← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 78

Sashe 2

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya bi kiran wayar, amma ta ƙi shiga, ya yi ya yi, amma ta ƙi shiga, sai haƙura ya yi ya ja motar.

Shukura mamakin abin da ya zaunar da shi a cikin mota take yi, bai tafi ba har yanzu, sai dai tana É—aga labule, ta hango ya ja motar ya tafi.

Video call É—in Hajiya Amina, Shukura ta gani, ta É—aga cikin fara'a tana faÉ—in "Hajiya Mummy, ya ibada?"

"Ibada Alhamdillah, Shukura dan Allah me yasa ba kya ji ne? Ina zaman zamana, ina ibada kin jawo mini ɓacin rai da damuwa"

Cikin rashin fahimta, ta ce "Ni É—in kuma? Me na yi?"

"Baban ki ya kira ni, bai taho ba tukuna yana Abuja. Yana yi mini faɗan wai ke ba ki san ƙaddara ba ne? Doctor Sharif ya kira shi cikin damuwa, yana gaya masa a gaban mutane ki na cewa yana kashe mutane, haka ake yi a kan ki a ka fara rasa ɗa? Me yasa ba za ki girma ba ne Shukura"

"Mummy ki na ji na, network ɗin ki mai ƙarfi ne ko?"

Ta ce "Eh, ina jin ki, kuma ina kallon ki"

"Ina son idan kin je gaban ka'aba, ki yi mini addu'a, muddin a kan gaskiya ta nake, Ubangiji Allah ya shiga lamarina ya ƙarfafa mini gwiwa. Idan kuma ba a kan daidai nake ba, Ubangiji Allah ya kawar da kaina daga kai. Ya bani juriya da dangana na daina jin abin da nake ji a zuciyata.
Sai dai kin dawo amma akwai matsala ne fa."

"Shukura matsala wace iri ce, za ta sanya musulmi kasa yin tawakkalli?"

"Ki bari dai ki dawo É—in"

"To shikenan, amma gaskiya mahaifinki ya yi fushi bai ji daÉ—in abin da ki ka yi ba sam"

Shukura ta lallaɓa ta, ta ajiye wayar.

*****

Nana tana jan ruwa a rijiya, tana zubawa a cikin bokitanta, za ta kai banÉ—aki.
Barira ta ce "Nana ki yi haƙuri dan Allah, jiya na haska ku, ba a son raina ba ne, kuskure ne" Nana ta ce "Babu komai"

Sajida ta ce "Uban me ki ka haska ki ka gani?"

Barira ta kwashe da dariya ta ce "Ni babu abin da na gani, duk da bai kyautu ba abin da na gani É—in. Amma Nana mijinki balarabe ne ko bature?" Nana ta É—aga ta kalle ta.
"Tun da ku ka zo dama bamu taɓa ganinsa ba, gashi na gani kamar na mace dogo sosai"

Nana ta maze ba ta kula ta ba, ta kwashi kayan ruwanta, ta nufi É—akin su.

Sajida ta tuntsure da dariya ta ce "Maganinki da shegen shishshigi, ga shi ta gwale ki"

"Shegiya ba, ta fiye jin kan ta,kamar 'yar uban wani, kuma da 'yar uban wanin ce, da ba su kama hayar É—aki É—aya ba" Duk abin da suke faÉ—a a kunnen Nana, amma ta yi kamar ba ta ji ba.

Bayan ta gama wanke banÉ—aki ta fito, ta zo gabansa ta zauna. Ya É—aukko sauran kuÉ—in nan, ya ajiye a gaban ta.

Ta kalle shi ta ce "A ina ka ɓoye ne, ban gan su ba?"

Ya yi murmushi ya ce "Su na cikin kayana fa, ba ki duba bane ba. A cikin leda suke. Kuma da sun fi haka yawa, Habu ne ya karɓa".

Nana ta duba kuÉ—in, sai tarin kuÉ—in nijar, na Nigeria ba su dubu É—ari da goma ba.

