← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 78

Sashe 4

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta ɗora hannunta a ƙirjinsa ta ce "Sayyid dan Allah ka din ga ɗaukar al'amurana da sauƙi. Ga shi har girki na yi, ina komai nawa lafiya. Ka san lallaɓawa muke yi, ba ka da cikakkiyar lafiya. Ka daina saurin tsorata ko fusata. Ya saka hannun sa yana ƙara danne hannunta a saitin zuciyarsa. Yana iya ƙoƙarin sa a kan ya din ga saita al'amuransa. Amma ya rasa dalili duk abin da ya shafi Nana, kai tsaye yake jin sa a tsakiyar zuciyarsa. Ba ya iya yi masa shinge ko ya dakatar da shi. Yana so Nana ta haihu da shi, amma wahalar da ya ga tana sha, sai da ya ji dama cikin ya zube ko zata huta.

*****

Tun da Jamila ta koma gida, jikinta a sanyaye yake, gani take yi, duk wanda ya ganta ya san abin da ya faru da ita. Mama kuwa baki ya ƙi rufuwa, saboda Jamila ta zo da abin Duniya. Kuma kamar yadda ta gaya mata, sarin kaya ta raka Hajiya, babu wani bincike ta yarda da hakan ta amince.

Ta zo ba ta iya bacci sam, da ta kwanta bacc6, sai ta ga tamkar za ta buÉ—e ido, ta sake ganinta, a wannan gurin da suka je da Hajiya Sa'a.

"Jamila" Suwaiba ta kira sunanta, ta waiwaya ta kalle ta.
"Wai ya na ga ki na abu kamar mara gaskiya ne?"

Gaban Jamila ya faÉ—i ta ce "Me na yi na rashin gaskiyar, me ki ka gani?"

"To ai gani na yi kin kasa sukuni, ki na ta wani mutsu-mutsu gaki nan dai"

"Dan Allah Suwaiba ki ji da abin da yake damun ki, ni babu abin da ya same ni, lafiya ƙalau nake "

Suwaiba ta ce "To ai shikenan"

****

Nana duk sammakon da suka yi, su ne na goma sha É—aya, a gurin ganin likita.

Wajen sha É—aya na safe aka zo kan su, Nana suka shiga, sai dai wannan karon wani likitan daban suka samu. Suka gaisa Nana ta yi wa likitan bayanin komai. Tare da ba shi takardun gwaje-gwajen da aka yi masa, da kuma katin da aka rubuta masa magunguna.

Ya karɓa ya duba a tsanake, ya duba Bp ɗin Sayyid, ya duba ƙirjinsa da stethoscope.

Nana ta ce "Doctor yaya jikin nasa? Me ka gani?"

Bai kalli Nana ba ya ce "Me yasa ba ku dawo follow up ba"

Ta ce "Ai ba a bamu lokacin dawowa ba. Dama ni ce naga yakamata mu dawo ɗin. mu na ta ƙoƙarin kuɗin allurar su haɗu ne, ko ba su haɗu ba, zamu yi ƙoƙari ko a anan Asibitin gwamnatin ne, sai mu yi booking a fara yi masa"

Likitan ya ce "Ki na ji na 'ya ta?"

Ta ce "Eh"

"Ai mijinki ne ko?"

Sayyid ya jinjina kai. "To a duniya babu wani abu da Allah ba zai iya ba, babu shi. Batun allura ki bar wannan a hannun Allah. Kuma dan babu kuɗin allaura ba za a daina ganinsa ba. Zamu ci gaba da gwada shi, mu na ba shi magungunan da suka dace. Idan Allah ya yassare kwa zo a yi daga baya. Kuma jikinsa Alhamdillah da sauƙi sosai da sosai. Jinin dai haryanzu bai sauka yadda ake so ba. Amma zai sauka da yardar Allah. Kawai ki din ga kiyaye damuwarsa da ɓacin ransa. Idan kuma akwai wani abu da yake damunsa, ki zauna da shi ku tattauna ki ga ta ina za ku shawo kan matsalar?. Amma babu wani abu in sha Allah" Duk da ba lafiya likitan ya ba su ba, amma kalamansa akwai dattaku da ƙwarewa a kan aiki a cikin sa. Dan haka sosai Nana ta samu relief.

