← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 78

Sashe 6

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da ƙarfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi ƙarfin mutum".

Sajida ta ce "Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?"

Barira ta ce "Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri"

"Ni fa ba na son kurman baƙi, a masu shigowa ne mayun, ko kuma zaunannun gidan"

"Na ce ki zuba ido ki ga ikon Allah"

Bai fi mintuna biyar ba, wani irin hayaƙi, mai azabar yaji, ya turnuƙe gidan.
Nana da take lafiya ƙalau ma, ta fara tari.
Shi m tarin yake yi, numfashinsa kamar zai ɗauke, ta ɗaukko mafici ta din ga yi masa fifita. Ta gaji ta tashi, da nufin ta je ta ga me ake ƙonawa yake wannan uban hayaƙin haka. Amma ya riƙe hannunta ya hana ta. Haka suka wuni a galabaice. Sajida ma sai bala'i take yi, tana cewa Barira za ta kashe ta da hayaƙi.

"Wai Sajida ko ke ce mayyar nan ne?"

"Ke kama bakin ki, wallahi ki ka ce mini mayya, sai mun yi shari'a da ke"

Barira ta ce "Sai ki saurara mini, tun da dai ba ke ba ce" Haka suka wuni, Barira tana gana musu azaba, da wannan azababben abin da take zubawa a cikin murhu.
Washegari ma, azabar hayaƙin nan ce ta tashi su Nana, numfashin Sayyid tamkar zai ɗauke saboda azaba.
Nana dai ta ci gaba da daurewa, amma yamma na yi, Barira ta sake cika kurfoti da gawayi, ta tayar da wuta ta afka hayaƙin nan.

A fusace Nana ta fita, ta tarar da ita tana ta girgiza kurfotin, tana zuba wani abu a ciki.

Nana ta ce "Barira, dan zatin Allah ki daina zuba wannan abin. Ina da mara lafiya a É—aki. Yana da matsalar numfashi, jiya kwana muka yi babu bacci. Kuma da sassafe kin banka wani, kuma yanzu ma ga shi kina sake kunnawa"

Ta kalli Nana ta ce "Ai duk wanda ya hana uwar shi bacci, wallahi shi ma ba zai yi ba"

Nana ta ce "Kamar yaya kenan?"

"Kamar yadda ki ka ji"

"Ni dai koma mene ne, ki yi haƙuri idan ba ki yadda ba, zo mu je ɗakin ki ga halin da yake ciki"

"Babu ruwana da halin da yake ciki, kurwata ce ta fi ƙarfin duk wani maye wallahi"

Nana ta ce "Barira mu ne mayun da ki ke faÉ—a dama? To Barira ko za mu ci mutum ma ci taki, jiki duk dauÉ—a?"

"Ko ma duk uban mene ne, tun da aka kama ni aka lasa, an ji zaƙin kurwa ta, wallahi sai mutum ya ci ubansa, miyagun banza kawai"

"Mu ne mayun Barira?"

"Eh ku ne, ko na ce ke"

Nana ta ƙarasa daf da Barira ta damƙi tsintsiyar hannun Barira ta ce "Ki ka ce ni mayya ce?" Barira ta yinƙura za ta fizge hannunta, ta yi bala'i. Kawai ta ji jikinta ya yi wani irin nauyi, kuma jikin ya yi mata wani irin sanyi, ta kasa motsa komai. Kawai ta silale ta faɗi ƙasa.

Ayshercool
08081012143
54

Ihu Sajida ta saka, tare da sauran matan da suke zaune, tamkar ana bajekolin kasuwar ƙauye, suka dare ganin daga riƙe hannun Barira da Nana ta yi, ta faɗi ƙasa. Faɗuwar da ba su da tabbacin, tana raye ko mutuwa ta yi.
Wasu suka yi waje da gudu su na ihu, tamkar garken tumakin da ba su san inda suka dosa ba.

