Sashe 24
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Babu amma tsakaninmu, believe me zan dawo da ke gidana in sha Allah" Jikinta ya yi sanyi. Ya cika ta a hankali, ya shiga motarsa. Ta tsaya ƙyam tana kallonsa, shi kansa da kyar ya tafi, tamkar ya ɗauki Yusra ya tafi da ita.
Har ya kama hanyar Kano, zuciyarsa cike da tunanin ta ina zai fara. Dan shi har ga Allah yana son matarsa, ba a son ransa ya rabu da Yusra ba. Yanzu kuma da ya ganta, gaba ɗaya ya ƙara rikicewa ba abin da yake sai tuno soyayyar da suka yi, daga saurayi da budurwa zuwa auren su.
Ko da ya je gida, Shukura ta karɓe shi tana yi masa sannu da zuwa.
Amsa mata ya yi yana kallon ta, kafin ya ƙaraso ta kira shi ya fi sau biyu, yana zuwa hatta ruwan da zai yi wanka ta tanadar masa.
Ya cire kayansa ya shiga wanka, kamar ta san ba zai iya salla ba, sai ya tsarkake jikinsa, saboda rungumar da ya yi wa Yusra.
Tana cikin tattare kayansa, hancinta ya ji ƙamshin turaren da ba na sa ba a jikin kayansa. Turarensa ɗaya ne da ta san shi da shi. Jikinta ne ya yi sanyi, domin ta daɗe da karantar alamomin rashin gaskiya a tattare da shi. Wani abu ne ya soki zuciyarta amma ta yi ta maza ta haɗiye tare da ajiye kayan.
****
Aka shiga kwana na biyar, ba tare da jin ko É—uriyar Sayyid ba.
Nana duk ta fita hayyacinta, ba ta iya cin abinci, ba ta bacci. Ga Uwani tun tana rarrashinta, ta koma yi mata faɗa tana ganin ta ƙi tawakalli ta ci gaba da addu'a.
Ga shi ta hana ta komawa gidan nasu, a nan gurinta take zaune tare da ita.
Yanzun ma Uwanin ce ta miƙo mata kofi da fura a ciki ta ce "Ungo ki samu ki sha furara nan Nana, ko ɗan cikinki ya samu wani abu shi ma. Rayuwa ba za ta yiwu a haka ba kina zaune babu Abinci, ga juna biyu ba. Idan wani gurin mutumin nan ya tafi, idan da rabo zai dawo ai"
Nana ta karɓi kofin, tana ajiyar zuciya. "Maza ki shanye, kan na fito daga banɗaki" Nana ta jinjina kai tana kallon kofin.
Uwani na shiga banÉ—aki, Nana ta É—auki mukullin da aka kulle gidansu, ta tafi.
Gani take kamar tana shiga za ta tarar da shi a inda ta bar shi. Ƙofar dama a lanjare take aka rufe ta.
Ta shiga É—akinsu, amma ta tarar wayam babu kowa a ciki.
Ta kalli kan katifar su, ta ga abin hiraminsa na rawani a kai. Ta durƙusa a kan gwiwoyinta, ta damƙi hiramin nan, da yake ta ƙamshin turaren sa. Tamkar ta damƙi Sayyid ɗin. Cikin kuka ta ce "Haba Sayyid, daga cewa na je na dawo, sai ka tafi ka bar ni? Haba Sayyid yau kwananka biyar ba ka tare da ni. Da mutuwa ka yi na san wannan hukuncin Allah ne, dole na tawakalli, amma me yasa zaka tafi ban san halin da ka ke ciki ba. Haba Sayyid Haba Sayyid Nana ce fa" ta din ga soki burutsu tamkar zararriya. Wani irin kuka take yi mai haɗe da gunji da ƙunar zuciya.
Ba ta san lokacin da Uwani ta shigo ba, tare da abokiyar zamanta Sabuwa ba, sai ji ta yi ta taɓa ta ta ce "Nana shi ne sai da ki ka fito ki ka zo ko? Ba na ce kar ki fito ba?"
"Uwani. Sayyid ya tafi ya bar ni, na zata mafarki nake yi, me yasa zai tafi ya bar ni?"
"Ke ki ji mini 'ya da rashin ta ido, yo ina zan san dalilin da ya sanya ya tafin ni? Ke ba za ki iya dakewa ki kama kanki ba, idan guduwa ya yi fa?"
Sabuwa ta ce "A'a Yaya, su fa yaran birni su na nunawa junansu kulawa, ya za a yi mutum mara lafiya a neme shi a rasa, ki ce hankalinta ba zai tashi ba? Kina kallon yadda take tiri-tiri da shi take nula da abin ta ke kin san ba ƙaramin so take yi masa ba, ai da tausayi"
Uwani ta ce "Kuma haka ne, amma tun da shi ya tafi nima jikata nake yi wa kar wani abu ya same ta, ga ciki. Ke Nana kuma ba garinsu ya tafi ba bai gaya miki ba? Ba kin ce É—an Nijar ba ne?"
"Ba shi da lafiya fa, ba zai iya wannan tafiyar ba"
"A'a kar ki ce haka, idan ki ka bibiya ma, can ɗin ya tafi, amma yanzu ki yi haƙuri ki tashi mu tafi gida"
"Uwani, dan Allah ki yi mini alfarma ki bar ni na kwana a nan"
"To ya za ki kwana a gida ke kaÉ—ai haka ake yi?"
