Sashe 71
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙwarewa Mahmud ya yi, Hammad ya miƙa masa ruwa yana yi masa sannu, ya yi shiru ya ce "Daga Nigeria kuma?"
"Eh"
"Lallai Imam ka na da rigima, amma duk Nijar sai da aka tsallaka Nigeria aka samo ta?"
Ya É—an É—age kafaÉ—a ya ce "Ka san rigimar Asal, wai a gurin cin abincin MaraÉ—i ta gano ta, ta kawo ta nan. Zan saka ta yi girki ka zo ka ci"
Mahmoud ya jinjina kai, daga bisani ya kawar da zancen, yana ci gaba da lissafa yadda za je Nigeria ya taho da Nana, dan ya san tun da Hammad ya dawo, yanzu duk inda za shi su na tare.
Da ƙwarin gwiwa yanzu Nana take girki, kasancewar ta sa wanda take yi wa girkin.
Bayan da Nana ta kammala girkin rana tana shirin, kai wa sashen Imam, Asal ta same ta ta ce "Ba sai kin kai wa Imam Abinci ba, baya nan sai dare zai dawo, ki shirya masa abincin dare kawai"
Nana ta amsa mata da to.
Tun da Imam ya dawo, yake kaiwa yana komowa yana jiran ya ga ta ina za a kawo Abinci, saboda yunwar da yake ji. Ga shi dududu ƙarfe goma ya dawo, amma Asal har ta kwanta bacci. Ya yi hamma bai san adadinta ba, saboda yunwar da yake ji.
Sallamar Nana ta saka ya kalli hanyar shigowa, wannan karon a kwando ta zubo kayan Abincin.
Sai dai yau saɓanin hijjabi, doguwar riga ce a jikinta milk, da mayafin rigar. Tun da ta yi sallama ya amsa a ƙasan maƙoshinsa ya sunkuyar da kansa ƙasa bai kuma magana ba.
Ta ƙarasa ta ajiye kwamdon, ta sauke kwanukan, har za ta yi masa zancen saƙon nan da aka bayar, sai ta fasa dan kar ta wargaza shirinta. Da wani na iya ganin halin da zuciyar wani ke ciki, da Imam ya daɗe da jin kunya, saboda bugun zuciyarsa, ga wani irin azalzalarsa da take yi, ya sake kallon Nana, dan ba ya tunanin ya taɓa ganin wanda doguwar riga ta yi kyau kamar baƙar kukunsa 'yar Nigeria.
Ta zuzzuba masa abincin, ga kayan marmari ga kuma shayi na musamman.
Da ta zuzzuba masa.
Ta numfasa ta ce "ÆŠazu na yi girkin rana, aka sanar mini da baka nan, na ce duk lokacin da ba zaka kasance a gida ba, ina son a yi mini izini na dafa maka ka fita da shi, ba zan so shugabana ya kasance da yunwa ba, tun da alhakina ne girka maka Abinci" Ta yi maganar cikin girmamawa tana sunkuyar da kai.
Jin ya yi shiru ya sanya ta ɗaga kanta, ta ga tuni ya ɗauki shayi ya kai bakinsa yana sha. Kawai ta ɗan juya ƙwayar idonta, tare da yin murmushi. Sai da ya kusa ƙwarewa, saboda tabbas ya san irin wannan kallon, amma a ina? Yana matuƙar son ya yi mata magana, amma ba ya iya wa. Nana ba ta ba shi damar ɗaukar wani mataki ba, ta tashi ta nufi hanyar fita. Tun da ta tashi ya bi ta da ido har ta fice.
Abin duniya duk ya dame shi, Nana kuwa ta cika da murna, ganin saƙonninta na isa yadda take so, sai dai tana buƙatar ƙara samun kusanci da shi.
Cikin marairaicewa yake kallonta, fuskarsa É—auke da damuwa ganin yadda take kuka tamkar ranta zai fita, ga shi ta yi duhu ta rame, ba kamar yadda ya santa ba a baya.
