Sashe 72
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ba a kanta na yi fushi ba, yadda ba kya jin magana ne ya ɓata mini rai, idan ki ka ci gaba da sanya wa ma'aikatanki ƙiyayyarki, babu abin da ba za a iya haɗa kai da su a yi miki ba. Idan na isa a bar maganar nan. Ba na son yadda ki ke tafiyar da ma'aikatanki wasu lokutan, ba na son yawan shiga maganar ne, amma raina ki za su yi"
Asal ta yi shiru ta tsuke fuska, ta sauka daga kan cinyarsa baki É—aya.
****
Alhaji Fatuhu ma duk da yadda yake fama da kansa, sai da ya je gurin jana'izar Abba, kuma da shi aka yi zaman makoki. Ya ji mutuwar nan sosai da sosai, saboda Abba mutuminsa ne. Ko da yake jinya a sati ya kan je sau biyu ko uku duba shi. Ya kan zauna su yi hira sosai mussaman idan ya tarar jikin nasa da sauƙi.
Kusan kullum Hajiya Sa'a gani take mafarki take yi, idan aka wayi gari za ta ga Abba bai mutu ba, amma ta ga babu alamun hakan. Ba ta ƙara kiɗimewa ba sai ma da aka yi kwana bakwai da mutuwar, kowa ya watse ya bar gidan.
ÆŠakin Abba ta tafi da daddare, ta buÉ—e É—akin tana rintse idanunta tana jin tamkar za ta gan shi ya É—ago, da wannan murmushin nasa irin na fuskar mahifinsa.
Amma ta ga É—akin nasa wayam, babu komai.
Wasu irin zafafan hawaye suka shiga sintiri a kan kumatunta, ba ta taɓa dana sanin shiga ƙungiyar asiri da duk wasu miyagun laifuka da take aikatawa ba, sai da ta rasa tilon ɗan da Allah ya ba ta a rayuwa. Wanda babu irin ƙoƙarin da ba ta yi, domin ganin ta kare shi da sadaukarwar ƙungiya. Ashe bonono ta yi rufe da ɓarawo bayan janyo Jamila cikin harkar ƙungiya, wanda ta yi hakan ne, domin janyo Jamila kusa da ita yadda za ta samu mallakar jinin Nana.
Ta zauna a gaban ƙatuwar katifarsa, ta din ga wani irin kuka mai sauti, da sai da ƙirjinta ya fara yi mata zafi.
*****
Asal ce zaune a kan carfet, saman kujerar da take kai kuma wani babban mutum ne, cikin shigar buzaye, kansa É—auke da rawani.
"Ki na ji na da kyau ko?"
Ta jinjina kai cikin nutsuwa, ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta yi.
"Ina fatan haryanzu ba ki manta dalilin da ya sanya ki ka auri Hammad ba"
Ta amsa da "Eh ban manta ba"
"To barka, yanzu ya dawo, kuma babu abin da zai canza, za ki ci gaba da gudanar da aiki, kamar yadda yake a baya. Ba na buƙatar kuskure ko kuma wani uzuri. Duk wani motsinsa da duk abin da yakamata mu sani mai muhimmanci ki sanar da ni, idan kuma ki ka bari ni na gano ba ki sanar da ni ba, ranki zai yi mummunan ɓaci"
Jiki a sanyaye ta jinjina kai. "Dole a ci gaba da aiki tuƙuru, domin nesanta shi da kujerar Sultan, da mahaifinsa ke ta ƙoƙarin kusantar da shi da ita, mu na buƙatar kujerar nan ko ta halin ƙaƙa, dan haka ina nan ina saka miki ido da kuma sauraren ki"
Asal ta sake jinjina kai, jikinta babu ƙwari ta tashi ta fice.
Da ƙyar take ɗaga ƙafafuwanta, damuwa duk ta cika mata kai, ta ma rasa wane tunanin yakamata ta yi.
Da ta koma gida, ta tarar da hadimai na gyara ɓangaren Imam, ga ƙamshin turaren sa, da alama bai daɗe da fita ba.
Cikin tsawa ta kore su gaba É—aya, ta ce su ajiye aikin su fita daga sashen, sannan su kira mata Nana. Jiki na rawa suka ajiye suka fita.
Nana tana tsaka da karatun Alkur'ani saƙon Asal ya iske ta, sai ta hau tunanin kiran me take yi mata. Duk da ta san abin da ta yi mata da safe.
Nana ta tashi cike da ƙwarin gwiwa, dan ji take yi daidai take da Asal, tun da duk abu dai ba za ta raba ta da ranta ba.
Nana ta shiga fuskarta a haÉ—e ita ma, ta shiga É—akin ta tsaya, tana ta huci tana son ta balbale Nana da faÉ—a, sai kuma ta kasa ganin yadda Nanan ta tsuke fuska ita ma, ta yi mata wani irin kwarjini.
