Sashe 58
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ramata ta kalli Nana ta yi mata kallon banza, ta ɗan kwaɓe baki sannan ta yi gaba Nana ta bi bayanta.
Duk yadda Nana ta so sarrafa kanta ta kasa, ta ɗaga kai ta din ga kallon ƙawataccen gurin tare da jinjina yadda masu gidan suka ƙware a iya almubazzaranci. Dan ba za ta kira shi ado ba kawai sai dai almubazzaranci.
Tana saka ƙafarta a cikin falon, ta ji tamkar an jona mata shocking, saboda rawar da jikinta ya yi, sai da farantin hannunta ma ya girgiza tamkar zai ɓare. Ramata ta kalle ta, ta yi tsaki kawai.
Nana ta ajiye kayan a hankali a kan carfet É—in É—akin.
Bayan ta ajiye ta yi taku huɗu zuwa biyar, ta ji yadda adadin sanyin da take ji yana ƙara yawa. Ta sauke idanunta a kan ƙaton frame da hotonsa a jiki. Danƙarewa ta yi a guri ɗaya, ta kasa motsa ko da ƙafarta.
Taku ta fara ji a bayanta, ana tahowa, muryar Asal ta ji tana magana da faransanci cikin shagwaɓa.
ÆŠan ja ya yi ya tsaya, jin yadda jikinsa ya yi wata girgiza.
"Lafiya dai ko?"
Ya jinjina mata kai alamar eh.
"Amm me ku ke yi a tsaye a gurin nan ne?"
Ramata ta ce "Abinci muka kawo"
"Waye ya yi?"
Ta nuna Nana da ba ta juyo ba.
"Zo" ta kira Nana sai dai Nanan ta ƙame ba ta juyo ba. A wulaƙance Ramata ta taɓa ta ta ce "Ana yi miki magana"
"Tana ji na rainin hankalin za ta yi mini"
Sannu a hankali Nana ta juyo, idonsa na kan wayar hannunsa.
Yanzu ta tabattar da mafarki ta yi ba, Sayyid ta gani, sai dai ganinsa bai razana ta ya kiÉ—imata ba, kamar yadda alamu suka nuna Asal matarsa ce ba.
Ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana jan ƙafafuwanta a hankali.
"Me ya same ki ne?"
Ta girgiza kai alamar ba komai.
"Ki yi mini magana kina girgiza kai kawai"
"Ba ni da lafiya"
Asal ta ja tsaki ta ce "Je ki kar ki ɓata mini rai"
Ta zuba masa shayin a kofi, ta zuba masa madara, ya É—auka a hankali ya kai bakinsa yana sha.
Nana kuwa a ɗakinta, gaba ɗaya ta burkice, tamkar za ta yi hauka ta ce "Dama abin da ka ke gargaɗina a kai kenan Ƙaisar? Sayyid me yasa za ka yi mini haka, dama ka na da wata matar ka aure ni? Yanzu ka na nufin ka manta ni, Sayyid anya alƙawari ya ce haka? Na haƙura zan ɗauki ɗa na na koma gida, ganinka da wata kawai ya isa ya yi ajalina. Wataƙila alhakin iyayena ne ma da na taho ba da izininsu ba. Yadda ka ke a cikin daular nan, yaya za a yi na ce ina da alaƙa da kai ma a yarda da ni?" Ka ce Ruhina da naka su na rayuwa a tare, kowannenmu yana ɗauke da ruhin ɗan uwansa, ni na yi dakon soyayyarka ashe ka na da matar da ta fi ni komai" Ta yi maganar cikin matsanancin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta.
Yana tsaye yana jin yadda ruwan yake ratsa shi daga cikin gashin kansa zuwa jikinsa.
Wani irin zafi yake ji a cikin ƙwaƙwalwarsa, tamkar kansa zai tarwatse.
Karo biyu yana jin jikinsa ya yi girgiza.
Ya yi wankan ya lulluɓo jikinsa da towel.
Asal ta sha kwalliya cikin baƙaƙen kaya na bacci.
Ta nufo shi tana rangwaɗa, ta cire towel ɗin da ya lulluɓa da shi. Ya ɗan lumshe idanunsa saboda ƙamshin turaren da Asal take yi mai jan hankali.
Ta shige jikinsa ta rungume shi, ta ce "Na yi kewarka sosai Imam"
"Nima ina jin kewar abin da ban san mene ba, bayan kewarki da na yi"
"Akwai abin da ya fi ni muhimmanci dama, da har ka ke kewarsa fiye da ni?"
"A'a ban ma san mene ba, kawai dai ina jin akwai wani abu da ba daidai ba"
Ya yi maganar yana shafa gefen wuyanta, yana son tambayarta wace ce yarinyar nan, amma ya haÉ—iye ya fasa.
Ya fara ƙoƙarin sumbatar ta, sai dai ya ja da baya da sauri yana dafe kansa, da yake jin wani sauti mara daɗin ji a cikin sa.
"Imam jikin ne dai?"
Bai yi magana ba, ya hau kan gadon ya kwanta ya lumshe idanunsa.
Washegari da safe, idanun Nana sun kumbura suntum, saboda ba ta rintsa ba ko kaÉ—an.
Ta saba da wuri take tashi, ta fara gudanar da aikinta, amma sai da aka zo aka kira ta, ta ce ba za ta yi aikin ba.