Nana kuwa idanunta a rufe, ta nufi ɗakin su tana tangaɗi, Sayyid kuwa da ƙyar ya lallaɓa ya tashi yana ƙoƙarin fitowa, amma mai afkuwa ta riga ta afku. Nana na shiga ɗakin ta faɗa jikinsa, ya taro ta. Gaba ɗaya jikinta ya saki kuma ya yi sanyi ƙalau, shaidar Ƙaisar ya buge ta.

Ya ɗauki wayarta, ya tura wa Ummi saƙo.

Tuni aka kira mijin Barira, jikinsa na rawa ya shigo gidan, tare da rakiyar wasu mazan.
Ya durƙusa a kan Barira ya taɓa ta, ya ɗago ta, sai dai ya ga tana numfashi, sai dai idanunta a kakkafe, ya girgiza ta yana kiran sunanta "Barira. Barira ki buɗe idonki. Ki na ji na?" Barira ba ta motsa ba, kuma ba ta yi magana ba. Sai dai numfashinta yana fita normal.

Mijinta ya ce "Dan a samo adaidaita sahu mu tafi Asibiti"

ÆŠaya daga matan da abin ya faru a gaban su ta ce "Wane Asibiti, ai ko an je Asibiti babu abin da za a gani, Nanan za a janyo daga É—akin, a yi wa dukan tsiya a sanya ta tsallaka ta, shi ne za ta tashi, kama mata kurwa ta yi"

ÆŠaya daga mazan ya ce "A'a ba za a dake ta ba, a kai ta dai gurin hukuma, a san abin yi."

Mijin Barira ya ce "Wane irin kar a dake ta, kana kallon halin da matata take ciki"

Ya miƙe ya nufi ƙofar ɗakin su Nana, cikin ɗaga murya ya ce "Kina ina, ki fito ki tsallake mini mata, ki sakar mata kurwa" Sai dai ya ji shiru, babu wanda ya yi magana. "Ki fito ko na shigo wallahi"

Wani ya ce "Kar a yi haka Gali, ka ga matar aure ce, bai kamata a bi abin da mata suka faÉ—a ba, kamata ya yi a zurfafa bincike tukuna, kar a É—auki doka a hannu, a zo daga baya a ji kunya"

Gali ya ce "Malam ni dai ba zan ji kunya ba da yardar Allah, kalli halin da yarinyar nan fa take ciki. Idan ta mutu fa? Wallahi ba zan yarda ba"

A fusace maƙwabcin na su ya ce "To a je Asibiti mana a duba, sai haƙilo ka ke yi, matarka matarka. Kamar ba nan ka ke jibgarta, ake ƙwatar ta da ƙyar ba, sai da aka haɗa ka hukuma ka daina, auren da ko shekara biyu bai yi ba, a lokacin ba ka yi tunanin ta mutun ba sai yanzu?"

A fusace Gali ya ce "Kar ka gaya mini maganar banza mana, ina ruwan ka da dukan da nake yi mata, dama munafunci ne ya sanya ku ke yi mana sulhun?"

Ummi ce ta yi sallama, Sajida ta yi caraf ta ce "Yauwwa ga yayarta, ita ce dama ta kawo ta gidan nan"

Cikin mamaki Ummi ke bin dandazon jama'ar da kallo. Ta ce "Wai lafiya me ya faru?"

Mijin Barira ya ce "Mene ma bai faru ba, kin kawo mana mayya ta kama mini kurwar mata. Dan haka sai ki shiga ki fito da ita ta tsallaka ta"

Tuni idon Ummi ya cika da hawaye, saboda ba ta ƙaunar tashin hankali ta ce "Wallahi mu ba mayu ba ne ba. Nana ƙanwata ce, akwai dai abin da ya faru amma ba wai Nana ta kama kurwar wani ba"

"To ƙarya aka yi mata? Ba ga Bariran can a kwance ba, ta tashi mana".