"Ma vie, ki yi mini afuwa, ba laifina ba ne, ina jin yadda ruhinki yake motsi a cikin jikina, dan Allah kar ki yi fushi da ni ki yi mini uzuri " Ya yi maganar yana ƙoƙarin rungume ta ya rarrashe ta. Ja da baya ta yi tana girgiza masa kai tana kuka ta ce "Ba ka so na Sayyid, ka yada alƙawari ka tafi ka bar ni, ka manta da ni, ka bar ni da dakon ruhinka, da ya hanani sukuni sai da na fito nemanka, ba ka yi mini adalci ba Sayyid"
"Ma vie, ban ya da alƙawari ba, gangar jikina ce a Nijar, amma ruhina yana Nigeria dan Allah ma vie"
Asal ta yi ƙuri da ido tana kallon yadda ya haɗa gumi a cikin bacci, sai numfarfashi yake yi da kyar yana faɗin "Ma vie, ke rayuwata ce, ban yi miki butulci ba"
AYSHERCOOL
1K NE VIA 0069685771
Aisha Adam stanbic bank
08081012143
76
Asal ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah.
Shiru ta yi jikinta ya yi sanyi tana kallonsa, sai dai ta yi shiru ta ci gaba da kallonsa. A razane ya farka, sai dai ya juya ya ci gaba da baccinsa.
Da safe ya lura da Asal ba ta walwala, ta ƙi sakin jiki da shi ma gaba ɗaya.
Har ya share ta sai kuma ya tambaye ta ko lafiya?
"Lafiya kalau" ta amsa masa a taƙaice.
Ya fita É—an tattaki, yana jin mafarkin da ya yi a jikinsa, amma ya kasa tuna mafarkin abin da ya yi. Cikin girmamawa ma'aikatan ke ta risunawa su na gaishe shi.
Babu yabo babu fallasa ya din ga amsa musu. Zuwa ƙarfe goma Nana ta kammala girki. Sai dai yau ba su haɗu ba kwata-kwata.
Har lumshe idanunsa yake yi bayan da ya sha kunun gyaɗar da ta yi, ga lafiyayyen ƙosai mai zafi.
Ya karya tsaf ya gama, Asal ta fito daga ɗaki ta cika ta batse. Kallo ɗaya ya yi mata ya maze, ganin ya basar da ita ya sanya ta ƙura masa ido ya kalle ta, yana mamakin dalilin da ya sanya ta ke yi masa wannan kallon.
"Imam ina fatan inda ka tafi, ba cin amanata ka yi ba"
Kallon rashin fahimta ya yi mata ya ce "Me ki ke nufi?"
"Ni kaina ban kai ga tantance abin da nake nufi ba, amma na fara ganin wasu abubuwa me da ban gane musu ba, abin ya tsaro ta ni ne"
Ya ce "Yi mini bayani"
"Ka na kiran wata da rayuwarka a cikin baccinka"
Ya yi mata ƙuri da ido, sannan ya ce "Kin tabattaa?"
"Ba ka yarda ba ƙarya nake yi maka kenan?"
