← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 78

Sashe 63

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sultan ya yi murmushi ya ce "Kamar dai yadda na gaya muku a baya, Imam Hammad yana Faransa neman lafiya, bayan tsawon wannan lokacin, yau ya kasance tare da mu a liyafarmu ta ƙarshen shekara, dama wannan ne bazatar da na ce zan yi muku"
Nana ta kalli hotunan nan, sai ta yanzu hotunan babu rawani, kowa hoton fuskarsa ce. Ta tsayar da idonta a kan hotonsa da aka rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. A take ta tuna da sunan gidan cin abinci da ta yi wa su Al Hussain aiki. H.J Agadez.
Sunan rukunin gidajen da ta fara zama da Asal shi ma sunan da ke jikin symbol É—in unguwar kenan. H.J Agadez.
Duk surutun da ake yi, da murnar ya dawo, yana ƙame a kan kujera, fuskarsa babu yabo babu fallasa.
Sai daga bisani ya saka hannunsa ɗaya a kan ƙirjinsa ya risunar da kansa ya ce musu "Merci(Na gode)
Duk da a hankali ya furta, amma ko cikin murya dubu Nana ba za ta gaza tantance ta Sayyid ba.

Abduou ya kalli su Nana, ya kalli mutumin É—azu da yake tambayar wace ce "Guda biyu daga cikin su ta zo ta É—anÉ—ana Abincin nan"

Mutumin ya ƙare musu kallo, ya nuna Nana ya nuna wata ya ce su je su ci kafin a ci.
Nana ba ta san a yadda take iya ɗaga ƙafafuwanta ba, saboda ba ta jin su a jikinta, zuciyarta kuwa kamar za ta tarwatse saboda bugun da take yi fiye kima. A hankali ta ƙarasa gaban teburin. Ɗayar ta din ga bubbuɗe Abincin, ta fara ɗanɗanawa.

"Ke kina da gaskiya kuwa? Ki É—anÉ—ana aka ce?" Abduou ya yi mata maganar cikin tsawa.

Rikicewa ta yi gaba É—aya, ya É—aga idonsa ya kalli inda jikinta yake rawa, suka yi ido huÉ—u, ya kawar da kansa yana mamakin yadda take a ruÉ—e.

Ta É—ebo shinkafa a cokali, amma hannunta karkarwa kawai yake yi.
Sultan ya ce mata "Kina lafiya kuwa?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Sultan ya ce "Na fuskanci a tsorace take ne kawai, a kaita ta je ta huta, wataƙila mun yi mata kwarjini ne"

Aka saka Nana a gaba aka fitar da ita daga gurin.

Fitarsu ke da wuya, jikin Nana ya din ga wata irin kyarma, haƙoranta na haɗuwa da juna, wani irin jiri ya din ga kwasarta.
Balaraba ta nufo su da sauri, ganin Nana na dafa bango.
Ya kalli Balaraba ya ce "Maza ki kaita ta huta, wataƙila ta yi aiki da yawa ne ta gaji, gaba ɗaya ta rikice, a kirawo likita kuma ya duba ta.

*****

A hankali Nana ta yi juyi, ta buÉ—e idonta ta ganta a É—akin da take kwana.
Wata irin ajiyar zuciya ta yi, da ta tabbatar da mafarki ta yi ba gaskiya ba ne abin da ya faru.
Hamdala ta yi ta ce "Ni dai na san mafarki ne da ma, dan babu yadda za ayi Sayyid ya ganni ya kasa kula ni, ya nuna kamar bai sanni ba. To wannan idan gaskiya ne ma, ta ina zan fara bayanin ni matarsa ce a yarda da ni? Mutumin da na ji ana batun ya daɗe a faransa yana jinya, anya ma Sayyid ɗina ne? Tun da dai mafarki ne duk da sauƙi.

Sallama aka yi a É—akin, ta ga Balaraba ta shigo É—akin. Ta ce "Kin tashi?"

Nana ta yi shiru tana kallonta.

"Ina ga aiki da ki ka sha a kwanakin nan ne, ya sanya ki ka gaji zazzaɓi ya kama ki, Likita ya ce a bari ki huta sosai da sosai. Gimbiya Asal ta ce a baki hutu na kwana uku ki warware kan ki koma bakin aiki."

Nana ta jinjina kai kawai, tana kokawa da ƙwaƙwalwarta, domin ta tabattar gaske ne, ko kuwa dai mafarkin ne? Ta tashi ta yi alwala ta yi salla, sai dai gaba ɗaya jikinta ciwo yake yi mata, ga matsanancin ciwon kai da jiri da take ji, dan haka ta nemi guri ta sake kwanciya.

*****

Jamila ta ɗauki jakarta ɗauke da wannan tarkacen da take kira da tarkacen jaraba, ta fita waje, ta samu ta sayo fetur a 'yar jarka, ta samu guri ta zuba musu fetur ɗin ta kunna musu ashana ta ƙone su.

Ta tashi tana kallon yadda suka din ga ci da wuta, ta bar gurin.
Kai tsaye ta tari abin hawa ta tafi gidan Hajiya Sa'a.
Hajiyar ta yi iya ƙoƙarinta gurin ɓoye jin haushin Jamila da take yi, ta karɓe ta hannu bibbiyu har ta taya ta lissafin kuɗin kasuwancinta da kuma kayan da take da su a ƙasa.
Bayan sun kammala ta ce "Ni kuwa Jamila, yaya batun ƙungiya wa za ki bayar ne?"
Jiki a sanyaye ta ce "Haryanzu ban gama tunani ba ne ba"

"Tsoron dai ki ke ji haryanzun ko?"

