← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 78

Sashe 46

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hansatu ta ce "Haba Nene, ya ki ke haka kamar ba ki yarda da ni ba ne?"

"A'a ba rashin yarda ba ne ba, 'yar amana ce shi yasa nake jadda da miki, ga kuma ƙaramin yaro da take da shi"

"Ba ki da matsala fa, ki kwantar da hankalinki"

Nana ta kalli Muhsin, da yake jikin Nene, yana wasansa, idanun Nana fal hawaye ta ce "My little Sayyid, zo ka yi sallama da Umminka" ya taso daga jikin Nene ya nufo Nana.

Hatta dogayen gaɓoɓin jikinsa, irin na Sayyid ne sak.

Ta rungume shi a jikinta, hawaye na zuba daga idanunta "Allah ka kula mini da ɗa na, Allah kar ka saka wani abin cutarwa ya same shi, Ubangiji Allah ka sanya na je na dawo na tarar da shi lafiya" ta furta a hankali ƙasa-ƙasa.

Ta ɗago ta kalle shi ta ga yana yi mata murmushi, ta sumbaci goshinsa, ta miƙe ta ɗauki jakar kayan nata, Nene ta rako su har bakin ƙofa, suka hau abin hawan da Hansatu ta zo da shi, suka tafi.

08081012143

68

Nana ta din ga waige, tana hango su Nene tare da Muhsin, har suka ɓacewa ganinta gaba ɗaya.

Hansatu su na tafe su na ta  hira da direban motar, aka biya gidanta, aka ɗauki wasu matasan matan sannan suka ɗauki hanyar tafiya.

Tana jin yadda suke ta hirarrakinsu a cikin motar, amma ta kasa tofa komai, da ta rufe ido, É—an jaririnta take hangowa, gefe guda kuma zuciyarta cike da fatan Allah ya sa tafiyar nan, ta yi mata rana.

A ƙalla sun yi tafiyar awanni biyu da rabi a mota, sannan suka isa wani gida.
Hansatu ta yi musu bayanin, a nan za su sauka su huta, washegari ta kai kowacce inda ta É—aukko ta za ta kai ta. Nana ta din ga addu'a da fatan Allah ya sanya ba mugun hannu ta faÉ—o ba, duk da kafin ta taho Nene ta bata layi ta saka a wayarta, ta ce mata duk abin da ta ga ba ta yarda da shi ba, ta kira ta ta sanar mata.
A duk lokacin da Nana ta É—aga wayar ta kalla, sai ta tuna Hajiya Amina, Haidar da kuma sauran jama'arta na Nigeria.

A gidan nan suka yi salla, aka ba su abinci suka ci, sai dai Nana ta yi mamaki ganin mata da yawa a gidan. Duk da ƙabilu ne daban-daban matan, akwai Zabarmawa, akwai Bugaje, da hausawa da sauran ƙabilun ma da ba ta sani ba a Nijar. Wai gidan kamar kamfani ne, wannan matan aiki ake nema musu, duk ciki Nana ce kawai 'Nigeria a cikinsu. Gaba ɗaya ta takure kanta ta kasa jikinta da su.
Gaba É—aya daren ranar, Nana ta kasa bacci, ta din ga tunanin Muhsin, da tunanin ko zai yi kukan rashin ganinta.
Washegari Hansatu ta ce wa Nana ta shirya, ta É—auki kayanta su tafi. Haka kuwa aka yi ta sake É—aukarta su ka fita.

Nana ta sha mamaki, ganin haɗuwar da gurin cin abincin ya yi, kuma babban abin da ya ƙara bata mamaki, gurin cin abincin tamkar hotel.
Suka shiga cikin gurin, Hansatu ta kai Nana wani katafaren ofishi, da yak3 gurin mai kula da É—aukar ma'aikatan, da yake namiji ne. Rawaninsa ne ya tabattar mata da buzu ne, ganinsa kawai sai Nana ta ji wani irin sanyi, tamkar ta ga Sayyid.

Nana ta gaishe shi, ya amsa sama-sama yana É—an basarwa.
Hansatu ta ce masa "Wannan ita ce ma'aikaciyar, na kawo ta a yi mata gwajin, a gani idan za ku ɗauke ta" Ya ɗaga kai ya  sake kallon Nana ya ce "Sannu ko"

Nana cikin girmamawa ta ce "Yauwwa sannu da aiki"

Ya miƙo mata ƙunshin wasu takardu ya ce "Ga wannan duba, ki ga yadda tsarin aikin namu yake, ki gani idan sun yi miki, kafin mu je inda za a yi miki gwajin, idan kin ci sai ki sanya hannu a takardun, ki fara aiki da mu"
Nana ta saka hannu ta karɓi takardun, amma ta ga rubutun French, ta kalli Hansatu, ta kalle shi ta ce "Ai ban iya fransanci ba"

Ya kalli Nana ya ce "Ba ki yi makaranta ba?"

Ta ce "Na yi, amma ni ban iya French ba, turanci na iya sai Hausa"

Hansatu ta ce "A yi haƙuri Yallaɓai, 'yar Nigeria ce, daga Nigeria take"

Sai kuma ya kalli Nana ya faɗaɗa murmushinsa ya ce "Daga Nigeria ki ke? Ki ka baro babbar ƙasa kamar Nigeria ki ka zo jamhuriyar Nijar ki yi aiki da mu?" Nana ta ɗan risunar da kai tana murmushin dole, ganin yana murmushi shi ma.