Bayan mintuna talatin sai ga Asal a ɗakin, ta kalli Nana a wulaƙance cikin isa da gadara ta ce "Ki ka ce ba za ki yi aiki ba yau? Saboda gidanki ne ko zaman kan ki ki ke yi a gidan? An kai wa Imam shayi ya ƙi sha ya ce ba irin na jiya ba ne"
"Eh ba zan yi girki ba, kuma barin gidan nan zan yi, na gaji da wannan aikin, zan je na ga yarona"
Asal ta yi dariya ta ce "Ai kuma ƙarya ki ke yi. Na ɗaukko ki gidan nan saboda nesanta mijin da waɗanann munafukan hadiman, na kawo bare da baki san komai a kan harkar gidan mulki ba. Kuma ba kya cikin kalar matan da za su iya ɗaukar hankalinsa. Dan haka na kawo ki ne dan ki din ga kula da abin da Imam zai ci aikin da ki ka zo yi gidan nan kenan.
Nana ta yi wa Asal wani irin kallo mai cike da tsana, ji take tamkar ta kama Asal ta yi ta jibgarta har sai ta ji ta huce.
"Gimbiya Asal, ai an bar kari tun ran tubani. Ba zan yi girki ba sai dai yunwa ta kashe Imam É—in, ke da yake aure idan ba za ki girka masa ba, to kar Allah ya sa ci, sai na bar gidan nan ba zan zauna ba" Ta yi maganar cikin É—aga murya da zazzaro ido.
Asal ta yi taku biyu, ta hankaɗa Nana baya ta ce "Ki kiyaye harshenki a kan abin da zai din ga fitowa daga bakinki, a kan mijina. Biyan buƙatata ce kawai ta sanya nake ƙyale ki, ki daina ƙoƙarin ƙetare iyaka. Tafiya kuma ga hanya nan maza ki tafi mu gani, idan kina tunanin da ka na kawo ki gidan nan na ajiye"
Ayshercool
08081012143
Littafin kuÉ—i ne, 1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic bank ku tura mini hakkina kan ku karanta.
72
Sai da Nene ta tabattar Nana ta É—an nutsu, sannan suka kwanta.
Washegari Nene ta fita, ta bar Nana a gidan tare da Muhsin. Bayan ta dawo daga gurin sama'arta ta cewa Nana, yakamata ta je ta ɗan sai abubuwan da za ta buƙata saboda tafiyar da za ta yi da nisa, kuma ba su san yaya tsarin aikin can ɗin yake ba.
Nana ta ce "Ni babu abin da nake buƙata, ki bani wani abin na riƙe a hannuna, sauran kuɗin kuma ki riƙe saboda kula da Muhsin na s...
"Biyana za ki yi kenan dan na riƙe miki Muhsin?" Nene ta katse ta.
"Allah ya baki haƙuri, ba haka nake nufi na, na ga dole ɗan abubuwan buƙatunsa duk ke ki ke yi masa Nene, tun da ga kuɗi sun"
"Kuɗinki ba su isa su saka na riƙe miki ɗa ba ko?"
Nana ta ce "Na sani, ai shi ya sanya na ce ki yi haƙuri.
Nene ta ce "Ba zan yi haƙurin ba sai na gama, kin iya kunna ni da na fara faɗa ki hau bani haƙuri, wato in ci kaina to sai na idar"
Nana ta yi mata shiru ta yi faÉ—anta ta gama.
Washegari Nene ta saka Nana a gaba suka je kasuwa, ta sata ta yi sayayyar kayan sakawa da na É—an shafe-shafe, ta yi wa Muhsin sayayyar kayan sakawa da pampers. Babu yadda ba ta yi da Nene ba ta É—auki wani abin ta ce ba za ta É—auka na.
Nana ta haɗe rai ta ce "Eh dama ba ki ɗauke ni 'yarki ba, shi ya sanya duk abin da zan yi miki ba kya karɓa"
"Ni za ki yi wa wayo, na ji ban ɗauke ki 'yar ba, ni ga ɗana nan" tayi maganar tana shafo Muhsin da ke bayanta. Da ƙyar sai da suka kai ruwan rana Sannan Nene ta karɓi abin da Nana ta saya mata.
Sai dai kan su bar kasuwar har sun shirya. Nana ta ce "Nene kin ce mini ki na da ɗa, amma ban taɓa ganinsa ya zo ba, ba ya zuwa ya gan ki ne?"
Nene ta ce "Kamar ban damu da shi ba ko?"
"A'a kawai dai tambaya na yi "
"Yana can Nigeria"
"To me yake yi a Nigeria ba ya zuwa inda ki ke?"
"Sana'a yake yi, ai ya zo ki na can gurin aiki"
Duk da Nana ba ta gamsu da amsoshin da Nene ta ba ta ba, amma ta basar ta ce "Allah sarki, Allah bai yi zamu haÉ—u ba".
Haka suka ci gaba da hira suka koma gida, Nana ji take yi tamkar ta É—auke É—anta ta tafi da shi.
Gidansu Ashura Nana ta je, ta samu keke ta É—iÉ—É—inka kayan da ta sayo, ta sake haÉ—a jakarta ta É—auki muhimman abubuwa a kayanta.
Duk da a ɗaki Nene take rufe mata su, ba ta taɓa ganin alamar Nenen tana yi bincike a cikin kayan ba.