Sashe 14
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da ƙyar ya yarda ya karɓa, ya ɗanɗana ya ji babu ɗaci, sannan ya ci gaba da sha, sai ma ya ji ɗumin maganin ya yi masa daɗi.
Bayan ya shanye, ta dafa masa shayi kuma, ya ɗora dan duk wahalar ciwon da yake ciki, ba ya iya haƙura da shan shayi.
Nana ta dage da bawa Sayyid, wannan ruwan maganin, tana addu'ar Ubangiji Allah ya taimake su, ya sanya ya karɓe shi.
Cikin ikon Allah, sai kumburin da ya yi, ya fara sacewa a hankali, har yana iya cin Abinci sosai. Nana kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.
Nana ta din ga murna, ganin ana samun ci gaba a yanayin jikinsa. Har banÉ—aki yana iya zuwa, ba tare da ta kama shi ba, yana tafiya a hankali a hankali da kansa yana iya yi wa kansa Wasu abubuwan.
Yana zaune tsakar gida, yana shan shayi ta ce "Ashe maganin Sarkin baka yana yi"
Ya kalle ta, ta ce "Ka san Sarkin baka?" Ya É—an yi shiru yana kallon ta.
"Ranar da aka kai ni, kai na an kai ka, zaku tafi lokacin, ni kuma a lokacin na ji na fita daga hayyacina. Kai mun fa daÉ—e muna haÉ—uwa da kai."
Ya yi murmushi ya ce "Ruhina ne ya addabe ki, sai da ki ka nemo ni, ki ka aure ni ki ka nutsu"
Ta ɓata fuska ta ce "Ba wani nan, kai ne ka din ga bi na dai, har ka aure ni".
Ya ɗan sake zuƙa shayin hannunsa ya ce "A'a. Har gidan da nake ki ka bi ni fa"
"Ni ba bin ka na yi ba, kuma ai kai ka ce a biya maka sadakin aurena"
Ya maze ya ce "Ai gani na yi kin liƙe mini, har cikin ɗakinmu na gadi ki ka bi ni, na ce kai yarinyar nan idan ban aureta ba, akwai matsala haka za ta yi ta bina saboda ruhinta da yake jikina. Kina ganina kuma ki ka rikice"
"Ni ba ina sane na shiga É—akinku ba, Jummai ce ta ce na ajiye muku Abinci, kawai na ji ana kirana a cikin É—akin, ban ma na san na shiga ba. Kuma ni da na shiga wannan tsohon na gani. Kuma ai kai ma idan ka ganni kallona ka ke yi"
"A'a faɗi gaskiya dai, ni ki ka leƙo ki gani, ranar ba ki ganni ba, sh... Kawai ya ga tana hawaye. A diririce ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Mene ne?" Ta yi masa shiru.
"Laifi na yi miki? Wasa fa nake yi" ta yi masa shiru, tana matse ƙwalla. Ba wai wasan da yake yi mata ne ya sanya ta kuka ba. Tuna yadda aka yi auren abin da Baba ya din ga faɗa da wanda Mama ta din ga yamaɗiɗi da ita, abin ne kawai ya dawo mata.
Ji ta yi yana goge mata hawaye, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya ce "Ba zan sake ba" Kwaɓe baki ta yi cikin shagwaɓa, wasu hawayen na ziraro mata.
"Na ce na daina fa, ki bari ƙirjina ya fara nauyi" da sauri ta saka bayan hannunta, tana goge hawayen fuskarta.
"Yauwwa dama ina so mu yi wata magana, mai muhimmanci da ke"
Ta tattara hankalinta, gabanta na dukan uku-uku cike da wasi-wasin wace maganar zai yi da ita haka?.
Ayshercool
08081012143
57
Ya yi mata alama da hannunsa, a kan ta nutsu ta kwantar da hankalinta. Ta jinjina masa kai, duk da gabanta na ci gaba da faÉ—uwa.
