Sashe 15
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ce "A'a ba za ki gani ba" . Ta miƙe ya kama hannunta, ya haska fitila har banɗaki, su na zuwa a tsorace ta yi fitsarin, sai dai tana yi sai ga jini. Wani irin kuka ta fashewa da Sayyid. Ta miƙe jikinta yana rawa.
Ya rungume ta ya ce "Ki yi haƙuri, kin ga dare ne, ki daina kuka. Kuma idan za ki yi ɓari, jinin da ki ke zubarwa ya fi wannan kin manta?"
"A'a idan jini ya fara zuba, shikenan ciki zai zube"
Ya ce "A'a, ba haka ba ne, ai bai zuba da yawa ba" Ya lallaɓa ta da ƙyar, ta gyara jikinta, ta ɗauraye jikinta, da banɗakin su ka koma ɗaki.
Karatun Alkur'ani ya kunna a waya, ya ajiye a gefen katifar da suke kai, kamar yadda ya ga tana yi, a duk lokacin da su ka shiga yanayi na tsoro.
Suka kwanta yana É—an shafa ta, cikin sigar rarrashi.
A hankali ta ce "Sayyid"
"Na'am"
"Da gaske mun fita É—azu ko?"
"Eh mun fita"
"Mun je can bayan gari, har ka ce mini kamar ka san gurin?"
"Eh haka aka yi, mun je"
Ta sake cewa "To daga nan meyafaru?"
"Faɗuwa ki ka yi, na riƙe ki muka dawo gida. Tun da muka dawo kuma ki ke bacci"
Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, ta ƙara lafewa a jikinsa cikin tsoro. Yau ma kwana suka yi, tana gane-gane da jin abubuwa daban-daban masu razanarwa.
Wannan bafulatanar matar ce, ta ƙara zuwa ta tsaya a saitin tagat Nana tana kiran ta, a kan lallai sai ta fito ta ga yadda suke gudanar da bikin girka. Nana ta ƙara rintse idanunta tare da ƙanƙame Sayyid.
Da safe ta tashi da wani irin nauyin jiki, ga sanyi da ta kasa daina ji. Ta duba ta ga ba ta kuma ganin jinin nan ba. Ta yi wanka ta rama sallolinta, sai dai Sayyid bai tashi ba. Da ƙyar ta samu ya yi alwala ya yi salla.
Ta gaishe shi, amma bai yi magana ba sai kallonta da yake yi. Hakan ya sanya ta fuskanci maganar ta É—auke.
Ta tambaye shi za ta fita, amma bai ko É—aga kai ya kalle ta ba. Ta saka hijjabi ta fita ta bi 'yan matan gidan Uwani gona roron gyaÉ—a a gona.
Allah ya taimake ta, ta samo da yawa ta zo tsakar gida ta baje ta domin ta sha iska.
Ta É—ora musu Abinci, ta kammala ta fara dafa masa maganinsa, kawai ta ga ya fito daga cikin É—akin. A zaton ta, ko banÉ—aki zai shiga, ta tashi da nufin kai masa ruwa, kawai ta ga ya nufi fita waje.
Da sauri ta bi shi tana faɗin "Sayyid ina za ka je ne haka?" Ya yi mata shiru yana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Ta riƙo hannunsa, amma ya waiwayo fuskarsa a ɗaura kamar bai taɓa dariya ba, saka hannu ya hankaɗe ta, ta faɗi a gurin, ya saka kai ya fice daga gidan. Da gudu ta shiga ɗaki, ta ɗaukko hijjabi, ko takalmi ba ta saka ba, ta bi bayan sa. Ga yamma ta yi liƙis, hanya babu kowa, ta ga ya nufi hanyar inda wannan bishiyar ta kuka take.
"Sayyid dan Allah, dan Allah kar ka koma gurin nan. Me za ka je ka yi?" Sai dai tamkar ba mara lafiya ba, saboda yadda yake sauri.
Sai da ta ɗan haɗa da gudu, Saboda saurin da yake yi, amma ta ji gefen mararta ya ƙulle. Ta daure ta cim masa.
Babu tsammani ta furta "Bismillah wa hifzan min kulli shaiɗanin marid." Aya ta bakwai cikin suratul saffat, kamar yadda Malam Auwal ya taɓa cewa ta yawaita nanata ayar. Gaba ɗaya ta shafe a cikin kanta, sai da ta faɗo mata yanzu. Tana karanta ayar, ta riƙe hannunsa ya ja ya tsaya ya yi shiru ya sunkuyar da kai.
"Mu koma gida" ta yi maganar tana jan hannunsa, tamkar raƙumi da akala, ya bi ta suka koma gida. Allah ya taimake ta, babu wanda ya gan su har su ka isa gida. Ta rufe ƙofar.
Su ka shiga ɗaki, ta kunna fitila ta kalli Sayyid cikin damuwa ta ce "Sayyid me yasa ka fita? Me za ka je ka yi a wajen da?" Ya yi shiru ya sunkuyar da kansa ƙasa fuskarsa babu annuri a ciki.
Ba ta sake ce masa komai ba, ta fita banÉ—aki ta yi alwala, ta dawo ta yi salla, amma ta ga ba shi da niyyar tashi ya yi.
"Sayyid, ba ka yi salla ba fa" Nan ma bai kula ta ba, dan haka ba ta sake magana ba, ta zubo masa Abinci ta zo gaban sa ta ajiye. Ta tashi ta ninke hijjabinta, tana waiwayowa, ta ga ya kifar da Abincin ya tarwatse a tsakar É—akin, yana wani irin huci.
