← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 78

Sashe 47

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɓangaren su  Shukura cikin jikinta ya tsufa sosai, sai dai a wannan karon ta dage fafur ta ƙi yin awo a Asibitin su Doctor Sharif.
Gefe Sagir ya jewa mahaifiyarsa, da maganar son dawo da Yusra, amma ta ce ba ta lamunta ba, ba ta buƙatar ya sake rayuwa da Yusra, gara yaje ya auro wata can daban, amma ba Yusra ba.
Gaba ɗaya ya shiga damuwa, saboda mugun sabo da shaƙuwar da ya kuma yi da Yusra.
Ita ma Hajiya Halima tun da ta samu labarin, Sagir ne tsohon mijin Yusra yake zuwa gurinta, ta din ga bala'i ta ce ko shi ne autan maza, Yusra ba za ta koma hannunsa ba, balle a sake ci mata mutunci a sako ta. Ga shi daga shi har ita su na son junansu. Dan haka ya yanke shawarar tafiya gurin ƙanin mahaifinsa ya yi masa magana.
Shi kuma ya kira Hajiya Halima ya din ga yi mata faÉ—an dan me za ta hana shi mayar da matarsa alhalin sulhu alkhairi ne, wancan karon da auren ya mutu ma, gutsuri tsomarsu ce ta kashe Auren.
Mussaman ta kira Sagir gida, ds ya je ya same ta, ta dirarar masa da bala'i.
"Wato ƙarata ka je ka kai wa ƙanin ubanka saboda mace ko Sagir?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a Hajiya ba ƙararki na kai ba"

"Rufen baki ko na make ka, ba ƙarata ka kai ba ya kira ni yana faɗa? Tun da abin da ka zaɓa kenan, ka je ka yi duk abin da ka ga dama"
Kalaman na Hajiya, tamkar É—sure shi ne da jijiyoyin jikinsa, gaba É—aya ya rasa abin da yake yi masa daÉ—i ba ya son ya yi abin da daga baya zai zo yana dana sani, saboda rashin amincewar Hajiyarsa.

****
Daren yau sam Nana ba ta samu isasshen bacci ba, da yake sai washegari aka ce za ta fara aikin, ba ta yi aikin komai ba ranar.
Raba dare ta yi tana nafilfili addu'oi, saboda a jikinta tana jin wani abu game da gurin, wanda ta kasa tantance ko mene ne.
Washegari da safe, suka shirya ita da 'yan É—akinsu, suka tafi gurin aikin Abincin.
Kayan girki ne ga su nan a zube, kamar abin banza, yanayin yadda aka jibge kayan a gurin, Nana ta sha jinin jikinta, ta san aiki ne tuƙuru za a yi shi gurin.
Aka ba su jadawalin abinccicikan da za a girka a ranar, Nana ta san wasu, wasu kuma ba ta san su ba.
Su na nan tsaye shugabar ɓangaren na ƙara yi wa Nana bayani, da gurɓatacciyar hausarta, sai ga mutumin jiya shigo.
Gaba ɗaya suka wani ruɗe, masu gyara tsayuwa na yi, masu kama aiki suna yi, Nana dai ta ƙame a gurin da take. Ba yabo ba fallasa ya din ga amsa gaisuwar da ake yi masa, sai da ya zo kan Nana ya saki murmushi ya ce "Baƙuwarmu, ya ki ka ga gurin namu, ba dai wata matsala ko?"
Nana ta girgiza kai ta ce "Babu matsala"

Ya ce "Yauwwa, ki saki jiki ki yi aikinki da mu, kamar kina Nigeria, duk abin da ba ki gane ba, ga shugabar sashin nan, idan kuma ba haka ba ni ki zo ki same ni ki yi mini magana"
Ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah, na gode sosai da sosai"

Ya kalli matar ya ce "Dan Allah kar a ce za a sakar mata aiki lokaci É—aya, a koya mata abin da ta sani ba a hankali, kafin a sakar mata aiki"

Matar ta risuna ta ce "In sha Allah, amma za a yi mata gwajin ne ita ma?"