"Amm na san kina haƙuri a kan abubuwan da suke faruwa, duk da kin ce mini ba kya so na din ga irin wannan maganganun, amma sun zama dole na yi. Ina ƙara yi miki godiya da nema miki yardar Allah, na san ba ni da abin da zan biya ki da shi a wannan Duniyar. Ke ce komai nawa da ki ka rage Asmy. Sannan ɓangaren abin da ya shafi auratayyarmu, shi ma na san...
Ta katse sh6ta hanyar cewa "Amm ni dai a bar wannan zancen, bari na je na É—ora wakena"
"A'a ki tsaya mu yi magana"
"A'a ba sai mun yi ba"
"To kar na sake jin kin bi dare ki na taɓa ni" Kamar ta yi tsuntuwa ta ɓace, saboda azabar kunya, ita a zatonta ma ya manta gaba ɗaya. Cikin azama ta miƙe ta ɗauki robar wakenta, ta nufi inda take girki. Tana tashi ya kashingiɗa yana dariya.
Nana tana ta fifita wuta, yana daga zaune yana kallonta. Wani irin abu ne yake yi masa yawo a jikinsa, a game da ita.
Yana jin zai iya yin komai, dan tabattar da ci gaba da zamanta mallakinsa, shikaÉ—ai.
Juriyarta, sadaukarwa da kuma tsananin tausayinta, ya sanya yake jin ina ma yana da wani abu da zai iya kamanta faranta mata rai, kamar yadda take ta wannan É—awainiyar da shi. Ya san in dai a wannan Duniyar ne ba shi da abin da zai biya ta. Duk da matsananciyar damuwar da ya kan shiga, da jin cewa ya zama silar nakasta rayuwarta, ta zama tana rayuwa ba tare da tunanin wani abu da take so ta cimma ba. Kullum tunaninta a kan sa ne kawai.
Tana É—agowa suka haÉ—a ido, ta murguÉ—a masa baki, ta ci gaba da fifitar wutar gabanta.
Ya tako zuwa gaban murhun ya tsuguna.
"Dan Allah ka tashi, saboda numfashinka fa"
"Kawo na yanka miki salak É—in"
"A'a kar ka yanke hannu"
Ya ce "Ki kawo zan iya" Ta tsuke fuska ta kalle shi ta ce "Saboda sauƙi ya samu, kana iya fitowa da kanka yanzu, shi ne za ka din ga damuna ko?"
Ya yi murmushi, ya zauna a gefe yana kallon ta, da ta É—aga ido, sai su yi ido huÉ—u da shi, sai ya yi mata murmushi.
Su na cikin cin abinci, ya ce "Ki na kiran Ummi?"
"Ba na samun ta, ita ma ta kira ni wayar ba na ji. Uwani ta ce haka garin nan yake babu network, sai a yi kira fiye da sau goma ba ka samu mutum ba.
"Idan na ƙara jin sauƙi, zamu je mu gaishe ta, mu yi mata godiya"
Ta ce "Alhamdillah, lallai sauƙi ya samu."
Ya ce "Eh, ina jin hakan a jikina nima. Mu je waje na É—an tattaka na ga gari"
Nana ta faÉ—aÉ—a murmushinta ta ce "Allah abin godiya, wallahi Sayyid da har na fara fitar da rai da kai, na karaya sosai wallahi" Cikin murna ta saka hijjabinta, suka fita. Su na tafe a hankali ta kalle shi ta ce "Gaskiya na yi mamaki, ashe da gaske magungunan sarkin Baka yana yi"
Ya tsuke fuska ya ce "Na gaji da jin zancen Sarkin Bakar nan"
Nana ma ta yamutsa fuska ta ce "Sayyid ka yi haƙuri, amma na yi farin cikin yadda maganin da na gani a gurinsa ya yi maka aiki. Ina yi masa fatan idan a kan daidai yake, Ubangiji Allah ya ƙarfefe shi ya dafa masa, ko dan saboda yadda yake taimakon mutane. Idan kuma a kan kuskure yake Ubangiji Allah ya ganar da shi, ya ba shi ikon tuba kafin lokaci ya ƙure masa."
