← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 78

Sashe 68

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayar Safiyya da ke aljihunta ce ta fara ringing, ta ciro ta sai ta ga Jamila ce take kiran wayar.
Ta kalli Hajiya Sa'a da ke zunduma ihu sannan ta É—aga.

"Na san zuwa yanzu Hajiya tana cikin mawuyacin hali. Ba za ta iya ɗaga waya ba, amma ina taya mu jaje da ni da ita, Abba ya zama sadaukarwarmu na shekara da ni da ita. Ina fatan zuwa yanzu ta ji abin da ake ji, a duk lokacin da ta bayar da jinin wani ga ƙungiya, ina fatan Allah ya gafarta wa Abba sadaukarwar da ya yi, ya ceci masoyiyyarsa da kuma tseratar da ɗan ƙanin mahaifiyarsa, kuma Abba bai mutu ba, sai da ya san abin da muke aikatawa. Sannan ina taya mu murna, ina ɗauke da cikin Abba a jikina. Ba zan gushe ba ina yi wa Abba a addu'a, da yi masa fatan rahama. Abba mutumin kirki ne, kuma rayayye da ya fita daga cikin matacciya Allah ya sa ya huta"

75

Jamila ta katse wayarta, wani irin kuka ya ƙwace mata, ta din ga wani irin kuka mai gunji.

Mama ce ta faÉ—o É—akin cikin damuwa ta kalli Jamila, ta ce "Jamila lafiya kuwa, nake jin kukanki tun daga tsakar gida?"

Jamila ta yi shiru tana ci gaba da gunjin kuka.

Cikin damuwa Mama ta ce "Jamila, ni fa na kasa gane miki a 'yan kwanakin nan, wai mene ne yake damunki ne? Gaba É—aya ba ki da sukuni, ga koke-koke ko Hajiyar ce ta kore ki ne?"

Ta girgiza mata kai alamar a'a.

"To mene ne?"

"Dan Allah ki ƙyale ni na ji da abin da ya dame ni, Wayyo Allahna"

Duk yadda Mama ta kaɗa ta raya, ta yi rarrashin amma fafur Jamila ta ƙi magana, taƙi gaya mata halin da take ciki, haka ta gaji ta bar ta a ɗakin.
Tana fita Jamila ta ƙara rushewa da kuka, wani irin zafi take ji a ƙirjinta, soyayyar Abba ta din ga ji sabuwa fil a cikin ranta, ba ta taɓa tunanin al'amura za su kasance kamar yadda suka kasance a yanzu ba. Ji take tamkar ta kashe kanta ta huta, ko ita ma tattara ta shiga uwa duniya kamar yadda yayarta Nana ta yi.

*****

"Imam Asad, haba ba kar manta sunan naka, kai jarumi ne, ina mai tabbatar maka da cewa Hammad ba zai zama Sultan a Agadez ba, duk wannan abubuwan da Sultan yake yi da rawar ƙafar da yake yi, mun san abin da yake nufi, dan mun san inda baki ya karkata ta nan yawu yake zuba. Amma Hammad akwai abubuwan da ya rasa, da ƙa'idojin da bai cika ba, dan haka burin Sultan na Hammad ya maye gurbinsa ba zai taɓa yiwuwa ba har abada"

Imam Asad ya gyara zamansa, fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Anya kuwa? Duk abin da Sultan yake so, dole shi muƙarrabansa za su yi su mara masa baya, ina jin tsoron ya furta Hammad ya maye gurbinsa, muddin ya furta ko yana raye ko ba ya raye, sai an zartar da shi, sai dai idan Hammad ne ya bar Duniya"

Mutumin ya ce "Kar ka yi la'akari da haka, ko me zai ɗauke mu zamu aikata, ko mene ne, babu wanda zai gaji Sultan sai Imam Asadullahi Jalal, dan haka ka ci gaba da ƙoƙari, burinmu dole ne ya cika"

Imam Asad ya jinjina kai cike da gamsuwa.

