Sashe 29
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba ya dasa faɗa, Ummi a sanyaye ta ce "Dan Allah Baba kar ka yi mata baki, wallahi idan aka nustu Nana ba ta da laifi a cikin lamarin nan. Tin fil azal fa ba bincike aka yi ba, ba a san daga ina mutumin nan yake ba, ka aura mata shi, saboda kawai ka na tunanin su na aikata ɓarna, alhalin babu cikakkiyar hujja da ta nuna hakan. Ba ta bujire maka ba ta yi biyayya, duk dan kar ta dawo gidan nan, kamar yadda ka gindaya mata cewar babu zawarci, ya sanya ta dage kai da fata, ta yi aiki tuƙuru ta jure wahala da ƙalubale take jinyar mutumin nan. Ka san Nana da gudun magana, duk tsoron abin da ka iya biyo baya ya sanya ta yanke wannan hukuncin, ka yi haƙuri a yi mata addu'a kamar yadda ta buƙata "
"Amma Ummi, Nana ko yayyanka Naman jikinta zan yi na cinye dan ba'i ba gara ta dawo mini nan ba! Dan me za ta kama hanya ta tafi Nijar? Gurin uban wa za ta je?"
Jamila ma ta ce "Tun da dai ta riga ta tafi, dan Allah ka yi haƙuri"
Baba ya rasa abin da yake yi masa daÉ—i, ya shuri takalmansa ya yi waje.
*****
Su na tafe a hanya, Nana tana addu'a, tana fatan Ubangiji Allah ya sauƙaƙa mata, ya taƙaita mata wahala. Ya haɗa ta da Sayyid cikin aminci, tare da fatan duk inda Sayyid yake, ya kasance cikin aminci. Ta maimaita Hsbunallahu wa ni'imal wakil, babu adadi, tare da tawasalli da ayoyin Alƙur'ani a kan Allah ya shiga lamarin ta, ya sauƙaƙa mata wahala.
Ƙarfe shida saura, Nana suka sauka a Maraɗi. Tun a Nigeria ta sai 'yan kayan ciye-ciye ta zuba a Jakarta.
Ta yi sallar la'asar ƙasaru, sannan ta tsaya tana ƙarewa tashar motar kallo, tana tunanin ma ta ina za ta fara. Ta ji ƙafafuwanta kamar ba a jikinta suke ba, saboda nauyi, sun kumbura sun yi suntum, saboda azabar nauyi da gajiyar tafiya. Ga ɗan cikinta ya yi jingim ko motsi ta ji ya daina yi saboda azabar wahalar tafiya, Bayanta da mararta suka ƙulle mata, saboda azabar wahala. Ga jikinta tamkar an sassara ta, saboda gajiya babu isasshen gurin miƙe ƙafa.
Masu babur na ta tambayarta ina za ta je, amma ta yi musu shiru, ta ɗauki bagcon kayanta, ta yi gaba. Tamkar ba ta jin jikinta, haka ta din ga jefa ƙafa tana tafiya. Ta yi nisa sosai da tasha, ta fara hango unguwanni da gidaje.
Duhun magariba ya rufa, ta samu wani gida kawai ta shiga. Matar na tsugune tana tuƙa tuwo Nana ta yi sallama.
Suka gaisa da Nana, matar ta tsaya tana kallon ta, ta ji abin da ya kawo ta.
Nana ta ce "Dan Allah baiwar Allah, ni baƙuwa ce, hanya ce ta biyo da ni, dan Allah salla nake son na yi, idan babu damuwa zan kama ruwa ne na yi alwala".
Matashiyar matar ta ce "To ba komai. Ga banÉ—aki nan da buta a ciki"
Nana ta ajiye kayanta, ta shiga banɗakin ta zubar da uban fitsarin da ya cika mata mara dam. Ta yi miƙa saboda gaɓoɓinta da suke yi mata ciwo.