"Kin ji na ambaci hakan ne, a maganata?"

Ta girgiza kai ta ce "Tuba nake"

Ya ce "'Yar Nigeria, a yi aiki lafiya"

"Na gode sosai" Nana ta yi maganar cikin girmamawa. Ya wuce ya fita. Bayan ya fita suka juya yare, suka É—an yi maganganu, sai dai duk da Nana ba ta jin yaren nasu, ta san gulmarta suke yi. Suna aiki amma gaba É—aya hankalin Nana ba a kan aikin yake ba, yana kan halin da Sabir yake ciki. Tana ta tunani yaya yake? Yana rigima ko kuwa bai damu ba ya kwantar hankalinsa, haka ta yi ta wasi-wasi a zuciyarta.

*****
Hajiya Amina ce ta yi shirin tafiya Umara, ta tsaya a Egypt za ta kwana biyu, ta tsaya a ɗan binciki lafiyarta. Sai dai ta din ga ji a ranta, yakamata a ƙara bincika mata matsalarta ta rashin haihuwa, mussaman da take tuna maganganun Nana. Sai dai gefe guda tana tuna yadda Alhaji Zailani yake gargaɗinta a kan shi ya fauwwala wa Allah, bai damu lallai sai ta haihu ba, tun da an nemi magani ba a dace ba.
Sai dai a wannan karon, ta sake jin tana son jarraba da bibiyar lafiyarta, da ganin likita, ko za a dace, tun da ba ta daina al'ada ba ma.
Da harshen turanci suka tattauna da Likitan, ta yi masa bayani, ya rubuta mata gwaje-gwaje ya ce ta je ta yi, ciki har da hoto.
Kasancewar komai na su ba kamar na ƙasarmu ba, cikin ƙanƙanin lokaci aka yi duk gwaje-gwajen, aka tura wa Likitan sakamakon.
Bayan ta koma gurin Likitan ya duba na'ura mai ƙwaƙwalwarsa, ya kalli Hajiya Halima ya ce mata "Sakamakon hoton da aka yi mata, ya nuna babu mahaifa a jikinta gaba ɗaya" wata irin ƙara cikinta yayi, zuciyarta ta buga a jejjere da ƙarfin gaske, sai ta hau kame-kame tana tunanin, ko kunnuwanta ba su ji daidai ba? Ko kuma turancin nata ne ya ƙwace.

Cikin rawar murya ta ce "Ka tabattar da abin da ka gaya mini, ko kuma nice ban fahimta ba?"

Ya ce "Na tabattar, shi ne sakamakon gwajin da aka turo mini, amma idan ba ki yadda da sakamakon ba, kina iya zuwa wani Asibitin a sake duba ki!.

Yammm ta ji kanta yana yi, ta daina gane komai, hankalinta ya rarrabu kashi-kashi, tana son yi wa likitan tarin tambayoyi amma kanta ya kulle.
Shin da gaske ana iya samun mace babu mahaifa, ko kuma wani abin ne daban? Ya aka yi duk tsawon lokacin da ta ɗauka tana bulayin neman haihuwa ba a taɓa gaya mata ba ta da mahaifa ba sai yanzu?.

Gaba É—aya Hajiya Amina, ta rasa kalmomin da za ta tattaro ta sake furta wani abu. Jikinta rawa kawai yake yi, wani irin gumi yana tsatstsafowa ta kowace kafa ta gashin jikinta.
Likitan ya ci gaba da yi mata bayani, amma ta kasa fahimta.
Ba ta san ma da ya aka yi ta bar Asibitin ba, ta koma masaukinta saboda tsabar É—imuwa. Ta kuma rasa wa za ta kira ta sanarwa wannan maganar.
Gaba ɗaya kanta ya juye, dan ba ta ma iya tuna yadda su ka ƙarƙare da Likitan ba.
Tana so ta zubar da hawaye, ta ji sanyi a ranta, amma abu ya gagara idanunta suka bushe zuciyarta ta yi nauyi. Babbar tambayarta ita ce, dama ana iya samun macen da ba ta da mahaifa? Ko kuwa ta ta ce ta yi ɓatan dabo?. Tambayar da ta rasa wa za ta yi wa, balle a ba ta amsa.

