Sashe 51
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nana ta koma gurin girkin, ta fara ƙoƙarin dafa shayin girfa, saboda babu shi, Adama ta saka ta wani aikin.
Wasu lokutan har rasa yadda za ta yi take yi, sai dai ta kan jure dan kar ta gaza ta sare, dan jikinta yana bata zamanta a gurin nan ka iya sanyawa ta yi nasara.
Sai dai abinka da É—an Adam, wasu lokutan ta kan bujire.
Ta kammala ta tambayi ofishin Hasna, aka nuna mata ta kai mata shayin har can.
Tana tare da Al Hussain ta tarar da ita, da wasu manyan mutane guda uku a office ɗin. Cikin girmamawa Nana ta gaishe su, cikin gurɓatacciyar hausa suka amsawa Nana.
Hasna ta sake mayar da Nana, wai ta kawowa baƙinsu shayi.
Haka Nana ta koma, ta sake kai musu wani shayin, duk da hakan ba aikinta ba ne ba.
Ta fito daga ofishin, Al Hussain ya biyo ta yana kiran sunanta. Ta tsaya ta waiwayo ta jira ya ƙaraso.
"Nana ko haryanzu jikin ne ba ki warke ba?"
Cikin ƙarfin hali ta girgiza kai ta ce "A'a jiki na warke"
"A'a idan ba ki warke ba, na saka a kai ki Asibiti, sai a baki hutu"
Ta girgiza kai cike da ƙwarin gwiwa ta ce "A'a na ji sauƙi fa, zan ci gaba da aiki in sha Allah, na gode sosai da sosai" Ta juya ta ci gaba da tafiya.
Shi dai haka kurum Nana tana ba shi tausayi, sai dai babu wata dama da ta bari, da za a iya zama da ita a ji matsalar ta, ko za a iya taimaka mata. Ya lura ko a cikin ma'aikatan ba ta da sukuni, ba ta sakin jiki da su. Kuma yanayin ta ƙarara yake bayyanar da damuwa duk da tana da ƙoƙarin dakiya.
*****
Alhaji Zailani ya din ga kiran lambar Hajiya Amina. Gaba É—aya ya rikice hankalinsa ya yi mummunan tashi, ya rasa abin da yake yi masa daÉ—i, yana tsoron kar ta aikata wani abin da zai kawo matsala. Ga jirginsa sai washegari zai koma Kano, ga shi yana da manyan uzururrukan da yake son yi a Abuja, da ba zai iya tsallakewa ya bar su ba.
Shukura ta je har gida, ta sake samun Hajiya Amina ta lallaɓa ta a kan ta amince su je gurin Doctor Sabo, amma ta ce babu inda za ta je. Da ƙyar ta amince ta ce ba za ta je a ranar ba sai washegari.
Shukura ta É—an numfasa ta ce "Mami ba na son yi miki maganar nan ki na cikin damuwa, sai dai nima ba a son raina ba, na rasa abin da yake yi mini daÉ—i"
Cikin damuwa Hajiya Amina ta ce "Dan Allah ki kwantar da hankalinki, kar wannan cikin ma ya sake samun matsala mene ne?"
Ta numfasa ta ce "Sagir ne fa yake ta ƙoƙarin dawo da tsohuwar matarsa"
Hajiya Amina ta ce "To shi ne ki ka damu haka? Dan Allah ki rabu da shi ya ƙarata, ki lallaɓa ki haihu lafiya kalau, kin ga ga hawan jini ki na fama fa"
"Wallahi Mami zuba masa idon na yi, takaicina bai gaya mini ba, su na ta ƙwarbai da Hajiya, ta ce ba zai dawo da ita, a bakin ƙannensa nake ji".
"To babu ruwanki, su sha'anin dangin mijin nan ba a zaƙalƙale musu, idan ta dawo ɗin ma wataƙila su tattara su haɗe kai, babu ruwan ki ki kula da kan ki, ki sauka lafiya"
Shukura ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, sannan dan Allah Mami ke ma ki kwantar da hankalinki, nutsuwarki ita ce ta wa, dan Allah Mami ki kwantar da hankalinki kema"
"Wallahi Shukura ƙarfin addu'a ya sanya mini nutsuwa da tawakalli, yadda ku ke yi mini biyayya da ke da Yusuf ko ni na haife ku, Alhamdillah na san iya abin da za ku yi mini kenan. Kuma na san ko yau na bar Duniya za ku tuna da ni ku yi mini addu'a"
Idon Shukura fal hawaye ta ce "Mami ke uwa ce abar alfahari, har Duniya ta naÉ—e ke uwa ce a gare mu, kuma muna alfahari da samun ki"
Suka rungume juna da ita da Shukura, Hajiya Amina ta ci gaba da gode wa Allah, tana jin da natan ta haifa wataƙila ma ba lallai su yi mata biyayya haka ba.
Sai bayan tafiyar Shukura, sannan ta shiga É—aki, ta tarar da kiran wayar Alhaji Zailani rututu.
Yana ganin kiranta ya É—aga, bai tsaya amsa gaisuwar ta ba, ya hau tambayarta abin da ya hana ta tafiya.
Ta ce "Matsala aka samu, kuma na yi ta kiran ka a waya, ba ka É—aga wa"
"Matsalar me?"
"Ba komai, idan ka dawo ma yi magana"
Ya ce "Yanzu nake son ki gaya mini koma mene ne, meye dalilinki na kiran Sharif kina tambayarsa ana haifar mace babu mahaifa?"