Ya rubuta musu lambarsa ya ce "Duk lokacin da za ku zo, ku kira ni, na baku ranar da nake aiki, ya zo ya din ga ganina." Nana ta din ga yi masa godiya da addu'a shi da iyayensa.

Sayyid ya ja wata takarda, ya yi rubutu ya miƙa wa likitan. Likitan ya karɓa ya duba. Ya yi murmushi ya ce "Madam, ashe kema babu lafiya ya ce na duba masa ke"

Nana ta yi murmushi ta ce "Rashin lafiyata, ai ba komai ba ce a kan tasa, ni na fi damuwa da shi É—in dai"

"A'a tun da ya nemi alfarma, ai dole a yi masa"

Ya duba Nana, ya yi wa Sayyid bayanin laulayi ne kawai yake damunta, ya rubuta mata abin da zai rubuta mata na magani. Ya kuma ba ta gwaje-gwaje. Sayyid ya ƙi tafiya, sai da suka yi gwaje-gwajen.
Suka koma, ya tabattar musu da babu wata matsala, satin cikinta uku da kwanaki, ya rubuta mata magungunan da za ta yi amfani da su.

Suna tafe a adaidaita sahu, Sayyid ya kasa riƙe murmushinsa, ya kai bakin sa kunnen Nana ya ce "Saura kwana nawa ki haihu?"
Ta kwashe da dariya, ta ce "Ina na sani, ko cika wata É—aya bai yi ba ma, mu dai ci gaba da addu'a Allah ya bar mana, ya bamu É—a na gari"

Ya amsa da "Amin."

A bakin titi, Nana ta yi sayayyar salak, saboda shi take sha'awar ci. Suka shiga layin gidan na su.
Su na zuwa gidan, Nana da sauri ta shiga banɗaki, saboda fitsarin da ya cika mata mara. Sayyid tsayawa ya yi, yai shiru yana ƙare wa ɗakin kallo.

Nana ta fito bai ce mata komai ba, ta ɗauki cylinder gas, ta ce "Sayyid gas ya kusa ƙarewa, idan zaka iya fita in anjima sai mu je titi tare mu ɗuro"

Ya ce "To"

"Bari na sake É—umama miyar"

Ta fito tsakar gidan kenan, Sajida ta ce "Nana, Allah ya taimake ki, da tuni da ke za a tafi bayar da shaida"

Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Shaidar me?"

"Jiya hirar da ku ka yi, har ki ke yi wa Barira faɗa, a kan matar nan. Daga jiyan nan zuwa yau magana har ta kai kunnen matar. Ta din ga kuka mijin ya ce ba zai yarda ba da 'yan uwanta. Da yyayyenta ne za su zo su zane Barira. Mijin matar ya hana aka kai ta police station. Tun bayan fitar ku tana can, duk sai da muka je bayar da shaida. Wataƙila dai kafin magariba a sako ta, ta dawo gida."

Nana ta numfasa ta ce "Gara da Allah ya sa ba na nan, dan babu inda zan je, shi yasa a rayuwa yake da muhimmanci mutum ya iya bakinsa. Wannan tara matan da ku ke yi, ku na surutai marasa amfani duk ba hanya ce mai ɓullewa ba"

Sajida ta ce "Wallahi haka ne, shi yasa ki ke burge mu ma"

"Allah ya kyauta"

Har Nana ta yi haÉ—in salak É—in ta, ta fara ci, ya lura ba ta fahimci abin da yake faruwa ba, shi ma kuma bai gaya mata ba, ya ci abincin. Ta gama ci ta kalle shi ta ce "Sayyid, ka yi mini addu'a, Allah ya sanya kar na yi aman salad É—in nan, na rufe sauran anjima zan sake ci"

"Kin cika yaji, sai kin yi ciwon ciki ko?"