Sannan ta yi alwala, bayan ta yi alwalar, ta tsaya ta ɗaga cikinta, tana ɗan tattaɓawa cike da damuwa, jin sa shiru bai dame ta da motsi ba.
"Haba yaron kirki, ka motsa mana ko na ji daÉ—i, haba É—an Baba. Nana na cikin damuwa dan Allah ka motsa" ta yi maganar a hankali cikin tsoro da damuwa, dan ta ji ana cewa idan É—a ba ya motsi, to mutuwa ya yi. Har ta fitar da ran É—an nan zai motsa, ta tsorata idonta ya fara cika da hawaye, kawai ta ji ya motsa a hankali, sai kuma ya ci gaba da motsawa.
Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta shafa cikin ta ce "Alhamdillah, Allah ya bayyana mana Sayyid É—inmu cikin aminci" Gaba É—aya ta manta a banÉ—aki take.
Ta fito matar ta ba ta dadduma a É—aki, ta shiga ta tayar da salla. Bayan ta idar da sallar, ta zauna a kan sallaya, ta din ga tasbihi tana gaya wa Allah damuwarta, har aka yi sallar isha'i.
Nan ma ta tayar da salla ta yi, tana cikin addu'a matar ta shigo da kwanuka, ta ajiye.
Nana ta shafa Addu'ar ta kalli matar ta ce "'yar uwa Na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi na gode ƙwarai da gaske"
"A'a babu komai, musulmi ai É—an uwan musulmi ne, ki ci abinci kafin ki tafi dan Allah"
Nana ta ce "A'a, na ƙoshi Alhamdillah, Allah ya saka da alkhairi, ya biya miki buƙatunki na alkhairi"
Matar ta ce "A'a daga gani daga tafiya ki ke, ga juna biyu, ai sai wahala, dan Allah ki ci ko kaɗan ne kafin ki tafi" Nana ta dage matar ma ta dage. Da ƙyar Nana ta amince ta ɗan ci Abincin kaɗan sai dai babu abin da take tunani, sai yadda za ta yi da gurin kwana.
Ta rufe sauran Abincin ta ce "Na gode sosai da sosai 'yar uwa, Allah ya saka da alkhairi"
Matar ta amsa da "Amin, Allah ya kiyaye hanya"
Nana ta amsa da Amin, ta É—auki jakar kayanta ta yi waje.
*****
Babar Nana wuni ta yi sukuku, gaba É—aya hankalinta a tashe, sai koke-koke take yi. Baban su Walida kuma ya yi burus da ita.
Ganin kuka da damuwa ba zai fishshe ta ba, ya sanya ta yi alwala ta hau kan sallaya, ta gabatar da salatul haja, sallar neman biyan buƙata a gurin Allah.
Ta É—aga hannayenta tana kuka, take yi wa Allah kirari da magiya.
"Allah kai ne Allah, Allah kai ne ka halicce ni ka kuma halicci Nana, ka rayata ta girma cikin ikonka da kulawarka. Ya rabbil arshil azim duk inda yarinyar nan take, Ubangiji Allah ka kai mata ɗauki, da ita da abin da yake cikinta. Allah ka kare ta daga dukkanin sharrin abin ƙi, Allah ka zama gatanta ka tsare mini ita. Ya hayyu ya ƙayyum domin kyawawan sunayenka maɗaukaka masu girma, Ubangiji Allah ka kai wa Nana ɗauki, ta inda ba ta zata ba" ko abinci ba ta iya ci ranar ba, gaba ɗaya addu'ar wunin ranar, Nana kawai take yi wa.
Can gida Baban su Nana ma, an ba shi Abincin dare, amma ya gagara ci sai uban tagumi da ya rafka. Lissafinsa kawai gidan uban wa za ta ga je a Nijar? Hannun wa za ta faÉ—a kuma a ina za ta kwana?
Nasiru kuwa tun da ya samu labari shi ma abin duniya ya dame shi, kuma ya É—ora alhakin hakan a kan mahaifin su.
