← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 78

Sashe 42

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dama idan Hajiya Sa'a na nan, ba ya iya yi mata magana, da zarar ta fita kuma sai Jamila ta kulle ƙofar sashen. Ya rasa abin da yake yi masa daɗi, har layi ya canza ya kira Jamila, amma tana ɗagawa ta ji muryarsa ta kashe.

Ga shi tun da Hajiya Sa'a ta fuskanci abin da yake tsakanin su, ta daina yawan fita ta bar Jamila a gidan, idan ma fita za ta yi sai dai su fita tare. Sai dai yau Jamila ba ta jin daÉ—i, dan haka Hajiya Sa'a ta fita ita kaÉ—ai, saboda ta sakankance Abba yana can kasuwa.

Awa guda da tafiyarta, Jamila na kan doguwar kujera tana bacci, ta ji tsayuwar mutum a kan ta. Ta buÉ—e idonta a hankali ta ga Abba a tsugune a gabanta yana kallonta.

Tashi ta yi zaune tana tsuke fuska tare da gyara zaman rigarta za ta tashi.

Cikin zafin nama da tsoron rashin sabo, ya riƙe hannunta ya ce "Dan Allah Jamila ki tsaya ki saurare ni" ya yi maganar cikin marairaicewa kamar zai yi kuka.

"In saurare ka ka ce mini me Yaya Abba? Dan Allah ka rabu da ni." Ta yi maganar itama idanunta fal hawaye, saboda ba ta taɓa sanin ta kamu da matsananciyar soyayyar Abba ba, sai yanzu da Hajiya Sa'a take ƙoƙarin farraƙa su.

"Jamila dan Allah ki fahimce ni, kin san a son raina ba zan auri wata ke ga ki na bar ki ba, wallahi Jamila ina son ki, ban taɓa son wata 'ya ba sai ke"

Ta kalle shi hawaye na zuba daga idonta ta ce "Ko ma mene ne, ai yanzu aure za ka yi, ka rabu da ni dan Allah"

Girgiza kai ya yi cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ganin yadda take zubar da hawaye, zai yi magana ta fizge hannunta ta shiga ɗaya falon, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya sake bin ta yana ƙoƙarin rarrashinta.

Sai dai kash, garin ya rarrashi Jamila, sai shaiɗan ya buga musu ganga su ka taka rawa, duk da Jamila ta fuskanci cin zarafi da keta haddi a ƙungiyarsu ta asiri, a wannan karon ma tsoro da rashin sabo suka yi tasiri a a gare ta, duk da a nasa ɓangaren ma haka ne.

Daga shi har ita suka saka kuka mai cike da nadama da dana sanin abin da suka aikata.

Maganganun Nana suka din ga dawo mata daki-daki, na nasihar da ta din ga yi mata a baya. Duk da babu wanda ya san halin da Nana ne ciki, a tsawon wannan lokacin kusan shekara guda, amma gara Nana da ita, Ko ba komai Nana aure ta yi, ita kuwa fa da fari bokaye da aljanu sun kwanta da ita, a wannan karon kuma ruÉ—in soyayya da sharrin shaiÉ—an.

"Jamila, dan Allah ki yi haƙuri, ki kuma rufa mini asiri, ke ma kin sa hakan ba halina ba ne ba, amma duk yadda zan yi, zan aure ki, ni na fara aikata ɓarnar nan, kuma zan gyara ta in sha Allah"

Jamila ta kalle shi ta kawar da kai, tana jinjina lallai Abba bai san komai ba, tun da bai iya gane ba budurwa ba ce ba, duk da bayan abin da Hajiya Sa'a ta kai ta aka yi mata, bazama ta yi neman magungunan gyara.

Ya lallaɓata ta gyara jikinta, ta nemi guri ta kwanta, ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Ya koma part ɗin sa ya rufe ƙofa, kawai ya fashe da kuka. Bai taɓa tunanin aikata zina a rayuwarsa ba, ba ta taɓa burge shi ba, bai kuma taɓa kawo ta a ransa ba. Sai dai yau ya wayi gari da aikata ta dumu-dumu.

Sai dai wani abin mamaki duk da abin da ya faru a tsakanin su, bai daina jin matsananciyar ƙaunar Jamila ba. Ya rasa dalilin da ya sanya Mummy ba ta son alaƙar su, duk da irin kusancin da yake tsakaninta da Jamilar.

A kwance Hajiya Sa'a ta dawo ta tarar da Jamila. Ta ce "Daughter haryanzu jikin ne? Ko Asibiti za mu je ne?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a Mummy na sha magani ai"

"Yakamata ki warke, mun kusa zuwa taron ƙungiya fa na shekara, lokaci ya kusa"

Kawai Jamila ta gyaÉ—a kai.

"Ga shi kuma haryanzu babu wani labari da ki ka samo, a kan 'yar uwakki, dan haka sai ki shirya sadaukar da jini"

Jamila dai ta yi shiru, tana jin kamar ta kashe tsinnaniyar matar ta huta.

*****

Nana na zaune tana shayar da Muhsin, Nene tana gefe tana lissafa kuÉ—in da aka kawo mata daga gurin sayar da Abincinta.

Nana ta numfasa ta ce "Nene wai me yasa kwana biyu ba kya fita gurin Abinci ne?"

Nene ta kalle ta ta ce "Na fita ki samu damar guduwa ko?"

Nana ta yi turus tana kallon Nene.

