← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 78

Sashe 18

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tsaya tana kallon Mama ta ce "Mene ne yake faruwar?"

"Ai tuni aka kore su daga wannan gida. Ke ba zama ki ke yi ba ne shi yasa, suka koma unguwar su Ummi, to kin santa duk inda ta zauna bala'i ne yake bibiyar gurin, hatsaniya ta haɗa ta da matan gidan da suke, suka ce mayya ce aka tashe su. Ai nan Babanku ya je aka yi ta fafatawa, da ta kwaso jiki ta taho nan, wai za ta dawo mijinta babu lafiya, na ce bani da gurin jinya a gidan nan. Allah ya raba ni da masifa, ba za ta dawo mini ba, to ƙarshe dai wai yanzu tana ƙauye, can gurin Uwani a can take jinyar mijin nata"

Jamila ta yi sak, ta ce "Mama Nana tana ƙauye fa ki ka ce?"

"Eh mana, to idan ba ƙauyen ba ina za ta je? Tana can"

"To waye yake ba ta Abinci?"

Mama ta ce "Oho ina na sani?"

"Amma ya aka yi tsawon wannan lokacin ban sani ba? Yanzu ba kamar da ba ne, ban ji daɗin abin da ki ka yi ba Mama, bai kamata a kore ta ba a ce ta koma ƙauye da zama ba. Da ina nan ko na sani, da na kama musu wani gidan, gaskiya sai ta baro ƙauye"

"To ke ina ruwanki? Mene ne naki a ciki uwar Iya? Kina kallon irin baƙar azabar da na sha, a kan zamana da ita a gidan nan. Na meye za ki kuma jajubo mana ita. Gara ki bani kuɗin da za ki kama mata hayar na bawa ɗanLadi, ɗan autanmu ya tafi kasuwa da zaman banzae da yake yi, na yi masa aure tun da Allah ya sanya kuttun arziki ya fashe mana, ba ki kai kuɗi inda babu amfani ba"

Jamila ta dubi Mama ta ce "Wannan ɗan uwanki ne, sai ki nemi kuɗinki ki yi masa, nima 'yar uwata nake tunani. Haba Mama, ko wani Nana ta kashe miki ƙiyayyar ta isa haka ai. Ai yakamata a tausaya mata, miji babu lafiya ga zaman ƙauye, ita Uwanin za ta ɗauki nauyin Abincinsu ne? Tun da muka tashi a wahala muke a gidan nan, amma ita nata ya fi na kowa ma" Jamila ta ƙarasa maganar cikin damuwa, ta shige ɗaki, ta bar Mama da buɗaɗɗen baki.

*****
Kallonsa Nana take yi, suna zaune sun yi juguum daga ita har shi. Bayan ta gama yi masa kitson zanen hannu guda takwas, ta yanke masa faratansa na hannu da na ƙafa.
Kamar wadda aka mintsina ta tashi tsaye, ta kalle shi ta ce "Sayyid, bari na je na dawo" ya bi bayanta da kallo har ta fice.