Ta ce "Amma laifin me na yi haka? Na tsaya a Egypt su duba lafiyata ne, tun ina can nake neman ka, ban same ka ba, sakamakon gwajinsu ne ya tabattar da ba na É—auke da mahaifa"
"To uban waye ya ce ki je? Ba sai da na ce miki ki bar batun yawon neman haihuwar nan ba, da yake ban isa na saka miki doka ki bi ba, kin raina ni bani da mutunci a idonki?" Duk bayanin da ta so ta yi masa, yaƙi saurararta, ya din ga zazzaga mata bala'i.
Ranta ya ɓaci, ta ga Sharif bai kyauta mata ba, ya za a yi daga tambayarsa abu ya ɗau waya ya kira shi ya gaya masa, ai gara ta gaya masa da kanta, duk da ba wani abin ta ce masa ba, tambaya ce kawai ta yi masa.
*****
Æamgaren Alhaji Fatuhu, Hajiya Suwaiba kamar ta yi bindiga, ganin ya amince ana yi masa maganin gargajiya, a ganinta dan Fadila ta saka baki ne, ta lallaÉ“a shi yake yi.
Yanzun ma Fadila tana ta ƙoƙarin kunna garwashin da za ta yi masa turare, gefe ta kunna mp sautin ayoyin ruƙiyya su na tashi a hankali.
Ya kalli Fadila ya ce "Baby, ina fatan dai magungunan nan, babu wani abu na kauce hanya a cikin su?"
Ta girgiza kai ta ce "Haba Daddy, kai ma ka san ba zan yi duk wani abu da zai taɓa imaninmu ba in sha Allah, Kawu ne duk ya bayar da su, kuma ka san shi ma masanin Addini ne sosai. Babu wani na shirka a ciki."
Ya ce "To ki yi haƙuri, kawai da na tambaya ne, kin san yanayin abin, kar garin magani mu kauce hanya na je na mutu a mummunan tafarki, ya zamana na kasa jure ƙaddarata na kauce hanya"
Fadila ta ce "In sha Allah ba zaka mutu yanzu ba, za ka samu lafiya"
"To ki yi haƙuri, na ga kin ji haushix
Ta girgiza kai ta na É—an murmushi ta ce "A'a ban ji ba"
"Kin ji mana, kin tura baki gaban ne ba ki ji haushi ba?" Sai kuma suka yi dariya a tare.
Ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah ba zan sake magana ba, na yarda da ke, ba zaki cutar da mu ba"
Hajiya Suwaiba ta shigo ɗakin, tana basarwa jin yadda ɗakin ya ɗume da ƙamshin jan almiski, da ƙaurin hayaƙi. Ta ɗan taɓa baki a ranta ta ce watakila ma a cikin wannan tsiyatakun take mallake ka.
Ta ajiye masa kwanukan Abinci, ta juya za ta fice.
Ya ce "Ba magana ne?"
"Sannu ya jiki?" Ta faɗa a daƙile.
"Jiki Alhamdillah, a hankali ji nake jikina ya yi daɗi, na ɗan samu sassauci daga abin da nake ji kamar an ɗaure ni, ba na iya motsi sai da ƙyar da dabara, da ƙirjina da yake yi mini nauyi nake jin kamar an toshe mini baki da hanci da kokowa nake numfashi" Duk da tana jin haushinsa sai kuma ta saki fuska ta ce "Alhamdillah, sauƙi yana samuwa kenan? Ubangiji Allah ya ɗorar da sauƙi, dama komai nufi ne na Allah"
Ta kalli Muhsin da yake ta tattaɓa kwanon abincin da ta kawo. Ta ce "Kai ɗan lukuti acici, ka zubar mini da Abinci sai ka biya ni. Ki zuba masa abincin ko ci zai yi" Ta yi maganar sama-sama tana ɗan kallon Fadila. Duk da matsanancin kishin da Hajiya Suwaiba take yi da ita, yanayin yadda take yi wa Muhsin wasu lokutan ya sanya Fadila ba ta fiye jin haushinta ba.
*****
Hasna kuwa ta sako Nana a gaba, bayan aikin da take yi, ta din ga sanya ta wasu ayyukan daban da ba sa cikin jadawalin wanda aka É—auke ta yi. Wasu lokutan sai ta gama aiki, ta koma É—akinsu, sai ta saka a taso ta, ta saka ta aiki. Abin ya ishi Nana amma ta danne.
A wannan karon ma, har ta yi shirin kwanciyar, aka zo aka kira ta. Kawai ta ji a ranta, ko Hasna za ta kashe ta yau, sai dai ta kashe ta, dan ba za ta yi mata kowane aiki ba, sai dai ta kore ta.
Ƙarafe goma sha ɗaya na dare, amma tana ofishinta ba ta tashi ba. Ko da Nana ta je, tsayawa ta yi ƙyam tana jiran ta ji me Hasnan za ta ce.
Sai dai ta ci gaba da aikin gabanta, sai da Nana ta fara ƙosawa, sannan ta kalle ta ta ce "Amma an ce 'yar Nigeria ce ke ko?"
"Eh" Nana ta amsa a ƙufule.
Ta ɗan ƙura wa Nana ido sannan ta ce "Ina da wasu baƙi ne gobe in Allah ya kaimu " Nana ta ɗago tana kallonta, ta ji ina ne ƙarshen zancen, dan kullum cikin baƙi suke kamar gurin boka.
"Dan haka ba aikin gurin cin abincin nan za ki yi ba gobe in Allah ya kaimu, aikina za ki yi. Zan saka a sanar musu ma. Ina son ki yi Abinci mai kyau da daÉ—i na Nigeria. Ina son na sauke su da shi. Wajen la'asar za su zo, dan haka za ki dafa abin karayawa, da abincin rana da na dare, za a zo a É—auka"
Nana ta yi ajiyar zuciya jin ba wani aikin rainin hankalin Hasna ta saka ta ba.
"Allah ya kaimu, zan iya tafiya?"