Nene ta yi murmushi ta ce "Yarinyar nan ki na wasa da ni, tuni na gane duk wani take-taken ki ai, jira nake yi na ga iya gudun ruwanki. Ke yanzu idan ki ka fita gidan uban wa za ki je? Ki na da tabbacin za ki iya sake haÉ—uwa da mutanen da za su kula da ke ne? Ko an gaya miki kowa ne zai iya yin taimako?

Kin tattara kayanki gaba ɗaya, kina ɗauke ɗanki daga ɗakina, jira ki ke yi ki samu dama ki gudu, to ki tafi duk inda za ki tafi, amma ba za ki tafi da jaririn nan kina gararanba a gari ba, tun da duk ƙoƙarin da nake yi a kan ki ba kya gani. Kina zaune a nan na saka ana ta yi mini cigiyar masu gadi da suke zuwa Nigeria, ko akwai wanda ya san mai suna Habu ko Sayyid ki ka ce sunansa ko wa? Anma ba kya gani, to ki fita ki tafi duk inda ki ka ga dama, tun da ba ki da kan gado, kuma ba ki san darajar igiyoyi ukun da ke kan ki ba"

Nana ta sha jinin jikinta, da faɗan da Nene take yi mata. Ta ce "Dan Allah Nene ki yi haƙuri, na ga na ɗora miki ɗawainiya ne ga shi haryanzu ina zaune babu wani labari a kan sa".

"Ni na ce kin É—aura mini É—awainiya ne uwar iya? Ki yi duk abin da ki ka ga dama"

Nana ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri ba zan sake ba" Nene ta yi mata shiru, daidai lokacin kuma Muhsin ya gantsarawa Nana cizo, da 'yan haƙoran da suka fara leƙowa.

A fusace ta dake shi a kan pampers ɗin jikinsa, ta cire shi daga jikin Nonon, ta zaunar da shi tana ƙara tsuke fuska tare da hararsa.

Sexy eyes ɗin sa irin na mahaifinsa ya zuba mata, yana kallonta ko ƙiftawa ba ya yi, gaba ɗaya ya rikiɗe fuskarsa ta koma ta Sayyid sak, farar fatarsa ta yi jawur.

Nene ta ce "Yaka yaron kirki, ka ƙyale ta da halin ta, shi ne za ki huce a kansa, ai ni na yi miki ba shi ba"

Ya rarrafa ya koma jikin Nene ya kwanta yana ci gaba da kallon Nana. Sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ji zuciyarta ta yi mata nauyi da abin da ta aikata, ba tare da duba ƙanƙantar ɗan yaron nata ba.

Ta shige ɗakinta ta mayar da kayanta da ta haɗe guri ɗaya inda suke. Wayarta ta ɗaukko da babu layi a cikinta, ta duba jakarta ta ɗaukko memorynta ta mayar kan wayar, ta fara duba hotunan Sayyid da ke ciki. Har da hotunan  Haidar ɗan gurin Shukura a cikin wayar, da hotunanta na aure da aka yi mata da wayar.

Gaba ɗaya ta ji tana kewar ƙasa Nigeria, amma hakan bai sanya ta ji za ta iya komawa a yanzu ba.

Tunaninta ya katse bayan da ta ji muryar wata ƙawar Nene a tsakar gida, wadda ita ta yi hanyar kai Nana gurin koyon girke-girke. Amma Nana ta ƙi fitowa.

Hira suke yi da Nene, take ba ta labarin ma'aikata ake nema, wanda suka iya girki sosai a wani restaurant, na wata Hajiya a can cikin birnin MaraÉ—i.

Nene ta ce "Ba na yi wa Nana irin wannan harkar ne, saboda mutanen banza, ba dan haka ba ai da na ce ta je, tun da ta iya girki sosai"
Matar ta ce "To ai a ɓangaren girki kawai za ta zauna, su na buƙatar kuku amma mai tsafta wadda ta iya girki, kuma tana biya sosai kin san buzayen nan kamar ba su san ciwon kuɗi ba, buzuwa ce mai gurin"

Nene ta ce "Ai kin ga tana da yaro, shayarwa take yi, ai da na ce a kaita, amma idan za su É—auke ta da yaron shikenan".

"Anya kuwa, gaskiya ba na tunanin haka, ba ma za su yadda ba. Idan ta tafi a ƙalla za ta iya yin wata, ba ta zo gida ba, za a ba ta komai a can. bari na tashi na tafi dama tsayawa na yi mu gaisa sai anjima"

Suka yi sallama matar ta tafi.

Nana ta fito da sauri ta ce "Nene, ina son zuwa gurin abincin buzayen nan"

Nene ta ce "Kin yarda mijin naki buzu ne kenan? Daga an ce gurin buzuwa kin rikice za ki je, bayan da kin ce mini ba ki san ƙabilarsa ba, Allah dai ya shirye ki."

Nana ta yi shiru, tana mamakin yadda aka yi Nene take iya gano ta idan ta yi mata ƙarya.

Nana tun dukan da ta yi wa Muhsin, juyin duniya har la'asar bai ƙara waiwayarta da sunan ta shayar da shi ba.

Sai da ta ji sun cika, sun fara damunta, sannan ta ɗauke shi ta ba shi, amma fafur ya ƙi karɓa, ta kaɗa ta raya ya ƙi sha.

Nene tana kallon su, ta ƙi magana, ta dama masa kunu ta haɗa da nono ta zaunar da shi ta ba shi ya sha, ya ci gaba da wasan sa.

Nana ta ga sun mayar da ita saniyar ware ma. Har garin Allah ya waye, bai saurari Nana ba.

Ta sake ɗaukarsa, saboda yadda nonon ya cika, yake yi mata ciwo, amma fafur yaron nan ya ƙi sha.
Chapter 42 · 0% Book details