Sashe 70
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jamila ta yinƙura ta tashi zaune, suka gaisa sama-sama.
"Wai ba ki da lafiya ne?"
Ta jinjina kai alamar eh.
"Jamila kin fiye yawan rashin lafiya, Allah ya kawo mana siriki mu sha biki. Ta ga dai mutanen gidan nasu duk sai a hankali, ta yi musu sallama ta tafi.
Hajiya Sa'a tamkar za ta haukace, kwana uku amma sai an yi da gaske take cin abinci kaÉ—an.
Ta rame ta zabge kamar ta shekara tana larura.
Ko gaisuwar aka yi mata ba ta iya amsawa, idanunta suka koÉ—e suka yi jawur.
Mutane da dama sun ji mutuwar Abba, saboda mutuwar fuju'a ga matashi, tana taɓa zukata, mussaman Abban da yake mutumin kirki ne, ga girmama mutane.
Ranar da Abba ya kwana uku da rasuwa, Safiyya ta samu Hajiya Sa'a a É—aki, ta ce "Hajiya yanzu mene ne abin yi, wani matakin ki ke ganin za ki É—auka a kan wannan lamarin?"
Hajiya Sa'a ta sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Duk matakin da zan É—auka, kafin mutuwarsa yakamata na É—auke shi, dana sani nake mara amfani na janyo yarinyar nan jikina, sannan idan na matsa, tsaf za ta tona mana asiri, dan haka ba zan saurare ta a yanzu ba, ina cikin matsanancin kewa da alhinin rashin tilon É—ana. Sai dai wallahi sai ta tafi inda Abba ya tafi, ko da kuwa nima zan rasa raina na"
Jiki a sanyaye ta ce "Hajiya ki bi a hankali, kar garin neman gira a rasa idanu"
"Ki zuba ido kawai" ta faɗa a taƙaice tana share hawaye.
Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya sanya Nana farkawa, ta ganta a É—akinta a kwance, ba ta iya tuna abun da ya faru ba tun daga biyo ta da Sayyid ya yi.
Ta kalli ƙwan fitilar ɗakin a kunne, ta yinƙura za ta tashi, kawai ta takardar nan, da ya nuna mata yake tambayarta waye ya aiko da ita.
A tsorace ta ja gefe, tana kallon takardar. Jikinta na rawa bakinta ɗauke da addu'a, ta ɗauki takardar ta sake ƙare mata kallo. Ta ninke ta ta saka a cikin kayanta, ta shiga banɗaki.
*****
Nana na tsaka da aiki a kitchen, ta ji motsi a kitchen É—in.
Ta waiwaya ta kalli inda take jin motsin, ta ga Asal.
Cike da takaicin babu yadda ta iya, ta ce mata "Barka da safiya"
"Barka, amm na ce akwai abin da ya faru ne? Imam ya ce lallai a tsananta tsaro a gurin girkin nan, ki gaya mini idan da wani abu da ya faru?"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a babu wani abu da ya faru fa"
Asal ta ce "Kar na kama ki da aikata rashin gaskiya, hukuncin da zan yi miki sai kin gwammace kiÉ—a da karatu" Nana ta yi mata shiru, a ranta ta ce "Kya ji da shi"
Asal ta juya ta fita, Nana ta raka ta da harara.
Mahmudu ne durƙushe a kan gwiwoyinsa, a gaban Abdou matawalle.
Ya numfasa ya dube shi ya ce "Imam Hammad ya samu lafiya, ya dawo Nijar"
Mahmudu ya É—ago kai a zabure, yana kallon Matawalle.
"Ka sani, koma me ka ke yi masa da ka ke mallake shi, mu na sane mun zaba maka ido,mun yi maka talala ne mu ga gudun ruwanka. Tun da ya sako ƙafarsa a ƙasar nan, tun ma yana can, yake zancenka yana cewa kana ina?. To ka tsaya da kyau ka saurare ni, zamu sake ka amma hakan ba ya nufin ka yi 'yanci ne, ko kuma mun daina zarginka, mu na nan mu na saka maka ido a ƙarƙashin takunkumi za mu sake ka.
Sannan kar ka kuskura ka gaya wa Imam batun sace shi da ka yi da rayuwar da ya yi a Nigeria. Dan babu yadda ba a yi ya tuna wani abu ba, amma abu ya gagara. Dan haka ba a buƙatar ya san ya yi wata rayuwa a Nigeria, balle maganar nan ta fita, idan kuwa ka bari a ka ji maganar nan a waje, hukuncin da zai biyo baya ba zai yi maka daɗi ba.
Wannan saƙo ne daga Sultan, ba a buƙatar ya san ya yi wata rayuwar daban, dole ka ja bakinka ka tsuke. Dan ka san hukuncin kisa shi ya dace da kai, an ɗaga maka ƙafa ne, saboda son da Imam yake yi maka, ba a buƙatar abin da zai taɓa masa zuciya"
Mahmudu ya saci kallon Matawalle, yana jin zafin yadda mutumin nan yake É—ora masa sace Imam.
Haka nan ya risuna ya yi wa Matwalle godiya.
*****
Asal ce zaune a gaban Sultan, yake yi mata magana cikin nutsuwa da dattaku.
"Yarinyar kirki, na san za ki yi mamakin sake kiran ki da na yi, duk da jiya kun zo gidan nan, to ina da baƙi ne ban samu mun yi magana ba a jiya, shi ya sanya na ce ki zo yau ina son ganinki"
Asal ta jinjina kai, tana saurarensa cikin nutsuwa.