Sai dai a ƙalla ta kai awanni biyu kafin ta dawo, ko da ta dawo ta tarar da shi ya haɗe fuska, ta yi shiru ba ta kula shi ba, ta koma tsakar gida.
Ta laluba kayanta, ta ɗaukko wata takarda mai ɗauke da ayoyin ruƙiyya da na karya sihiri, sannan ta hura wuta a cikin murhu.
Ta dawo tsakar gida ta zauna, ta fara da Bismillah da karanta Suratul fatiha, sai Suratul falaƙi da nasi. Ta karanta ayoyi biyar ɗin farko na Suratul Baƙara, ta fara karanta Suratul mulk, a hankali sai ta fara gani dishi-dishi, ta fara daina ganewa. Ta busa ayoyin a cikin ruwan, Sai ta ajiye takardar. Ta ɗauki wata leda da ta zo da ita, ta fito da man habbatussauda da jan Almiski.
Saboda wauta sai ta buÉ—e miskin, ta kai hancinta, da sauri ta dungurar da shi a gurin, ta ja da baya, dan tuni ta ji jikinta ya fara tsuma.
Sai da ta ɗan samu nutsuwa, sannan ta zazzaga tazargaɗe a cikin bokitin, ta kawo ganyen magarya guda bakwai, ta saka a leda ta ɗan bubbuga musu muciya, ta haɗa a cikin ruwan. Ta yi shiru tana tunani a ranta ta ce "Allah ya sa ba mai magani na zama ba, Ƙaisar bai mayar da ni 'yar bori mai bayar da magani ba, larurar Sayyid ta saka na fara koyi da magungunan sarkin baka."
"Amma ai ayoyin Alkur'ani ki ka karanta, shi ma kuma Sarkin Bakar yana amfani da Alkur'ani" wata zuciyar ta tunatar da ita. Haka dai ta ci gaba da wasi-wasi.
Can yamma, bayan ta tabbatar da ganyen magarya da tazargaden sun tsumu, ta ɗumama ruwa ta tsiyayi ruwan tofin ta tace ta haɗa da ruwan ɗumin, ta kawo man habbatussauda ta tsiyaya a ciki, ta kawo jan miskin nan da ta saka kwalbar a ruwan ɗumi, ya narke ta tsiyaya a ciki, ta ɗebo garwashi a kasko ta shiga ɗakin. Yana ganin Nana ya tashi zaune yana kallon ta, ya ga ta samu ƙyalle ta ɗaure hancinta da bakinta.
Ta nufo shi ya ga ta hau tuɓe masa kaya, ya din ga bin ta da ido, ta bar shi daga shi sai gajeren wando. Hannunsa da yake maƙale take kallo cikin damuwa, ta shafa hannun.
Sai kuma ta yi Bismillah ta fara shafa masa wannan ruwan. Tun daga cikin kansa.
Girgiza kai ya fara yi, yana ture ta da lafiyayyen hannunsa, yana toshe hancinsa. Ya din ga girgiza kai jikinsa yana karkarwa bakinsa yana rawa, ya din ga wani irin gunji yana miƙa. Amma sai da Nana ta jiƙe shi da ruwan nan tsaf.
Ta kunna kiran salla a wayarta. Ta kawo tazargade, da habbatussauda da ganyen magarya ta zuba su a kan garwashin nan, hayaƙin ya turnuƙe ɗakin, ta ajiye shi a nesa da shi kaɗan. Ta fice daga ɗakin ta kulle shi a ciki. Ta tafi ta din ga wanke hannunta. Wani irin jiri ya din ga ɗaukar ta, ga matsanancin ciwon kai, ɓari ɗaya da ya sanya take jin, tamkar kan zai yi bindiga ya rabe.
Ta samu guri ta zauna a tsakar gida, ta dafe saitin zuciyarta da yake ta bugawa da sauri.

Bayan wasu mintuna, ta tashi ta je ta leƙa ta window, ta hango shi a kwance a ƙasa. A tsorace ta buɗe shi, ta nufe shi da sauri tana kiran sunansa.
Gaba ɗaya ƙwayar idonsa baƙar ta ɗauke sai farar, ta durƙusa a kansa kawai ya miƙo hannu zai shaƙe ta, amma ta riƙe hannunsa. Hannun ya din ga rawa, ya sauke shi a hankali.

"Sayyid" tana ambatar sunansa, ƙwayar idonsa ta dawo ya kalle ta.

"Sannu Shugaba" hararta ya yi ya juya mata baya. Dariya ta fara yi ƙasa-ƙasa.

