Sashe 12
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A'a kar ki tsallake ki bar shi, amma ki yi ɗamara fiye da ta baya, garin Buda ki ka zo za ki zauna, ban sani ba ko kin fahimci abin da nake faɗa ko ba ki fahimta ba. Idan ma ba ki fahimta ba, za ki gane daga baya. Bil adama ku na tausayi da nuna kulawa ga wanda ku ke ƙauna, ku ke iya ɗaukar jinin makusantanku ku bayar, a yi muku tsafi ko? Da kyau matsala kuma ki sani, ba ki ga komai ba" Daga haka ya ɓace ɓat. Ta buɗe idonta a hankali.
Tana buÉ—e idonta, ta ji ana kaÉ—a kacakaura, da garaya a tsakar gidan su. Ana ta hayaniya tamkar ana cin kasuwa a tsakar gidan.
Sanyi ta fara ji yana ratsa ta, bugun zuciyarta ya ƙaru, fiye da da, waiwaya ta yi tana son ganin ta inda za ta ga Ƙaisar, ko makamancin hakan amma ba ta ga kowa ba.
Wata irin guÉ—a ta ji an rangaÉ—a da wata irin murya, mai sauti, sai kuma aka ce "Yeeee barka da zuwa wakilin rafi, ku matsa ku bayar da hanya ga ango mairamu ya iso" ta ji wata murya na faÉ—a, ana ci gaba da shewa da kaÉ—e-kaÉ—en garaya.
"Ku kawo Nono da suga, a kirawo 'yar Mairo ga mijinta ya iso. Ga farin goro ƙwarya dubu biyu ta rafi ta ce a bawa mamman wakilin rafi, gaisuwar iyaye" sai kuma aka saka shewa. Ba yau Nana ta fara ire-iren wannan jiye-jiyen ba, amma ta tsorata da wannan sosai da sosai. Ta rirriƙe Sayyid, ga sanyin da take ji ya fara damunta.
Cas cas cas, ta fara jin sautin kaÉ—awar wani abu mai kama da abin ado na mata.
Ta kalli tsakar gidan ta hango wata irin zanƙaleliyar mata, mai tsawon gaske ƙafafuwanta duk sarƙoƙi, ta yi shigar Fulani, sai dai ita ma ba a iya ganin sawayenta tamkar a kan iska take tafiya. Ta ɗan ƙara buɗe idonta, ta ga rana ce tarwai a tsakar gidan, ga dandazon mutane ana ta hada-hada. Sai dai shigar mutanen irin na zamanin da ne can baya sosai, kamar dai taron wani abu ake yi.
Wata mata ta hango sanye da kayan saƙi farare tas, ƙugunta sanye da wuri, kanta babu ɗan kwali duk ta yi wa tulin gashinta adon wurin, hannunta riƙe da sandar dargaza, tana kaɗa ta tana juyi.
Wannan bafulatanar ce ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin Nana ta ce "Baƙuwarmu, bikin girka ake yi, ko za ki taso ki ga yadda muke gudanar da al'adun bikin girka?" ta yi maganar tana zuro zanƙalelen hannunta cikin ɗakin Nana".
"La'ilahaillalah, Sayyid, Sayyid wayyo Baba" ta tashi a gigice, rirriƙe ta ya yi, ya janyo wayarta, ya haska ta. Fuskar sa cike da mamaki yake kallon ta, yanayin fuskarsa ke bayyanar da alamar tambaya.
"Sayyid wata mata ce, wata mata ce take ziro hannunta, tsoro nake ji, wasu mutane ne a tsakar gidan nan" ya haska ɗakin ta ga babu komai, haka tsakar gidan ma dare nesai hasken farin wata, babu komai. Sai a lokacin ta fahimci mafarki take yi. Ya ji jikinta ya yi sanyi ƙalau, amma bai ga Ƙaisar a gurin ba, bai kuma ga wata alama da take nuna yana gurin ba.