*****

Nana kuwa gurin nan aiki ake yi tamkar babu gobe, duk da ba ta da son jiki, amma aikin yana da yawa ga babu isasshen hutu, sai aikin É—orawa da saukewa.
Ga shi ta kasa sakin jiki da ma'aikatan gurin, saboda yadda suke tsangwamarta, da nuna mata ƙabilanci, saboda ita ba 'yar ƙasar su ba ce ba. Sam ba sa gaban Nana, duk da tana ɗan saka ido ta ga, ko akwai wata mai hankali da za ta ji ta yarda da ita, a kaikaice ta ɗan fara ƙwanƙwasa cigiyar Sayyid. Sai dai gaba ɗaya ba su yi mata ba ma'aikatan gurin, gaba ɗaya ba ta ji ta aminta da ko mutum ɗaya daga cikin su ba.
Kullum da safe Al hussain, mutumin da ya É—auke ta aiki, sai ya zagaya su ya ga yadda suke gudanar da aikin safe da yamma.
Da ya zo ma'aikatan suke nutsuwa, kowa ce ta kame kanta, marasa kamun kai kuma su fara É—an karairaya. Shi kuma ya tsuke fuska yana basarwa. Sai dai da ya ga Nana sai ya saki fuska, ko ba ta kula shi ba, shi sai ya yi mata magana.

"'yar Nigeria ya alƙawarinmu ne?"

Nana ta É—an saki fuska ta ce "Wanne?"

"Au har kin manta?"

Ta yi murmushi ta ce "Duk lokacin da ka shirya, sai mu fara"

Ya ce "Kin san akwai wani abokina, sonake kafin na haÉ—u da shi, ko gaisuwa na iya da turanci, saboda ya iya turanci ni ban iya ba, ya juya yare ya yi ta magana ba na gane me yake cewa, to kin ga yakamata na ba shi mamaki nima"

Nana ta ce "Gaskiya ne, shi ma Buzu ne kamar ka?"

Al Hussain ya ce "Ya aka yi ki ka san ni Buzu ne?"

"Ga rawani nan ka na yi" ya yi dariya ya ce "Kash, to shikenan tun da kin gane, shi ma buzu ne, mun kwana biyu ma bamu haÉ—u ba, ban je Agadez ba"

"Duk Buzaye a Agadez ku ke?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a, sai dai mun fi yawa a can, ko kina son zuwa ne? Mu na da wani gurin Abincin ma a can, babban wannan sai a mayar da ke can" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a tamabaya dai kawai na yi"

Ya jinjina kan ya ce "To yaya aikin?"

"Alhamdillah"

"To ma sha Allah, Allah ya taimaka"

Tun da suka fara hirar nan, Nana ta lura da irin kallon da ake yi mata, saboda ya tsaya sun yi hira. Sai dai ita ba kallon ne ya dame ta ba, a jikinta take jin sam ba ta kyauta ba, tsayawa da ta yi tana magana da Al Hussain har take yi masa murmushi ba, saboda ta san da Sayyid yana gurin, ko da makamancin wasa ba za ta taɓa aikata hakan ba, saboda yadda yake tsananin kishinta.
A hankali ta ce "Ka yi haƙuri Sayyid, babu yadda na iya ne, duk a ƙoƙarina na son zuwa gare ka ne, ka yi mini afuwa" ta furta a hankali kamar mai raɗa.
Chapter 47 · 0% Book details