← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 78

Sashe 10

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jamila ya ne? Ki saki jiki ki ci abinci mana" Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba.

"Ko dai haryanzu abin da ya faru ɗin ne yake damun ki? Tun wuri ki ajiye wannan abin, ki ci gaba da rayuwar ki cikin kwanciyar hankali. Ɗan ƙaramin abu ne fa, ranar da aka ce ki bayar da jini kuma ya zaki yi? Ki na gani Safiyya ta tafi Dubai ma sarin kaya, kuma duk harka ce ta ƙungiya ta ɗaukakata haka. Har gara ke ma da ba ki da aure, Safiyya da aurenta, amma kalli yadda ta kama ƙasa, mijin ma ita yake yi wa biyayya, ki saki jikinki dan Allah ki daina wannan damuwar.
Ki ƙarasa cin abincin, Talatu ta gyara gidan, idan an zo ana son kaya, kin san gurin da suke, zan je sake duba Fatuhu ne, daga nan na je a gyara mini kaina"

"To Mummy a dawo lafiya"

"Yauwwa Daughter Allah ya sa"

Ta gama abin da take yi ta fita, bayan fitar ta, Jamila ta tashi ta nufi harabar gidan, tana kallon flowers ɗin da aka ƙawata harabar da su. Jibga-jibgan motocin Hajiya Sa'a uku na hawa. Ga na ɗanta Abba biyu. Iya harabar gidan abar burgewa ce, ta yadda duk mai rai zai yi fatan ya samu wannan wadatar. Sai dai kash, hanyar da aka bi gurin tara dukiyar, duk wanda ya ji muddin yana da imani, sai ya gudu da ƙafafuwansa.

Ji ta yi kamar wani abu yana bin wuyanta, ta juya a hankali ta ga Abba ne a tsaye, yana saka abin fulawa a wuya.
Ta yi guntun murmushi ta ce "Yaya Abba"

"Na'am ƙanwar Abba. Ya na ganki nan lafiya dai ko?"

"Lafiya ƙalau, ba ka fita ba?"

"Yau ba zan fita ba, ba na jin daɗi ne gaba ɗaya, dan da zazzaɓi ma na kwana wallahi"

Cikin tausayawa ta ce "Kash, sannu Allah ya ba ka lafiya. Ka je Asibiti mana"

Abba ya ɗan numfasa ya ce "Na sha magani already, dan haka ba sai na je ba, zo mu je mu zauna ki yi mini hira, na san zazzaɓin zai sauka gaba ɗaya" Dariya ta ɗan yi ta ce "Ai ni ban iya hira ba"

"Ba wani nan, amma ki na yi da Mummy ai, gaskiya mu je sai kin yi mini" Tana dariya ya wuce gaba ta bi bayan sa. Sanyin halin Abba ya fara tasiri a zuciyar Jamila.

*****
Alhaji Fatuhu na zaune, Hajiya Suwaiba ta gama gyara jikinsa, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya kalli uwar 'ya'yan nasa ya ce "Haryanzu Fadilan ba ta haihu ba?" Ta taɓe baki ta ce "Tana can ba ta haihun ba tukuna."

"Allah ya sauke ta lafiya" ta yi shiru ba ta amsa ba.

"Yakamata a sallame ni na koma gida haka, na gaji da zaman Asibitin nan gaba É—aya"

A hasale ta ce "To mu koma gida mu yi yaya ne? Nan É—in ba dai magani ake baka ba ana kula da kai, komai sai ka nuna kai ba a kyauta maka ba, ba a iya ba haba dan Allah"

Jiki a sanyaye ya ce "Yi haƙuri, Allah ya baki haƙuri" daga haka ya sunkuyar da kansa.
Sai kuma jikinta ya yi sanyi, ta zauna a kusa da shi, tana tunanin ta yi magana. Ta ga yana share hawaye.

Cikin damuwa ta ce "Alhaji kuka ka ke yi? Dan Allah ka yi haƙuri raina ne a ɓace, amma dan Allah ka yi haƙuri"

Ya yi mata shiru, gaba ɗaya ta rikice ta rasa abin da za ta ce. Raudah ce ta turo ƙofa hannunta da towel ta ce "Daddy guess what?" Ta miƙa masa narkeken jaririn da Fadila ta haifa.

Hannunsa na karkarwa ya riƙe jaririn ya ce "Another Muhsin" ya yi maganar yana murmushi.

Ya din ga yi wa jaririn kiss, yana shafa shi kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba.

****

Fafur Sayyid ya hana Nana zuwa ko nan da can, har aka yi azahar.Uwani ta sake aiko musu da dambu, ta ce a cewa Nana ba za ta zo ba, sai ta zo da kanta.

Cikin damuwa ta ce "Sayyid dan Allah ka bari na je, na ji kiran me take yi mini" fafur ya sha kunu ya tsuke fuska.
Babu yadda Nana ta iya, ta zauna ta ƙi fita. Ta zazzage kayansu, tana ƙara gyara musu, ta fito da kayan wankin gashinsa, da turarrukansa da duk wata sai su Habu sun sayo sun kawo. Ta ɗaga kai ta ga ita yake kallo, ta ɗan yi murmushi ta haɗe su a guri ɗaya da combs ɗin sa na taje gashi.

Sai yamma bayan sallar la'asar, ta yayyafawa tsakar gidan ruwa, ta share shi.
Ta yi shimfiÉ—ar tabarma a tsakar gidan, ta saka wa Sayyi fululluka ta kamo hannunsa zuwa waje.
Ya zauna, ta É—aukko mayafin rawaninsa ta yafa masa a kansa.

