Sashe 41
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta jinjina kai ta ce "To shikenan Nene, duk yadda ki ce Shikenan, na gode sosai da sosai Ubangiji Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"
Nene ta ce "Amin yarinyar kirki"
Fitar Nene babu jimawa sosai, sai ga Ashura ta faÉ—o gidan.
Nana ta ba ta ce mata ta shigo ɗakin, amma ta ƙi.
Nana ta tashi ta fita ta shimfiÉ—a mata tabarma, sannan ta É—aukko Muhsin, ta zo ta zauna ta ba wa Ashura shi.
Ta karɓe shi tana buɗe baki cikin murna, ta kalli Nana ta ce "Ina son yaron nan"
Nana ta ce "Da gaske?"
Ta jinjina wa Nana kai, ya jima a hannun Ashura, sannan ta ba wa Nana shi, Nana ta mayar da shi ɗaki ta kwantar. Sai dai tana dawowa ta tarar da Ashura a tsaye tana kuka, gefenta ga ƙwarangwal ɗin nan.
Nana ta ce "Me ka ke buƙata ne?"
"Ki na ganina kenan?"
"Eh ina ganin ka, sannan wannan mahaifar da ka ke lasa mene ne ma'anar hakan? Tun da ƙazanta ce"
Ya ce "Lokacin da aka haife ta ne, da za su dawo daga Asibiti, aka manta mahaifar, shi kuma mai motar ya yar a bola, ni kuma na tsinta na biyo ta."
Cikin damuwa Nana ta ce "Amma baka kyauta ba, tun da babu wanda ya yi maka wani laifi ka ke yi mata abin da ka ke yi mata".
Ya ce "Ai mu ba sai an yi mana abu ba, idan mu na son mutum. Kin ga ke ma da ki ke addu'a wasu lokutan, ba dan tasirin Addu'a da ki ke yi, da kuma tsoron uban duƙusa da ake yi ba, da bataliyar da za su shiga jikinki da yawa. Saboda da guda ɗaya ya yi hanya, wasu ma suke samun kafar shiga jikin mutum. Kuma Allah ya taimake ki, Sarkin baka ya rage tasirin uban duƙusa a tare da ke, da duk inda muke sai kin din ga ganinmu, kuma muraran za ki din ga ganin cututtuka da sihiri a zahiri, sai kin kusa haukacewa idan ba ki bayar da magani ba. Kawai dai shi yana lallaɓa ki ne"
Nana ta ce "Yaya aka yi ka san Ƙaisar, kuma ka san Sarkin baka?"
Ya ce "Jaddul Jinn babu wanda bai san shi a nahiyar nan ba, dan haka sanin jikansa uban duƙusa ba abin mamaki ba ne. Sarkin baka kuma shi ne ya mayar da ni ƙwarangwal, mun taɓa artabu da shi da na shiga jikin sata mesa, ya ƙona ni. Kuma na ga kin haɗa jini da shi, ba yadda na iya da ke ne kawai, da sai na ɗauki fansar abin da aka yi mini a kan ki"
Nana ta yi shiru jikinta ya yi sanyi, su na gama maganar Ashura ta juya ta fita ya bi ta a baya.
Nana ta din ga jinjina azabar naci da riƙo irin na halittun nan.
****
BAYAN WANI LOKACI.
Girman É—an mutum babu wuya, in ji masu iya magana, Muhsin ya cika watanni bakwai, Nana na zaune tare da Nene.
Nene ta kai ta gurin koyon girke-girke, yanzu kuma tana zuwa koyon É—inki. Nana har mamakin yadda Nene take yi mata take. Sai dai ta fara karaya da yanke tsammannin haÉ—uwa da Sayyid.
Nene ce ta shigo gidan, bayanta goye da Muhsin, yana ta mamular cukui.
