← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 78

Sashe 16

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su na zuwa gidan, Nana ta shiga ta tarar da shi a zaune ya tashi, ta ce "Sayyid kar ka ga na fita ban gaya maka ba. Na je na samo wani ma'aikaci ne, ya zo ya duba jininka a gani, idan jinin ne ya hau ya sanya hannunka ya shanye, mu tafi Asibiti. Idan kuma ba shi ba ne, sai mu san abin yi." Bai ce komai ba, ta yi wa mai chemist magana, ya shigo ya gwada jininsa.
Ya gwada ya kalli Nana ya ce "Jininsa bai wani hau sosai ba, 140/90 ne" Ajiyar zuciya Nana ta yi. Ta ce "A ganinka wannan hawan zai iya sanya masa shanyewar hannu?.
Ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba na tunanin haka, amma ban tabattar ba tun da ni ba likita ba ne ba. Amma a shekarunaa bana tunanin jinin 140 zai shanye masa wata gaɓa a jikinsa, amma dai ku je Asibiti a ƙara bincikawa"
Nana ta ba shi kuɗin sa, ta yi tai masa godiya. Ta koma ɗaki ta zauna ta yi shiru, tana tunanin ko Uwani za ta tambaya, idan akwai wani mai magani, ta raka su, sai dai ta fasa saboda akwai sauran ɓurɓushin jahilci a tattare su, ba ta son surutu kuma tana tsoron a kai su gurin da ba shikenan ba.

****

Alhaji Fatuhu kuwa kamar yadda ya matsa, sai da aka sallame shi ya koma gida. Gidan nasa ma wani abokin kasuwancinsa ne ya saya, ya bar shi a ciki ya zauna ya bar masa aro.

Sagir yana kwance a kan gadonsa, yana kaɗa ƙafa ya ƙura wa screen ɗin wayarsa ido. Yusra ce zaune sanye da doguwar rigar material, kanta ko ɗan kwali babu, dogon gashin kanta ya sha gyara. Tana ta zuba masa surutu.
Har mamaki yake yi, yadda Yusra ta zama mai É—an karen surutun tsiya, wanda da ba haka take ba.

"Ya ka yi shiru ne?" Ya wani lumshe ido ya ce "Ina jin ki ai".

"So talk, ka yi magana mana" ta yi maganar tana cika bakinta da guggurun hannunta.

"Ina ga zan shigo Abuja mu haÉ—u very soon in sha Allah" wata irin zabura ta yi ta ce "Are You serious, dan Allah da gaske?"

"Da gaske nake, zan zo na ganki, amma ki na ganin babu matsala a zuwan nawa? Kar a yi miki faÉ—a fa, ba zan ji daÉ—i hakan ba"

Yusra ta ce "Babu wata matsala, ba za a yi mini faÉ—a ba, ai ba na tare da su Mami, ina gidan Anty Sumayya. Dan Allah ka zo"

Sagir ya yi murmushi ya ce "Kin yi missing É—ina ne?"

Ta gyaÉ—a masa kai tana murmushi.

"Shikenan, i miss you too, ban taɓa tunanin ma za ki neme ni ba, na za ta ki na jin haushina haryanzu, amma in sha Allah zan shigo, zan sanar miki lokacin da zan shigo na zo na ganki" ya yi maganar yana kashe mata ido.

Shukura ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, a burkice ya kif wayar yana kallon ta. Ƙarara yanayinsa ya nuna alamun rashin gaskiya, amma ta share shi, ta haye kan gadon ta ja bargo ta lulluɓe jikinta.
Ya matsa kusa da ita yana É—an shafa ta ya ce "Sweetheart, ya na gan ki kamar a fusace ne? Lafiya dai ko?"

"Lafiya ƙalau" ta amsa a taƙaice. Ɗan shiru ya yi yana tunanin ko dai ji wayar da yake yi ne? Amma a yadda ya santa da azababben kishi, da zargi da ta ji sai ta yi masa magana. Sai dai ya bar abin a haka bai matsa mata da tambayoyi ba gudun kar su yi faɗa.

Tana ankare da take-taken Sagir, na rashin gaskiya. Sai dai ita yanzu ba wannan ne a gabanta ba, bin diddigin mutuwar ɗanta take son yi. Dan haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da natural mutuwa ya yi. Domin haryanzu tana mafarke-mafarke marasa  daɗi da mahaifinta da kuma Doctor Sharif.

****
Aka shiga sati na biyu, Sayyid yana cikin wannan yanayi na rashin lafiya, kuma hannunsa bai saki ba, yana nan a maƙale.
Ga hauka da yake yi tuburan wasu lokutan, wasu lokutan idan ya burkice sai ya shaƙe ta, ko ya hankaɗe ta ƙasa, sai dai ta yi ƙoƙarin kare cikinta. Ko kuma Ya ya ta watsi da duk abin da ya ci karo da shi, a ɗaki ko a tsakar gida. Wasu lokutan ma katangar ɗakin yake duka da kansa. Ya ƙi cin abinci ya ƙi shan magani, ba salla, komai sai dai ta yi masa cikin rarrashi da ban haƙuri. Tun tana jin tsoron ya yi mata wani abin, har ta daina ji, ta zuba wa sarautar Allah ido.
Sannu a hankali ta rage yawan amai, sai dai zazzaɓi da rashin son cin abinci da take yi, hakan ya sanya ta tabattar da cikin jikinta bai fita ba haryanzu. Sai dai ba ma ta cikin nutsuwar da za ta nemi inda Asibiti yake ta je, ta tabattar da halin da suke ciki ita da jaririn saboda tashin hankalin da take ciki.
Yanayin yadda uwani ta lura kamar Nana na ɓoye wani abu, ya sanya ta daina zuwa gidan,ta rage aika yara ma. Sai dai lokaci lokaci, ta kan aika mata da Abinci.
Haka sauran 'yan uwansu na garin ma, su kan aiko mata da sha tara ta arziki saboda su na tausayin Nana, sun san mijinta a kwance yake babu lafiya.
Yawon roro a gona kuwa yanzu Nana ta ƙware, ranar kasuwa ta je ta sayar da abin ta.
Kasancewar ranar Asbar kasuwar garin take ci, sai ta tashi ta yi fanke da sassafe, jikan Uwani Haladu, ya kai mata kasuwa. Ko ta dafa masa zoɓo ta ƙuƙƙula ya tafi da shi.
Idan ta gama komai kuma, ta bi yara gona roro.

