Sashe 11
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Zailani ya ce "A'a ku bar shi ya yi, ɗan mutum fa, kyauta ce Allah ya ba shi, da duk Duniya babu mai ba shi. Ni ba gani ba 'ya'yan duk babu sai biyu ne suka tsaya." Ya yi maganar yana zuba wa jaririn ido, yana tuna na Shukura. Tun da yake harkar ƙungiya, bai taɓa bayar da jinin da ya tsaya masa ya kasa mantawa ba, sai na Shukura. Mussaman idan yana tuna irin baƙar wahalar da ta sha.
Ya kalli Fadila, da take É—akin a zaune, ga jego tana yi, amma ta tare a Asibiti da É—anyen jaririn da ko suna ba a yi ba.
Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Wane sunan za ka saka masa?"
"Muhsin É—ina zan mayar" ya yi maganar muryarsa É—auke da rauni.
Hajiya Sa'a ta ce "Wai an din ga saka Muhsin É—in kenan?"
"Sunan mahaifin Fadila ne, shi za a mayar mu ci gaba da kiransa Muhsin, ni na yi mata alƙawari shi yasa. Na so Muhsin ɗina da ya rasu sosai da sosai. Na ji zafin rashin sa, sai dai ina tausayawa wannan Muhsin ɗin. Ya zo lokacin da mahaifinsa ba shi da komai, ba zan iya ɗaukar nauyinsa na kula da shi ba. Wataƙila ma kafin ya yi wayon sani na na rasu. Ga shi ko hakika ba zan iya yi masa ba" ya yi maganar hawaye na zubowa daga idanunsa.
"Haba Fatuhu, ya haka? Dan dai Hakikar da za ayi wa jaririn nan, ka san ba za ta gagara ba, amma ya za ka zauna kana kuka kamar ƙaramin yaro, a gaban iyalinka da 'yan uwanka hakan bai kyautu ba ai".
Alhaji Fatuhu ya ɗago idanunsa da suka yi jawur ya ce "Zailani. Ka san me nake ji kuwa? Gidaje da motocin hawa nake da, ina kyautar maƙudan kuɗaɗe ba tare da na ji komai ba, da abu ya dame ni, zan sai ticket na tafi umara. Ina da shaguna dukiya Allah ya yarje mini, bayan gwagwarmaya da na sha ta rayuwa. Astagfirillah ba ƙarar Allah nake kawowa ba, ko rashin imani da ƙaddara ba, ina jinjina girman lamarin Ubangiji, kuma ina jin babu daɗi ɗa na na cikina, ba zan iya saya masa ko wando ba"
Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka yi haƙuri. Mu na murna sauƙi yana samuwa, ga shi ka na ta magana sosai da sosai, kukan nan karya mana zuciya yake yi. Kuma da ka yi mana a baya, yanzu kuma da Allah ya kawo jarrabawa shikenan sai a yi haƙuri"
Su na nan zaune, sai ga ƙanin Baban Fadila, ya zo duba Alhaji Fatuhu ya kuma jaririn Fadila, wanda shi ne waliyyin Fadila. Sai dai shi ma ya tsorata da ganin Alhaji Fatuhu.
"Alhaji haka jiki ya zama? Subhanallah Allah ya baka lafiya"
"Amin kawu, amma jiki ya yi kyau Alhamdillah, tun da ina ta magana"
"Haka ne, amma menene takamaiman abin da aka ce ya same ka ne?"
Fadila ta ce "Haryanzu ba a gano takamaiman mene ne ba, yau a ce ƙodarsa ta kumbura, gobe a ce ko cancer ce, an yi gwaji ba ita ba ce. An yi gwajin zuciya shi ma lafiya ƙalau"
Cikin damuwa ya ce "Amma Fatuhu ana haÉ—a maka da na addini kuwa? Ka san muna da ido ne ba na ganin gari ba. Mussaman ku da ku ke shahararrun mutane da Allah ya ba wa wadata. Yakamata a yi na sihiri da shaiÉ—anu"
Alhaji Zailani ya ce "A'a ga likitoci su na kula da shi, ya za a yi a ce kuma a kawo wani abu daban? Magungunan gargajiyar nan kashe mutane suke yi ai, tun da ba auna su ake yi ba".