Ta ce "Sayyid, idan ka ɗan ƙara hutawa, ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ne, za mu koma Asibiti a sake duba ka. Da za su kai da na haɗa da sauran na guri na, a fara yi maka allurar nan ko guda ɗaya ce"

"A'a, kin manta yanzu mu zamu din ga sayen Abinci. Idan su ka ƙare ba mu da hanyar samun kuɗi. Kuma da akwai isassun kuɗi, gara mu bar gidan nan, da a yi mini magani"

"Ni kaina Sayyid ba na son gidan nan. Mama za ta aiko mini buhun barkono, idan aka kawo, na ga ana ciniki, sai mu ci gaba da sayarwa".

Ya jinjina kai ya ce "To, in anjima ki raka ni masallaci" Ta kalle shi ta ce "Da gaske masallaci za ka je?"

"Eh, ina son zuwa masallaci. Idan ki ka raka ni, sai ki dawo"

Ta yi murmushi ta ce "To shikenan, Alhamdillah sauƙi yana samuwa. In sha Allah zan kai ka. Bari na ajiye kuɗin nan, idan na raka ka ma, dan Allah zan je gidan Ummi" ya jinjina kai. Har za ta tashi ya riƙo ta, ya cire hijjabin da yake jikinta.

Ƙonuwar da take wuyanta ya gani, ya ƙura wa gurin ido sosai sannna ya ce "Mene ne wannan?"

Ta ɗan basar ta ce "Ba komai fa, ɗan ƙonewa ne kawai na yi"

"Ba É—a ba ne ba, me ya kai ruwan zafi wuyan ki? Waye ya zuba miki?"

"Ba wanda ya zuba mini, sha nake yi ya zube" kawai ya rabu da ita, ba dan ya gamsu da amsar da ta ba shi ba.

Ta tattare kuÉ—in nan, na Nijar ta zuba su a cikin jakar gidan Sarkin Baka. Na Nigeria kuma ta haÉ—e su, ta saka a cikin kayan ta. Ana kiran salla, ya yi alwala, Nana ta ba shi mayafin rawaninsa, ya yafa a kan sa.
Nana ce ta fito tsakar gida. Barira ta gani, tana girki sanye da wata 'yar riga, milik ce amma ta yi baƙi saboda dauɗa, ko brezia babu a jikinta. Ga gashin hammata ya fito zaro-zaro idan ta ɗaga hannunta. Zanin jikinta ma baƙi ƙirin, tamkar an yi matsar man ƙuli da shi, sai annakiya take yi.

Nana ta ce "Barira, dan Allah ko za ki gyara, zamu wuce"

Barira ta ce "Bismillah ki wuce mana"

"A'a ai ni da mijina ne"

"Ku wuce ba wani abu ai" Nana ta yi shiru tana jinjina tumasanci da rashin sanin ciwon kai, na mutanen gidan. Babu yadda ta iya, haka ta kammo hannun Sayyid, ya fito ta rufe É—akin. Ya ja mayafin ya rufe fuskarsa da rawanin, saboda yanzu ba ya iya naÉ—a shi, saboda numfashinsa.
Tun da ya fito Barira take kallon sa, ta na son ganin ainihin fuskarsa, amma ya sunkuyar da kai, kuma ya rufe fuskar sa suka fice.

Su na tafe Yana hutawa, saboda haki, a hankali har suka isa masallacin. Ta ce "Za ka jira ni na je gidan Ummin na dawo?"

"Zan koma gida da kaina"

"Har ka gane hanya?"

Ya ce "Eh ki gaishe ta"

Nana ta ce "Ai ba daÉ—ewa zan yi ba ma"

Ya shiga Masallaci Nana kuma ta tafi gidan Ummi.

Su Nana na fita, Barira ta buga banɗakin tsakar gida ta ce "Ke Sajida kashin danƙo ki ke yi ne? Ki na manne a banɗaki yau mijin 'yar rainin hankalin nan dai ya fito. Ashe dole ta ɓoye shi, fari ne tas wannan gashin da na gani, da gaske nasa ne."