Babu jimawa sai ga Uwani ta zo, tana faÉ—in "Tun da ba za ki zo ba, ni ga ni na zo da kaina"

Nana ta ce "Ba ƙin zuwa na yi ba Uwani, yanayin jikinsa ne sai a hankali, shi yasa ban fito ba"

"Koma dai mene ne gani na zo ai" Ta kalli Sayyid ta ce "Sannu ko" ya jinjina mata kawai.

"Dama kiran ki nake yi, na ji idan akwai wani abu da ku ke buƙata?"

"Eh, ina son yin sayayya ba mu da fitila sai ta waya, da kuma 'yan kayan buƙatu"

"To da kin sanar, ai da na saka yara sun raka ki, dama zan ce miki kuma idan an kwana biyu, yakamata ki zo a É—an zagaya da ke cikin dangi, su san kina garin nan, tun da dama ba zuwa ku ke yi ba, dui ba sanin ku aka yi ba"

Nana ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah"

"Wai ni Nana ina Mai jidda kuwa?"

"Tana can Bauchi inda take aure"

Uwani ta ce "Kuma tana zuwa?" Jiki a sanyaye Nana ta girgiza kai.

"Ai dama na san babu lallai ta zo, ko dan saboda baƙin halin Isa. Ai ya bamu mamaki. Ita ma tun da suka rabu ba ta sake zuwa garin nan ba. Kuma yakamata mu je na zagaya da ke, har inda danginta suke a nan"

Cikin mamaki ta kalli Uwani ta ce "Danginta kuma?"

"Ƙwarai da gaske, tushen Maijidda garin Buda ne. Kakanninta 'yan nan garin ne, can wajen unguwar Wanzamai, ƙarewa ma a nan garin suka haɗu da babanku. Ai kakarta aka raina a Bauchi, aka haifi babarta da ita a can.
Har an saka mata rana, suka zo garin nan, ke ma Babanki ya zo gida, suka haɗu a dandali. Aka yi ta ɗauki ba daɗi suka ƙulla soyayya. Ga shi can garinsu an saka mata rana da wani, ina ga shi ne mijinta na yanzu da take aure. Asali tun kan ta auri babanku da shi aka fara saka mata rana. Kakarta ta ce sai an warware wancan baikon ta auri babanku, ko ba komai sa din ga zuwa gida a kai kai. Haka aka mayarwa da wancan kuɗinsa ta auri babanku.
Ya Babanku ya  so ta sosai da sosai, kuma aka ƙulla auren nasu da tunanin hakan ya ƙara kawo zaman lafiya a tsakanin zuriyarmu da zuriyar wanzamai kin san a tarihin garin nan ba zaman lafiya ake ba.
Kuma dai cikin ikon Allah sun fara zamansu lafiya gwanin sha'awa, amma Allah ya ƙaddara rabuwar su."

Nana ta yi shiru tana tunanin, kamar ta san wani abu mai kama da wannan labarin da Uwani take ba ta, amma sam ta kasa tunawa. Gaba ɗaya hirar ta Uwani ta gundure ta, saboda ta san shi kansa Sayyid a takure yake, ba ya son mutane ko kaɗan, balle uwa uba dogon surutu. Ita kuwa Uwani tamkar an ƙona ta a ka ko gajiya ba ta yi. Babu wanda ya taɓa ba ta wannan labarin, sai yanzu babu wanda ya taɓa gaya mata cewar mahaifiyarsu tushenta a garin Buda yake, sai dai kamar ta san labarin da Uwanin ta bata.

"Ga wata 'yar rama na zo muku da ita, sai ku ci kafin Abincin dare ya sauka. Wai shi mijin naki kurma ne?"

"A'a ai kin ga ba shi da lafiya ne"

"Eh gaskiya ne, Allah ya ba shi lafiya, amma a ina ki ka samo Buzu haka? Ni wai anya ma labarin da Rabi ta din ga bayar wa ranar bikinki nan gaskiya ne? Abin dai da mamaki. Allah ya ba shi lafiya bari na tafi, dan Allah idan ki ka samu lokaci kya zo a je a gaggaisa.

"To in sha Allah zan zo"

"Yauwwa, zan din ga turo miki yara, idan da aike kya din ga ba su, duk 'yan uwanki ne, 'ya'yan 'yan uwa ne. Kuma ki kwantar da hankalinki duk abin da ku ke buƙata ku sanar mini, da yardar Allah ba zai gagara ba"

Nana ta ce "In sha Allah, mun gode sosai da sosai"

"Ba komai, ki yi haƙuri ki riƙe mijinki ki kula da shi, sai ki ga kaf ayyukan ki, Allah bai karɓa ba, silar wannan jinyar ta sa ki shiga aljanna, a yi ta haƙuri yayata"

Nana ta tashi ta raka ta, ta ce "In sha Allah"

Ta yi ƙasa da murya ta cewa Nana "Dan ubanki, ki din ga ɓoye mijinki, kar ki bari 'yan mata su din ga zuwa su na kallon sa." Uwani ita iya rage muryarta kenan, amma Sayyid na jin ta. Nana ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, ya yi murmushi yana sunkuyar da kai.

*****

Alhaji Fatuhu, farin cikinsa ya kasa ɓuya, duk da halin rashin lafiya da yake ciki, idan aka zo duba shi, sai ya yashe haƙoransa da sukaɗai suka rage farare a jikinsa.
Alhaji Zailani ya ƙura wa jaririn ido, ya kalli Alhaji Fatuhu da yake ta yashe baki.

Hajiya Sa'a ta ce "Kai Fatuhu. Sai ka ce ba a taɓa yi maka haihuwa ba, ji yadda ka ke washe baki, kana fama da kan ka"

Hajiya Suwaiba ta kwaɓe baki ta ce "Abin da na gani kenan"
Chapter 10 · 0% Book details