Ta ce "Haba Shugaba, ya ka juya mini baya, juyo ka kalle ni" ya ƙi juyowa. Ta tashi ta buɗe labule saboda yadda warin ita ma ya fara damunta.
Ta É—aukko tsumma, ta hau goge masa jikinsa, saboda ya daina warin miskin nan ita ma ba ta so.
Ya tashi zaune, tana goge masa. Ta ce "Ko a yi wanka?" Ya ɗaga idonsa yana hararta, jikinsa ya koma jawur kamar wanda ya ƙone.
Ta din ga ɓoye dariyarta, ta yi masa wanka, ya din ga sinsuna jikinsa yana yamutsa fuska.
Ya shafa fuskarsa ta ce "Ka yi haƙuri, magani ne, ina son ran Ubangiji Allah ya kawo mana afuwa" Ya ture ta daga jikinsa. Amma ta manne masa ta hau cinyarsa ta zauna tana dariya.

Ta juyo da fuskarsa suna kallon juna, ta lumshe ido ta buÉ—e ta ce "Sannu shugaba" Ya jinjina mata kai. "In zubo Abinci ne?" Ya girgiza kai.

"Sai an yi salla?" Ya gyaÉ—a mata kai.

Ya yi sallar magariba da isha'i, ta zubo masa Abinci.

Washegari ma da sassafe, ta kuma rutsa shi tana shafa masa ruwan nan. Yau ma ture ta ya din ga yi yana girgiza mata kai. Ta kunna masa hayaƙi, ta gudu ta rufe shi a ɗakin. Haka ta sake tarar da shi, ya koma ja ya haɗa uban gumi. Ta yi masa wanka. Ta ba shi Abinci ya karya.
Allah ya dafa wa Nana, ba su taɓa rasa abin da za su ci ba. Kuma haka take ta jujjuya kuɗin.

Sai da ta gama yi masa duk abin da zai buƙata, sannan ta tashi za ta yi wanka, tana tsaye daga ita sai bra da zani a ƙugunta, sai cika bakinta take da aya mai gishiri, ga cikinta ya ɗaga sosai.
Ta waiwayo suka haÉ—a ido. "Ya ake kallona haka?"

Ya yi mata alama da hannunsa mai lafiya ta zo.
Ta ƙaraso gabansa ta durƙusa ta ce "Gani" ya nuna mata cinyarsa.
Ta ce "Ina da nauyi fa, jiya ma dan na tsokane ka na zauna, ka ga baka da lafiya" ya saka hannu ya janyo ta, ta hau cinyar tasa tana dariya.
Yatsansa ya saka ya É—an latsa cikinta, ya kalle ta yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi ta ce "Kullum sai ya ce ko ta ce tana gaishe ka" Da hannunsa yake tambayarta yaushe za ta haihu?

"Nima ban sani ba, amma dai bai fi wata  huɗu ba, saura wata biyar in Allah ya sa mu na raye. Idan ka samu lafiya sosai, za mu je mu ƙara dubawa idan su Habu sun dawo, idan ba su dawo ba sai mu tafi Nijar. Duk da na san da sun dawo zuwa yanzu za su neme mu" Ya yi shiru yana ci gaba da kallon cikinta, da lokaci lokaci yake dan harbawa.
"Zan je na yi wanka"

Da hannunsa ya yi mata alamar, su je ya yi mata.

"Kana fama da kanka za ka yi mini wankan? Wato a ramawa kura aniyarta ko? To na yafe idan Allah ya baka lafiya sai ka yi mini Rayuwata" Cikin murmushi ya sunkuyo da kanta ya sumbaci goshinta ta da laɓɓanta. Hira yake so ya yi da ita, amma ya kasa sai dai ya kalle ta yana murmushi ko kuma ya din ga yi mata nuni da hannunsa.

Ya ɗauki wayarta, ya kunna waƙar da take yi masa, yana yi mata nuni da ta yi masa. Ta ce "A'a karatu za mu ji ba waƙa ba, a wannan yanayin da muke ciki, ai ba mu ga ta waƙa ba Sayyid" Ya tsuke fuska yana hararta. Ta ce "To shikenan, bari a kashe waƙar, sai na raira maka da bakina ko?" Kawai ya tsare ta da ido yana wani lumshe ido.
Chapter 18 · 0% Book details