Alhaji Fatuhu ma ya ce "A'a ba wannan ba ne, wa ya damu da ni da zai yi mini sihiri. Larura ce kawai kuma likitoci na kula da ni"
"Kai, kalle ni da kyau. Duk bokon ka, nima É—an boko ne, kuma na san ilimin addini, amma sihiri da shaiÉ—anu gaskiya ne. Tun da aka yi Annabi Sallallahu alaihi Wasallam sihiri, duk duniya ban ga wanda ba za a yi wa ba.
Ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinye wa ai akwai alamar tambaya, ga lalacewar dukiya lokaci guda. A dai tsananta addu'a. Ya gama bambaminsa ya fita. Alhaji Zailani ya din ga ziga Alhaji Fatuhu, tare da kushe magungunan gargajiya. Ba tare da jin nauyin Fadila da take gurin ba.
Ya gama soki burutsunsa, ya tashi ya yi musu sallama, tare da cewa zai aiko da abin hakika.
Har ya kusa ƙarasa wajen motarsa, ya waiwaya ya ga Hajiya Sa'a ta nufo shi, ya tsaya ta ƙarasa.
Ya ce "Ya dai?" Ya yi maganar yana kallonta.
"Zailani"
"Na'am
"An sauke ɗan uwana daga shugabancin 'yan kasuwa an ɗora ka, ka saka an dawo da shi Asibitin nan, ƙarƙashin kulawarka, an ce a yi masa maganin gargajiya ka haƙiƙance kana kushewa.
Kar ka kuskura na tarar da sanya hannunka, a cikin wannan abubuwan da suke faruwa da É—an uwana"
Ya gyara tsayuwarsa ya yi murmushi ya ce "Babu sanya hannuna a ciki. Ina ƙoƙarin zama aboki mai halacci ne kawai.
Sannan ki daina mazewa kamar ke ɗin mai ƙaunarsa ce, bayan sadaukar da 'ya'yansa maza da ki ke yi"
"Duk da haka, munin abin da na yi bai kai wanda ka ke aikatawa ba, ka fi ni sanin kai da me da me ka sadaukar, dan haka ka kiyaye ni". Ta juya ta koma. Bin bayanta ya yi da kallo, ya ji wani abu ya tsirga masa, tabbas idan Hajiya Sa'a ta ci gaba da wannan gigin, zai É—auki matakin da ya dace a kanta."
*****
Cikin bacci, take jin hayaniya a bayan ɗakin, tamkar ana cin kasuwa. Ga wata irin sukuwa da take ji a roofing ɗakin, tamkar ta dawakai.
Tun da ta farka sai juyi take yi, bacci ya gagari idanunta, ayatul kursiyyu ce ta zo bakinta ta din ga maimaitawa, har ta samu nutsuwa daga razanin da take ciki.
Ta ruge idanunta, sai dai a maimakon ta yi bacci, sai wata irin kewar Sayyid take addabar ta. Ta rasa dallin da ya sanya, ba ya kula ta yanzu. Duk da ba shi da lafiya tana yi masa wannan uzurin, amma duk da haka da ya kan yi attempting sai ya ƙyale ta, yanzu kuma gaba ɗaya ya daina yinƙurin aikata komai ma.
Wanda da idan ya sako ta gaba, har takura take yi.
Ta tashi zaune ta gyara maganin sauro, ta taka a hankali ta ɗaga labulen ɗakin, saboda zafi. Ta dawo ta ɗauki fitilar wayarta ta kunna. Ta haska shi ta ga idanunsa a lumshe, yana bacci. Ta zuba masa ido, ta fara tunanin ko ita ce mai matsala gaya mata ne bai yi ba, ko ma sharrin Ƙaisar ne?.