"Sayyid wai meye haka ne? Idan ba ka cin abincin sai ka zubar mini a ƙasa?" Sai dai tana rufe baki, ya wulwula kwanon ya yi jifa da shi guri ɗaya. Ya miƙe ya fara fatali da kayan ɗakin. Take Nana ta fuskanci ba lafiya ba. Jiki a sanyaye ta rakuɓe tana kallon sa.
Tana tunanin yanzu kuma abin har ya kai ga haka? Ba ta yi yinƙurin hana shi ba, ya yi kaca-kaca da ɗakin, ya fita tsakar gida ya nemi guri ya kwanta a dandaryar ƙasa.
Inda ta yi wa Allah godiya ba su da maƙwabta, da kowa sai ya san abin da ya faru. Haka ta durƙusa ta hau aikin gyaran ɗakin, ta kintsa abin da za ta iya kintsawa. Ta dawo tsakar gida inda yake kwance. Ta durƙusa a kan sa, ta dafa shi ta ce "Tashi mu je ka kwanta a ɗaki, nan akwai sauro kuma ƙwari za su cije ka"
Da ƙyar ya tashi, suka koma ɗaki, ya nemi guri ya kwanta a ƙasa. Kawai Nana ta zauna ta zura masa ido, cikin matsananciyar damuwa, duba da yadda take maganin ƙaba amma kai na daɗa kumbura.
A haka dare ya tsala, ta gaji ta kwanta a gefen sa, zuciyarta fal da damuwa. Bacci na ƙoƙarin ɗaukar ta, ta ji tasowar guguwa ta buɗe idonta, ta gan su kwance a cikin sahara, ga yashin saharar na wani irin hanƙoro iska za ta mamaye su. Ta saka hannu ta rungume shi saboda guguwar saharar. Sautin tsohon nan ta ji yana wata irin dariya. Ji ta yi an hankaɗa ta, sai da ta wuntsula ɗakin gauraye da duhu, amma ta ga alamun Sayyid ne zaune a kan katifa shi ne ya hankaɗa ta. Ya tashi ya koma bakin ƙofa ya yi zamansa.
Da kyar ta sake lallaɓa shi, ya koma ya kwanta. Ita ba ta sake komawa bacci ba, ta yi alwala ta zauna tana tasbihi har aka yi sallar asuba. Sai dai fafur ya yi salla ya ƙi yi. Ya nemi guri ya zauna ƙyam yana kallon ta.
Ta dama masa kunu, ta soya fanke, ta zo ɗaki ta zauna a gaban sa. Ta ce "Ga kunu ka sha, amma dan Allah kar ka zubar Sayyid ka ji?" Ta yi maganar tana miƙa masa kofin kunun. Sai ya miƙo hannun hagu zai karɓa. Ta janye kofin ta ce "Hannun dama dai, wannan hannun za ka bani" Ta yi maganar tana nuna hannun damansa, amma bai miƙo mata ba, ya zura mata ido.
Ta kai hannu ta janyo hannun nasa, dan ta damƙa masa kofin kunun, amma ta ji hannun a ƙame ƙam. Ta sake ƙoƙarin janyowa, amma ta ji tamkar tana jan itace.
Ta kalli hannun sosai, sai ta ga shanyewa ya yi.
Gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid me ya same ka haka? Me ya samu hannunka? Ya Allah!" Ta yi maganar tana kuma ƙoƙarin ganin ta miƙar da hannun nasa, amma hannun yana maƙale, kamar an tsotse shi.
Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, fuskarsa É—auke da damuwa. Ta aro jarumta, ta matsa daf da shi, ta É—ebo kunun ta kai bakinsa. Amma ya tsaya yana kallonta, bai buÉ—e bakinsa ba.
"Buɗe baninka na baka" Ta yi maganar tana ƙoƙarin danne hawayen da ke ƙoƙarin ƙwace mata.
A hankali ya buɗe bakin, sai ta ga shi ma bakin ya karkace, yawu na ƙoƙarin zubowa. Kawai ya rufe bakin hawaye ya fara gangarowa daga cikin idanunsa. Ta ajiye kofin kunun ta rasa abin yi. Kawai rungume shi, ta fashe da matsanancin kuka, sai da ta yi iya yin ta.
Sannan ta cika shi, ta share masa hawayensa.
Ta fara ƙoƙarin ba shi kunun, sai dai tana ba shi, ya haɗiye wani kuma ya zubo.
Ta na yi tana goge masa wanda yake zubowa, ta gama ba shi, ta kama hannunsa su ka je waje, ta taimaka masa ya yi alwala. Ya dawo ya rama sallolin da ta gaya masa ana bin sa. Sai dai ba magana ga hannu a maƙale, da ta kalle shi sai ta ji hawaye ya cika mata ido.
Ganin yana gyangyaÉ—i a zaune, ya sanya ta saka masa pillow ya kwanta, ta saka hijjabi ta fita.
Tafiya mai nisa ta yi, ta je ta samu wani chemist, bayan sun gaisa ta ce "Dan Allah malam, idan babu damuwa, Bp nake son mu je ka gwadawa mijina a gida"
Ya kalle ta ya ce "A ina ne?"
"Cikin Budu ne, nan unguwar maharba"
"Taɓ gaskiya da nisa gurin nan ba kaɗan ba, ba zan iya zuwa ba sai dai ki je ku zo tare a yi masa"
"Wallahi da zai yiwu, da ba zan zo na roƙe ka ba, yana kwance babu lafiya ka taimaka mini dan Allah"
Ya ce "Gaskiya kin san cajin zuwa gida ma ka yi wa mutum abu daban yake, sai dai idan za ki ba ni dubu biyu"
Nana ta ce "Eh na yarda mu je zan baka in sha Allah" Ya rufe chemist É—in ya bi Nana.