Sajida ta fito da buta a hannunta ta ce "Kai haba, ban gama ba ne shi yasa ban fito ba, zogala na ci da ƙuli ya ruɗa mini ciki"

"Aikuwa kin rasa, ba ki gan shi ba. Sai na ga kamar mata na rako, da na tuna Gali, ga baƙi ga ƙeya"

Sajida ta ce "Ba gara Gali ba da nawa mijin? Ke Gali na da tsawo, ni nawa ga gajarta ga muni"

"Gaskiya Sajida mijinki akwai muni kam, dogon baki kamar dangin burrai"

Sajida ta tsuke fuska ta ce "Ba na son iskanci kuma. Gara shi dai a kan Galin, da ki ka ce ba ya iya tsinana miki komai a shimfiɗa. Kalarsa kalar... Kafin ta ƙarasa Barira ta ƙunduma mata Ashariya, take faɗa ya kaure, suka ci wa junan su mutunci tsaf, suka tona wa kan su Asiri. Suka gaji dan kan su, suka haƙura.

****
Nana ta bawa Ummi labarin barkono da za a kawo mata.
Ta ce "Amma Ummi sai dai a kawo miki nan, can É—akinmu babu gurin da zan ajiye a can"

"Bakomai a kawo, kuma nan da nan za ki ga an saye shi ba, ai unguwar nan fuskar jama'a ce, idan ka kasa kaya za ka samu alkhairi"

Su na tsaka da hira, babu zato babu tsammani sai ga Saleh ya afko cikin gidan. Wata irin mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Nana, bayan da ta gan shi babu tsammani. Duk ya ƙara lalacewa.

Turus ya yi yana kallon Nana, cikin mamaki ya ce "Nana, dama kina nan?"

"Eh" ta amsa a taƙaice.

"Nana da yanzu nine mijinki, amma ki ka guje ni"

Ummi ta haÉ—e rai ta ce "Saleh Nana fa matar aure ce, dan haka babu ruwan ka da ita dan Allah"

Saleh ya ce "Dan matar aure ce, kuma shikenan ba za mu yi zumunci ba? Nana kina lafiya? Na ji an ce wani baroroji aka aura miki ko?"

Nana ta haÉ—e rai ta tashi ta ce "Ummi zan tafi, zuba mini Abincin idan kin gama"

Ummi ta ce "Bari na wanke babban flask, kuma idan Islam ta zo ki ba ta kwano na, dan ba zan bar miki ba"

Nana ta ce "Gaskiya sai kin bar mini, ki zo ɗakina, ki ɗauki duk abin da ya yi miki. Kuma a ƙaramin kwano za ki zuba mini. Sayyid na yi masa girki, ni zan ci wannan"

Ummi ta ce "Hajiya Nana, an sake haÉ—iyar wake kenan, to Allah ya inganta"

"Dawa na haÉ—iya ba wake ba"

Tsulum Saleh ya sake cewa "A nan unguwar gidanki yake kenan? Na ji Ummi ta ce Islam na zuwa gidan naki. Da aka ce mijin naki gadi yake yi"

A ƙufule Ummi ta ce "Dan zatin Allah Saleh ka fita, ba da kai muke magana ba, babu ruwan ka da mu. Wai har ka manta har ubanmu ka saka a rufe saboda kuɗinka, dan rashin kunya kuma, ka zo zaka addabe mu?"

Sum-sum Saleh ya fice daga gidan. Ummi ta zubawa Nana tuwon shinkafa da miyar yauƙi, har da man shanu, Nana sai haɗiye yawu take yi cikin farin ciki, kamar ta durƙusa ta ci a gurin.
Ummi ta shiga É—aki, ta É—aukko wa Nana dambun kifi ta ce "Ungo, jiya na yi shi aka kai mini shago, na É—ebar miki"
Chapter 2 · 0% Book details