*****

Cikin damuwa Sagir yake kallon agogon hannunsa, yana sake kiran lambar Shukura, ƙarfe biyar da rabi na yamma amma shiru ba ta dawo ba.

Duk da Yusra sai da suka yi rigima da shi, a kan yadda ya tafi ya bar ta É—azu, sai dai ta damu ganin fuskarsa babu walwala yana ta kallon waya.

"Baby wai wa ka ke ta kira haka ne?"

"Shukura nake kira, ta ce mini 9zata daÉ—e ba, tun safe da ta fita haryanzu ba ta dawo ba"

Yusra ta basar ba ta kuma cewa komai ba, sai dai abin ita ma sai ta ji hankalinta ya tashi, ganin har ya fita masallaci sallar magariba Shukura ba ta dawo ba.
Yana dawowa ya dubi Yusar ya ce "Ba ta dawo ba ko?"

"Eh ba ta dawo ba, ko ta biya wani gurin ne?"

Jiki a sanyaye ya ce "Ba na tunanin hakan, ko za ta biya wani gurin, duk faÉ—an da muka yi tana gaya mini, ba ma ta da yawan yawo, ba ta fiye son fita ba, idan ba gidansu za ta je ba. Bari na je gidansu, na kuma je Asibitin na ji"

"To Allah ya sa tana lafiya, to ko haihuwa ta yi a Asibitin suka riƙe ta, na ga cikin nata ma sha Allah ya tsufa sosai"

Ya girgiza kai ya ce "Da haihuwa za ta yi, da tuni an kira ni an sanar mini, bari na je na gani"

Yusra ta ce "To Allah ya sa tana nan lafiya dai"

Ya amsa da Amin, ya fita.

Gaba É—aya sai Yusra ta ji hankalinta ya tashi.

Gidansu ya fara zuwa, ya shiga suka gaisa da Hajiya Amina, sai dai bai ga alamar Shukura ta je gidan ba, ya wayance da nufin zai tafi da Haidar, amma Haidar ɗin ya ƙi bin sa.
Hankali a tashe ya tafi Asibitin doctor Sabo, aka ce masa tun safe ta je awo, sha É—aya da rabi kuma ta bar Asibitin, kamar yadda har a cc camera ya nuna.

Nan hankalin Sagir ya dunguzuma, ya ƙara ruɗewa ya burkice, duk inda yake tunanin Shukura za ta je, ya je bai same ta ba. Wayoyinta da su na shiga, amma suka daina.
Ya tafi gurin 'yan sanda ya kai report ɗin ɓatan Shukura, bai koma gida ba sai sha biyun dare.

Yusra na ganinsa ta tashi tana tambayarsa "Yaya an ganta?"

Jiki a sanyaye ya girgiza mata, take gabanta ya faÉ—i ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa ba saboda ka dawo da ni ne ta tafi ba, Ubangiji Allah ya sa ta dawo, ni zan iya tafiya ma na bar muku gidan, idan zamana ne ba ta so ta bar gidan"

"Shukura ba za ta bar gidan nan saboda na dawo da ke ba. Dan kan ta fita mun yi magana ta fahimta da ita, mun daÉ—e mu na magana, ba saboda ke ne ta bar gidan nan ba"

Gaba ɗaya Sagir ya kasa rintsawa, sai damuwa da tashin hankali, haka ita ma Yusra, ƙarshe ma kuka ta saka tana cewa saboda ita ne Shukura ta fita ba ta dawo ba.

*****

Yau da Nana ta bushi iska, harabar gidan ta fita tana zagayawa, sai dai zuciyarta a cunkushe take, gaba É—aya tunaninta yana kan Muhsin, kewar É—anta take yi sosai da sosai, ga wannan azzalumar matar ta hana ta tafiya, sai dai ita kanta hankalinta ya rabu kashi-kashi ne, ga tunanin Muhsin ga kuma Sayyid da take ganin samu a lokaci guda take ganin rashi.