Ta yi ajiyar zuciya, ta kashe fitilar, ta kwanta a gefen sa tana wasa da gashin ƙirjinsa. Zuwa na fuskarsa.
Ta sake matsawa a hankali, tana sumbatar leɓansa, tamkar mara gaskiya. Gaba ɗaya a tunaninta bacci yake yi, sai da ta ji ya sanya hannayen sa, ya zagaye ta, tare da ba ta damar sumbatar bakin nasa.
Nana za ta iya cewa, tun da Allah ya sa ta buɗi ido a duniya, ba ta taɓa jin kunya irin ta yau ba, cikin sauri ta fara ƙoƙarin rabuwa da jikinsa ta matsa, amma ya mirgina ya rungume ta gam a jikinsa yana numfashi a hankali.
Ayshercool
08081012143
56
Yana jin yadda jikinta yake tsuma, tamkar wadda aka kama tana aikata wani abin ashsha! Ko kuma wadda ake kaÉ—awa mazari.
Magana yake son yi mata, amma abu ya gagara, duk ƙoƙarin da ya yi amma abu ya ci tura.
Ya ƙara ƙanƙame ta tamkar wani zai ƙwace ta, ya din ga murza hannunta har ta fara jin zafin riƙon da ya yi mata. Yanayin ya ƙara ninka mata halin da take ciki, ta rintse idanunta.
A hankali ta ji yana hura mata iska a cikin kunnenta, tamkar yana zuba mata wani sindari, haka ta ji wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.
Ƙamshin nan ta ji yana ratsa hancinta, ta buɗe idonta a hankali, kamar yadda ta yi tsammani, a wannan ɗakin ta gan su. Ta hau waige-waige. Ta wata ƙofa ta ga ya fito, ƙugunsa ɗaure da wani abu kamar zani, ya zauna a kusa da ita yana kashe mata ido.
"Sayyid ka warke?"
"Eh mana"
"Ka daina jin duk abin da ka ke ji?" Ya jinjina kai yana murmushi. "To ka yi mini magana mana"
"Ma vieee" ya faɗa yana ɗan jan maganar yana kwanciya a gefen ta. "Har na ji daɗi da ka samu lafiya, Allah ya ɗorar maka da sauƙin nan Sayyid"
"Amin rayuwata, matso ki kwanta mu yi bacci"
Ta noƙe kafaɗa ta ce "A'a"ya saki murmushi yana kama hannunta. Duhu ne ya gauraye ɗakin. Dariya ta fara jin Sayyid ɗin yana yi mata cakulkuli. Ta kasance da shi cikin wani yanayi mai tsayawa a zukata.
Ba ta iya tantance a wani hali take, ta daina ganinta a ɗakin, sai a libraryn Ƙaisar.
Ta tsaya tana kallon gurin, tana tunanin yaushe rabon da ta zo gurin nan.
Ƙaisar ta hanga, a tsaye yana gyara litattafan sa.
"Ƙaisar ka warke kenan?"
Yayi shiru yana goge wani littafi, ya gama ya ajiye littafin sannan ya ce "Eh, na warke. Waye ya ce ki je ƙauyen nan?"
"Ban gane waye ya ce na je ba? Zan kwana a titi ne? Ga mara lafiya ina da shi"
"Gaskiya ne, bai kamata ki kwana a titi ba. Wannan dalilin ya sanya tun a farkon auren nan, na din ga haska miki matsalolin da za ki iya fuskanta, amma gani ki ke yi kamar ƙarya nake yi, to yanzu sai ki san yadda za ki yi, ki rayu da ke da wannan lanjararren mijin naki, da duk larurar duniya ta ƙare a kansa".
A ƙule Nana ta ce "Larura Allah ne ya ɗora masa, kuma kun taka muhimmiyar rawa a larurarsa. Kuma ka daina ganin laifina. Zan tsallake shi ne a wannan yanayin da yake ciki, na bar shi? Mu bil adama mu na da bambanci da ku, mu na da tausayi da kuma nuna kulawa ga waɗanda muke ƙauna"