Sashe 48
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nana wai a ina ki ka san Al Hussain ne?"
Nana ta É—aga kai ta kalli Shugabar gurin nasu, da take yi mata tamabaya cike da tuhuma. Kamar Nana ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce "Waye hakan?"
Matar ta ce "Kamar yaya?"
Nana ta ce "Wanda ki ke tambayata"
Gaba É—aya suka kalli Nana, jin yadda take bawa Adama, shugabar É—akin girki. Ita kuwa Nana ko a jikinta da irin amsar da ta bawa Adaman.
Cike da takaici Adama ta ce"Mutumin da ya fita yanzu"
Nana ta ce "Au sunansa kenan dama? A nan Nijar na san shi, meyafaru?" Ta yi maganar tana tsare Adama da ido, tana jiran abin da za ta sake cewa.
Sai dai ta yi shiru ba ta kuma magana ba, su kuma suka hau mamakin irin amsar da Nana ta bata, kuma ba ta iya ce mata komai ba.
Gaba É—aya Nana hankalinta ya koma kan sauran kwanaki nawa ta koma gida, duk da kullum sai ta yi waya da Nene. Amma ta ga kamar kwanakin ba sa matsawa sam.
****
Hajiya Amina revers ta yi, ta dawo gida Nigeria, saboda kiɗima da tashin hankali da take ciki, ta rasa wanda za ta fara tunkara da maganar. Ta so samun mijin Alhaji Zailani a waya, ta fara yi masa bayani, amma ba ta same shi a waya ba. Ta koma gida a kiɗime, amma ta tarar da saƙon ya yi balaguro zuwa Abuja.
Jikinta na rawa ta kira Doctor Sharif, ya É—aga yana faÉ—in "Hajjaju barka da yamma"
"Sharif abu zan tambaye ka dan Allah"
Gabansa ya faÉ—i, saboda yadda ya ji muryarta cike da tsoro da kuma damuwa.
"Hajiya lafiya dai?"
"Lafiya ƙalau, tambaya zan yi maka dan Allah"
"To Allah ya sa na sani"
"Dan Allah Sharif ana iya samun matar da ba ta da mahaifa dama?"
Ya yi shiru sanann ya ce "Me yasa ki ka tamabaya?"
"Ka bani amsa kawai"
Nutsuwa ya yi ya tattara hankalinsa, kar ya ba ta amsar da zai fallasa wani ɓoyayyen abin da bai kamata ba.
Duk da bai san dalilin da ya sanya ta yi tambayar ba.
"Eh ana samu Hajiya, sosai ana samu wani abu ne ya faru?"
"A'a shikenan na gode sosai" ta kashe wayar, sai a lokacin hawaye ya fara gangaro mata, da ta ƙara tabattar da har abada ba za ta samu haihuwa ba.
"Amina butulci za ki yi wa Ubangiji? Sauran ni'imomin da ya yi miki fa?" Wata zuciyar ta tunatar da ita. Sai dai kasancewarta biladama mai ɗauke da zuciya irin ta ɗan adam, sai ta kasa jurewa ta bi nasihar da zuciyarta take yi mata, ta fashe da matsanancin kuka mai taɓa zuciya. Duk da ta daɗe tana yin sa a ɓoye, amma ba ta yanke tsammani ba ta ci gaba da addu'a, amma a wannan karon da ta san ba ta da rabo baki ɗaya, sai ta sare.
*****
Shirye-shiryen bikin Abba yayi nisa, dan bai fi saura sati biyu bikin ba, ta ƙara saka masa ido da shi da Jamila. Jamila sam ba ta nuna mata cewar ta san abin da take yi ba, ta rabu da ita.
Ya kasance taronsu na ƙungiya lokaci yayi, dan haka suka shirya tafiya a wannan karon har da maman Khairat.
Da suka je masaukinsu ma a garin Abuja, Jamila ba ta shiga sabgarsu ba, harkokinta kawai take yi.
Maman Khairat ta ce "Wai Jamsy ya ne? Duk kin zama so silenta, babu wannan rawar kan"
Jamila ta ɗan taɓe baki kawai.
Hajiya Sa'a ta ce "Jamila haushina take ji, ban san me na yi mata ba"
Jamila ta ce "Mummy kenan"
"A'a ba wani Mummy kenan, magana za ki yi"
"To Mummy, ki na ta daughter daughter, amma ƙarara ki ka nuna ba kya ƙaunata, daga ganina tare da Abba, ki ka haɗe rai ki ka yi kicin-kicin, ki ka tashi nema masa aure. Abin ya bani mamaki"
Hajiya Sa'a suka haɗa idi da maman Khairat, ta ce "Haba daughter, ya za a yi na ƙi ki da Abba, ke me ma za ki yi da aure? Na daɗe ina gaya miki za ki iya rayuwa ki da kuɗinki, ba tare da kin yi aure ba. Za ki huta ki yi duk abin da ki ke so."
"Amma Abba ma ai yana da kuɗi, shi me yasa ba ki ce ya yi rayuwa da kuɗi kawai ba, ki ke shirin yi masa aure? Duk wata ƙasaita, kuɗi da wadatar mace, inuwar aure ginshiƙi ce kuma sutura ce ga 'ya mace.
Amma na san saboda ni rayuwata ta gama lalacewa, ke kuma kina son ɗan ki ya yi kyakykywar rayuwa, ki ka yi ƙoƙarin raba ni da shi. Sai dai tun ran gini tun ran zane. Ban ji haushinki ba ko kaɗan Mummy, abin da ki ka yi shi kowacce uwa za ta yi. Ina yi mana fatan dacewa da ƙarshe mai kyau" Tana gama maganar ta yinƙura ta tashi, ta bar ɗakin.