Sai a yau ta ƙara tabattar da girma da ƙasaitar gidan, ba ta taɓa ganin raƙumi da ake faɗa ba, sai yau a cikin gidan.
Ban da dawakai, da wasu dabbobin ma da ba ta san sunansu ba, ba kuma ta taɓa ganinsu ba.
Asal ta hango hannunta a cikin na Sayyid, an fito da wata danƙareriyar mota, sun shiga an ja sun fice. Nana ta tsaya ta yi shiru cikin damuwa.

Cikin matuƙar farin ciki dattijuwar matar fara ƙal, ta miƙe ta rungume Imam Hammad.
Cikin girmamawa ya durƙusa zai gaishe ta, amma ta hana shi ta ce "Ai ni yakamata na kwashi gaisuwa shugabana. Ina ta yi wa Sultan ciwon bakin ban gan ka ba, ya ce a bari ka huta kar wanda ya je gida aka dame ka, har sai ka fito dan kan ka"

Ya yi murmushi ya ce "Na same ku lafiya?"

Ta ce "Alhamdillah, sannu Imam Hammad, an sha jinya Ubangiji Allah ya sanya kaffara"

Asal ta ce "Wai ni ba za ki yi mini sanun ba, kin maze kamar ba ki ganni ba"

Matar ta ce "Wa yake ta taki, ga mara lafiya"

Gimbiya Bilkisu ta yi musu kyakykywar tarba, aka karrama su da Abinci kala-kala, amma ya ƙi ci. Hirar ma idan ta yi sai dai ya yi murmushi kawai, bai fiye tofawa ba.

Bayan sun gama da sashen Gimbiya, suka nufi sashen Sultan.

Imam Hammad na shiga falon Sultan, Sultan ya miƙe cikin farin ciki fuskarsa ɗauke da murmushi.

Abdou ma murmushin ya saki, cikin girmamawa suka gaisa.

Imam Nuradden, da Imam Asad duk su na tare da Sultan.
Cikin girmamawa suka gaida Hammad, fuskarsa É—auke da murmushi ya amsa musu.

Sun taɓa hira kafin Sultan ya ce "Imam Hammad, zo muje ka raka ni tattaki mana, na miƙe ƙafafuwana"

Imam Asad ya ce "Sultan, mu ma mu yi maka rakiyar ne?"

"A'a ku da kullum muna tare ga baƙona da muka yi shekaru ba ma tare"

Yayi maganar yana riƙe hannun Hammad, suka fita ta wata ƙofa. Imam ya din ga kallon gidan tamkar baƙonsa, kamar ba a ciki yake rayuwa ba a baya.

"Hammad"

"Na'am Abi"

"Kamar wani abu yana damunka, ka gaya mini mene ne"

Imam ya yi murmushi ya ce "Babu abin da yake damuna, idan ma akwai ban san mene ne ba"

Sultan ya ƙara tattara hankalinsa a kan Hammad ya ce "Ka tabattar? ba ka fa da wanda zaka gaya wa dauwarka idan ba ni ba, ka daina wannan zurfin cikin Imam ba na so ka gaya mini"
"Babu abin da yake damun Hammad É—inka fa"

Sultan ya yi murmushi yana dafa kafaÉ—ar Hammad.
"Ka san haryanzu miskilin ɗan yaron nan, mai guje-guje a harabar nan nake gani, ya yi guje-gujensa ya faɗi ya ji ciwo, ya zo ya yi ta yi wa Abinsa kuka, ya ce sai na ce ciwon ya daina yi masa zafi, kuma na daki rama masa na daki ƙasar na rama masa"
Hammad ya yi dariya sai da haƙoransa suka bayyana ya ce "Duk da wannan gemun na fuskata haryanzu wannan ɗan yaron naka ka ke gani?"

"Eh mana, gani nake kamar jiya Sarah ta haifa mini kai. Allah ya jaddada rahama ga Umminka"

Ya amsa da Amin cikin sanyin jiki.
Chapter 68 · 0% Book details