← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 78

Sashe 60

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba ɗaya Shukura ta burkicewa Sagir, ba ɗaga masa hankali ta yi da rigima ba, tattara shi ta yi ta watsar gaja ɗaya take harkokinta, da gaske take ƙoƙarin gano abin da mahaifinta yake ɓoyewa tsawon wannan lokacin da har ya hana Hajiya Amina bincike a kan lafiyarta.
Ga shirin tariyar Yusra Sagir na yi, ga damuwar rashin sakin jiki da shi da Shukura ta yi, ta tattara shi ta watsar.
Ɓangarensa ya saka aka gyarawa Yusra, dama ba amfani yake yi da shi ba, aka ƙara gyara shi, aka haɗa gidan gaba ɗaya aka sake yi masa fenti. Daga gaya mata batun dawo da Yusra zuwa gyaran gidan da kawo kayanta, ba a yi sati guda ba, gida ya ɗau harama.
Duk yadda ya so ya lallaɓa Shukura, ta saukko ta din ga saurararsa ta yi burus da shi.

Nana ta shafe sati guda tana gidan Asal, tana yi mata hidima, ta hantare ta ta kyare ta, dandazon ƙawayen da take tarawa ma, su hana ta sukuni da aiki. Nana ta din ga iya ƙoƙarinta, gurin kai zuciyarta nesa, amma abin ya fara isarta.
Tana tsaka da nazarin yadda za ta ɓullowa lamarin, da safe Asal za ta fita ta kalli Nana ta ce "Ki shirya nan da sati ɗaya zamu bar nan, zamu je asalin inda na ɗauke ki ki yi mini aiki a gurin"

Nana ta ce "Ina kenan? Kuma aikin me?

"Idan mun je za ki gani" Ta ba wa Nana amsar a taƙaice.

*****
Jamila tana kwance tana chatting da Abba, bikinsa saura sati biyu.
Hajiya Sa'a tana ta zaginsa da yi masa bala'i, a kan yadda yarinyar take ta ƙorafin ba ya kula ta, waya ma sai dai ita ta kira shi, babu abin da ya yi masa zafi da ita.
Yanzun ma kamar ya yi wa Jamila kuka.
Ita take ta rarrashinsa tana nuna masa babu komai ya yi aurensa kawai.

"Ƙanwata ko na yi aure hankalina ba zai kwanta ba, kar ki manta da ɓarnar da ta faru tsakanina da ke, ya zan yi da shi"

Ta ce "Na san kai mutumin kirki ne yayana, hakan ne ya sanya ka ke jin damuwa a kan abin da ya faru, amma ka yi haƙuri ka yi aurenka kawai, ina roƙon Ubangiji Allah ya kawo mini wani mijin"

"A'a ki daina faɗa mini haka, zuciyata tana sosuwa, baki da wani miji sai ni in sha Allah" haka suka kasance tana ƙarfafa masa gwiwa, shi kuma yana rarrashinta.
Ta gama wayar ta ajiye, ta ga Suwaiba ta ƙuro mata ido tamkar ba ta taɓa ganinta ba.

"Meye ki ke kallona, lafiya?" Suwaiba ta yi shiru ba ta bata amsa ba, kuma ba ta yi magana ba.

Jamila ta ja tsaki, tana ƙoƙarin kwanciya, Suwaiba ta ce "Jamila"

"Na'am mene ne?"

"Ki ɗauki saƙonki mana"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wane saƙon?"

"Na cikin jakarki"

"Cikin jakata kuma? Mene ne a jakar tawa? Wato bincike ki ke yi mini a jakar ko?"

"A'a ni tuni kawai nake yi miki da saƙonki na cikin jakar"

Jamila ta tashi zaune ta ce "Wai wani saƙon? Miƙo mini jakar dai na gani"

Suwaiba ta ce "A'a ba zan taɓa miki jaka ba"

Jamila ta janyo jakar ta fara buɗewa ta ga abin da Suwaibabta dame ta a kai. Cin karo ta yi da wannan 'yar tsanar da ta riga ta jefar. Saura ƙiris ta kurma ihu, ta rikice gaba ɗaya jikinta ya hau rawa, a tunaninta tun da ta yar shikenan ta rabu da ita.
Suwaiba kuwa ta tuntsure da wata irin mahaukaciyar dariya, ta din ga yi tana ƙyaƙyatawa tana kallon Jamila. Gaba ɗaya Jamila ta kiɗime ta rasa abin da yake yi mata daɗi, gaba ɗaya jikinta ya hau rawa tamkar ta kurma ihu, sannu a hankali kanta ya fara juyawa ta fara gani dishi-dishi, dole ta rufe jakar ta nemi guri ta kwanta.

*****

Alhaji Zailani ya kwana biyu bai je gidan Alhaji Fatuhu ba sai yau. Sai dai ya sha mamakin ganinsa a harabar gidan da sanda yana dogarawa yana tattakawa a hankali, yana tsaye a kan ƙafafuwansa yana kallon yadda Muhsin yake ta gudu a harabar gidan.
Sai da ya aro jarumta sannan ya iya danne abin da ya ji ya taso masa na tashin hankali da mummunan baƙin ciki.
Da ƙyar ya iya washe baki ya ce "Ikon Allah, Abokina kai ne haka nake gani?"

Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Ka ga ikon Allah ko? Sannu da zuwa Bismillah" ya yi maganar yana nuna masa É—aya daga kujerun da ke ajiye a gurin.
Alhaji Zailani ya zauna suka ƙara gaisawa

"Bani labari, ya aka yi sauƙi ya samu haka, wani Asibitin ka je ne?"

Alhaji Fatuhu ya ce "A'a na ga an yi na Asibitin ne babu wani ci gaba, Fadila ta zauna ta din ga yi mini bayani, na amince muka fara gwada na islamic, cikin ikon Allah sannu a hankali wannan ɗaurewa da nake ji a jikina ya yi mini sauƙi, wannan gigicewar da nake na ji kamar zan yi hauka shi ma Alhamdillah ina daɗewa ban ji ba, wannan warin ma da nake ji ya ragux

"Amma Fatuhu ya za a yi ka biye wa mace da shirmen ta, ga na Asibiti ana yi kawai ta saka ka fara wani na shirme, sai ka je ka yi abin da za ka kauce wa hanya tukuna?"

"A'a nima na jaddada mata, ta kuma tabattar mini da babu kauce hanya a ciki, kuma nima shaida ne, shi ya sanya ma nake amfani da magungunan kuma ana samun ci gaba"

Alhaji Zailani ya miƙe ya ce "Haka ne, to bari na je dama ina da gurin da zan je na biyo, sauri nake yi"

"Ba zaka tsaya ku gaisa da mutanen gidan ba?"

"Sauri nake yi zan sake dawowa"ya yi maganar yana yin gaba cikin ƙunar rai, ji yake yi tamkar ya kashe Alhaji Fatuhu ya huta, dan shi bai taɓa zaton zai kawo yanzu bai mutu ba.

*****

Al Hussain ne a tsaye ya tsare Hasna da ido, yana yi mata faɗa cikin matsanancin ɓacin rai.
"A kan me za ki yi haka? Dan me za ku yi mata dole, ai ba ɗaukar ta aiki muka yi saboda buƙatar mutum guda ba. Abin da yake cikin yarjejeniya shi ne ta yi wa gidan Abincinmu aiki, idan ma canza gurin aikin ne, wani reshen zamu mayar da ita, amma dan me za ku haɗa kai ku yi mata haka wannan wulaƙanci ne da cin zarafi, kuma ga shi bama 'yar ƙasarmu ba"

"Ni fa Al Hussain na kasa gane maka, ko son yarinyar nan ka ke yi ne? To bari na tuna maka kai Buzu ne, buzun ma farin buzu ka san abin da nake nufi ai, kuma matar aure ce ko bazawara dan ta ce mana tana da É—a ma"
"Ni ba wannan na tambaye ki ba, dan me Asal za ta yi amfani da ƙarfi da kuɗi ta tursasa mata yin abin da ba ta so, ai ba haka ake rayuwa ba"

"Ai na san za a yi haka, babu bayanin da ban yi mata ba taƙi yadda, ga shi ni yanzu ka zo ka saka ni a gaba da jaraba, sai ka je ka dawo da ita ni ba zan iya ba"

"Ke dai da ki ka yi hakan ki je ki dawo da ita, idan ba haka ba daga ke har ita na rubuta masa abin da ku ka aikata, daida yake da ku"

Ta kwaɓe baki ta ce "Wa ya san ma inda yake, mutumin da ake tunanin ya ɓata babu wanda ya san ma yana raye ko yana mace?"

"Hakan ya baku damar cin karenku babu babbaka daga ke har Asal ko? Yayi muku kyau" Hasna ta fice tana jin haushin masifar da Al Hussain yake ta yi mata, duk yadda ta yi ƙoƙarin hana Asal ɗaukar Nana.

*****

Ana gobe su Nana za su bar wannan gidan, Asal ta sanar da Nana ta shirya washegari za su bar nan.
Ita dai Nana ta sanya wa sarautar Allah ido, rayuwarta ta zama tamkar tamaula daga nan zuwa can, ba ma ta da 'yancin tambayar ko sanin inda za a kaita sai dai inda ta tsinci kanta kawai.
Ta sha aiki ta gama, ta ɗan zauna a falo tana hutawa, sai ga ɗaya daga gayyar ƙawayen Asal ta saukko ta kalli Nana ta ce "Dan Allah ina son shayi"
Nana ta ce "Akwai a kayan Abincin da na girka"
"Shayin kanumfari kawai nake so bana son Shan na girfa"

"Ga gurin dafawar can, idan ki ka je akwai komai, ki dafa ki sha idan kin matsu"

"Ke, kin san wace ce ni ki ke gaya mini haka?"

"Ban san wace ce ke ba, kuma ba na buƙatar sani"

Asal ta saukko tana tambayar lafiya.

Ta gaya mata abin da ya faru, ta kalli Nana ta ce "Wai ke me yasa ba ki da mutunci, ban gaya miki dole ki girmama baƙina ba, mene ne a cikin dafa shayi mintinan nawa ne kin yi kin gama?"

Ta kalli Asal ta ce "Ki yi haƙuri, wallahi ko cokali ba zan iya sake ɗauka ba, yau na bautu a gidan nan ke kin sani, kuma ban taɓa yi miki ƙorafi ba, amma yanzu dai na gaji gaskiya"

Suka juya yare suka yi magana, ba ta san me suka ce ba, ta ga sun koma kan bene.
Chapter 60 · 0% Book details