Sashe 43
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dan Allah yaron kirki ka yi haƙuri ka sha, ba zan sake dukan ka ba, dan Allah ka sha ba ka isa yaye ba" Nana ta yi maganar cikin damuwa.
Nene ta kwashe da dariya, ta ce "Kin ga ki ƙyale yaron nan, ina ga fa ya yi zuciya ya yaye kansa, sai dai yi haƙuri"
Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas sai ya yaye kansa? Ya yi wuri ai"
"To ba ke ki ka janyo koma mene ne ba?, tun da kin ce da babansa yake kama komai da komai, wataƙila har halayensa ya ɗaukko, kuma wataƙila wannan abin da ya yi akwai abin da yake nunawa bamu gane ba. Tun da yana shan kununsa, yana rarrafensa, ki rabu da shi kawai. A haɗa sabaya da sauran saiwoyi, ki yi ta sha saboda kar su lalace".
Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas fa"
"To ai ga ki nan ga shi. Sai ki ba shi ya sha ai"
Da Nana ta ɗauke shi da nufin, ta shayar da shi, sai ya hau zunduma ihu,yana turjewa sai dai ta ƙyale shi.
Nana ta din ga jinjina yadda aka yi, É—an wata takwas ya san ya yi zuciya da abu.
Sai da aka kwana huÉ—u, Nana ta ga da gaske ya yaye kansa, iyaka ya zo jikinta ya yi wasan sa ya tafi.
Nene ta ce "Nana ki daina damuwa fa, girmansa tubarkallah da ƙiriniyarsa kamar ta ɗan shekara guda ce, ki rabu da shi kawai, daga yanzu idan za ki yi magana ki din ga yi masa da girmamawa, ki daina yi masa tsawa, manya ba sa son wargi. Kuma ki din ga duba darajar sunan da ki ka sanya masa" ta yi maganar tana yi wa Muhsin rawa.
"To Nene sai na bari ya lalace ba zan ce masa bari ba?"
"A'a ban ce kar ki ce masa bari ba, amma a wannan yanayin shi sarki ne, abin da yake so haka za ki yi haƙuri ki yi masa. Da kin tsaya a zare masa ido kawai da haɗe rai, amma saboda na yi miki faɗa, ki ka haɗa masa da duka, kuma ki ka ƙwace ki ka dungurar da shi, dole ya bar miki abin ki ai".
Nana kalle shi yana ta wasa da kofi, yana bugawa a ƙasa, shi ma ya ɗago ya kalle ta. Sayyid ta tuna lokacin da ya ritsa ta yana yi mata kashedin a kan daina yi masa tsawa ko ɗaga masa murya.
Wani guntun murmushi ya suɓuce mata.
Nene ta ce "Ni kuwa Nana ga shawara"
Ta ce "To Nene"
"Kamar yadda ki ke faɗa motsi ya fi laɓewa, na ce ko dai za a jarraba ki je gurin aikin nan, na harkar dafe-dafen ko Allah zai sanya a dace. Duk da ba na jin a jikina, masu kuɗi a cikin buzaye masu katafaren gurin abinci, za su iya tafiya aikin gadi, amma bamu san ina rana za ta faɗi ba"
Nana ta É—an yi jimm sannan ta ce "Ban san ya zan yi ba ne, tun da kin ga ga Muhsin. Ko za su din ga bari na je na dawo kullum?".
Nene ta ce "Ki na ji fa ta ce sai ki yi wata ba ki zo gida ba, kuma akwai tazara a tsakaninmu sosai, kuma ba zai yiwu ki tafi da Muhsin ba, ba za su yarda ba. Amma ga shawara idan kin ga kin yarda da ni, ki bar mini Muhsin a nan, ki je ko ai
kin na wata uku ki yi, ko Allah zai sanya a dace, sai ki ci gaba da cigiyarsa a gurin."
Ayshercool
08081012143
67
Nana ta yi turus, tana kallon Nene.
Nene ta ce "Ba zan yi miki dole ba, dan kuwa wannan magana ce da kowacce uwa sai ta jinjina girmanta da nauyinta.
Sai dai ni ba zan takura miki ba kuma ban ce sai kin yadda da ni ba, ko mene ne za mu yi shi ne a gaban hukuma, mu je mu yi yarjejeniya mu saka hannu sannan ki tafi. Ban san dalilin da Allah ya sanya ya haÉ—a ni da ke ba, duk rashin son mutane na, ki ka shiga raina ba nake tausayinki ke da yaronki. Har ga Allah ina fatan ki haÉ—u da mijinki ko danginsa, ki samu ki koma gida ki nutsu ki kula da yaronki. Kamar yadda na gaya miki ne, ba zan yi miki dole ba, ki je ki yi shawara idan kin amince shikenan, idan ba ki amince ba babu wani abu, ni dai fatana Ubangiji Allah ya bayyana abin da ki ka fito nema".
Nana ta yi shiru, ƙwaƙwalwarta gaba ɗaya ta ɗauki caji da tunani daban-daban.
****
Jamila kuwa tun da ta je gida, Mama take tambayarta ko lafiya ta ganta wani iri, amma ta ce mata babu komai.
Ta shiga É—aki ta nemi guri ta kwanta, sallolinta kawai ta yi na magariba da isha'i ta sake kwanciya. Gaba É—aya abin Duniya ya gama damunta, dana sani da takaici duk ya cunkushe mata zuciya.
Wayarta ce ta fara ringing, ta duba ta ga baƙuwar lamba ce, jikinta ya ba ta Abba ne, ta ɗaga kiran ta saka a kunnenta.
