← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 78

Sashe 30

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da dare yayi, Maijidda bacci gagarar idanunta ya yi, ta tattara Iliyasu ta watsa a gefe, addu'a kawai take yi Ubangiji Allah ya sanya Nana ta kasance cikin aminci da kwanciyar hankali.
Tana zaune a kan gado, ta yi shiru abin duniya ya ishe ta. Ji ta yi yana lalubata, wani irin baƙin ciki ya turnuƙo zuciyarta.
Ƙoƙarin janyo ta yake yi, ta buge hannunsa a fusace, saboda ko ƙaunar ganinsa ba ta son yi.
Ya ce "Mai Jidda meye haka ne wai?"

"Dan Allah ni ka rabu da ni, wallahi ko ƙaunar ganin ka ba na yi. Ni dan zatin Allah ka sake ni, gara na yi zaman 'ya'yana kawai, da na ci gaba da zama da mutumin da ba ya ƙaunata, na yi kuskure tun farko da na biye wa son zuciyarka na banzatar da 'ya'yana" Ta yi maganar tana kuka mai ƙunar zuciya.

"Maijidda da ba na sonki, ke kin san ba za ki je ki yi wani auren ki fito na aure ki ba. Ni kishinki nake yi, kuma na gaya miki tsanar da na yi wa mijinki ne ya shafi 'ya'yansa"

"Ka na ƙaunata, ina cikin wannan mawuyacin halin, da kai ne sila, za ka zo ka na naniƙata buƙatarka ce kawai a gabanka? Wallahi ba ka ƙauna ta. Kuma haƙurina ya riga ya ƙare, ka sauwwaƙe mini kawai, ni zan tafi neman 'ya ta. Allah kaɗai ya san a yaya za ta kwana a ƙasar da ba ta san kowa ba, ga tsohon ciki"
Kasancewar buƙatarsa a gabansa, ya sanya ya kwantar da murya, kamar yadda ya saba ba ya tashi kalailaye ta, da kwantar da murya sai a irin wannan lokacin.
"Wataƙila ma fa ba Niger ɗin ta tafi ba, ai ba yarinya ce ƙarama ba, na san gidan babanta ta koma, ki ke ta ɗaga hankalinki"
"Da akwai damar zama a gurin Baban nata, ka na ganin za ta zo inda nake ne? Nana ba za ta ajiye mini wannan rubutun ta koma gidan babanta ba, ni ka riga ka cuce ni" Ta yi maganar tana sauka daga kan gadon. Ya bi bayan ta yana lallaɓa ta, amma ta wuce ko saurarasa ba ta yi ba ta bar ɗakin, abin da ba ta taɓa yi masa ba a tsawon zaman su.

Baba ma abin Duniya ya dame shi, ya fito ƙofar gida yana takaicin abin da Nana ta yi, sai ga kiran Uwani.
Kamar ya share sai kuma ya ɗaga, suka gaisa Uwani ta ce "Isa kiran ka na yi na ja maka kunne, tun jiya da su Ummi suka taho nake son na kira ka na ja maka kunne, kar ka kuskura ka kira yarinyar nan ka ce za yi mata faɗa, ko ka kira uwatta ka yi musu jaraba, saboda Nana ta tafi can, ita ma mafitarta take nema, tuntuni da ka kama 'yar ka ka riƙe, babu yadda za a yi ta tafi Bauchi gurin babarta. Kuma ga halin da take ciki an nemi miji an rasa, ba a san kowa nasa ba, yarinyar nan na cikin wani hali, dan haka kar ka ce za ka yi mata faɗa tun da kai ne ummul aba'isin duk wannan lamarin. Da ka binciki dangin mutumin nan kafin ka aura mata shi, da duk haka ba ta faru ba".

"Uwani"

"Na'am"

"Nana fa ba ta Nigeria ma gaba ɗaya, mijin Babarta ya kore ta, ta rubuta wa Ummi saƙo ta tafi Niger neman mijinta"

"Me? Ta tafi Nijar ta san a inda za ta gan shi ne?"

