← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 78

Sashe 17

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ɗaukko kofin kunun da cokali, sai wani ɗan ƙaramin tsumma, ta zauna a gabansa ta ɗebo kunun a cokali ta kai bakinsa, sai dai ya tsaya yana bin ta da ido, kamar ya ga baƙuwar halitta, ta buɗe nata bakin, ya kalleta shi ma ya buɗe nasa.
Ta fara zuba kunun a bakinta ta haɗiye, sannan ta zuba masa a bakinsa shi ma. Ya haɗiye sai dai wani na biyo gefen bakinsa, bai haɗiye duka ba. Tana bashi tana goge masa wanda yake  zubowa. Sai da ta tabattar ya ƙoshi, sannan ta goge masa bakinsa. Ta ɗauki kofin ta nufi ƙofa ta buɗe a hankali ta ga an daina iskar, ta fita da kofin ta ajiye, ta tattara abin da guguwar ta watsa sannan ta dawo ɗakin.

Jiki a sanyaye, ta zauna a gabansa tana ƙare wa kyakyawar fuskarsa kallo. Da ƙyar yake jan numfashi yana saukewa.  Ta sanya hannayenta biyu, ta gyara masa gashinsa, da ya rufe masa gefen idonsa, ta saka idonta a cikin nasa, cikin rauni da karaya, idanunta na zubar da hawaye ta motsa bakinta, ta fara magana

"Sayyid, dan Allah ka yi magana ko na ji daɗi, wannan karon ka daɗe ba ka ce mini komai ba. Da na sanya ran ka fara samun  lafiya, amma kullum lamarin nan gaba yake yi. Ka gaya mini wane ne kai? Daga ina ka ke? Ina zan samu danginka da 'yan uwanka, wataƙila kai naka dangin ba za su guje mu ba, za su karɓe mu, tare da sarƙar da ta haɗa ƙaddarorinmu wuri guda, duk da ban kasance ɗaya daga cikinku ba, ni fatana a nema maka magani ka samu lafiya, ba na son ganin ka cikin wannan mummunan yanayin, idan na ci gaba da ganain ka a haka, zuciyata za ta iya bugawa. Dan Allah ka yi magana" Ta yi maganar wasu hawayen na zirarowa daga cikin idanunta.

Ayshercool
08081012143

58
Ya haɗiye wani irin yawu, da yake yi masa zafi a ƙirjinsa, yayi ƙoƙarin ɗago hannunsa na dama, sai ya tuna ya riga ya shanye, ba ya iya komai da shi. Ya buɗe baki da nufin ya kira sunanta, saboda tasiri da kuma ciwon da kukanta yake yi masa a zuciyarsa, amma ya gaza bakin ya karkace yawu ya fara zubowa daga bakin nasa, maimakon kiran sunanta da ya yi yinƙurin yi.
Tana kuka, ta sanya tsumman da tayi amfani da shi wurin ba shi abinci, ta goge masa bakinsa. Ba shi da zaɓin da ya wuce, ba wa hawayen da yake maƙale a cikin idanunsa damar zubowa, ko shi ma ya samu sassauci abin da yake ji.
A hankali ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta, a take ta silale ta faÉ—i a jikinsa.
Ya sanya hannunsa mai lafiya, ya rungume ta, ya ci gaba da kuka. Jikinta gaba É—aya ya saki.

Ƙaisar ta gani a gurin haɗe-haɗen magungunan sa, yana ta haɗa wani abu a cikin kwalba. Zuciyarta ce take ta azalzalarta, da ƙoƙarin ingizata, sai dai ba ta yi magana ba.

