sun dawo daidai yana kallon ta. A rikice ta ce "Sayyid"

"Ma vie"

Cikin tsananin murna ta ce "Alhamdillah, ka tashi?" Ya jinjina kai yana lumshe idanunsa da suka yi masa nauyi. Ya ja jikinsa ya tashi zaune da kyar. Sai dai jikin nan duk a kumbure,ga kuma haki da ya farfaÉ—o da shi. Haka yau ma ta taimaka masa ya yi wanka ya ci Abinci ya fara rama sallolinsa a zaune.

Kallonsa take yi cikin damuwa, yakamata a ce sun koma Asibiti. Amma kafin a nemo mota a saka shi, su yi sammako su koma Asibiti, aiki ne. Mussaman da babu wadattacen kuÉ—i a hannun ta.
A take ta tuna da maganin da sarkin baka yake haɗawa masu hawan jini, da wanda ɓarin jikinsu ya shanye a sakamakon hawan jini da matsalar zuciya.

Ba ta jira ya idar ba, ta zari hijjabi ta yi waje. Ta din ga tuhumar kanta da yadda aka yi tuntuni ba ta tuna ba, sai yanzu. Tun da su magunguna ne da yake haÉ—a s da saiwoyi ba wani surkullen ya yi ba.

Ta dawo ta tarar ya dawo bakin ƙofa ya zauna yana kallon hanya.

Tafiya mai nisa ta yi sosai da ta fita, ta samo ɓawon kwakwa da sassaƙen zogale, sai kuma farin zoɓo.
Ta hura wuta ta wanke su, duk ta zuba a tukunya ta zuba ruwa, ta kawo É—an kanumfari ta zuba a ciki.
Sai da ta kammala sannan ta koma gurinsa, ta ce "Ka yi haƙuri, magunguna na je samo maka, na fita ka na salla"

"To na gode"

"Allah ya baka lafiya shugabana, Allah ya sanya ya wuce kamar ba a yi ba"

"Amin. Ke ma Allah ya baki lada, ya saka mini ke a aljanna. Ya sanya ki maƙwabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam a aljanna" waro ido ta yi  ta gigice gaba ɗaya hawaye ya fara zirarowa daga idanunta ta ce "Sayyid ba ni da aikin da zai kai ni wannan matsayin. Amma ban san matsayinka a gurin Allah ba. Ban sani ba ko Allah ya karɓi addu'ar da ka yi mini. Amma a ce na maƙwabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Innalillahi wa Innalillahi raji'un Sayyid na rasa me zan ce. Baiwa ce mai tarin zunubai kuma mai tarin rauni. Amma Allah kai mai yawan rahama ne da falala, Allah ka amsa wannan addu'a da ya yi mini shi ma ka ba shi abin da ya roƙa mini"

Ya yi murmushi ya ce "Amin rayuwata"

"Sayyid, anya an taɓa yi mini addu'a da ta tsuma ni kamar wannan? Subhanallah, subhanallah. Na ji daɗi wallahi"
Shima idanunsa ne ya cika da hawayen, ya ci gaba da bin ta da idanunsa. Kawai sai Nana ta ji ta manta kaso mafi yawa na damuwarta. Da ta tuna Addu'ar da ya yi mata sai murmushi ya kasa barin fuskarta.

Maganinta ya daÉ—e yana dahuwa, ta sauke ta mayar da ruwan girki. Ta tsiyaya masa a kofi, ta je ta zauna a gaban sa.

"Sayyid ga magani na dafa maka, mu jarraba, bamu sani ba, ko Allah zai sanya a dace" ya kalli kofin ya kawar da kansa gefe, yana ɓata rai.

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka sha, babu É—aci ko bauri fa"

"Ba na son magungunan nan, babu yadda na iya ne nake shan na Asibitin ma, ni wahalar da ni suke yi"

"To ai wannan ba na Asibiti ne ba, dan Allah ka daure ka taimaka, ba dan ni ba"
Chapter 13 · 0% Book details