Gaba ɗaya ta nemi ko addu'a ɗaya, ta rasa a cikin kanta. Ta kaɗa ta raya amma babu abin da ya zo da kanta. Tana so ta karɓi wayarta ta kunna karatun Alƙur'ani, amma ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta son yi, saboda tsoron da take ji.
Da ƙyar wani baccin ya ƙara sace ta.
Babu babban abin da ya ba shi mamaki, irin yadda da safe take komawa normal, babu ma alamar akwai wani abu da yake ba ta tsoro cikin daren.
Haka ta ci gaba da sabgoginta. Sai dai gaba É—aya a kunyace take, ko idonsa ba ta iya kallo, saboda abin da ta aikata ya kama ta cikin dare. Shi ga tausayin kan su, ga kuma dariya ta ba shi.
*****
Baba yana zaune yana shan koko da ƙosai a tsakar gida, sai ga kiran wayar Uwani.
Ya kalli wayar tasa ya ce "Tofa! Wannan jarababbar tsohuwar ko me za ta ce mini, take kira na da safiyar nan oho.
Ya ɗaga kiran ya saka a kunnensa. Sai dai ba ya jin ta sosai saboda rashin network. Ba ta haƙura ba ta din ga kira har sai da ransa ya fara ɓaci.
"Uwani ko a haƙura da wayar ne, kin ga babu network ne"
"A'a ina jin ka yanzu. Amm dama kiran ka na yi, na tambaye ka ina Nana kuwa?"
"Nana, tana gidan mijinta"
"Gidan mijinta wanne?"
"Mijinta dai na aure"
Uwani ta ce "Eh a ina gidan yake?"
"Amm can wajen gidan Ummi ne"
"Rufe mini baki, mutumin banza da na wofi. Ai kwana uku kenan ina neman layinka, amma bana samu saboda garin nan bamu da natiyok ake cewa ko me?"
"Uwani wai me ya faru ne?"
"Ai ba za ka san meyafaru ba, tun da ka bar yarinya tana ragaita ita kaɗai ranta ga miji mai larura,an kore su daga gidan haya, ba su san ma inda za su je ba, kana zaune hankalinka kwance. Ai ko 'yar riƙo ce Nana ka duba lamarinta"
Ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, ta wanke shi ta tas, ta ƙare masa zagi da cin mutunci, ta ce kuma za ta kira Yaya Atine ma, sai ta ci ubanta.
Ran Baba ya yi mummunan ɓaci, kenan Ummi da Nana haɗa kai suka yi, suka kai ƙararsa gurin Uwani. Ya kira Ummi ita ma ya fara sauke mata kwandon tijara. Ranta ya ɓaci ta ce "Ni fa Baba ban kai ƙarar ka gurin kowa ba, Uwani ce ta kira waya, mu na tsaka da alhinin halin da Nana ne ciki, na gaya mata komai, kuma ni na faɗa ba Nana ba. Shi ne ta ce Nana su koma Ƙauye can gurin ta".
Sai kuma Baba ya yi sak. "Ƙauye kuma? Ta yi me a ƙauye?"
"To Baba zaman nan ɗin ya ƙi, kai kuma ka ƙi taimakawa, babu yadda muka iya Nana tana Buda"
"Ke Ummi ki na ji na, duk yadda za ki yi, ki nemi kuÉ—in mota, ki je Buda ki taho mini da 'ya ta. Lallai ya sakar mini 'ya ku taho tare, ya je Allah ya ba shi lafiya"
"Baba ya sake ta, 'yan uwansa ma ba a sa inda suke ba, wa za ta bar wa shi a can?" Yana cikin bambami kuɗin wayar suka ƙare.
