Sashe 28
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jiki a sanyaye ta miƙa masa takardar da Nana ta bari a kan shimfiɗarta.
"Wannan É—in na mene ne?"
"Ku duba" ta yi maganar hawaye na zubo wa daga idonta.
Adda Saude ta karɓa, ta buɗe takardar "Assalamu alaikum, na san lokacin da za ki ga takardata, na riga na yi nisa. Mama ina mai baki haƙuri da matakin da na ɗauka ban sanar da ke ba. Ba zan so a dadlilina nikaɗai ki bar ƙannena ba, dan Allah Mama ki yi haƙuri ki zauna da su. Na tafi neman mijina, a bawa baban su Walida haƙuri, amma kwana biyun nan da muka yi tare, ya fi kowane kwanaki yi mini daɗi a rayuwata na gode sosai Nana Asma'u"
Shiru suka yi bayan da Adda Saude ta gama karanta rubutun, sai sautin kukan Maijidda da yake tashi. Cikin kuka ta ce "Shekara nawa ina yi masa kara, na riƙe nasa 'ya'yan? Amma ni sau ɗaya ya gaza yi mini kara, 'ya'yana sun tsane ni, a kan laifin da ba su suka yi ba, bai yadda su zo inda nake ba, nima kuma ba zan je ba. Idan na yi magana a ce na yi haƙuri, yarinyar nan ga tsohon ciki ina za ta tafi? Mijin da ita kanta ba ta san a ina yake ba" ta ƙarasa maganar tana ƙara rushewa da kuka. Kawu cikin sanyin jiki ya ce "To ita Nanan ya aka ta tafi babu sanarwa?"
"Tun da ta zo yake masifar sai ta bar gidan nan, babu irin magiyar da ban yi masa ba, amma ya din ga É—aga murya yana bala'i, gaskiya bayan Nana zan bi, ko zan ganta, ban san ina za ta je ba, da ta fita da tsohon cikin nan"
"A'a ba za a yi haka ba, ki yi haƙuri Mai Jidda, rashin kyautawa Iliyasu ba ka kyauta ba, shi ɗa na kowa ne. Kuma tabbas mun daɗe mu na tausar ta, a kan ra'ayinka, ba tare da ba ta damar jin ta bakinta ba. Ka san raɗaɗin da yake cikin raba ɗa da uwa kuwa? Ba ka kyauta ba"
Cikin kuka ta ce "Kawu dama ya bani zaɓi, na zaɓi 'ya ta, ya sauwwaƙe mini na fita na nemi yarinyata"
Kawu ya ce "A'a ba za a yi haka ba, duk inda Nana take yanzu ta yi nisa, kuma idan aka ƙyale ki, ke kan ki ba ki san ina za ki nufa ki neme ta ba. Amma tun da ba yarinya ce ƙarama ba, na san duk inda take Allah zai kare ta, ki ci gaba da yi mata addu'a. Na san ina sha Allah, babu abin da zai same ta, amma batun ki ce ki kashe aure, ki bi ta ki zauna da ita ba mafita ba ce ba, haƙuri kin saba yin sa, a wannan karon ma shi ɗin dai zan baki, na san duk wanda aka ce wa ya yi haƙuri an zalunce shi ne, amma dai ki yi haƙuri.
Kai kuma Iliyasu magana ta domin Allah, ba ka yi kara ba, ba ka kyauta ba ko kaɗan. Yaran nan saboda halinka sun daina zuwa inda take tsawon shekaru, amma daga zuwan yarinyar ka hau bala'i har ta ji, ta yanke wannan hukuncin. Ina kai auren ƙanwarka ne ya mutu, mijinta ya ƙi riƙe 'yar ka karɓo ka kawo mata ta riƙe maka? Har zama fa ta yi da ƙanwarka ta riƙe maka kan ta sake wani auren, amma kai ka kasa yi mata kara, a kan yarinya guda ɗaya tal".
Iliyasu ya zata a wannan karon ma, za a goya masa baya, kamar yadda aka saba tsawon shekaru goma sha, sai dai ya ji wannan karon ba a goyi bayansa ba, sai ya yi tsuru-tsuru, dan haƙuri tabbas ya san Mai Jidda na da haƙuri da kawaici. Kawai ya tsani babansu Nana ne, saboda yadda aka fasa aurensa da ita, ta aure shi, shi yasa tsanar ta shafi su Nana.
Haka aka din ga ba ta haƙuri, Kawunta ya yi ta rarrashinta.
Nana tana zaune a cikin mota, daga jikin taga, tana kallon hanya, yadda ake ta kwarara gudu a motar, tamkar direban zai tashi sama. Gudun da motar take yi, bai dame ta ba, fatanta Allah ya sanya matakin da ta É—auka, ya zama alkhairi a gare ta.
Duk da ta san Nijar ba gida ne ba, ba unguwa ba ba kuma ɗan ƙaramin gari ba, ƙasa ce sukutum, mai ɗauke da garuruwa daban-daban da ƙabilu masu tarin yawa, balle kai tsaye tana zuwa ta doshi inda za ta gan shi. Duk ba abu ne mai sauƙi neman mutumin da ko ainihin sunansa ba ta sani ba a gari kamar wannan, amma tana jin a ranta motsi ya fi laɓewa, kuma rashin jini rashin tsagawa. Wannan shi ne mataki na ƙarshe da za ta iya ɗauka domin nemawa kanta mafita. Ta yarda da cewa Sarƙar, ƙaddara ce ta haɗa ta da Sayyid, ta yi wa rayuwarta dabaibayi, mussaman da ya tafi ya bar ta da ajiyarsa a tare da ita. Sai dai bayan wannan tana cike da zullumin halin da yake ciki, saboda ta san kaso mafi yawa na mafarkin ta ya kan zama gaske, a jikinta take jin duk a inda yake, yana buƙatarta a kusa da shi.