"Ni dai dan Allah ki bar ni a nan, wallahi da safe zan dawo na yi miki alƙawari"
"A'a sai dai na turo yarinya É—aya ta tayaki kwana" Nana ta amince da hakan, aka turo mata yarinya.
Tuni yarinyar ta yi bacci, Nana kuma kwana ta yi aikin kuka.
Lokaci Lokaci, sai ta yi tasbihi tare da ajiyar zuciya.
Washegari da sassafe Uwani ta zo ta kawo mata abin karyawa.
Yadda idanun Nana suka kumbura, ya sanya ta fahimci Nana ba ta yi bacci ba.
"Wai ni Nana, babu wani wanda za ki kira, ki tambaye shi ko yaje? Ko kuma wani guri da za ki je a duba?"
Jiki a sanyaye Nana ta girgiza mata kai. "To shikenan sha kunun nan da ƙosai, kar su huce"
Nana ta karɓi kunun tana kurɓa a hankali, ji take tamkar tana shan magani, saboda wani irin ɗaci da take ji kunun yake yi mata a bakinta. Amma saboda ba ta son faɗan Uwani, haka ta din ga shan kunun nan da ƙyar.
Ta É—an saci kallon Uwani ta ce "Uwani, ina ga gobe in Allah ya kaimu zan shirya na koma Kano"
"Gurin wa?" Uwani ta jefe ta ta tambayar.
Nana ta ɗan yi shiru, Uwani ta ce "Gurin wannan masoron Ubannaki da bai san ciwon kansa ba balle ya san naki? Ya kasa tallafa miki da larura ta samu mijinki, yanzu ne idan kin koma zai tsinana miki wani abu? Ga cikin fari ke ba sanin kan abubuwa ki ka yi ba, ga wannan shu'umar matar tasa, da ƙafa duk dama ba tsayawa za ta yi ta kula da ke ba?. Ban ƙi ba ki kira shi, ki sanar masa abin da yake faruwa a matsayin sa na ubanki ba, amma ba dai ki koma wannan gidan ba. Ki yi zaman ki a nan ki haihu, ki yi biƙinki idan mijin naki bai dawo ba, a san abin yi"
Tabbas Uwani tana da gaskiya, idan ta koma gidansu rayuwarta ta sake komawa baya, ta san babu wani abin kirki ko kulawa da za ta samu a gidan, wataƙila ma a kore ta. Ummi kuma ta yi mata ɗawainiya da yawa, tana jin nauyin ta sake koma mata da matsala.
Kuma ba ta ji a ranta za ta iya sake ko nufar hanyar gidan Alhaji Zailani ba, saboda yin hakan tamkar cin amanar Sayyid ne, kuma ita ba dolensu ba ce, da za ta je ta É—ora musu É—awaniya. Dan haka Uwani na da gaskiya. Amma zamanta a nan É—in ma, shi ma dai É—awainiyar ce.
Ta sake É—ago kai ta ce "To ina son na je Bauchi gurin Mamana"
"Kai Nana ki na da gardama, gurin nawa ne dai ba za ki zauna ba, kin ƙallafa rai tun da mijinki ya bar garin nan kema sai kin bar shi?"
"Ba haka ba ne Uwani, ina da dalili dan Allah ki bani damar hakan"
"Shikenan Nana, ba zan matsa miki ba, Ubangiji Allah ya tabattar da alkhairi, amma ki bari kamar nan da sati ɗaya, ki ɗan ƙara samun nutsuwa. Nima na lalubi na mota na baki"
"Ai ina da kuÉ—in mota"
"Nima na san ki na da kuÉ—in motar, na ce zan baki ai" Nana ta ja bakinta ta tsuke.
****
Jamila ta yi shirin fita, tana tsaye tana latsa wayarta ta ce "Baba har ya fita ne?"
Mama ta ce "Tun da uwar kashinsa ta cika ya fita. Da dai bai ci ba da yanzu yana nan yana bin bango yana zabga hamma yana faɗa da ƙadangaru da bokitai"
Jamila ta basar ta ce "Sonake ya bani cikakken kwatancen Buda, zan saka a kai ni, na je na ga Nana"
"Wai ba za ki bar maganar Nanan na ba ko Jamila?"
"Mama meye laifi idan na je na gan ta ne wai?"
Nasiru ya ce "Laaa rannan kuwa wannan É—an uwan mijin nata, da suka zo a ka kaita gidanta ranar biki, suka zo shi da wasu mutane, suka ce mini wai yanzu Nana a ina suke. Na dawo daga makarantar allo, na ce musu tana Buda can garin su Baba, shi ne ya ce na gaida Baba"
Mama ta ce "Ikon Allah, amma yarinyar nan ta ce 'yan uwansa an neme su an rasa. Kai Nana muguwar makira ce ta ƙarshe"
Jamila ta ce "Amm na tafi sai na dawo"
"To Allah ya tsare, a gaida Hajiyar"
" Za ta ji" ta amsa a taƙaice ta fita.
Nana ta zauna ta haɗa kayan da za ta buƙata a cikin jaka guda ɗaya.
Tattara sauran guri É—aya, ta É—auki jakar gurin Sarkin Baka, da kuÉ—in Nijar É—in da suke ciki. Ta tattara sauran kuÉ—in da suke É—akinta, tana tunanin ta tafi ko da Uwani ba ta sani ba.
Ta tattara kayan kitchen É—in ta, ta ce wa Uwani sayarwa za ta yi.
"Me yasa za ki sayar da kayan ki Nana?"
"Kawai kuɗin nake buƙata ne"