Babu tsammanni, ta ji ya fara magana "Zaɓi ɗaya ya rage miki, a halin yanzu, ko dai ki yadda da abin da na zo miki da shi, ki rungumi ƙaddararki, ko ki na kallo Buzun nan zai mutu, domin ba zai taɓa tuna waye shi ba har abada, muddin Giyaz yana tare da shi. Dan ba na tunanin akwai wanda zai iya raba shi da shi. Idan har bai iya tuna waye shi ba, shikenan kin ga ba ki da wata makoma. Abu ɗaya zai sanya a wannan karon na bar miki abin da yake cikinki, duk da ba ni da tabbacin zai zama mai cikakkiyar lafiya ko akasin haka, Giyaz da muƙarrabansa sun riga sun fara taɓa shi a cikin ki. Kin san meyasa ban ƙarasa lalata wannan cikin ba?" Bai jira ta ba shi amsa ba ya ce "Saboda zan so na ga yadda za ki yi, a lokacin da ɗan zai amsa sunan shege, kuma ba za ki iya hanawa ba, domin ba ki da hujjar kare kanki. Idan Buzun nan ya rayu bai san waye shi ba, ga kuma nakasa. Idan kuma ya mutu suwaye dangin baban ɗan ki? Daga ina yake? Suwaye ahalinsa? Kin san ku a jinsinku na bil'adam da uba ake ado ba riga ba. Babu wanda zai damu da wacece ta haifi mutum, amma za a damu da waye ubansa meye nasabarsa? Tun da ki ka zo garin nan, zuriyarmu suke alwashin yadda fansar su za ta kasance a kan ki. Kafin zuwa wannan ƙadamin babu abin da ban gaya miki ba, na gargaɗi. Dan haka dabara ta rage ga mai shiga rijiya"

Cikin kuka Nana ta hau girgiza kai ta ce "Ba zan yi bori ba Ƙaisar, ba zan yi shirka da Allah ba. Babu tsanani ko wahalar da za ta sanya na rabu da imanina. Amma na rasa gaba na rasa baya, ba dan ina neman taimakon ka ba, ko ka kawo mini ɗauki ba. Na san Ubangiji Allah shi zai taimake ni.
Amma dan zatin Allah idan ka na da hannu a ciwon Sayyid, ka yi mini rai ka rabu da shi, shi ne kaɗai duniyata. Ina matuƙar tausayin sa, ban damu da jinya da nake yi ba, wahalar da yake sha ta isa haka. Idan kuma laifikan zuriyarmu ne suke shafar sa, dan Allah ku yi haƙuri ki ƙyale shi haka"

Cikin sautin muryarsa mai ban tsoro, da ya kan yi amfani da ita, idan ya so razana ta, ko yi mata magana mai muhimmanci  ya ce "Na sha gaya miki na maimaita miki, daga lokacin da ki ka fara bani umarni, kin yadda kin amince da buƙata ta ne. Ba ni da hannu a ciwon mijinki, kuma bai ya cikin zuriyar ku, sai dai ƙaddara mai ƙarfin gaske, ta haɗa ku tarayya guri guda. Amma muddin ki na son ya warke daga wannan rashin lafiya, ba ma iya haka ba, ya tuna waye shi, sai kin karɓi ƙaddararki.".

Nana ta sake marairaicewa ta ce "Ba zan iya shirka ba, ba zan iya zama 'yar bori ba. Zan jure jarrabawata komai zafinta amma ba zan yadda rasa imanina ba"

Ƙaisar ya ce "A cikin biyu dole abu ɗaya ya faru, tunda kakaninki su suka ƙyanƙyashi wannan matsalar. Na yi iya ƙoƙarina gurin dakatar da ita a wancan lokacin, amma ta sake tasowa a wannan karon. Dole a cikinku ɗaya zai warke ya rayu ɗaya ya mutu a haka, dan babu alamar Giyaz zai sassauta wannan mummunan ƙudirin nasa a kan zuriyar ku. Gefe ga aikin da ya karɓa yake yi a akan mijinki, ko dai ki ci gaba da rayuwa da shi, laifukan ku na shafar sa, ko kuma ki yarda ki karɓe ni a matsayin hadiminki ki yi abin da nake so, ni kuma na san yadda zan yi da Giyaz, na baki maganin da mijinki zai warke"