Muryarsa ƙasa-ƙasa ya kira sunanta ya ce "Ya jikin naki?"
"Da sauƙi" ta amsa a hankali hawaye na ci gaba da gangarowa kan kumatunta.
"Dan Allah Jamila ina ƙara ba ki haƙuri, kuma ki dubi girman Allah ki rufa mini Asiri, ke ma kin san hakan ba halina ba ne ba. Wallahi na rasa inda zan sanya zuciyata na rasa abin da yake yi mini daɗi. Yanzu haka zazzaɓi ne a jikina. Dan Allah ki yafe mini Jamila, na san koma mene ne duk laifina ne. Amma in sha Allah kamar yadda na yi miki alƙawari zan aure ki Jamila, wallahi ina son ki, duk abin nan laifin Mummy ne amma ki yi haƙuri ki yafe mini"
Jamila ta ci gaba da kuka, ta kasa ce masa komai, ya ƙara ruɗewa ya ce "Dan Allah ki yi mini magana, dan Allah ki yafe mini idan ba ki yafe mini ba na san har na koma ga Allah, ba zan samu nutsuwa ba" Ya yi maganar yana kuka mai cike da nadama tamkar ƙaramin yaro.
Duk yadda Jamila ta so jin haushinsa sai ta kasa, tabbas ita shaida ce wannan ba halin Abba ba ne, dan da halinsa ne da ba zai din ga wannan kukan ba, zai ga ya ci bulus ne kawai.
"Yaya Abba na yafe maka, mu haÉ—u mu nemi yafiyar Allah, sannan ka daina kukan nan dan Allah, ka sha magani ka kwanta. Kuma Asiri idan na tona kaina na tonawa ba kai ba, Ubangiji Allah ya yafe mana"
Ya tashi zaune a kan gadonsa, cikin damuwa ya ce "Da gaske kin yafe mini Jamila?"
"Eh Yaya Abba, sai da safe, kaina yana ciwo sosai"
"To na zo na kai ki Asibiti ne?"
Jamila ta ce "A'a, na sha magani ina jin bacci ma, sai da safe" ta katse kiran tana ƙara duƙunƙunewa a cikin bargo.
Wata irin ajiyar zuciya ya din ga yi, ya nemi guri shi ma ya kwanta, zuciyarsa fal tunani daban-daban.
*****
Nana hankalinta ya rabu kashi-kashi, a jikinta ba ta jin Nene za ta cutar da ita, duba da yadda take É—awainiya da ita da É—anta, tamkar ita ta haife ta. Sai dai ta yaya za ta iya ta tafi ta bar É—an ta, da matar da babu dangin iya babu na Baba a tsakanin su.
Sai dai tabbas akwai buƙatar ta gusa, ta yi wani yinƙuri, domin ci gaba da ƙoƙarin haɗuwa da mijin nata, amma ba ta ji ta gamsu da wannan shawarar ba.
Sai dai tun da suka yi maganar nan, da ta kwanta take mafarki ga ta a gurin girke-girken, tana cikin gurin girkin, ta waje sai ga din ga jiyo muryar Sayyid yana magana. Idan ta fita sai ta neme shi ta rasa, sai dai ta ci gaba da jin muryar ta sa, nesa da ita kaɗan, sai dai ba ta san daga wane ɓangaren muryar tasa take ba. Sai ta yi irin wannan mafarkin sai ta farka.
Ta rasa abin da yake yi mata daɗi, kawai sai ta ci gaba da addu'a a kan lamarin, ta juya ta ci gaba da bacci, sai dai babu tsammani sai ga ta a ɗakin karatun Ƙaisar, an yi mata gyara sosai, an ƙara yawan litattafan da suke ciki.
Ya saka mudubinsa a gaba, yana ta zuba masa wani ruwa yana wanke shi.
Bai ce wa Nana komai ba, har ta gaji da tsayuwa, ta É—an yi gyaran murya. Ya É—aga kai ya kalle ta. Ta ce "Sannu da aiki"
"Yauwwa" ya amsa yana tashi tsaye.
Ta ce "Kwana biyu ina ka shiga ne?"
Ya É—aga kai ya kalle ta ya mayar ya sunkuyar yana É—aukar wani littafi.
"Amm dama ina ta son na ganka, na tambaye ka, sannan na roƙe ka alfarma. Dan da kai da Giyaz da duk wani mai son ɗaukar fansa a kan zuriyarmu, ya ɗauka a kaina, dan Allah ku ƙyale mini yarona. Na ga rannan ka ba shi wani abu da ban san ko mene ne ba, dan Allah kar ku yi masa komai"
Bai ko motsa ba, balle ta sanya ran zai yi mata magana.
"Ƙaisar ka yi magana ma dan Allah"
"Na ce miki ne? Ko har kin manta abin da ki ka faÉ—a a kaina, saboda abin da na yi wa mahaifina a kan na kare ki?"
Sai kuma Nana ta yi shiru, ta sha jinin jikinta.
Ya wurgo mata littafin nan da ta fara karantawa, ya ce "Ga wannan ki ci gaba da karantawa, wataƙila zai yi miki amfani a gaba" Ta kalli littafin ta kalle shi, ta ce "Me yasa ka amince na karanta wannan littafin, wancan kuma ka hana ni karantawa? Ni ba zan iya ci gaba da karantawa ba, babu komai a ciki sai tashin hankali da zubar da jini na tsagwaron rashin tausayi da adalci, ni bai burge ni ba, ba zan karanta ba"