Nene ta sauke shi ta zaunar da shi ta ce "Wannan ɗan naki, idan bai nuna mini halinsa ba, ai ba za a ce ɗan buzaye ne ba, mun taho hanya ya ga raƙuma, wai sai dai mu tsaya ya kalli raƙumi, sai zillo yake a bayana yana ihu, sai da na tsaya na ɓata lokaci yana kallon raƙuma yana miƙa musu hannu. Ya cire hular kansa ya yar, kowa ya ga kansa da wannan kitson sai an tambayi mace ce ko namiji. Ke ma da taurin kan tsiya, kin ƙi bari a yi masa aski, kuma kina yi masa kitso kamar wani mace."
Nana ta yi murmushi ta ce "Ni babu ruwana, ba shiga faÉ—anku zan yi ba, balle na ji kunya ku gwale ni"
Shi kuwa cukun hannunsa kawai yake mamulawa a bakinsa, Nene ta juya za ta fita tsakar gida ya rarrafa ya bi ta yana kukan ta É—auke shi.
Nana ta sake yin murmushi ta ce "Na haifa wa Nene É—a"
Tana jiyo rigimarsa da Nene, ya hana ta aiki, idan ta hana shi wannan ya koma wancan.
Nana ta din ga dariya daga É—aki, aka jima kuma Nene ta zuba masa shayi sai kuma ya nutsu, guri É—aya, yana sha yana wasa da gashinsa.
Ashura tana son zuwa gidan Nene gurin Nana, amma tana tsoron Nene, ga Muhsin da ya ganta yake sanya ihu, tsoronta yake ji.
Æangare guda kuma, zuciyar Nana na saÆ™a mata ya kamata ta gusa ta bar gidan Nene, saboda ta ja lokaci a gidan. Amma tana tuna tijarar Nene, da rashin sanin ina za ta dosa. Ba ta san wani irin mutum ne Sayyid ba, mutumin da za a yi alfahari da haÉ—a nasaba da shi ne ko akasin haka, duk da tana kyautata masa zato. Shi yasa take É“oye wasu abubuwan, dan kare mutuncin sa da rashin sanin a yaya za ta haÉ—u da shi.
Washegari da safe Nana ta tashi, ta jiyo hirar Muhsin a tsakar gida.
Ta tashi ta fita kar ya yi wata ɓarnar, sai ta gan shi a lungun kitchen ɗin Nene, ya juyo bayansa, kamar dai wani abun ya samu yana wasa da shi.
"Kai babyn Sayyid, me ka yi a gurin nan, taho ka sha" bai waiwayo ba ya ci gaba da abin da yake yi. Nana ta nufe inda yake. Wata irin narkekiyar mesa ta gani a cikin lungun, shi kuma yana ta duƙunƙuna kanta da hannu bibbiyu yana hira.
Ji ta yi tamkar an É—aure ta tamau, ta kasa gaba ta kasa baya, kuma ta kasa magana.
Mesar ta miƙe sai ga Ƙaisar ya bayyana a gurin. Muhsin ya ɗaga kai yana dariya yana kallon Ƙaisar.
Ƙaisar ya ciro wani abu a kwalba, ya buɗe bakin Muhsin ya zuba masa, Nana ta rikice amma ta kasa motsa kowace gaɓa ta jikinta.
Muhsin ya kama rigar Ƙaisar yana wasa da ita, yana yi yana kallon Ƙaisar ɗin.
Ƙaisar ya saka hannu ya shafa kitson kan sa, ya miƙe tsaye ya ɓace. Sai da ya ɓace Nana ta iya motsawa, amma duk da haka ta kasa zuwa inda Muhsin yake, sai shi ne ya rarrafo ya nufo inda take.
Ta saka hannu da ƙyar tana dudduba jikinsa, ko wani abin ya yi masa amma jikinsa lafiya ƙalau. Ta shiga fargaba da tsoron me ya ba shi ya sha?.
Ta ja jikinta ta koma jikin bango, ta fara shayar da shi, tana roƙon Ubangiji Allah ya kare mata yaronta daga sharrin su Ƙaisar da kowane irin nau'i na shaiɗani.