Dare ya tsala, amma Nana tana zaune tunkurkur, wuni Sayyid ya yi yana wani irin nishi, ga wannan azababben zafin jiki da yake fama da dhi.
Tana zaune tana tunani, tana jin yadda mararta take motsi, cikin jikinta yake motsawa.
Ba ta da sauran wanda za ta kai kukanta bayan Ubangiji. Ta fara tunanin ƙoƙarin tara musu kuɗin mota, su tafi Nijar, neman danginsa, sai dai idan sun je Nijar ɗin ina za su nufa? Babu tsammani ta ji Sayyid ɗin ya laluba cinyarta, ya kwantar da kansa.
Ta shafa gashinsa ta ce "Sayyid" bai amsa ba, sai dai ya riƙe hannunta. Hakan ya tabattar mata da ya dawo hayyacinsa ne. Haka ta tashi a cikin daren ta tsiyayo ruwan zafi, ta ba shi shayi ta yi masa wanka suka kwanta, ta lulluɓe su da bargo.
Sheshsheƙar kukansa ta ji, duk da yadda ta san ya daɗe yana dauriya, da son ɓoye gazawarsa, sai dai ta ga hakan a idanunsa.

"Sayyid idan ka na kuka, ni kuma ya zan yi kenan? Dan Allah ka daina" ta yi maganar muryarta na rawa. Ta din ga shafa bayansa a hankali, har ya yi shiru, bacci ya É—auke shi.
Sai dai tun daga wannan, haka aka sake shafe kwanaki biyu, bai sha ko ruwa ba. Dama rashin maganarsa ya daina damunta.
Ga shi yau abin ya tashi sosai, haukan yake yi da gaske. Ta rufe shi a gidan, ta je ta samo gasara a gidan Uwani, ta dawo ta dama masa kunu. Ta nufi É—akin cike da fargaba tare da fatan ya samu ya sha ko kaÉ—an ne.
Sai dai ta ji wata irin guguwa ta taso mai ƙarfi.

Jin yadda guguwar ta taso da ƙarfinta, take fatali da duk abin da ta ci karo da shi a tsakar gida, ya sanya ta tashi da azama, ta fara ƙoƙarin rufe ƙofar katakon da take ɗakin. Sai dai tana danna ƙofar guguwar ma na danno ƙofar.

A take ta fara karanto "A'uzubillah, Allahumma inni as'aluka khairiha wa a'uzubika min sharriha. Allahumma inni as'aluka khairiha wa khairi ma fihi, wa khairi ma ursulat bihi, wa a'uzubika min sharriha wa sharri ma fiha, wa sharri ma urisilat biha" take ta ji nauyin da ƙofar ta yi ya ragu, ta samu ta rufe ta, ta juya da sauri ta nufin gurin da yake.

Da fari yana zaune a guri ɗaya ne, amma yanzu Jifa yake da kayan ɗakin da hannu ɗaya, da sauri ta fara  bi tana tattarewa, cike da damuwa.
Cikin siriryar muryarta ta ce "Sayyid za ka ji wa kan ka ciwo, ka saurara ka saurari muryar matarka, ni ce a gare ka, ni ce fa, Husnan ka ce fa" Ta ƙarasa maganar a raunane, duk yadda take ƙoƙarin tare shi ta kasa, domin ta gama firgita da lamarinsa. Tun safe take fama da shi, ya ƙi cin komai, kuma ta kasa sarrafa shi duk rarrashin da ta yi a banza.
Cikin matsananciyar damuwa, hawaye na bin kuncinta ta ce "Ubangiji ka dubi mijin Nana, ka cire masa zafi da raɗaɗin da yake ji, ka saita masa tunani da ƙwaƙwalwarsa, ya yi rayuwa mai cike da nutsuwa da farin ciki irin na sauran mutane" sai kuma ya tsaya cak, ya juyo yana kallonta.
Ta ƙarasa gurinsa, ba tare da fargaba ba ta  riƙo hannunsa cikin nata jikinsa zafi sosai. Ta kalli cikin idanunsa sai taga yana birkice mata yana rikiɗewa kamar ba Sayyid ɗin ta ba, idanunsa har wani hayaƙi yake fitarwa, gaba ɗaya kaminsa sun sauya.
Ta lallaɓa ta zaunar da shi, Ta yunƙura zata tashi, domin ta ɗaukko kununsa ta sake jarraba ba shi, ta ji ya cafko ta yana wani irin sambatu bakinsa na kumfa da dalalar da yawu, da alama magana yake son ya yi mata. Rashin ƙarfin jiki ya sanya ta faɗa jikinsa. Ya ƙanƙame ta sosai, saboda zafin da yake ji, ita kuma jikinta sanyi ƙalau. Ita ma jikinta ya ɗauki rawa, ta lafe a jikinsa ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tsawon mintuna, jin ya ɗan nutsu jikinsa ya rage zafin ya sanya ta zare jikinta a hankali.
Chapter 16 · 0% Book details