Hankalinta ne ya dawo jikinta, bayan da ta ji ana cewa, an tsallaka boda sun shiga ƙasar Nijar!.
AYSHERCOOL
08081012143
62
Jamila na É—aki tana jiyo maganar Baba ya dawo, ba ta fito ba, sai da aka jima sannan ta fito tsakar gida.
Ya ce"Jamila kun dawo ashe? Yaya ku ka baro Nanan?"
Jamila ta yamutsa fuska ta ce "Bamu tarar da Nana ba, ta bar Buda ta tafi Bauchi gurin mamanta, kamar yadda Uwani ta gaya mana"
A fusace ya ce "Bauchi gurin Maijidda? Lallai yarinyar nan ta riƙa ba ta ganin mutuncina, gidan ubanta ne a Bauchin da ta tafi? Uban me za ta yi a can?"
Jamila ta ce "A'a Baba, kar ka ga laifinta fa, a lokacin da take buƙatar taimako, ba a duba ta ba. Na san ta bar Buda ne dan kar ta din ga ɗora wa Uwani ɗawainiya"
Cikin kumfar baki ya ce "Wallahi ba zai yiwu ba, sai ta baro Bauchin nan, tun da dai ba gidan ubanta ba ne ba, kuma laifin Uwani ne ai da sai ta sako ta a gaba ta dawo da ita nan Kano, dan me za ta tafi wata Bauchi" Ummi ce ta yi sallama, suka amsa su na kallon ta.
Jamila ta ce "Ummi ya dai? Ya na gan ki kuma?"
"Ke Ummi, ke ce babbar algunguma, na san duk abin da Nana take yi kin sani, tun da da ke take shawara, ke ki ka bata shawarar ta tafi Bauchi ko?"
Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a, ba ni ba ce ba. Dan hatta ɓatan mijinta ni ban sani ba, ba ta gaya mini ba sai yau da muka je Buda".
Cikin rashin fahimta Baba ya ce "Æatan mijinta kamar yaya?"
Ummi ta ce "Baba, duk ba wannan ba. Jamila bayan rabuwarmu ina shiga gida, saƙon Nana ya faɗo wayata, hankalina a tashe yake fa"
"Ban gane ba, saƙon mene ne, ke Ummi ki yi mini bayani gwari-gwari sai wani kwalo-kwalo ki ke yi mini"
"Baba, yau da muka je Buda, Uwani ta sanar mana, mijin Nana an neme shi an rasa kusan sati biyu. Har gurin 'yan sanda suka kai cigiya ba a san inda ya tafi ba.
Bayan mun dawo ina shiga gida, saƙon tex message ɗin ta, ya shigo wayata. Ungo ka karanta message ne kusan kashi uku ga shi nan"
Ya saka hannu ya karɓa, cike da fargabar abin da zai gani.
"Assalamu alaikum, Ummi ya ki ke, ya su Islam. Ki yi haƙuri ban sanar miki ba, ba na son ɗaga miki hankali ne. Sayyid fa ya ɓata, daga na je sayo abu, na dawo na neme shi na rasa, ba na son ci gaba da ɗora miki ɗawainiya, ita ma Uwani yau da gobe sai Allah, ba ƙarfi ne da ita ba. Na je Bauchi Mama ta karɓe ni hannu bibbiyu, amma kamar zuwana zai zame mata matsala a gurin mijinta. Na san ko na koma gida, babu lallai Baba ya karɓe ni, na yanke shawarar na tafi Nijar, ko zan ga Sayyid ko danginsa. Kar ku ɗaga hankali gurin nema na, in sha Allah ba zan aikata abin da zai zame mana abin Allah wadai ba. Yanzu haka ina hanyar Niger, kar ku yi wahalar nema na, in sha Allah zan kasance cikin aminci, ku taya ni da addu'a. Nana Asma'u" A fili Baba ya karanta saƙon. Cikin fusata da tashin hankali ya ce "Wace irin mahaukaciyar yarinya ce Nana? Uban wa ye da ita a Nijar ɗin da ta wanke ƙafa ta tafi can? Banda tsabar hauka da rashin hankali da wauta, a gidan uban wa za ta sauka? Ba nan ta ce mini ba ta san suwaye danginsa a can ɗin ba, to gidan uban wa ta tafi?"
"To Allah dai ya kiyaye ya sa ba ɗaukar magana ta tafi ba" Mama ta yi maganar tana kwaɓe baki, wanda tun da aka fara magana da ba ta saka baki ba.
Bai kula ta ba ya ce wa Ummi "Ke kira mini ita dan ubanta ta dawo gida, ko ƙasa nake ci ta zauna mu ci tare"
Ummi ta ce "Baba wayarta fa ba ta shiga, tun kafin na zo gidan nan, nake ta gwadawa, amma ba ta shiga."
"Ki sake kira ki ji dai"
Ummi ta karɓi wayar ta kira Nana, amma aka ce wayar a kashe take.