"Oho ina san mata ma, na samu wani malami, na ba shi abin sadaka ya yi mata kiranye, gaba É—aya yarinyar nan ba ta da lissafi"

"A'a ai duk kai ka janyo, amma Nana ba ta yi dabara ba, wallahi da na san abin da zai faru kenan, da ban bari ta tafi ba"

"Sai anjima bari na koma gurin malamin na gode " ya kashe wayar dan ita kanta Uwanin haushinta yake ji.
Yana shirin yin gaba, sai ga wata mota ta tsaya a gaban Baba.
Har Baba zai wuce, sai kuma ya tsaya. Wani matashin saurayi ne ya fito Baba ya din ga yi masa kallon sani.
Matashin ya ƙaraso su ka gaisa. Matashin ya ce "Baba dama, Mamanmu ce ta aiko ni, can gidan da Nana ta yi aikin rainon yaro. To wai Hajiya ce kwana biyu suna ta kiran wayarta, ba ta shiga sam, kuma an je can gidan da suke gadi, amma ba sa nan, shi ne ta ce na zo gida na tambaya ko lafiya, ko kuma a bani lambarta da take shiga na kai mata"

Baba ya kwaɓe fuska ya ce "Kai ne ta auri Buzun yaron nan a gidanku kenan?"

"Eh ni ne Baba"

"To ai 'yan uwansa ne suka fara guduwa, ya yi ta rashin lafiya, to yanzu dai shi ma ya gudu, ta tafi can Nijar neman sa".
Yusuf ya yi sororo cikin rashin fahimta ya ce  "Ya gudu ta tafi nemansa kuma?"

"Eh kamar dai yadda ka ji na gaya maka"

Ganin kamar Baba a fusace yake, ya sanya Yusuf cewa "To shikenan Baba, Allah ya kyauta, ya bayyana su cikin aminci" Ya koma ya shiga motarsa ya tafi.

*****

Sanyin iskar sahara ce ta din ga ratsa Nana, har ta fara karkarwa saboda sanyin.
Ta É—aga kai, ta ga sararin samaniya ta yi tarwai, sai hasken farin wata da ya haska cikin saharar.
Wani irin ƙugi ta ji saharar tana yi, da alamun tasowar iska. Ta kalli gabas ta ga iskar sahara daga nesa, tana wani irin hanƙoro da alama iskar tana da ƙarfi.
Sauke Numfashin Sayyid ta din ga ji a cikin saharar. Waige-waige ta fara tana neman ina za ta gan shi.
"Sayyid, ka na ta ina ban ganka ba"

"Ma viee"

"Na'am Sayyid, ka na ina ne?"

"Za su kashe ni, dan Allah ki zo mu koma gida, na fi son rayuwata da ke, na nufi nutsuwa"

Cikin rauni ta ce "Sayyid ba na ganin ka, ka na gurin ina?"

"Husna" ta sake jin muryarsa yana ajiyar zuciya. Gadan-gadan Nana ta nufi inda ƙurar Saharar nan take tasowa, saboda daga nan take jin sautin muryarsa.
A ɗan razane ta farka, saboda taɓa ƙofar gidan da aka yi. Tana kwance a cikin duhu, ta hangi mai gidan ya fito, da alama masallaci ya tafi.
Ta tashi da ƙyar, ta buɗe kayan ta, ta ɗauki ruwa pure water, ta kama ruwa ta yi alwala. Tana jin yadda magidanta suke buɗe gidaje, su na tafiya masallaci. Ita ma ta tayar da salla.
Kusan mintuna Arba'in mai gidan ya dawo, sai da ya tsorata kasancewar gari ya fara haske. Ya ga mace tana salla a kan dadduma a cikin rilar gidan. Nana ta ɗaga kai ta kalle shi, ta mayar ta sunkuyar ta ci gaba da tasbihi. Sai dai duk iya ƙoƙarinsa a kan ya yi mata magana, ya kasa kamar an saka masa sakata a bakinsa.
Ya lallaɓa ya buɗe ƙofa ya shiga gidansa, ya tarar da matarsa tana bacci, kasancewar Al'ada take yi, ba ta salla. Kamar ya tashe ta ya gaya mata batun matar da ya gani, amma ya kasa, ya haƙura ya ƙyale ta.

