← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 78

Sashe 25

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gaskiya ba za ki sayar da kayan nan ba, ki bari ranar kasuwa, zan kai Tinkiyata kasuwa, na baki kuÉ—in amma ba za a sayar da kayan ba" Gaba É—aya Nana ta ji ta damu yadda ta É—orawa Uwani É—awainiya.
"Uwani kar ki sayar da Tinkiyarki dan Allah, gara a sayar... "Za ki rufe mini wannan dogon bakin naki, ko sai na kwaÉ—e ki? Ke ki ka sani na sayar? Ke dai akwai gardama"
Babu yadda Nana ta iya, haka ta haƙura sai ranar kasuwa, aka sayar da Tinkiyar. Uwani ta ɗauki dubu talatin a kuɗin ta bawa Nana ta ce "Ban san iya adadin kuɗin da ki ke buƙata ba, amma ga wannan kya jalauta. Dan Allah ki kula da kan ki Nana, duk inda ki ka je idan kin ga akwai matsala, ki dawo mini nan ni zan riƙe ki na kula da ke" Nana ta din ga juya kuɗin, ta kalli Uwani idonta fal hawaye ta ce "Na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi na gode"

"Babu komai, Ubangiji Allah ya sauke ki lafiya, ya bayyana mijinki cikin aminci. Nan ma za mu ci gaba da jiran jami'an tsaro ko za a samu wani labari daga gurinsu. Allah ya bayyana shi"

Nana ta amsa da Amin. Jin washegari Nana za ta bar garin, ya sanya 'yan uwa, suka din ga kawo mata abin alheri cikin mutunci da karramawa, tare da yi mata fatan alkhairi.

Washegari da sassafe, Nana ta yi sallama da su Uwani, aka ɗauke ta a babur aka kai ta tashar ƙauyen. Aka kaita Garko, daga nan ta hau motar Kano. A Kano ta hau motar da za ta sada ta da garin Bauchi.
Tsawon awanni huɗu da aka shafe, ana tafiya a motar, babu abin da Nana take yi, banda tunani ta saƙa wannan ta kwance wancan. Tunaninta a wani hali yake ciki, ya jikinsa? Su waye suka ɗauke shi? Mene ne makomarta idan bai dawo ba.
Lokaci-lokaci ta kan shiga hijjabinta ta yi kuka, ta share hawayenta.

Da ta sauka a tasha ƙarfe sha biyu na rana, ta samu abin hawa, har sunan unguwar da Mamanta take ta sani, sai dai ba ta san takamai ina ne gidan ba. Shi ma daga tashar zuwa garin da maman nata take, sai da aka yi tafiyar awa ɗaya da rabi. Ƙafafun Nana duk sun kumbura, da ƙyar take jan su. Ta ɗaukko wayarta ta kira lambar Anty Fati, ta ji ba ta shiga. Ta kira ta Adda Saude ba ta ɗaga ba. Ta nemi guri ta zauna, ta ci gaba da kiran wayar Adda Saude da ita kaɗai take shiga.
Sai dai still ba a É—aga wayar, ga shi ba ta san daga garin, ina ce unguwar da za ta nufa ba.
Ta samu guri ta yi alwala, ta ciro sallaya a kayanta, ta shimfiÉ—a ta yi sallar azahar.
Bayan Azahar sosai, Adda Saude ta kira wayar Nana.
Nana ta ɗaga tare da yin sallama. Ta amsa mata ta ce "Nana yi haƙuri, caji na kai wayar ne aka kunna mini, ya ki ke ya gida?"

"Lafiya kalau Adda, kin ganni na zo Bauchi ne na sauka, sai dai ban san sunan unguwar da Mama take ba"

"Ke haba dai, da gaske ki na Bauchi Nana?"

"Eh Adda, na sauka ma tun É—azu"

"Subhanallah, ai ba ki gaya mini za ki zo ba, da tuni an shirya karɓar ki, ban sani ba an bar ki ki na jira, dan Allah ki yi haƙuri yanzu ki na daidai ina, na zo na tafi da ke?"

Nana ta ce "Kar ki wahalar da kan ki dan Allah, ina garin ma, sunan Unguwar za ki gaya mini" Sai da Adda Saude ta É—an ji dumm, amma ta maze ta cewa Nana ta samu abin hawa, ta haÉ—a ta da mai abin hawan ta yi mata kwatance.
Nana ta ce "To" ta samu abin hawa, ta haÉ—a su ta kwatanta masa, sannan ta hau.
Nana ba ta isa gidan da Mamanta take ba, sai ana kiraye-kirayen sallar la'asar.
Mama na tsakar gida tana ta fama da yara, kawai ta ji sallamar Nana. Ta É—ago da hanzari, sai dai ta kasa amsa sallamar ta nufi Nana da sauri suka rungume juna su na kuka.

Ta É—ago Nana ta ce "Nana ba ki yi fushi da ni ba?"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ban yi ba"

Ta ja hannun Nana zuwa ɗaki, ta saka yaran su shigo mata da ƙatuwar jakarta.

"Sannu da zuwa, tare ku ke da mai gidan naki ne?" Nana ta sunkuyar da kai jikinta a sanyaye ta girgiza kai alamar a'a.

"To yana ina shi?" Nana ta yi shiru.

Cikin tashin hankali Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nana ba dai auren naki ne ya mutu ba?" Nan ma ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta.