Nene na fitowa, ya cika Nana ya tafi gurinta, sai da ya gama wasansa, ya sake komawa gurin Nana.
Tana shayar da shi, tana ganin fuskar Sayyid a tattare da shi, dan hatta idan ya ɓata rai, tamkar mahaifinsa.
Sai dai tunani da tsoron abin da ka iya samun sa, ya gaza barin zuciyarta, tun daga ganin da ta yi wa Ƙaisar da shi.
Ta so gaya wa Nene, amma ta ja bakinta ta yi shiru ba ta gaya mata ba.
Sai dai tun gabatowar magariba, take jin sanyi.
Ta shige ɗakin ta ƙudundune, ta bar su Nene.
Tana tsaye a sahara, sai dai a wannan karon babu ƙurar Saharar, ta hangi Sayyid a zaune yana shan shayi, shikaɗai.
Ta taka sannu a hankali ta ƙarasa inda yake, ya ɗago ya kalle ta yana murmushi.
Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Ka warke ne?"
"Da sauƙi, na yi nesa da inda nake jin ciwon, kuma na yi nisa da gurin waɗanda za su kashe ni"
Cikin damuwa ta ce "Ni fa?"
Ya ajiye kofin hannunsa, ya rungumota jikinsa yana kallon fuskarta, idanunsa cike da hawaye ya ce "Yadda ruhinki da gangar jikinki, suka gaza samun nutsuwa, tun bayan rabuwarmu haka nima nawa suka gaza samun nutsuwa. Ina kewarku gangar jikina ta kasa samun nutsuwa, ina buƙatar ki a kusa da ni"
Ita Nana gaza riƙe nata hawayen ta yi, tuni ta ba su dama suke zuba.
Ya girgiza mata kai tare da cewa "Kar ki manta, muddin kina raye kuma ina raye a doron duniya, gangar jikinmu ba za ta samu nutsuwa ba, sai mun haÉ—u. Ina kewar ki ma vie."
Ya yi maganar yana ƙanƙame ta a jikinsa. Ta buɗe idonta tana ji yadda hawaye ya jiƙa mata fuska.
Ta tashi zaune da ƙyar, ta yi shiru ta tafi tunani. "Nana ba a bori da sanyin jiki, ci gaba da zaman ki a gidan nan, tamkar ki na matsawa dattijuwar nan ne da take ɗawainiya da ke, kuma ba za ki taɓa haɗuwa da Sayyid ki na zaune guri ɗaya ba, yakamata ki motsa".
Ta tashi ta yi alwala, ta yi sallar magariba da isha'i, ta idar ta shiga É—akin Nene ta É—aukko Muhsin, ta dawo da shi É—akinta saboda ko zai farka cikin dare.
Nana ji ta yi tamkar ta fice daga gidan a cikin daren nan, amma ta kasa saboda ba ta san ina za ta nufa ba, a wannan uban daren.
Ta haƙura da niyyar da Asubar fari, ta tashi ta fice, amma bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita, sai da aka kusa idar da salla, Nene ta tashe ta yi sallar Asuba.
Tana idar da sallar kuma, Muhsin ya tashi ya saka rigima, Nene ta É—auke shi suka tafi É—akinta.
Tun da wuri yaran Nene suka zo, suka ɗauki kayan Abinci, amma Nene ta ƙi fita ranar ta wuni a gida, yaranta ne suka je suka sayar da Abincin.
Abu kamar wasa a jere kwanaki huɗu Nana tana yinƙurin guduwa, amma Nene ta kasa ta tsare tamkar ta san abin da Nana take shiryawa.
*****
Jamila ta nuna wa Hajiya Sa'a tamkar ba ta san ita ta taka wa É—an ta Abba burki a kanta ba, Hajiya Sa'a sai shirin bikin Abba take yi, yayin da gefe guda kuma Jamila ta yi blocking É—in sa, ta daina É—aga wayarsa gaba É—aya.