Ta É—an waro ido ta ce "Dama ka gani?"

"Eh ina kallon ki"

Ta É—an yi murmushi ta ce "Idan babu yajin, ba zai yi daÉ—i sosai ba. Amma yanzu ya ka ke ji a jikin ka?"

"Ba sauƙi"
"Subhanallah, ba sauƙi kuma?"

Ya ce "Eh, kin je ki na hira da likita a gabana"

"Amma ko ba komai, ya kwantar mini da hankali, bai ce mini zaka mutu ba, kalamansa sun bani ƙwarin gwiwar da yakamata na samu" ta yi maganar ƙwalla na cika mata idanu.

Ya girgiza mata kai ya ce "Kar ki bari su zubo".

"To ba kai ne ba, komai na yi sai ka ji haushi na?"

Murmushin sa mai matuƙar ƙayatarwa ya yi, ya ce "Ba haushinki nake ji ba, tsaro nake ba ki, saboda tawa ce nikaɗai. sourire (smile) ki yi murmushi mana" ta noƙe kafaɗarta tana tura baki,ta juya masa baya.
Ya matsa bayan nata, ya sumbaci saman bayan ta, ya zagayo da hannunsa ta cikinta, ya kwantar da kansa a kan kafaÉ—arta. Gaba É—aya jikinta ya yi sanyi. Damuwa ce ya ziyarce zuciyarsa, jin yadda Nana ta saki jiki sosai da rungumar da ya yi mata, ko ba a gaya masa ba ya san abin da yake ranta, tuna cewar babu abin da zai iya tsinana mata, ya sanya a hankali ya raba jikinsa da nata, wani irin tausayinta na ratsa ilahirin jikinsa.

Ta maze cikin yaƙe ta ce "Sayyid, ya na ji ka yi shiru ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Babu komai"

"A'a akwai wani abu. Dama likita ya ce mu zauna na tambaye ka, ko akwai wani abu da yake damun ka, haryanzu fa jininka bai sauka ba Sayyid"

Ya É—an sake yin guntun murmushi ya ce "Damuwa ai akwai ta, ba na son É—aga miki hankali ne kawai.
Haryanzu ina tunanin inda su Habu suka tafi, suka bar ki da É—awainiya, Kodayake ko suna nan ma, kula da ni ba dolen su ba ne. Sai wahala ki ke sha, wallahi idan ina tuna hakan, sai na ji tamkar numfashina zai É—auke a cikin damuwa nake sosai da sosai. Ba na son saka ki a damuwa ne kawai".

Nana ta tattara hankalinta ta matsa kusa da shi, ta riƙo hannunsa, ta kalli idanunsa da suka yi jawur. "Idan su Habu ba hakkinsu ba ne kula da ki. Ni yanzu ya zama haƙƙina, na san ba a banza Allah ya haɗa mu ba. Mu ci gaba da addu'a Allah ya kawo mana komai da sauƙi. Amma ina fatan dan Allah ka daina damuwa, idan ciwon nan ya matsanta maka a jikina nake ji, ka daina ba na so" ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa.

KafaÉ—arta ya ciza cikin wasa, yana rungume ta. Tamkar ba a cikin damuwa suke ba, suka ci gaba da raha, duk da yadda hayaniyar mata ta cika gidan, tamkar a na taro, saboda dawowar Barira, an cika gidan ana mayar da yadda aka yi.
Ana fara kiran sallar magariba, ta kai masa ruwan É—umi banÉ—aki ya yi alwala.
"Za ka je masallaci ne?"

"A'a a nan zan yi"
Chapter 4 · 0% Book details