"Ta yaya? Me yasa sai ni? Me yasa ni zan biya zunubin da lokacin da aka aikata shi ba na nan, zunubin da zamanin da aka aikata shi, ya yi nisa da nawa zamanin? Me ya sa kakannina suka zaɓi zama 'yan bori? Suka gada mini wahala da masifa take ta bibiyar rayuwata. Na zama mujiya a cikin mutane, duk inda na tsuguna sai wata masifa ta afku, da za a jefa mini zargi, kasantuwata ni ba mutum ba ni ba wani jinsi daban ba? Me yasa zan girbe baƙar shukar da ban san a lokacin da aka dasa ta ba? Ina son mijina duk da daga ni har shi, ba mu san waye shi ba.
Duk da Nijar ba ɗaki ɗaya bane ba, ba kuma ƙaramar alƙarya ba ce ba, ƙasa guda ce, na gwammace zagaye ta neman ahalinsa na damƙa shi a gare su, da na ci gaba da zama da shi, mummunar ƙaddarata tana shafarsa, ko kuma na zama 'yar bori na ci gaba da gadar da wahala da masifa ga zuriyarmu, gara ko ma mene ne ya ƙare a kaina." Ta ƙarasa maganar cikin ƙaraji, tana kuka mai bayyanar da tsantsar baƙin cikin da yake binne a cikin zuciyarta.

*****

A hankali yake driving cikin nutsuwa, yana sauraren Jamila, da ke bin waƙar da ke tashi a cikin motar ƙasa-ƙasa, sai kuma ta yi shiru.

"Ya ki ka yi shiru kuma?" Ta ce "Au wai ka na ji na?"
Abba ya ce "Eh mana, har kin fi masu waƙar ma iyawa" Dariya ta yi ta ce "Ka ji ziga, muryar ta su da aka tace, aka goge tawa kuma a haka, ka ke cewa na fi su iyawa"

"Au ba ki yarda ba? To shikenan ni dai na san kin fi iyawa" ya yi maganar yana parking ɗin motar a harabar gurin shan ice-cream ɗin. Abba bai taɓa soyayya ba, duk wannan abubuwan da yake yi wa Jamila, bai taɓa furta mata cewar yana sonta ba. Sai dai ita sarai ta gane sonta yake yi, so kuma ba na wasa ba. Sai dai tana mamakin yadda duk wannan abin da yake yi mata, ba ya iya nuna wa a gaban Hajiya Sa'a, hakan ya sanya ta fara tunanin ko dai yana da wata manufa a kanta ne.
Sai dai ta lura halaye da ɗabi'unsa, sun sha banban da na Hajiya Sa'a, shi Abba akwai tsantseni, da gudun saɓa wa Allah. Dan duk da son da yake yi mata, sai da ya yi mata faɗa a kan shigar banza da ta kan yi wasu lokutan.

Ice cream su ka sha, yana ba ta labarin yadda ya yi karatu, da irin ƙalubalen da ya fuskanta na rayuwa. Su ka gama ya ɗauke ta ya mayar da ita gida.

Bayan ta shiga gida, Mama ta ce "Yauwwa ke nake jira dama, gas ya ƙare na kira wayar ki kuma ba ki ɗaga ba"

"Ina hanya ne, ga ATM É—ina, a bawa Nasiru ya je ya É—uro. Har za ta shiga É—aki sai ta fasa ta ce "Ni kuwa jama'a ina Nana ne? Wayarta ba ta shiga, shekaranjiya waccan ma na biya gidan da mijinta yake gadi, na ga kamar babu kowa a gidan"

Mama ta taɓe baki ta ce "Au ke ba ki san abin da yake faruwa ba dama?"
Chapter 17 · 0% Book details