Amma duk da haka ta maze cikin dakiya da ƙarfin hali ta ce "Amm tambaya nake son yi miki, ban sani ba ko nice a ƙarƙashinki, da zan din ga yi miki magana kina ji na ki yi mini banza"
Nana ta É—aga kai tana kallonta. "Ko ba ki gane me nake nufi ba ne? Abin da ki ka aikata da safe"
Nana ta ce "Na gane, gani na yi bai kamata na tsaya ina kallon ku a yanayin da ku ke ba, ko na din ga sauraren maganganunku ba. Hakan zai zama kamar munafunci ne, shi ya sanya na tafi, amma ki yi haƙuri"
Asal ta watsa mata wani banzan kallo cike da tsana ta yi ƙwafa sannan ta ce "Daga yanzu aikinki ba iya girkin Imam ba ne ba, har da gyaran sashen sa, ba na buƙatar kowa ya din ga raɓar inda yake."
"Amma É—aukko ni ki ka yi na din ga girki kawai, ya za ki haÉ—a mini da aikin shara da goge-goge. Kuma masu yin aikin su uku ne, ni kuma nikaÉ—ai ce, aikin bai yi mini yawa ba kuwa?"
"Kin san a kan kuɗi nawa na biya na ɗaukko ki? Ko a Nigeria ba na tunanin ko za a sayar da kaf danginku, za ku iya biyan kuɗin da na biya na karɓo ki ba. Dan haka ina da hurumin sanya ki duk abin da na ga dama"
"To Gimbiya Asal, babu damuwa zan yi abin da ki ke so. Duk da dangina ba za su iya biyan kuɗin da ki ka biya ba. Amma na san wataƙila mijina zai iya biya ya fanshe ni" Nana ta yi maganar tana murmushin da Asal ba ta gama gane kansa ba.
Nana ce ta ƙarasa aikin gyaran falon nan, ta yi goge-goge. Haƙurƙurtar da kanta ta din ga yi, da ta tuna mijinta take yi wa wannan aikin. Duk da ayyukan sun yi mata yawa. Ita dai fatanta Ubangiji Allah ya sanya Sayyid ya tuna ta domin ta san matsayinta.
Tana kammalawa ta koma kitchen, ta É—ora girkin rana. Ta kammala ta kai ajiye.
Ta ƙara goge ɗakin saboda ta san halin Asal sai ta tafi za ta huta, za ta sanya a kirawo ta, ta hau yi mata kinibibi da sanabe kala-kala.
Ta gama aikin goge-gogen kenan, ta gano wani photo album. Ta É—auka ta nutsu tana dubawa, duk rubutun French ne a jiki.
Shafin Farko hoton Sultan ne, wanda ba dan yanayin shekaru da fuskarsa ta nuna ba, sai ka ce Imam Hammad ne, wanda tsananin kamannin har Muhsin da ta baro a gurin Nene.
Ta buɗe ɗaya shafin ta ga hoton wani, shi ma fari tas mai kama da su Sayyid sai dai shi ma babba ne. Kowanne a ƙasa da sunan sarautarsa.
Sai kuma ta shiga wani shafi mai ɗauke da hoton Sayyid a ƙasa an rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. Wani murmushi ya suɓuce mata ta ce "Ka fi kowa kyau a cikin album ɗin nan Shugabana." Ta furta cikin murmushi. Hotunan wannan matasan da suka yi wa girki a gidan Sultan su ma kowanne da sunansa a ƙasa. Amma a farkon sunan kowanne da Imam.
Nana ta din ga mamakin to kowa ma Imam ne kenan?.
Muryar Asal ta jiyo sun nufo cikin falon, ta hanyar da take kyautata zaton a nan turakar Imam take, kuma tana tunanin É—aya hanyar sashen Asal za ta mayar da kai, kai tsaye.
"Imam, wai ina zobenka ne?"
Ta yi maganar tana É—ago hannunsa, Nana kuma tana hango su daga inda take zaune.
"Ya karye yana gurin gyara"
"Gurin gyara kuma Imam? Ya za a yi dakakkiyar azurfa kamar wannan a ce ta karye? Ka san fa muhimmancin da zoben nan yake da shi a gurinka, ya za a yi ya karye?"
Daidai lokacin suka ƙaraso tsakiyar falon, ya ce "Zobe ya ɓata ban san inda yake ba, ina fatan kin gamsu yanzu. Kar ki sake yi mini maganarsa.
Yanzu zan fita, kar ki manta da saƙona"
Sai a lokacin suka ga Nana da ke zaune a cikin falon.
"Me ki ke yi a nan?" Asal ta tambaye ta.
"Babu komai, gyra É—akin na yi"
"Kuma sai ki nemi guri ki zauna sai ka ce ɗakinki? Imam yana da baƙi anjima, za ki sake dafa wani abin, kuma za su sha shayi, ba na son wauta ko makamancin haka" Nana ta jinjina kai ta kalle shi ta ce "Barka da yammaci Sayyid, in sha Allah zan yi"
Asal ta É—an yi shiru tana nazari jin ta kira shi Sayyid ba Imam ba.