"Na san kin ɗauki dogon lokaci mijinki baya kusa da ke, wasu faɗi tashin duk da ke aka yi kin san komai. To ga shi Ubangiji Allah ya yi masa dawowa cikin aminci. Sai dai duk da haka haryanzu bai gama samun lafiya ba. Dan Allah dan Annabi ina roƙon ki, ki zama mai haƙuri da juriya da kuma rufa masa asiri. Kin san yadda yake da magauta ta kowacce kusurwa, dan Allah ina sake roƙon ki, ki zama rufin asiri ga Imam, duk abin da ki ka gani wanda ba ki yadda da shi ba, ki zo ki sanar mini ban yarda ki gaya wa kowa ba. Dan Allah ki yi haƙuri da shi ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali daga gare ki"
Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Abie, ba zaka same ni da wata matsala ba, zan zama mai rufa wa mijina asiri"
"Na gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya yi muku albarka, ya baku zuriya ta gari masu jin ƙai"
"Amin Abbie, muna godiya sosai da sosai"
Sosai Imam Hammad yake son ya ci gaba da gudanar da al'amuransa da ayyukansa da yake yi, kamar a baya, amma abu ya gagara gaba É—aya ji yake komai ya fita daga ransa. Jin jikinsa yake yi kamar a É—aÉ—É—aure duniyar sam ba ta yi masa daÉ—i, ga shi takamaima bai san abin da yake damunsa ba.
Sultan ne ya aika da mota aka ɗauke shi, bai san ina za a kai shi ba, bai kuma tambaya ba. Gidan da ake sauke baƙin Sultan nan aka kai shi. Sai ya fara mamakin ko wata ganawar zai yi da baƙin, amma Sultan bai gaya masa ba?.
Sai dai babu zato babu tsammani ya ga Mahmudu.
Cikin matsanancin farin ciki suka nufi juna, Imam ya ce "Mahmudu" Ya rungume shi cikin farin ciki. Sai dai wata irin karaya ta shiga zuciyar Mahmoud.
Imam ya ce "Tun da na dawo nake cigiyarka, na ce ko ba ka san na dawo ba, a Faransa ma sai da na roƙi a kawo mini kai, mu zauna tare na yi jinyar, amma ba a bani dama ba" sai dai jin sheshsheƙar kukan Mahmoud ya ɗaga masa hankali, ya ɗago shi cikin damuwa ya ce "Mahmoud, ko na yi maka wani abu ne?"
Ya girgiza kai yana share hawayensa ya ce "Ai ba ka yi mini laifi, ko me za ka yi mini a duniya kuwa. Murna ce da kewa ta sanya ni kuka"
Jiki a sanyaye ya ce "Dan Allah ka bari, zuciyata ta karaya nima" Sai dai maimakon ya yi shirun, tamkar tunzura shi ya yi, ya sake fashewa da kuka.
Hawaye ne ya cika idanun Imam, ya ce "Dan Allah ka gaya mini idan wani abin ne ya faru, duk ka sanya jikina ya yi sanyi, kamar ban taɓa ganin kana kuka ba"
Ya share hawayensa ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na ce maka murna ce kawai nake da ganinka ya shugabana, ina fatan ka dawo cikin ƙoshin lafiya"
Ya yi tsaki ya ce "Za ka fara ko? Waye shugaban naka?"
"Kai mana Allah ya baka nasara"
Kawai ya yi wata dariya ya ce '"Ka ci gaba, zan rama ne"
Mahmudu ya yi dariyar shi ma ya ce "Ba zan iya fasalta adadin yadda na yi kewar ka ba, da farincikin da nake ciki, a sanadin dawowarka ba"
Imam ya ce "Na fika murna da ganinka"
Duk da yau suka haÉ—u tun dawowarsa, amma ji yake kamar ya gaya wa Mahmudu abubuwan da yake ji, amma sai ya fasa ya ga kamar ya yi wuri.
Shi kuma Mahmudu zuciyarsa cike take da karaya, da kuma tunanin tayaya zai gaya wa Imam Hammad cewa ya yi aure a Nigeria, alhalin ga kashedin da aka yi masa. Ita Nana da suka baro a Nigeria mene ne matsayinta. Ya tuna irin É—awainiyar da ta din ga yi da shi, da rayuwar da suka yi, amma alamu ya nuna sam Hammad bai san an yi hakan na, dan da ya tuna zai yi masa maganar. A ransa ya yanke dole ya shirya da kansa ya tafi Nigeria neman Nana, kuma ko me za a yi masa idan ya gano ta, dole ya kawo ta ya gabatar da abin da ya faru, ko da hakan yana nufin a yanke masa hukuncin kisa ne, gara ya yi da ya mutu da hakkin Nana a kansa.
Ya din ga mamaki da tambayar kansa, yaya aka yi a wannan karon, Imam ya dawo hayyacinsa ya sake mantawa da rayuwarsa da Nana, bakinsa fal tambayoyi amma babu halin furta su, saboda kashedin da aka riga aka yi masa.
Tare da Mahmoud suka zauna suka sha hira sai dai abincin da aka shirya musu, Imam ya ƙi ci.
"Imam, wai ya na ga ba ka cin abincin ne?"
"Abincin da ya fito daga hannu É—aya ne tal yake yi mini É—anÉ—ano a bakina yanzu, idan ba shi ba duk wanda na ci salam nake ji"
Cikin mamaki ya ce "Abincin wani hannu kenan?"
Ya É—an yi shiru ya ce "Asal ce ta kawo wata mai yin girki daga Nigeria, idan ba ita ta dafa ba, ba na gane kan Abincin"