****
Jamila bata taɓa sanin ta damu da Nana har haka ba, duk da takun saƙa da sukan yi wasu lokutan, saboda ƙuruciya da sakunta, wasu lokutan kuma saboda zigar Mama. Amma ta damu sosai da halin da Nanan ke ciki. Jikinta ya yi sanyi sosai da sosai, da Ummi ta ba ta labarin wahalar da ta yi ta faman yi, ga miji ga laulayin ciki. Yanzu mai ɗungurungun ta tafi inda babu mataimaki sai Allah.
"Amm Jamila"
"Na'am Mummy"

"Kwana biyu na ɗaga miki ƙafa da batun Nana, saboda ki samu ki ƙara sakin jikinki, yanzu dai ki na ganin yadda al'amuran ƙungiya suke wakana, kuma na ga kin saki jikinki yanzu.
Dole fa ki yi ƙoƙari a wannan karon, ki samo mana jinin Nana, saboda ba ƙaramin alkhairi ne a tattare da taurarinta ba. Tun da dai kin ga Uba ku ka haɗa kawai da ita."
Jamila ta yi murmushi cike da takaici, amma a zahiri ta danne ta ce "To ai Nana mijinta ya ɗauke ta, ya tafi da ita can ƙasar su Nijar a can ma ina ga za ta haihu"

"What? Jamila amma ya aka yi ba ki gaya mini ba, bayan kin san ƙudurina a kanta?"

Jamila a ranta ta ce "Da yake ki ka halicce ta ba"

A zahiri ta ce "To ai ni ban san haryanzu ana buƙatar jininta ba, da na ga ba ki kuma yi mini maganarta ba, na zata shikenan ya wuce"

Kamar ta rufe Jamila da duka ta ce "Amma wallahi ba karamar shashasha ba ce, ɗaga miki ƙafa kawai na yi ki ƙara dawowa hayyacinki, aikuwa ko ki nemo Nana a samu jininta, ko kuma ƙungiya ta nemi jinin wani shaƙiƙinki, sai ki zaɓa".
Jamila ta waro ido ta ce "Shaƙiƙina kuma Mummy, na shiga uku na lalace"
"Ahh to dabara ta rage ga mai shiga rijiya ai, sai ki yi tunani, ni na haura sama zan yi bacci" Gaba É—aya jikin Jamila ya yi sanyi, ta bi bayan Hajiya Sa'a da wani irin kallo.

Har rana ta ɗaga gurin ƙarfe goma, Nana na zaune a rilar gidan nan, sai da rana ta tarar da ita, sannan ta yinƙura, ta ɗauki jakar kayanta, ta koma barandar da ke kallon gidan, ta zauna.
Mai gidan da ta kwana ya fito zai tafi kasuwa, kawai ya sake ganin Nana, da hijjabinta da wannan bagcon kayan nata ya gane ta. Ƙarasa fitowa ya yi, da niyyar ya tambayi Nana me take nema ne? Amma su na haɗa ido da Nana ya kawar da kansa cikin sauri, saboda wata irin mummunar faɗuwar gaba da ta ziyarce shi.
Sum-sum ya wuce ya tafi, ba tare da ya ce wa Nana komai ba.
Rana ta fara zafi, ta sake ɗaukar jakarta ta yi gaba, ta din ga nanata lahaula wa la ƙuwwata illa billah. Hasbunallahu wa ni'imal wakil.

*****
Alhaji Zailani yana zaune a falo, tare da Hajiya Amina, Yusuf ya shigo falon.
Hajiya Amina ta kalle shi ta ce "Yusufa daga ina?"
"Aiken ki na je Mami"
Chapter 30 · 0% Book details