Cikin tashin hankali Ummi ta ce "Wallahi kaf zuriyarmu babu mayu, Nanan ma matsalar mutanen ɓoye ne da ita, amma ba maita ba, bari na duba ta" Ta nufi ɗakin da su Nana suke. Tuni gidan ya sake ɗinkewa da mutane, ya cika fal wasu suna a fito da Nana, a zane ta a saka ta tsallake Barira.

A zaune ta tarar da Sayyid, rungume da Nana a jikinsa. Cikin damuwa da tashin Ummi ta ce "Wai me ya faru ne?" Ya yi shiru yana kallon Ummi, sannan ya mayar da idonsa kan Nana.

Ta É—auki wayarta ta kira Baba. Tana jin ya É—aga ta fashe da kuka.

Baba ya ce "Ke meye haka lafiya?"

"Baba babu lafiya, dan Allah ka zo gidan Nana, akwai matsala ne"

"Gidan Nana kuma? Ina ne gidan Nanan, kuma matsalar mene?"

"Baba mutanen unguwa sun taru, za su dake ta, kar su kashe ta ni ban ya zan yi ba"

A sukwane Baba ya miƙe ya ce "Ƙarya ne. Nanan za su kashe mini, ai zan yarda kowa zai iya ɗaukko magana a cikin ku, amma ban da Nana. A can gidan gadin nata ne za su dake ta?"

"Baba wane gidan gadi kuma, ai sun bar gidan tana nan kusa da ni, ka manta ne? Ka cewa Nasiru ya rako ka ya san gidan"

"Gani nan zuwa" ya kashe wayar ya yi waje da sauri.

Ummi ta tsaya a bakin ƙofar, tana ta ba su haƙuri. Amma sai nema suke yi su ture ta, su shiga ɗakin.

"To ban da wulaƙanci ma, ta shige ɗaki taƙi fitowa, da yake ba ta da gaskiya. Maimakon mijinta ya fito ya bayar da haƙuri, shi ma ya yi zamansa saboda rashin tsoron Allah, da rashin gaskiya"

Ummi ta ce "Mijinta ba shi da cikakkiyar lafiya, ita ma aljanu sun buge ta, dan Allah ku yi haƙuri" Sai dai abin ya fi ƙarfin Ummi, ƙoƙarin hankaɗe ta kawai suke yi, su cimma Nana.
Ana haka sai ga maƙwabcin su Nana, tare da jami'an tsaro. A dole mutanen suka saurara. 'yan sanda suka ce, a tafi da Barira Asibiti, abin da likitoci suka ce, da shi za a yi amfani.

Ana haka Baba ya ƙaraso, cikin tashin hankali.

Ummi na ganin sa ta yi ajiyar zuciya. Ummi ta ce "Baba ka zo?"

"Eh, ina Nanan take, kuma uban me ta yi za a dake ta da?"

"Ai gama 'yan sanda sun zo, saɓani suka samu da wanda suke zaune gida ɗaya, shi ne suka ce mayya ce"

Baba ya ce "Maita kuma? In ji uban wa?"

Mijin Barira ya ce "Ga shaida Baba, kalli matata a baje a kwance"

"Kuma sai ka ce 'yata mayya ce? To wallahi ƙarya ne, kaf danginmu babu mayu, ku dai nemo wani abun, ba maita ba wallahi" 'Yan sanda suka shiga maganar, aka tafi da Barira Asibiti.

Sai da aka bar 'yan sanda biyu, gudun abin da ka iya faruwa, saboda matan da abun ya faru a gaban su, su na ta ƙara balbalawa wutar fetur. Tare da mayar da abin da aka yi da wanda ma ba a yi ba. Gaba ɗaya zancen ya zagaya unguwa.
Har sha ɗayan dare case bai ƙare ba, Nana ta farfaɗo ta ga Ummi a ɗakin su, ga duhun dare ya fara yi.

"Ummi lafiya kuwa?"
Chapter 6 · 0% Book details