"A'a ban ce haka ba, amma kin ce bacci nake yi, kin ga mai bacci kuma bai san abin da yake aikatawa ba. Wataƙila shirmen mafarki ne kawai, wataƙila ma ke na gani a cikin baccin nake kira da rayuwata"
Sai kuma ta yi murmushi ta ce "Kuma haka ne, wallahi har na ji zuciyata ta yi sanyi, ka yi haƙuri da abin da na yi "
Ya yi murmushi yana kashingiɗa ya ce "Ban haƙura ba tukuna"
Ta ce "Ai ba zan sake ba, ina kishinka ne sosai. Da ina da hali ko fita sai ka daina yi. Ina sane da duk masu ƙoƙarin yi maka kyautar 'ya'aynsu su na so ka aura. Imam kai nawa ne nikaɗai Imam Hammad, babu wata mace da za ta iya samun kafar da za ta shiga zuciyarka. Inda na gode wa Allah, ka yi daban Imam, ba ka da rawar kai, da kule-kulen nan, da ko a cikin barorin nan, da suke rawar ƙafa ka yi saɗaka da su, sai ka saurare su. Shi yasa nake ƙara ƙoƙarin na kare gidana ina fatan ba ka ga laifina ba"
Ya sanya hannunsa yana shafa gashin kanta, ya ƙanƙance idanunsa yana kallonta, daga bisani ya saki murmushi ya ce "Gimbiya Asal, sarauniyar mata masu kishi ta duk faɗin Agadez"
Ta zumɓura baki ta ce "Ta duk Duniya dai, ni in dai a kan ka ne. Da ina da yadda zan yi ma sai ka daina kallon kowace mace, sai maza kawai" Ta yi maganar har cikin zuciyarta.
Kawai ya kama dariya, dan shi gaba É—aya dariya ma ta ba shi.
"Ya ka ke dariya kuma?"
Hammad ya ce "To ya ba zan yi dariya ba, ina ji ina gani an bani kyautar mata na mayar da hannun kyauta"
Fuskarta É—auke da damuwa ta ce "Dama ka na so kenan?"
"To waye ba ya son mace? Ina so mana. Amma tawa kawai"
"So ka ke sai ka saka ni kuka" Ta yi maganar idanunta na cika da hawaye.
Lumshe idanunsa ya yi yana buɗewa, yana kallonta. "Ga abinci ki karya" Ta noƙe kafaɗa.
Nana ce ta yi sallama, Asal ta kalli inda ta shigo, ta tsuke fuska haka kurum yau ta ji haushin Nana ya ninku a zuciyarta.
Nana ta yi saurin sunkuyar da kanta, dan Asal a zaune take a kan cinyar Sayyid.
"Zan kwashe kwanuka" ta yi maganar muryarta har harÉ—ewa take yi, saboda abin da ya taso mata.
"To ni dai yanzu ka kira ni da rayuwarka a zahiri, tun da ka ce ni ka ke kira a mafarki" Ta yi maganar kamar ba ta san Nana ta shigo ba.
Ras gaban Nana ya faɗi, ya lumshe idanunsa yana murmushi ya ƙi magana.
Kawai Nana ta fusata ta tattare kwanukan za ta yi waje.
"Malama ki ajiye ban karya ba, ki fita kya dawo ki kwashe" Ko waiwayowa Nana ba ta yi ba, wata irin zabura ta yi cikin matsanancin fushi, amma ya riƙe ta ya ce "Cherie na sha gaya miki, irin wannan halayen naki ga na ƙasa da ke, babu abin da za su janyo miki sai tsana da raini. Ita kuma rayuwa a na son ko kana guzurin maƙiyi ka yi na masoyi"
"Amma Amour kana kallon abin da ta yi mini, ko sau É—aya sai na sanya a ladabtar da yarinyar nan ta san matsayina a gidan nan"
Ya ce "A'a, ke ce baki kyauta ba abin da ki ka yi. Ita ba ta tashi cikin jerin hadimanki ba, kawai dai kin É—aukko ta ta yi miki aiki ne, dan haka sai kin din ga yi mata uzuri"
"Wane uzuri ne ba na yi mata, abin da ta yi mini wulaƙanci ne tana sane, ban da yadda take kula da abincinka na aminta da ita a kan hakan, da sai na hora ta sannan na kore ta ta bar gidan nan"
"Shikenan ki yi yadda ki ke so, tun da ba zan faÉ—a ki ji ba"
Ya yi maganar yana ture ta daga jikinsa.
"Imam fushi ka yi da ni a kan wannan mummunar yarinyar?"