Mama ta ce "Wai baban Jamila ba za ka ci Abincin ba sai ya sandare?"
"Wai wane Abinci zan iya ci? Wanan shashashar yarinyar, tana can babu uban da ya san a yaya za ta kwana? Kai Nana muguwar sokuwa ce. Kin ga É—auke Abincin nan, gurin Malamin Almajiran can zan je na gaya masa, ko kiranye ne a yi mata ta dawo gida dan ubanta".
"Kiranye kuma?"
"Eh mana, tun da dai shi mijin nata mutumin banza ne, bai san abin da ya dace ba, ya tafi ya bar ta, ai sai ta dawo gida, tun da ba ƙanin ubanta ba ne"
Jamila ta ce "Kayya! Ba na tunanin wani kiranye zai yi wa Nana tasiri, ka san tana da haƙuri amma akwai taurin kai"
"Aikuwa wannan karon, dole ya kama ta, duk gidan uban da ta tafi, sai ta dawo"
ya yi maganar a fusace ya fice fuuuuu.
Sagir yana tsaka da bacci, ya buÉ—e idonsa ya ga Shukura a zaune. "Sweetheart lafiya kuwa? Ya na gan ki a zaune?" Ji ta yi tamkar ta kifa masa mari, amma ta maze ta ce "Ba na jin daÉ—i ne"
ÆŠan rikicewa ya yi, ya tashi ya matsa kusa da ita. Da gaske jikinta da zafi.
"Ya salam, bari na duba miki pcm" ya tashi ya kunna fitila, ya kawo mata ruwa da magani. A dole ta karɓa ta sha. Ya kashe fitilar ya zauna a kusa da ita, ya riƙe hannunta yana ɗan murzawa a hankali.
"Sannu"
"Yauwwa" ta amsa a taƙaice.
"Beb anya ba wani cikin ba ne?"
"Ahha haba dai, ba wani ciki maybe malaria ce"
Sagir ya ce "Ban yadda ba, gobe in Allah ya kaimu zan kai ki Asibiti a sake duba mini ke. Ubangiji Allah ya sa cikin ne" shiru ta yi ba ta amsa masa ba, shi kum hakan bai dame shi ba. Duk haushin Sagir da take ji, yana da halayen da duk ƙiyayyarka da shi, muddin za ka yi masa adalci dole ka kira shi mutumin kirki. Yana da matuƙar tausayi, duk faɗan da za su yi, da ya ganta a yanayi na rashin lafiya, zai rikice gaba ɗaya. Haka ya lallaɓa ta ta kwanta, sai dai da ya fara bacci sai ya farka, ya taɓa goshinta da wuyanta. Ita kuma idonta biyu duk abin da yake yi tana jin sa.
****
Sai da Nana ta tabattar da sawu ya ɗauke, sannan ta ɗauki jakarta, ta koma gidan da ta shiga ta yi salla. An kulle ƙofar gidan, amma ƙofar rilar gidan a buɗe.
Ta shiga rilar, ta ciro daddumarta ta shimfiÉ—a, ta É—aukko zani a kayanta ta yi kwanciyar ta.
Har a wannan lokacin, da take shirin kwana a waje haka, ba ta ji ta yi nadamar tahowarta Nijar ba. Sai ma ji da take yi ta zo inda babu wanda ya santa, balle a din ga gudunta, a din ga ganin da ta rabu mutum sai wata masifar ta afka masa.
Ta saka hannu ta tallafo cikinta, da ita ma take jin nauyinsa, ya wuce adadin watannin da take tunani.
Tana jin yadda yake motsi, wanda motsin nasa kaÉ—ai, wani irin farinciki da nishaÉ—i yake sanya ta.
Sai kuma damuwa ta biyo bayan farincikin nata, bayan da ta tuno Sayyid, da kuma rashin sanin halin da yake ciki. Da haka bacci nannauya ya yi awon gaba da ita a gurin.