Ya ce "Ahh to ai 'yan Nigeria ƙawayenmu ne, ba ma ƙawaye ba 'yan uwanmu ne. Dan haka zan ba ki aiki amma da sharaɗin za ki koya mini turanci, idan kin yarda na baki aiki" Nana ta yi murmushi, saboda yanayin yadda ya yi maganar cikin zolaya. Ya yi 'yar dariya ya ce "Ai duk wanda ya zo Nijar, mussaman daga Nigeria baƙonmu ne, akwai buƙatar mu karrama shi sosai da sosai, ko dan ƙara zumuncinmu da mutanen Nigeria. Dan haka babu wani abu, wannan wani ci gaba ne ma zan iya cewa gurin Abincinmu ya samu, kin ga girke-girken da ba a yi a nan, na can ƙasar kya din ga yi mana.
Mu na da gurin kwana na ma'aikatanmu, awa ashirin da huÉ—u muke yi mu na aiki. Kamar yadda ki ka gani babban gurin cin abinci ne da manyan mutane ke zuwa cin abinci.
Masu sayar da abinci daban, masu girki daban, ke za ki kasance a ɓangaren masu girki ne. Mu je mu zagaya ku ga gurin sosai da sosai.

Ya jagoranci su Nana, ya nuna musu gurin, tsarin ya yi wa Nana sosai, duk da abin da ba ta ji daɗi ba, maganar zuwa hutun sati ɗaya ne kacal, duk ƙarshen wata.
Su Hansatu za a din ga tura wa albashinta, su cire nasu kason su bawa Nana sauran.
Ita Nana duk hakan bai dame ta ba, babban fatanta buƙatarta ta biya kawai.

Suka kammala duk cike-ciken da za su yi, aka sallami Hansatu, Nana kuma aka kaita gurin kwanan ma'aikata.
Ɗakin da aka kai Nana, su uku ne a ciki, da banɗaki a ciki. Ta ajiye jakar kayanta, Hansatu ta kalle ta ta ce "To Nana, kamar dai yadda ya gaya miki, mu kamfani ne, kuma a ƙarƙashinmu ki ka zo nan, dan haka gurinmu albashinki zai din ga tafiya, mu zamu din ga sallamar ki"
Nana hakan ko a jikinta, dan ita ko ba za su ba ta komai ba, indai akwai gurin kwana da abinci, kuma kwalliya za ta biya kuÉ—in sabulu, hakan ba damuwarta ba ne ba.

A fili ta ce "Babu damuwa, hakan ma na gode sosai da sosai, Allah ya saka da mafificin Alkhairi".

"Amin, a hakan ma gaskiya kina da sa'a sosai da sosai, sai da muka kawo musu mata uku, da ƙyar suka ɗauki ɗaya, wai duk ba su yi musu ba, wasu kuma sai an zo yi musu gwaji sai su faɗi. Amma ke ya ce ba zai yi miki ma gwaji ba, kawai an ɗauke ki aikin.
Abin da zan gaya miki kawai shi ne ki kula, ki kula da kanki sosai da sosai, banda ƙazanta banda son jiki.
Sannan kar ki ga kin tsallake wannan matakin, ya ɗauke ki aiki a haka cikin sauƙi, ki zata miƙe ƙafa za ki yi, mace ce mai gurin nan, kuskure kaɗan za ki ta ci mutuncinki ta kore ki. Su kan su ma'aikatan kwantar da kai suke yi, su na yi mata biyayya, duk wata tijara da bala'inta kawai ki toshe kunnenki ki yi haƙuri." Nana ta yi shiru, sai da Hansatu ta gama gaba ɗaya sannan ta numfasa ta ce "To Ubangiji Allah ya iya mana"

Hansatu ta amsa da "Yauwwa Amin"

Hakanan Nana ta ji a jikinta, ba za ta ɗauki wulaƙanci da cin zarafi ba, duk da kuwa abin da take son cimma. Ko Nene da ake kambama faɗanta da masifarta, ba ta cin mutunci, kuma duk abin da za ta yi faɗa a kai, to a kan gaskiya ne. Amm yanayin yadda Hansatu take yi mata bayanin mai gurin nan, a kaikaice dai ba ta san darajar mutane ba.

ÆŠakin da Nana take, ita da wasu Zabarmawa ne guda biyu. Ta yi alwala ta yi sallar Azahar.
Ta daɗe a kan abin salla, tana gaya wa Allah, cikin magiya a kan ya sanya ta samu abin da ta fito nema, ya kuma raba ta da duk wani sharri da abin ƙi.
Bayan ta idar, É—aya daga cikin 'yan É—akin, ta ce mata ta zo su je ta zagaya da ita.
Can ɓangaren da ake girke-girken ta kai Nana, suka zagaya daga nan ta kaita cikin gurin da ake sayar da abincin. Nana ta yi mamakin girman gurin, da yadda gurin Abincin yake da tarin kwastomomi. Sai dai da gani ka san na manya ne, dan duk waɗanda suke zuwa gurin cin abinci akwai alamun abin hannu a tattare da su.

*****
Chapter 46 · 0% Book details