Sayyid ya yi mata banza, suka ci gaba da takawa a hankali su na zagayawa.
Wani irin sanyi ne ya fara ratsa Nana, ganin Sayyid ya durfafi wata hanya, ta kuma kasa ce masa uffan, balle ta hana shi. Su na tunkarar gurin, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri.
Wata irin narkekiyar bishiyar kuka suka tarar a gurin mai ban tsoro. Yanayin yadda take ɗauke da wasu irin murɗaɗɗun rassa, da yadda murtuka-murtukan jijiyoyinta suka huda ƙasa suka mamaye gurin. Ga wani irin ƙaton kogo a jikinta, hakan ya nuna daɗewar da bishiyar ta yi da wanzuwa a gurin.
"Asma'u" ya kira sunanta kai tsaye. Ta kalle shi cikin matsanancin mamakin yadda ya kira sunanta na yanka kai tsaye.
"Ji nake yi kamar na san gurin nan"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Nima haka, amma ni dai na san ban taɓa zuwa gurin nan ba, amma ina jin kamar na san gurin, amma dai... Sai kuma ta yi shiru bayan da gurin ya gauraye da duhu aka yi wata irin walƙiyya, haske ya mamaye gurin. Tsohon nan ta gani a tsaye, riƙe da sandarsa ya zubo wa Nana idanunsa marasa kyan gani. Jikinta ne ya ɗau kyarma, ta ƙara rikicewa bayan ganin a hankali wasu halittu da take kyautata zaton ire-iren su Ƙaisar ne su na bayyana a bayansa.
Tsohon ya kalle ta, ya buɗe baki ya fara magana. "Ina sake yi miki barka da zuwa, garin da kakanin kakaninki su ka durƙusa suka haifo matsalar da har abada ba za ta daina bibiyar zuriyar su ba. Zan ci gaba da azabtar da rayuwarki, za ki ci gaba da biyan bashin nan, ko bayan ranki, muddin aka ci gaba da samun haihuwar masu irin tauraronki."
Yana rufe bakinsa, É—aya daga cikinsu da Nana take kyautata zaton jininsin mace ce, saboda yanayin wani irin tsohon mayafi da ta yafa a kanta. Ta tunkaro Nana gadan-gadan.
Tana zuwa matar, ta hankaɗa Nana ƙasa, sauran suka rufu a kan Nana, su na zira hannunsu a mararta, su na ciro gudan jini.
"Ya hayyu ya ƙayyum ya Allah. Allah ka kawo mini ɗauki, Sayyid, Sayyid, Sayyid ka tashi" Ta yi maganar tana jijjiga Sayyid da yake kwance a gefen ta yana bacci.
Ya ja jikinsa ya tashi ya ce "Ma viee lafiya kuwa?"
"Sayyid marata ciwo take yi. Sayyid marata. Sayyid babyna. Ba na son na rasa jaririna a wannan karon, Dan Allah ka taimake ni"
Cikin rashin fahimta ya ce "Meyafaru ne?"
"Marata ce take ciwo, Sayyid ba na son cikina ya zube, ina son jaririna Sayyid ciwo marata take yi sosai" Ta yi maganar tana zubar da hawaye. Ya saka hannunsa a mararta, ta saka hannayenta ya dafe hannunsa tamkar hakan ne zai hana cikin zubewa.
Ya ce "Ki yi Addu'a" Kawai ta jinjina kai, amma Addu'a kam, ko É—aya ba ta zo kanta ba, dan ta manta komai daga cikin kanta.
Cikin rauni Nana ta ce "Sayyid fitsari nake ji, ya matse ni"
Ya ce "To mu je ki yi"
Ta girgiza kai ta ce "A'a ba na son na je na ga jini ya zubo, cikin ne zai zube"