"Shikenan, yanzu nutsu. Bari na ɗora miki ruwa ki yi wanka, sai ki yi salla" Nana tana iya ganin tsantsar farinciki a kwance a fuskar mahaifiyarta. Ƙannenta suka kewaye ta, Nana ta din ga kallon su cike da so da ƙauna. Har gara Walida ta ɗan santa sauran kuwa duk ba su san Nana ba.
Ruwa mai É—umi ta haÉ—a wa Nana, ta yi wanka, ta yi sallar la'asar.
Ta zubo wa Nana lafiyayyen Abinci, duk da yadda ranta ya biya a kan Abincin, amma ta kasa sakin jiki ta ci.
Mama ta din ga kaiwa tana komowa, tana ta É—awainiya da Nana tamkar ta goya ta, sai ta ji ina ma tuntuni ta samu irin wannan kulawar ta uwa.

"Nana ina Imrana kuwa, ya daina zuwa gaba É—aya"

Nana ta ce "Lagos yake tafiya neman kuÉ—i"

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ai shikenan, ya aka yi ina mijin naki ne? Me ya faru?"

"Nemansa na yi na rasa"

Cikin rashin fahimta ta ce "Kamar yaya?"

Nana tana kuka ta yi mata bayani. Cikin mamaki ta ce "To ina 'yan uwansa? A ina yake a Nijar ɗin?" Sai a lokacin ta fayyace wa Maman komai, game da auren zuwa ɓatan sa.

"Nana, me yasa baki neme ni kin gaya mini ba? Yanzu duk wannan abin yake faruwa amma idan muka yi waya sai ki ce mini komai lafiya ƙalau? Ni kaina nan kina raina, ina ta fafutuka na ga yadda zan yi na zo na gan ki. Ba ki kyauta ba Nana, komai lalacewata, ni mahaifiyarki ce, yakamata a ce kin sanar da ni.
Yanzu dai ki zauna a nan, mu ga abin da Allah zai yi, kafin ki haihu mu gani ko Allah zai sanya a ga mijin naki. Amma na yi mamaki matuƙa da mahaifinki ya aura miki wanda bai san usulinsa ba? Yanzu ƙiyayyar da yake yi minin har ta kai haka?
Ko yana jin haushina amma ai ke 'yar sa ce, bai cancanci ya yi miki haka ba, amma babu komai.
Nana abin da nake so da ke, daga yanzu duk abin da ya faru Nana, ko ba zan yi miki komai ba, ki sanar da ni, ki bani dama na taka rawa ta ta uwa a rayuwar ki ko yaya ne" Ta yi maganar tana riƙe hannun Nana.

Sallamarsa ce ta tilastawa Nana haÉ—iye abin da take shirin furtawa, cike da tsoro.
Ba ita ba hatta Maijidda, sai da zuciyarta ta buga da ƙarfi cike da tsoro.

AYSHERCOOL
08081012143
61

Har zai gifta, zai shiga É—aki ya hango Nana, cikin rawar baki, Nana ta gaishe shi, ya amsa mata sama-sama ya wuce, dan kallo É—aya ya yi mata, ya gane ta.

Jiki a sanyaye Maijidda ta tashi ta bi shi ɗaki, tana ɗan sinne kai, tana jiran ta ji me zai ce, amma bai ce komai ba. Ta kawo masa Abinci, tana jiran ta ji me zai ce, ga hankalinta a kan Nana, tana so ta je ta yi hira da 'yar ta, su yi hira ta ji ɗuminta, amma ta haƙura.
Nana ma na ta gaban ne yake faÉ—uwa, tana tsoron abin da zai ce, saboda ba ta manta karan battarsu.
Haka dai a É—arare suke hira da yaran gidan.
Maijidda na ta son yi masa magana, amma ta kasa.
Ya gama cin abincin ya fita, ba tare da ya ce komai ba.
Yana fita ta koma gurin Nana, suka ci gaba da hira, Nana ta kwanta a kan cinyar Mamanta, tana jin wani irin farinciki yana ratsa ta.

"Kin fara zuwa awo ne Nana?"

Wata irin kunya ta kama Nana, ta É—an sinne kai ta girgiza mata kai. "Gaskiya yakamata, wata nawa ne cikin? Mu je a yi awo a duba, mu ga abin da zamu fara ajiyewa. Mu jira mu ga ikon Allah, idan an ga mijin naki shikenan, idan ba a gan shi ba kuma, ma san abin yi" Nana dai ta yi shiru, sai kuma ta ce "Mama ki yi mini addu'a, ki ce Allah ya bayyana shi cikin aminci"

Mama ta yi dariya, ta ce "Lallai kam, to shikenan, Ubangiji Allah ya bayyana mini sirikina cikin aminci"

Nana ta yi murmushi, dan kunya ce ta kama ta daga baya, da tuna katoɓarar da ta yi.

Da daddare Mai Jidda ta yi wa Nana shimfiÉ—a, ta saka nata net. Sannan ta tafi nata É—akin gurin mijinta, har za su kwanta, Mai Jidda ta dubi Iliyasu, jiki a sanyaye cikin ladabi ta ce "Baban Walida, na ga ka dawo ka ga Nana a gidan nan, ba ka ce komai ba"

Ya dube ta ya ce "To me ki ke so na ce?"

"Ahh dama kar ka ce ban gaya maka ba ne, dama ta É—an zo ta zauna da ni ne, duba da yadda...

"Kin ga dakata, na ɗaga miki ƙafa ne na yi shiru, na ga gudun ruwanki, kar ta wuce mini gobe a gida, ta wuce ta koma inda ta fito"

"Dan Allah ka yi haƙuri Baban Walida, Nana ta samu matsala a aurenta ne, dan Allah ka yi haƙuri ba za ta daɗe ba, amma dan Allah kar ka ce ta tafi yanzu. Ni ko ruwan gidanka ka ce ba za ta sha ba, na amince dan Allah"
Chapter 25 · 0% Book details