"A'a na rage ji"

"To ki yi ki hanzarta ki yi abin da yakamata amma kin tsaya. Ni kalli nawa nan na shirya komai aiwatar wa kawai ya rage mini, sai na je gidan zan yi, na sake bayar da É—an Fatuhu"

Jamila ta kalli drower da Hajjya Sa'a ta janyo, tana nuna mata 'yar tsanar nan.

Jamila ta ce "To idan ban kai kowa ba, akwai wani abu da zai faru ne?"

Ta ce "Au da kara zube za ki zauna ki ƙi bin umarnin ƙungiya? To idan ba ki kai kowa ba, jininki aljanin zan shanye ki mutu" Cikin Jamila ya yi wata irin ƙara bayan tuna ta ƙona kayan. A tunaninta shikenan ta huta sun rabu.
A ranta ta ce "Wannan wane irin bala'i ne na jefa kaina a ciki, Ubangiji Allah ka kawo mini agaji na rabu da wannan masifar.

*****
Fafur Nana ta ƙi yadda zuciyarta ta amince abin da ya faru gaskiya ne ba mafarki ba, saboda ta riga ta saba da irin wannan cazan kan da Ƙaisar ya kan yi mata wasu lokutan, har ta gaza banbance abin da yake zahiri da kuma mafarki.

Nana suna É—akin girki su na ta É—orawa da saukewa, ta kalli shugabar su ta ce "Dan Allah a gidan nan, babu yadda zan yi na samu waya, ina son na kira gida ne, na ji halin da yarona yake ciki"

Balaraba ba ta bata amsa ba, ta ji Muryar Asal ta ce "Babu wannan damar, sai dai idan kina buƙata ki zo gurina ki karɓi wayar ki kira"
Nana ta É—an yi shiru sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ki bar shi na gode"

"Me yasa ki ka ce haka? Kina tunanin wani abu a ranki ne?"

"Bana tunanin komai, kawai dai na fasa ne"

Ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ga saƙo can daga gidan Sultan, tukuicin aikin da ku ka yi na girki"

Balaraba ta risuna tana yi wa Asal magana da yarensu, Nana kuma ta cigaba da aikinta, tana sane ta cewa Asal ba ta so, dan ba ta gama gane ina Asal É—in ta saka gaba ba, da kuma cikakkiyar manufarta a kanta ba. Tana tsoron ta yi amfani da wata dama da za ta samu ta cutar da ita.

Katafaren É—akin bacci ne, mai É—auke da kayan alatun more rayuwa irin na masu mulki.
Duhun dare ne, sai dai hasken fitilun É—akin ya gauraye ko ina, kai ba ka ce dare ne ba.
Yana zaune a gefen gadon, tare da dattijon. Cikin kamala dattijon ya ce "Imam, ina ƙara yi maka gargaɗi da jan kunne a kan ka ƙara kula da kan ka. Kar ka ɗauka kowane murmushi ne na soyayya, wani murmushin na babu yadda aka iya da kai ne. Kar ka kuskura ka faɗi wani abu da zai rusa shirinmu, mun ɓoye abubuwa da dama a game da kai, duk abin da baka fahimta ba, ka tambaye ni, kar ka wani ya buƙaci sanin wani abu daga gare ka, ka sanar masa kawai jinya ka yi tsawon wannan lokacin.

"Abii"

"Na'am abin ƙaunata" Imam Hammad ya yi murmushi ya ce "Me ka ke ɓoye mini ne, akwai abubuwan da suka hargitse a rayuwata, tsawon wani lokaci na ɗauka ina jinya ba a hayyacina ba?"

"Ka na ji na? Haryanzu ba ka warke ba, ka na buƙatar hutu mussaman a ƙwaƙwalwarka, kar ka takurawa kanka da tunanin abubuwan da suka faru. Jita-jitar da ake yaɗawa a kan ka, da surutai daban-daban shi ne dalilin da ya sanya muka dawo da kai ƙasar nan, a shaida dai kana raye, cikin ƙoshin lafiya"

"Mahaukaci ne ni kenan? Tun da ina iya tuna yadda ciwon nawa ya fara, amma ban san yaya ya ƙare ba"

Sultan ya tsuke fuska ya ce "Ya ishe ka haka. Kar ka kuskura na ji labarin nan ya fita, waye ya ce kai mahaukaci ne? Larurar zuciya ce take damun ka, babu daɗi babu ƙari daga haka. Babu wata larurar hauka a tattare da kai".

"Amma Sultan ko zaka saka na ɓoye wa duniya, yakamata na san matsayin lafiyata...

"Hammad!" Tilas ya ja bakinsa ya yi shiru, ganin yadda ya fusata Sultan É—in.

*****

Tun da garin Allah ya waye, Nana take jin faÉ—uwar gaba da matsananciyar fargaba, ga sanyin da take jin yana ratasa ta, ta san ba na lafiya ne kawai ba. Dan haka ta É—aura alwala take ta addu'a.
Bayan fitowarta ta cika da mamakin ganin yadda ma'aikatan gidan, suke ta aiki tuƙuru suke gyara gidan duk da ko ina a gyare yake.
Ko ta ina ƙamshin turaruka ne ke tashi daban-daban. Har sun so su yi yawa ma.
Ɓangaren da take aiki, sai azalzalarsu ake yi, ta fahimci dai wani baƙo ne mai muhimmanci zai sauka a gidan.
Har mamaki take yi yadda suke ba wa abinci muhimmanci, baƙo ɗaya sai a saka a yi masa abinci biyar, kuma duk da an san ba iya cinyewa zai yi ba.
Chapter 63 · 0% Book details