Dama Mama na tsaye tana jiran ya gama wayar, yana gamawa ta dube shi ta ce "Wato Nana ta kaso aurenta ta dawo ko? To wallahi ta dawo gidan nan ba ta da gurin zama, wai har ka manta irin zaman azabar da muka yi da yarinyar nan a cikin gidan nan? Babu bacci kullum bala'i da tashin hankalin iskokai, ba zai yiwu ba wallahi"
Sai dai kafin Baba ya ba ta amsa, suka ji Suwaiba ta ƙyaƙyace da wata irin dariya mara daɗin ji tana faɗin "Asma'u a ƙauyen Buda, tushiya masomar dawa, kowa ya bar gida gida ya bar shi" ta yi maganar tana ci gaba da ƙyaƙyata dariya kamar ba mace ba.
"Ke Suwaiba meye haka, wannan wace irin dariya ce? Ban hana ki irin wannan dariyar ba kamar ba mace ba?"
Suwaiba ta ce "Ina ruwan ki da dariyata"
Baba kawai ya gyaÉ—a kai, ya gyara hularsa ya fice ya bar gidan gaba É—aya.
****
Rashin maganar nan ta Sayyid, ba ƙaramin damun Nana take yi ba, abin ya yi yawa sosai.
A wannan karon ta yi sa'a, ya bar ta ta je gurin Uwani, daga nan kuma ta je ta yo musu sayayya. Ta tafi ta bar shi da wayarta, domin ta É—ebe masa kewa.
*****
Alhaji Zailani ya saka sabon layin da ya sayo a cikin waya, ya kira lambar Nana. Sayyid yana kwance yana jin yadda wayar take ta vibrating, amma ya yi banza. Saboda ko ya É—aga ba iya magana zai yi ba.
Jin mai kiran ba shi da niyyar daina kiran, ya sanya ya É—auki wayar zai kashe. Sai dai ya fasa kawai ya É—aga kiran ya kara a kunnensa.
"A tunanki dan kin yi blocking É—in lambata, zai sanya na kasa cimma burina a kan ki ne? Yanzu hankalina ya dawo gare ki, na saka an kori mijinki daga gurin aiki. Kuma zan nemo ki duk inda ki ka shiga sai na cika burika a kanki" wani irin jiri Sayyid ya ji ya fara É—ibar sa.
"Ba za ki yi magana ba?" Alhaji Zailani ya yi maganar yana kallon wayarsa. Wani irin haske ya ga wayar tana yi, tana fafar fafar za ta ɗauke. Mamaki ya kama shi, dan wayar ba ta taɓa yin haka ba. Fitilun ɗakin suka ɗauke, duhu ya gauraye ɗakin nasa. Sai ya rikice ya tashi tsaye yana waige-waige.
"Karo na biyu, ka sake shigowa hanyata, duk da gargaÉ—in da na yi maka, cewar mallakina ce, ina sake yi maka gargaÉ—i, kafin na tona maka asiri." Alhaji Zailani ya toshe kunnensa, saboda wani irin sauti da yake ji mara daÉ—i, ga É—akin yana ta jujjuya masa.
Can ya ji shiru ya daina jin sautin, ya buɗe idanunsa a hankali. Sai dai ya ga Shukura a tsaye a gabansa, jini yana bin ƙafafuwanta, ga wuƙa a hannunta, tsirara ta.
Ya miƙe cike da razani, ya fara ja da baya.
"Daddy ina jaririna? Ka bani jaririna Daddy" Ya ci gaba da ja da baya. Da gudu ta bi shi, da wuƙar tsirararta. Ya fita da gudu yana ihu.
"Alhaji lafiya kuwa? Anya hawan jinin nan bai fara taɓa maka ƙwaƙwalwa ba, ya ya zaka din ga ihu haka?" Hajiya Amina ta yi maganar cikin mamaki tana kallonsa. Ya kalli gurin ya gan shi a kan gado, a ɗakinsa. Yana son yi wa Hajiya Amina tambayoyi, amma abu ya gagara saboda tsabar razani da tashin hankalin da yake ciki.
AREWABOOKS