Safiyya ta ce "Kin ga Hajiya, ki bi yarinyar nan a hankali, alamu sun nuna hankali ya fara shigarta, ta san ciwon kanta, kuma abin da aka yi mata duk da ta samu kuɗi ya yi mata ciwo. Kar ki bi ta da ƙarfin tsiya ta yi tawaye"
Hajiya Sa'a ta numfasa ta ce "Na ga alama, amma ba zan taɓa rainon ɗan kwiykwiyo, ya girma ya fara yi mini haushi ba. Ina son samun jinin 'yar uwatta na riga Zailani samu ko ta halin ƙaƙa, daga nan zan yi maganinta"
Safiyya ta jinjina kai.
Doctor Sharif ya din ga kiran Alhaji Zailani, ya sanar da shi kiran da Hajiya Amina ta yi masa, amma ya kasa samunsa a waya, saboda su shinga taron manyan ƙungiya da suke yi, wanda sai sun kwana uku suke fitowa, sannan ayi babban taro na kowa da kowa da ke cikin ƙungiya.
Ganin kiran Hajiya Amina ya bawa Shukura mamaki, dan idan tana Saudiyya sai dai su yi video call.
Ta É—aga ta ce "Mami, yaya ba ki samu tafiyar ba ne?"
"Shukura za ki iya zuwa gida, ban takura miki ba"
Cikin tashin hankali Shukura ta ce "Lafiya kuwa, ya na ji muryarki a haka?"
"Dan Allah idan da hali ki zo gida"
"Shikenan, gani nan zan kira baban Haidar na gaya masa, gani nan Allah ya sa lafiya"
Hankali a tashe, ga tsohon ciki haka ta ɗauki mota ta tafi gida. Tana matuƙar jin Hajiya Amina a zuciyarta, saboda bayan rasuwar mahaifiyarsu, tun su na ƙanana babu yadda ba ta so cuzguna mata ba, amma Hajiya Amina babu ruwanta. Ba ta damu da abin da mutane za su ce ba, ta riƙe ta da halin ta, sai da ta ƙara wayo sannan ta gane ba ta da wata uwa da ta wuce ta. Shi yasa take matuƙar jin damuwarta a ranta tamkar uwar da ta haife ta.
A bedroom ta tarar da ita, idanunta jawur sun kumbura. Cikin tashin hankali ta ƙarasa ta zauna ta ce "Lafiya kuwa? Ko ba ki da lafiya ne?"
Ta girgiza kai ta ce "Yi haƙuri Shukura, na taso ki ga tsohon ciki, na rasa da wanda zan yi zancen nan na ji daɗi a raina."
Cikin damuwa ta ce "To meyafaru?"
"Shukura wai ba ni da mahaifa"
Shukura ta yi saroro, ta ce "Kamar yaya?"
Ta share hawayenta ta gaya mata duk abin da ya faru. A ƙarshe ta ce "Na kira Doctor Sharif ya ce mini eh ana iya samun mata da basu da mahaifa, amma na yi mamakin yadda duk yawon Asibiti da na yi a nan, ba a taɓa gaya mini ba"
Shukura ta É—an yi shiru sannan ta ce "Anya kuwa? Kin san fa kin daÉ—e da daina zuwa Asibiti a kan matsalar nan, Daddy ba ya so. Sannan ku ne ku ke yarda da maganar Sharif É—in nan, ki rabu da shi mu je wani Asibitin daban, a sake duba ki a tabattar da abin da yake faruwa. Duk da ba na tunanin za a samu matsala a abin da can Egypt É—in suka gaya miki."
Ta girgiza kai ta ce "A'a Shukura, babu inda zan sake zuwa, na yi maganar ne da ke dama na samu sanyi a raina, na kira babanki ba ta shiga"
Shukura ta yi shiru, kawai dai ta ji ita abin kamar akwai lauje cikin naÉ—i.
*****
Nana ta shafe sati na biyu, tana aiki a wannan gidan Abinci. Sai dai ita kanta tana mamakin irin yadda Al Hussain yake kyautata mata. Hakan ya sanya gaba ɗaya suka ƙara saka mata ido suka tsangwame ta, mussaman Adama da 'yar ta Raliya, da alamu suka nuna Al Hussain take so.
Idan aiki ya ɗan yi sauƙi, Nana kan fita ta shiga cikin gurin cin abincin, ta zagaya ko za ta ga ko mai da Sayyid ne, amma ba ta ga kowa ba. Sai dai gabanta ya kan faɗi a duk lokacin da ta ga masu rawani sun zo gurin cin abinci, sai ta ga kamar za ta gan shi a cikin su.
Ta gama zagayenta, ta koma cikin gurin girkin, Adama ta kalle ta ta tsuke fuska ta ce "Daga ina ki ke, ana tsaka da aiki?"
"Na É—an je wani uzuri ne"
"Na me, kuma a ina?"
Nana ta ce "Uzuri dai na ɗan Adam, na yau da gobe, ai rayuwa na buƙatar sirri ko?"
"Ni fa na fuskanci take-takenki na rashin kunya baki da kunya ko kaɗan, saboda kin ga Al Hussain yana tsaya miki, wallahi idan ba ki yi wasa ba sai na kawo ƙarshen aikinki a nan, sai na saka an kore ki daga gurin nan"
Kallonta kawai Nana ta yi ta kawar da kai, ta ci gaba da abin da take yi. Har ta gama bala'inta, 'yan korenta suka taya ta, Nana ba ta tanka mata ba.
Washegari da sassafe, Nana ta baro É—akinsu, ta tafi kitchen ta fara aikinta, duk da wasu lokutan suna yi mata mugunta, su din ga sakar mata aiki.